AlmizanAlmizan logo
Jum'a 17 ga Sha'aban, 1441 Bugu na 1440 ISSN 1595-4474

Tunatarwa

Tafarkin gwagwarmayar Imam Khumaini (KS)

Shaikh Zakzaky


Shaikh Zakzaky

’Yan’uwa musulmi assalamu alaikum warahmatullahi ta’ala wa barakatuhu.

GABATARWA

Idan ba a manta ba ranar Asabar da ta wuce mun yi taro a nan na Ranar Shuhada, wanda muka saba muna yi ranar 25 ga watan Rajab, wanda ya dace da ranar shahadar Imam Musa bin Ja’afar (AS). To, da yake kowane lokaci akan nemi karshen mako ne, Asabar ko Lahadi, sai ya zama wannan karon yau ne 25 Talata, kuma tun ranar Asabar 22 ga wata aka yi. Har nake cewa ga wadanda suka tsince mu muna tunawa da shahadar Imam Musa a wannan rana, ganin cewa ran nan 22 ne ga wata.

Sai ya zamana kuma akwai shirin tunawa da wafatin Imam Khumaini, wanda shi kuma ana yin sa da kidayar Shamsiyya ne, sai ya zamana da yake yana caccanzawa, wannan karon sai ya zama wafatin Imam Khumaini ya hadu da lokacin shahadar Imam Musa bin Ja’afar (AS). A Iran yau ne ko kuma tun jiya ne, wanda yake a kalanda 3 ga watan Yuni ne, amma da yake Mako guda ne na Imam Khumaini din, an fara shi tun ranar Asabar. Sai ya zamana yau muna iya yin magana dangane da shahadar Imam Musa da kuma wafatin Imam Khumaini.

ABIN DA YA SA AKE CE WA IMAM KHUMAINI ALMUSAWI

Wannan ya zama muna iya cewa, faduwa ta zo daidai da zama, domin shi Imam Khumaini a sunansa ana ce masa Almusawi, wanda yake nufin shi Jikan Imam Musa bin Ja’afar ne. Shi Musa bin Ja’afar shi ne Imam Kazim. In ka ji an ce wa mutum Musawi, to yana nufin shi Jikan Imam Musa ne, amma ba ta hanyar Imam Ridha ba, don shi Imam Musa yana da ’ya’yaye da yawa bayan Imam Ridha Magajinsa. Idan mutum dan Imam Ridha ne, sai a ce masa Radhawi, wato shi dan Imam Ridha ne, amma ba ta hanyar Magajinsa Imam Jawwad ba. In kuma dan Imam Jawwad ne ba ta hanyar Imam Ali Alhadi ba, sai a ce masa Jawadi. In dan Imam Ali Alhadi ne sai a ce masa….. Ka ga yanzu daidai wannan lokacin ya zama ana tuna shahadar Kakan Imam Khumaini.

To, shi Imam Khumaini wafati ya yi. Haka Allah ya so, wanda yakan zama bisa turmuza hancin makiya. Har Imam Khumaini ya gama isar da sakonsa, ya gama aikinsa, har ma shi da kansa ya yi wata shaida, ya ce, na gama nawa. A cikin wasiyyar da ya bari, wanda yana nan, in mutum yana bukata yana iya samu. Wanda ya yi nasihohi ga sauran mutane, abin da zai bar musu baya; ya bi kowane bangare na al’umma ya yi musu nasiha. ’Yan siyasa ne, sojoji ne, Malaman makaranta ne da sauransu, kowane bangare sai da aka yi masa nasiha. Shi dai ya gama nasa, ya rage saura namu kuma.

Haka Allah ya so har ya iya isar da wannan sako, ya kai kamar shekaru 93 ma a kidayar kamariyya, sannan ya rasu. Wani lokacin in mutum ya lura da al’amarin Imam Khumaini, sai ya ce, ya aka yi aka samu mutum irin wannan? Na wata kalma da Janar Hyser ya ce a littafinsa ya kira shi da ‘cantankerous’, wani irin Ingilishi ne, wato wani kankankamo, wato an yi, an yi a ji dan sassauci a tare da shi, an rasa yadda za a yi da shi, har sai da abin ya tabbata. Muna iya tambayar wannan cewa, ‘cantankerously’ ne ya sa ainihin ya ki ya mutu sai da ya kai shekaru 93? Idan kai kankamo ne ka iya kankamewa kam-kam, to kana iya kankame wa mutuwa ne, har ka ki ka mutu?

Ballantana ma wani abin al’ajabi dangane da Imam Khumaini shi ne an samu ciwon kansa a jikinsa, wanda yake lokacin da ya samu ciwon, da ainihin ta ci gaba, da nan da nan ta yi masa kwaf daya. Amma cikin ikon Allah sai ta tsaya, wanda yake ba al’adar kansa ba ne, takan ci gaba ne. Sai ta tsaya ta shekara wajen talatin ba ta motsa ba. Za ka iya cewa wannan ‘cantankerously’ ne? Kankamonci ne ya sa ya kankame kansa, ya kansare ta, ta tsaya kyam, ta ki ci gaba? Wanda yake adatan kansa kamar kaguwa ne, tana tafiya ne tana cin jiki. In ta fara ci, sai ta bi layi ta ci har ta gama. In hanta ta kama, sai ta sakwarkwata shi. In koda ne, sai ta dagargaza shi. Amma shi sai ya tsaya cik, bai ci gaba ba, kuma yana nan. Ciwon na nan, amma bai ci gaba ba. Wannan wani abu ne da za ka ga cewa yin Allah (T) ne, wanda haka Allah ya so, ya zama Imam ya yi tsawon rai bisa turmuzawar hancin makiya, wadanda sun rasa yadda za su yi.

Misali a cikin littafin Janar Hyser ya ce Janarorin Iran lokacin Sha suna tattaunawa, suna cewa wai su Amerika me suke jira ne da shi Imam? Su rufe bakin mana a huta. Su yi ‘silencing’ dinsa mana a huta. To, akwai wani kamfani mai yin wannan aikin ko a Switzerland, wadanda akan biya su kudi su yi wannan aikin. Amma dai shi a littafinsa sai ya rubuta cewa me ya sa suke son Amerika ta kashe musu Imam Khumaini? Su su yi mana. Wato ku lura kashe Imam Khumaini har tattauna shi ma an yi, Janarori na jin tsoro.

Shi kuma Imam kan taka a kafa a lokacin yana Faransa daga inda ya zauna Neauphle-le-Chateau, tafiya mai ’yar tazara, ya taka da kafa ya je inda suka yi rumfa ya zauna da dalibansa da sukan zo daga Iran su yi salla, ya dan yi jawabi a dauka a kaset; lokacin hanyar ‘communication’ dinsu ke nan. Sai a tura Iran a yi ta rabawa. Ta kai ma hanyar da yakan bi zuwa masallaci, wasu har kan itatuwa suke hawa suna kallon sa yana wucewa. Ka ga in abin a ce wani ya labe ne da bindiga ya harbe shi, sassaukan abu ne, amma kuma ta Allah ba tasu ba. Ko tunanin wannan ma ya gagare su.

MAGANA DANGANE DA SHAHADAR IMAM MUSA (AS)

To, farko zan fara magana dangane da shahadar Imam Musa (AS). Shi Imam Musa bin Ja’afar dan Imam Ja’afar Assadik ne, wanda aka san shi da yawaita ibada da yawan shiru da yawan hadiye fushi, don haka ne ma aka yi masa kinaya da Alkazim. Lafazin da za a yi masa wanda za ka tsammaci zai fusata, sai ka ga bai fusata ba. Amma duk da haka, ka san ’yan gaza-gani, sai da suka kai labari Bagadaza wajen Halifa cewa ya yi hattara, Imam Musa fa yana tashe. Su abin da yake damun su yadda mutane suke tudada su je wajen Imam Musa a birnin Madina, shi kuma yana karantar da darussa na Kakanninsa.

Sai ya zamana rahotanni na ta shiga zuwa Bagadaza cewa lallai Imam Musa fa yana tashe. To, tashen da yake yi kuma zai iya zama hadari ga mulkin Harun. Har wasu suka fara cewa wannan fa mutumin yadda yake da karfi jama’a na tare da shi, karshenta fa zai nemi Halifanci ne. Har ma suka zo wa Halifa da cewa, gaskiya ya fara maganar cewa shi ne Halifa. “Ya fara cewa shi ne Halifa ba kai ba.”

To, sannan Halifa daga Bagadaza ya aika a kama shi. Lokacin da suka je suka dauke shi, sai suka rabu biyu. Farko wadanda suka fara tafiya da shi sai suka nufi hanyar Bagadaza, a tafiyar wancan lokaci na rakuma da dawakai. Saboda haka sai aka dauka Bagadaza aka kai shi, alhali sun yi wani shiri na daban, suka hadu a wani wuri suka yi Basra da shi, wanda ba za a taba tunanin Basra za su je da shi ba, tafiya mai nisa. Aka tsare shi a Basra. Mai tsare shi a Basra yana kawo rahoto na halin da yake ciki. Aka ce Imam Musa, shi kowane lokaci salla yake yana addu’a. Addu’ar nan kuma yana neman gafara ne, yana addu’a ga al’umma. ’Yan rahoto su make su yi ta jin addu’a; ba su taba jin ko da da rana daya ya yi addu’a a kan wadanda suka kama shi ba. Shi ne suka ce wannan mutumin addu’arsa kawai yake yi ga kansa da al’umma. Bai taba ma roka wa wanda ya kama shi mummunan abu ba, sai ma cewa yake Allah ya yafe musu. Amma duk da haka abin ka da wanda ba ya son abu, aka tura wa Halifa cewa a kai shi can Bagadaza. A can din ma aka yi ta canza masa wurin tsaro. A ba wannan ya tsare shi, sai a koma da shi wajen wancan ya tsare shi.

Ya zama duk wanda aka ba shi tsaron sa aka ce masa ya kashe shi, sai ya ga shi ba zai iya kashe shi ba. Akwai wanda aka ce kullum yake shiga inda ake tsare da shi, a yanzu sai mu ce ‘prison’ din da ake tsare da shi, yakan zagaya, da yake shi ma’aikacin tsaro din ne, sai ya zagaya ya ga wadanda suke tsare. Wani lokaci sai yake tambaya cewa, “kullum na zo na zagaya, sai in ga an aje tsumma a can. Wannan tsumman mene ne?” Sai aka ce masa ai Imam Musa ne. In ya yi salla yana da wata doguwar sujada da yake yi, bai dagawa. Saboda haka yakan rufe jikinsa da abaya. To, shi in ya wuce yakan dauka kamar an tara tsumma ne. Sai aka ce ai shi ne, in rana ta fito yakan yi wata doguwar sujada, sai can rana yake dagowa. Kuma haka yake yi kullu yaumin. Al’adar Imam Musa Alkazim ke nan a kurkuku, kowane lokaci yana cikin ibadodi ne. To, amma dai shi Halifa ya nace sai dai kawai ya kawar da shi.

A wani lokaci wadansu mutane sun nemi su gan shi su yi masa wadansu tambayoyi. Suka bi ta hanyar mai tsaron gidan ‘prison’ din, suna so su ga Imam Musa. To, shi ne sai ya kai su. Suka ce sun zo da tambayoyi ne. Wadannan ba za su kasance mabiyansa ba, tunda in mabiyansa ne ba za a ba su dama ba. Sun zo da tambayoyi ne kan wadansu abubuwa na addini. Kafin su yi tambaya din, ko sun fara tambayar, sai mai tsaron ‘prison’ din ya zo ya ce “zan tafi gida, wato na gama aikina na yau, ko kana da wata bukata gobe in kawo maka?” Sai ya ce, “a’a ba ni da wata bukata.” Sai ya fita.

Sai Imam Musa yake gaya wa wadannan cewa, “yana cewa ko ina da bukata gobe ya kawo min, alhali yau zai mutu.” Sai daya daga cikin su ya ce, “mun zo mu tambaye ka dangane da hukunce-hukuncen shari’a, to ga shi kana ba mu labarin gaibu, to ya ka san cewa zai mutu yau? Saboda haka ba mu bukatar tambayar ka. Mun fasa!” Sai suka fita.

Sai ko daya ya ce, to ni ko sai na ga kwakwaf. Sai ya dinga bi har zuwa gidansa, ya ga inda ya shiga. Sai ya shiga wani masallaci kusa da gidan. Mutumin ya lura da shi, ya fito ya zo an yi sallar magariba da Isha tare da shi. To, sai ya kwanta a masallaci, shi wannan mutumin. Cikin dare sai ya ji an fasa kuka a gidan wancan mutumin. Da safe bayan sallar subahi, sai ya ga an fito da gawa an ce Maigidan nan ne ya rasu. Ya yi ta mamaki. Yadda Imam Musa ya gaya musu din nan haka nan ne, cewa yau wannan zai rasu. Kuma ran nan ya rasu.

Cikin ilmummuka wanda Allah (T) ya ba su shi ne za su iya sanin abin da ka-je-ya-dawo. Don haka ne ma aka ce, lokacin da wani almajirinsa ya nemi ya gan shi ta hanyar mai tsaronsa ya samu ganin sa din. Da ya gan shi, sai ya ga dakin da yake ciki sun haka kabari, yana zaune kusa da kabarin. Kila hanya ce ta tursasawa, kana ganin kabarinka, ana cewa kowane lokaci ana iya wurga ka ciki. A dakinsa akwai kabari. Sai shi almajirin nasa ya shiga kuka, yana ta kuka. Sai Imam Musa ya ce masa “kana kukan mene?” Sai ya ce yanzu irin wannan hali da na gan ka a ciki, ya ba zan yi kuka ba? Sai Imam Musa ya ce masa, “ba ka san mu sharri ba ya samun mu ba? Sharri ba ya samun mumini. Duk abin da ya sami mumini alheri ne.” Sannan sai ya ce masa, yaushe ne faraj? Yaushe ne mafita? Yaushe karshen wannan musiba ke nan? Sai ya ce ranar Juma’a mai zuwa, ran nan ne za a samu mafita.

Yalai kuwa sai ya fito ya bayyana wa duk mabiya Imam da suke bobboye a Bagadaza cewa ya ga Imam, kuma ya gaya masa cewa ranar Juma’a mai zuwa ran nan ne za su gan shi. Ya ce ina za mu gan ka. Ya ce a masallaci. Saboda haka sai duk suka sa fararen kaya, suka bulbula turarurruka suka je masallaci da tunanin za su ga Imam ran nan an sako shi. To, bayan da aka idar da sallah sai aka zo da gawa. Aka ce ga wannan gawar wani mutum ne ya mutu, to amma ba a san ko waye shi ba. Suka duba sai suka ga gawar Imam Musa bin Ja’afar ne. Aka ce har wani Likita Bayahude ya gan shi ya daga hannunsa ya ce, “wannan mutumin ba shi da dangi ne, wadanda za su bi hakkinsa? Ko da ganin fatarsa ga shi ta zama koriya, guba aka ba shi. Ba shi da ’yan’uwa ne da za su bi hakkinsa? Guba aka sa masa, ko da gani.”

Sannan fa mabiyansa suka yi ta fafutukar sai an ba su gawar Imam Musa. Karshe da Halifa ya ga abin zai zama rigima, ya yarda a ba su din kuma har ma ya je jana’iza. Shi wannan Halifan shi ne suke ce masa Harun, wai Rashid. Ya bi jana’iza din har yana kuka, yana cewa “da wanne zan ji? Da mutuwar dan Ammina, ko da tuhumar da mutane suke yi mini cewa, wai ni na kashe shi?”

Ya kashe shi ne ta hanyar wani mai tsaron sa da ake ce masa Sindi bin Shahik, wanda ya ba shi dabino mai guba a yayin da ya zo yin buda baki. Ya yi azumi, da ya zo yin buda baki, Sindi ya kawo dabino wanda ya zuba wa guba mai yawa. Ya san cewa guban nan ko kwara daya ya ci, to zai kashe shi. Da ya dauka ya ce bismillah, ya ci guda daya. Ya sake daukan na biyu, Sindi ya make ta taga yana kallon sa, sai ya ga ya ci na biyu. Sai ya ga ya ci na uku. Sai ya ce ka kara mana! Sai ya ce, “ai wadannan ma da na ci, bukatarka ta biya.” Da haka nan ya zama karshen al’amarinsa.

To, da yake al’amarin A’imma sun riga sun san abin da zai je ya dawo, ya san wannan lokacin tafiya ne. Kamar yadda Imam Hasan yayin da ya ga an sha ba shi guba yana ci, amma ba ya mutuwa, amma ran da aka kawo guban karshe, wanda yake daga shi sai mutuwa, sai ya ce “Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un! Lokacin haduwa da Kakana Annabi, da Mahaifina Amirilmuminin da Uwata Zahra ya yi.” Shi ma an sa masa guba ne a zuma wanda ya yi buda baki.

Ta yiwu mutum ya ce, ya aka yi sun san da guba a abinci, sai kuma su ci? Sai mu ce, kamar kai in ba ka san gaibu ba, za ka dauki wani mataki wanda yake halakarka ne, amma ran nan da za ka mutu ko a tafiya ne sai ka shiga motar ka tafi. Kamar mu akwai wani dan’uwanmu da ya rasu a aji. Kafin ya tafi sai yana cewa, “ni kamar ba na son in je ajin nan.” Sai dai ya tafi, kuma ya rasu. Misali da ya san gaibu, ya san in ya je zai mutu, kila ya ce ba zai je ba. Amma shi wanda ya san lamuhalata akwai karshe, kuma karshen nan mutuwa ake yi, kuma akwai yadda aka kaddara mutuwa, zai kautar da kaddarar ne? Haka nan zai je, amma ya sani. Bai gagare shi sani ba.

BA LAIFI NE SHAHIDI YAKE WA MUTANE BA

Abin da na maimaita ranar Asabar da ta wuce, kuma na sha fadi shi ne, shahada na nuna ke nan, ba laifi ne Shahidi yake wa mutane ba, domin shi Imam Musa ba laifin da ya yi wa Halifa. Bai yi masa laifin komai ba. Hatta addu’a bai yi a kansa ba. Na’am an ce a cikin tsare shin da aka yi akwai lokacin da abin ya tsananta masa har ya yi addu’a ya ce, “ya Allah ka fitar da ni daga tsaron Harun.” Sai kuwa Harun din ya ji cewa a sake shi. Sai aka sake shi, amma na ’yan kwanaki, ya sake komawa cikin tsarewa. Hatta addu’a a kan Harun ba a ji yana yi ba, kawai yana addu’a, yana ibadodinsa ne.

Kuma cikin abin da Imam Musa yake cewa, yana cewa ya gode wa Allah da ya ba shi dama ya samu ya bauta masa. Akwai irin wannan a nemi wuri a takura ka, sai a ba ka dama. Kamar irin doguwar sujada din nan da za a yi tun bayan dagawar rana har rana ta take, to yaushe mutumin da ke harkokin yau da kullum zai iya yin wannan doguwar sujada? Imma dai akwai dalibai na jira, akwai ba da karatu, ko kuma akwai wasu hidimomi. Amma sai ya zama al’adarsa tsawon zamani yana wannan. Wato Allah Ta’ala ya ba shi dama, sai ya yi amfani da wannan damar ya yi abin da ba zai iya yi in ba yana tsare ba, har yana godiya ga Allah Ta’ala.

Yalai kuwa wanda duk ya yi kurkuku, aka tsare shi, in ya fito zai ga lalle ya rasa dama. Saboda in an tsare ka, kakan samu dama wanda za ka yi abubuwan da in kana waje ba za ka iya yi ba. In kana da hankali daidai wannan lokacin, in an tsare ka, sai ka yi amfani da wannan lokacin ka yi abin da in kana waje ne ba za ka iya yi ba. Kamar Annabi Yunus, wanda kifi ya hadiye shi, yana jin kansa a tumbin kifi, sai ya fara sallah. Har ma yakan rika tinkaho da cewa, “Ya Rabbi na bauta maka a inda ba wanda ya shiga ya bauta maka.” Wa ya shiga tumbin kifi ya bauta wa Allah? Wato shi ya samu tumbin kifi ya maishe shi masallaci. Na’am da zafi kam, ka san tumbi da zafi, ga duhu; amma dai yana ganin shi ya shiga, kawai sai ya fara ibada. Shi ya sa yake cewa, “Ya Rabbi na bauta maka a inda ba wanda ya shiga ya bauta maka in banda ni.” Allah (T) yake cewa, “Da ba don ya kasance cikin masu tasbihi ba, (wato da ba don a lokacin yana bautar Allah a cikin cikin kifin nan ba), da ya zauna a cikin cikin kifin har ranar da za a yi tashin kiyama.” Shi ke nan da wurin zamansa ke nan. Amma da ya shiga ya yi tasbihi, sanadiyyar wannan sai aka fitar da shi.

Ina kokarin in nuna shi Shahidi ba laifi yake yi ba, illa tsayawarsa kyam a kan tafarki. A kan haka ne aka kashe Annabawa. A kan haka ne aka kashe bayin Allah nagargaru. In ka duba su za ka ga ba su yi laifin komai ba. Laifinsu shi ne sun tsaya kyam a kan tafarkin Allah. Shi ne babban laifi a wajen azzalumai. Kullum abin da ba su so shi ne, don me za a samu wani shi Allah zai bi, ba su zai bi ba? Su suna son ya bi su ne.

An ce Harun din nan, wanda ya kashe Imam Musa, ya taba tattara iyalan gidan Annabi daban-daban, babba da yaro, har tsofaffi da yara, duk ya tattara ya zuba su a wani daki ya kulle. Aka ce ya ce wa wani dogarinsa, “da wane mikdari ne kake yi min biyayya?” Yana so ne ya gwada mikdarin biyayyar wannan dogarin gare shi. Ya ce, “iyayena su zama fansa gare ka.” Harun ya ce, “bai ishe ni ba.” Wato na ba da Uwata da Ubana su zama fansa a gare ka. Wato zan iya ‘sacrificing’ iyayena domin kai ka rayu. Ya ce, “wannan bai ishe ni ba.” Ya ce, “duk abin da na mallaka, fansa gare ka.” Ya ce, “zan iya ba da komai nawa in zauna zikau fansa gare ka.” Ya ce, “bai ishe ni ba.” Ya ce, “zan ba da raina domin ka.” Ya ce, “bai ishe ni ba.” Sai ya yi shiru, to me ya rage kuma? Ya ce Uwarsa da Ubansa, ya ce bai ishe shi ba. Ya ce, duk abin da ya mallaka, ya ce bai ishe shi ba. Ya ce ransa, ya ce bai isa ba. Sai ya ce, “sai ka sayar min da lahirarka. Sai ka ce lahirarka ka ba ni.” Ma’ana yanzu zan iya sa ka kowane aiki, in ya so ka je ka shiga wuta; to wannan zan yarda.

To, dogari ya yi shiru. Can ya ce, “lahirata na kadar maka.” Ya ce, “ka ban?” Ya ce, “to shiga wannan dakin. Duk wanda ka gani ka sare masa wuya. Aka ba shi takobi, ya kuwa shiga, duk ga su a daddaure. Ya duba ya ga duk iyalan Annabi ne. Ya ce, to shi fa ya riga ya sayar da lahira. Ya ko fara saran wuya. Har wani dattijo yake cewa, “yaro me za ka je ka gaya wa Annabi? Ba ka ga mune iyalan Annabi ba? Me za ka gaya wa Annabi gobe kiyama in ka gan shi?” Sai ya ce, “to na riga na sayar da lahirata.” Ya yi ta fillan wuya har ya gama. Ya fito ya ce, yaya? Ka bar wani da rai? Ya ce, a’a. Ya ce, “to yanzu na aminta maka. Yanzu na san da gaske kake, ka ba ni lahirarka.” To, Allah ya sawwake, wannan irin gayan bata!

Ina ganin wannan shi ne irin abin da azzalumai suke nema – ka ba su lahirarka. Ma’ana su su sa ka yi wani abin da za ka aikata, gobe ka shiga wuta. To, wannan in ka aminta, shi ke nan. Don su sun san ina za su je. Yanzu wanda za shi Aljanna zai yarda ya bi su? Ai ba zai yiwu ba. Shi ya sa ba za su amince masa ba. Zai yiwu mu ci duniyar tare, gobe lahira ka je Aljanna, ni in je wuta? Ai ba zai yiwu ba. Ai sai dai mu yi aiki iri daya, mu tafi duk inda za mu je tare. Wanda ko duk bai dauki wannan tafarkin ba, ka san cewa lallai ba za a amince masa ba.

BA A YI WA SHAIDAN WA’AZI

Kamar Shaidan ne wanda Allah (T) ya ba mu labarin cewa, “Shi fa Shaidan abokin gabanku ne. ku dauke shi abokin gabanku. Yana kiran rundunarsa ne don su zama ’yan wuta, (tunda shi ya san can za shi). Yana neman wadanda za su raka shi ne. Saboda haka ku dauke shi a matsayin makiyi kawai.” In abin ka ga Iblis ne, to nemi tsari ka yi ta kanka. Kar ka ce za ka yi masa wa’azi!

Zan ba ku wani labari. An ce Isa Almasihu (AS), wata rana yana halwa a dokar daji shi kadai, sai ya ji barci, sai ya dauko wani dan dutse dan karami, ya kwanta ya ta da kai a matsayin kamar matashi ke nan. Yana cikin barci, farkawar nan da zai yi, sai ya ga Iblis a tsaye a gabansa. Ya ce, “makiyin Allah me ya kawo ka nan?” Sai Iblis ya bata rai, ya ce, “an dauki kayana kuma ana zagi na.” Ya ce, “wane kayan naka?” Ya ce, “wannan dutsen da ka yi matashin kai da shi. Kai mutumin duniya ne ko na lahira? Meye naka na yin matashi da dutse?” Sai Annabi Isa ya tunkude wannan dutsen, ya ce, to ga kayan tsiyanka nan! Wato ba ma ko matashin dutse din.

Har wala yau dangane da Isa (AS) din, aka ce ya yi azumi na wadansu kwanaki ya yi ta addu’a. Ya ce ya san yadda Shaidan yake ta batar da mutane, yana neman hanyar da zai bi ya sasanta tsakanin sa da Allah domin ya daina batar da mutane. Ya yi ta addu’a yana cewa, “Ya Rabbi wannan Shaidan din, kai ka halicce shi, yanzu yadda yake ta batar da mutane, ba zai yiwu ba ne ya tuba a huta?” Sai Allah ya ce, “to in ya ce na yarda na yi laifi, a yafe min, zan yafe masa.” Sai Isa ya ji dadi. Shi ke nan abin da zai ce? Allah ya ce masa eh. Ya ce, to ai ko akwai sauki.

Sannan sai ya kira Shaidan, ya ce, “to na san ba ka da dauriyar sara tara da Mala’ika Mika’ilu zai yi maka ranar kiyama. Kowace sara za ka ji zafin gidan wuta bakwai.” Sara tara, kowace sara za ka ji zafin Jahannama bakwai. Ba ka da dauriyar wannan. Ya ce, “to ka fadi wadannan kalmomi, duk a yafe maka, komai ya wuce.” Ya ce, to meye wadannan kalmomin? Ya ce, “ka ce na yi laifi, ya Allah ka yafe min.” Sai ya ce, “eh zan fada amma da sharadi.” Meye sharadin? Ya ce, “in ce shi ma Allah zai fada min haka?” Ya ce, “Allah din ne zai ce maka ya yi maka laifi ka yafe masa?” Ya ce, “tafi ka ba ni wuri tsinanne!” Shi ne Allah ya ce wa Isa (AS), “to ya ka gani?” Saboda haka in abin ka ga Shaidan ne, ka yi ta kanka kawai. Ba batun wa’azi.

SHAIDAN YANA DA RUNDUNA DA MA’AIKATANSA

Shaidan yana da runduna, yana da ma’aikatansa. To wadanda suka sallama lahirarsu, su duniyar kawai suka sa a gaba. To, su wadannan in ba irin tafarkinsu ka bi ba, to ba fa za ku shirya ba. To, wannan shi ne shigen irin laifin da Imam Musa (AS) ya yi. Imam Musa (AS) ibadarsa kawai yake yi. Ba a taba jin wani ya yi masa wani abu ya rike shi da shi ba. Shi ya sa ake masa lakabi da Alkazim. Daga ‘Kazimul gaiz’, mai hadiye fushi, ba a taba fusata shi ya fusata ba. Komai aka yi masa sai ya yi dariya. In ka gaya masa magana zazzafa ne, sai ya yi murmushi kawai. Ba za ka taba cewa Imam Musa ya yi wa wani wani abu ba, wanda mutum zai ce ya ji haushin sa. Ibadarsa kawai yake yi, mai doguwar sujada, mai yawan salla. Ba shi da komai sai ibada, amma kuma ka ga bai tsira ba a hannunsu, duk da haka nan.

Wala’alla kila laifin shi ne, da ya kaurace wa al’umma ya koma dokar daji ba wanda ke ganin sa, kila in ba su san da shi ba; amma ko a can din ne ne, aka san da shi, za a zo a ce “Ranka ya dade akwai wani mutum can a kogon dutse, sallah kawai yake yi, abin tsoro ne, in ya fito za a yi rigima.” A ce a je can a gama da shi. Ko a ce a je a toshe kogon, kar ya fito, don ba a san irin tashin hankalin da zai kawo wa kasa ba. Amma in dai za a ji labarinsa, za a bi shi a yi masa wannan ko da ya buya ne, to ballantana kuma ya zama yana cikin al’umma, kuma al’umma suna ganin sa da girma. Suna girmama shi, suna hankoron su gan shi. Mutum yana hankoron ya ga Imam Musa (AS) ne ko daga nesa ne.

Shigen abin da nake fada ranar Asabar da ta wuce, nake cewa su wadannan mutanen da suke cewa suna da farin jini, sun ci zabe, to mutum ya zo ya shiga lunguna mana ya sadu da wadanda suka zabe shi, tunda yana da wannan farin jinin. Tsoron mutane yake ji, saboda ya san cewa hakkinsu yake ci. Tsoronsu yake ji, in ba haka ba, ya shiga cikin su mana. Amma idan wani bawan Allah ne wanda bai ci hakkin kowa ba, za ka ga zai shiga cikin mutane, wasu suna hankoron su gan shi ne ma. Kamar yadda ya kasance ga Annabawa da bayin Allah na gargaru, jama’a na hankoron su hango su ne ma kawai da ido. Kuma da za su shiga cikin mutane ba su fuskantar wani hadari.

Wannan ya nuna maka laifin Shahidi shi ne ya tsaya kyam a tafarkin Allah. Ba abin da za ka yi ka kaucewa shahadar, sai dai ka bar tafarkin Allah din. In ka bari, shi ke nan. In ka je ka ce ka yi musu saranda, za su ce, to yawwa ya yi daidai. Da kana cikin ‘hit list’, to amma yanzu za a cire ka a ‘hit list’. To, amma kana tsammanin sai mene kuma? Mene ne ‘limit’ din abin da za su bukata wajenka? Ku gaya min! Ka sayar da lahirarka. In ce ko za ka ba su lahirarka? Yanzu za ka yi musu biyayya a ‘terms’ dinsu, ba a naka ‘terms’ din ba. To, wannan kuwa. To, wannan magana ce a gurguje kan shahadar Imam Musa.

To, wannan munasabar Imam Khumaini ne. shi kuma Imam Khumaini sai ya zama Jikan wannan Imam Musa ne. Imam Musa akwai abin da na so na fada, cikin lakubbansa ana masa lakabi da Babul hawa’ij, kofar biyar bukatu. Wato mutane da dama sun sha tawassuli da Imam Musa su samu ijaba. Wannan ko’ina kake, za ka yi tawassuli da Imam Musa, ka ce Ya Allah albarkacin bawanka Imam Musa biya min wannan bukata. Yanzun nan ka ga biyan bukata. Shi ya sa ake ce masa kofar biyan bukata, Babul hawa’ij, daga cikin sunannakinsa. Saboda shi ya sallama wa Allah gayan sallamawa. Kuma Allah (T) ya karbe shi gayan karbuwa, saboda haka ya zama nasa, har ma mutane suna gama Allah da shi su sami biyan bukata. Da da lokaci sosai, sai mu yi magana sosai dangane da Imam Kazim (AS), amma wannan mikdarin ya wadatar.

DA’AWAR IMAM KHUMAINI TA NUNA IKO NA HANNUN MUTANE NE

Shekaranjiya na yi lacca a nan dangane da ‘Islamic Awakening’, farkawar Musulunci a matsayin ‘remote consequence’ na da’awar Imam, ba ‘directly’ ba, amma ‘remotely.’ Maganar da na yi tana da tsawo a shekaranjiya. Mai bukata yana iya saurara. A intanet ma an sa. In mutum a duba www.harkarmusulunci.org zai ga ‘icon’ da ya nuna cikakken bayanin, kuma zai iya ‘downloading.’

A takaice a cikin wannan maganar na nuna cewa wannan farkawar da muke gani, sakamakon da’awar Imam Khumaini ne. Domin da’awar Imam Khumaini nan da nan ta nuna wa mutane wani abu guda, cewa iko na hannun mutane ne, ba yana hannun mahukunta ba ne. Don haka ne ma bayan ‘revolution’ din Iran na 1979, nan da nan sai aka samu wadansu kasashe, al’umma suka daga. Na farko aka samu na Nicaragua, suka kawar da Samoza, ya gudu. Sai kuma Haiti, inda suka kori Dubalia. Sai kuma Phillipinnes, inda suka kori Marcos. Duk sakamako ‘revolution’ din Iran ne. Ya zama mutane suka dago, kuma bindiga ta kasa iyar musu.

Lokacin da Marcos ya fadi, lokacin ina London, ina kallon talabijin, kuma da alama, kamar yadda duk shugabannin nan suke, sun makala wa Marcos kyamara a fadarsa, kuma ana nuna abin da ke faruwa a fadarsa. Sosai suka nuna Marcos yana gaya wa Janar dinsa, “na ba ka umurni ka je ka tarwatsa wannan ‘crowd’ din.” Shi kuma yana ce masa “Sir!” Da dukkan girmamawa, “hakan ba zai yiwu ba, saboda duk mutane ne suka fito.” A lokacin aka nuna mutane fululu, duk sun fito kan titi, maza da mata. Dole Marcos ya gudu. To wannan ‘power’ din mutane shi ne kowane azzalumi yake tsoro.

Bari in ba ku kissar wani Malami da na ji Sayyid Muhammad Ridah ke fadi. Ya ce, wata rana wani Malami yana tashe a Isfahan, sai Sarkin Isfahan ya aika wa Gwamnan Isfahan cewa ga wani Malami yana tashe a garin nan. Ya ce, to wace shawara kake bayarwa? Ya ce shawarata ita ce a raba shi da Isfahan ne, inda yake da mutane. A koma da shi Tehran, inda ba shi da mabiya, sai ‘influence’dinsa ya rushe. To, sai aka aika a dauko wannan Malamin daga Isfahan a dawo da shi birnin Tehran, inda zai zama ba shi da mabiya.

To a Tehran akwai Malamai. Wani Malami da ya ji labari, cikin dare ya je ya buga wa wani Malami, ya kwankwasa masa kofa. Ya ce, bako cikin wannan dare, wane ne? Aka ce ai Ayatullah wane ne. Ya yi ta mamaki. Ya ce, “me ya taso da kai da wannan dare haka?” Ya ce, “ka ji, ka ji, wani Ayatullah ne daga Isfahan za a koro shi ya dawo Tehran. To, in muka kyale Sarki ya yi wannan, farko ke nan, to duk Malamai ba su tsira ba.” Ya ce, “to meye abin yi?” Ya ce, “to ni ina ganin da ni da kai mu gaya wa duk mutanenmu cewa, duk a fita a tarbe shi.”

Yalai kuwa da shi Malamin ya iso Tehran, duk jama’a sai aka fada cewa Ayatullah Wane da Ayatullah Wane sun ce a je a tarbo Ayatullah Wane. Duk jama’a suka rufe kantuna, duk kasuwa aka rufe, tituna suka cika makil. Sai Waziri ya zo ya ce wa Sarki, abin gudu fa ya auku. Ya ce, meye? Ya ce, duk jama’an Tehran sun je taryan wannan Malamin. Sarki ya leka ta bene, ya ga jama’a fululu. Sarki ya ce, “mene abin yi?” Waziri ya ce, “ban sani ba.” Ya ce, “to ni na san abin yi.”

Ya ce, “a kawo abin hawa ni ma in je in tarbe shi.” Shi ma sai ya je tarya. Da yake Sarki ne, sai ya ce “muna murna da zuwanka Tehran, wata hidima ce ta kawo ka?” Sai Malam ya ce, “ai kai ka ce a dawo da ni nan.” Ya ce, “wa ya gaya maka?” Ya ce, “Gwamnanka na Isfahan.” Ya ce, “a’a, kila dai Gwamnan bai fahimce ni ba ne. Ya zan ce ka dawo nan? Amma dai tunda Allah ya kawo ka yanzu, to ka zo fadata ma ka zauna, in ka gama hidimarka ka koma Isfahan dinka.” Sai ya ce, “a’a, dama akwai inda zan sauka.” To, bayan kwana biyu sai ya koma Isfahan din, magana ta kare. Shi Sarkin da yake yana da wayo, ya ce “yadda mutanen nan suka fito, in suka nufo fadata, to karshena ke nan.” Saboda haka sai ya yi wayo, wai shi ma ya zo tarya. To, Imam Khumaini ya nuna wa mutane wannan ‘power’ na mutane.

Shi Imam da ya zo ya samu mutane da al’ada ta makaranta, akan yi ta karatu ne, a yi ta karatu, amma mutanen da ake cudanye da su ba su san halin da masu karatun ke ciki ba, ko na kusa da su. Kamar yadda Jawad Mugniya, wanda ya rubuta littafin Fikihun Imam Ja’afarus Sadik, mai mujalladi bakwai, a cikin mukaddamar littafin yake cewa, lalle mu Shi’a mun yi sake, ba mu cimma mutane. Mun zauna mun kebe kanmu kawai, muna ta karatu. Yake cewa sanadiyyar da ya yi tunanin rubuta littafin shi ne, sun tafi wani kauye ba shi da nisa daga birnin Najaf, kamar ko kilomita 25 ne, mutanen nan suka karbe su hannu bibbiyu. Su mutanen suka ga mutanen kirki sun zo an zauna lafiya, sai suka fahimci su Shi’a ne. Suka ce ku Shi’a ne? Suka ce eh. Suka ce, amma da ban mamaki, ga shi kuma mun ga ku mutanen kirki ne. Sai ya ce, to su mutane ba su dauka Shi’a mutumin kirki ba ne, ga shi ba su da nisa daga birnin Najaf. Sai ya ga ana ta zuba karatu ne, amma ba a hadu da mutane ba. Sai yake cewa lallai laifinmu ne, ya kamata mu hadu da mutane.

A lokacin su masu karatu sukan zauna ne su yi ta karatun, su yi ta ibadarsu, ba ruwansu. Al’umma tana zaune shiru, Sarki na ta gudanar da al’amura yadda ya ga dama. Sarki ya sayar wa Amerika da kasa. Man Iran, man Amerika ne. Kuma har ma’aikatan man ma suna da ‘immunity’. Aka ce ko kisan kai suka yi, dan sandan Iran ba zai kama su ba. Kuma ba za a yi ‘trial’ dinsa a kotun Iran ba. Kamar dai yadda yanzu suke yi, kwanakin baya wani ya kashe mutum 16 a Afghanistan, wai yanzu za su yi ‘trial’ din sa. Amma za su yanke masa hukuncin kisa ne, daga baya su yafe masa. Yanzu ma za ka je ka same shi yana harkokinsa kawai, saboda Afghanistan ba su isa su hukunta shi ba, illa iyaka a ce ya koma Amerika ya daina aiki, amma ba wai za a yi masa hukunci ba. Saboda su ba mutane ya kashe ba, ’yan Afghanistan ya kashe. Da ya kashe Ba’amurke ne, shi ne za a yi masa hukunci. Ya kashe mutum ke nan.

Amerikawa a lokacin da suke Iran suna birbishin dokar Iran ne. Dansanda bai isa ya kama su ba. Ko wucewa ya yi, ya yi ganganci ya banke mutum ya mutu, dansanda ba ruwansa. Shi kuma can sai dai a gargade shi, ka daina gudu a cikin mutane. Shi ke nan. Tunda ‘after all’ dan Iran ne. Malamai kuma ana ta zuba karatu. A yi ta karatu, a yi ta karatu, a yi ta karatu. Kai karatun ne ma su kawai! Ka ga mutum ya karantu har ya zama karatu. Shi kuma ba ruwansa da abin da ke gudana a cikin al’umma.

To, sai Imam ya fita daban. Shi sai yana magana dangane da abin da ke faruwa cewa, kasa, kasarsu ce, dukiyar kasar, dukiyarsu ce. Shi Sha ya dauki dukiyar kasarsu ya mika wa mutanen waje, kuma ya sai da mutuncinsu ga mutanen waje. To, sai su mutanen makaranta suka fara ganin cewa wannan wane irin abu ne, me ya shafi mai addini da maganar siyasa? Me ya hada ka da siyasa? Kai naka kawai ka ce a yi sallah, a yi addu’a. Ina ruwanka da abin da Sarki yake yi? Ka shiga siyasa ne? Shi kuma ya ci gaba da wannan. Har ya zama ma’abota makaranta suka gane abin da yake yi ba daidai ba ne. Don an ce wani babban Marja’i a lokacin ya dan gargadi Imam cewa, lallai ya sassauta, don su abin da suka saba kawai karatu, kar a ja musu.

Yalai kuwa, sai Sha ya kai hari makaranta din. Aka shiga kai hari. Aka yi, aka yi da Imam ya yi shiru, ya ki. Sai aka ce su kai hari makaranta. Da dalibai lafiya lau, sukan yi ta karatunsu ne kawai. Suna fama da muguwar talauci da wahala, amma suna karatu, to yanzu kuma ga shi ’yansanda suna zuwa, a dirar wa mutane a kakkama su, a yi ta tursasawa. Sun rika hawa da dalibai kan hasumiyar masallaci, wanda ake kiran salla din nan, sai sun je can sama din, sai su tunkudo mutum ya fado. Kuma da yawa idan mutum ya fado, wasu su karairaye, wasu su mutu. Kuma suka ga dai sun ci gaba. Suka kara daukar wasu matakan.

Sukan dibi wasu a helikofta, aka je aka wurga su a tafki, wanda ake ce wa ‘Salt lake’. Akwai ‘Salt lake’ tsakanin Tehran zuwa Kum. Akwai wani ‘lake’, wasu suna ce masa ‘Salt lake’, amma in mutum ya duba ‘map’ zai ga ba shi ba ne, kodayake shi ma ya yi kama da ‘salt lake’ din, amma ‘salt lake’ din ya fi shi muni. Ma’anar ‘salt lake’ shi ne Tafkin gishiri. Gefensa tabo ne. In mutum ya shiga tabon nan ya nutse, shi ke nan. Ko dabba ba ta zuwa, don tabo ne mai kasa mara karfi. In mutum ya taka zai nutse ne. Saboda haka in aka wurga mutum a nan ba dama ya fito kawai, nutsewa zai yi saboda tabo. Amma sai su hau helikofta su wurgo mutum. Shi ke nan kuma. Ba yadda za a yi mutum ya fito saboda tabo. Ba tsandaurin kasa ba ne, nutsewa ne mutum zai yi.

To, duk sun yi wadannan. Har ta kama al’amarin dada karfi yake yi. Aka yi tunanin a kori shi Imam Khumaini ne. An ma so a kashe shi. Sun so su kashe shi, Sha ya ce a yanke masa hukuncin kisa, sai sauran Malamai suka ce lallai wannan zai zama cin zarafi ga Marji’iyya. A bisa dokarsu ba zai yiwu a kashe Ayatullah ba. Sai ya kore shi daga kasar. Da aka kore shi, shi ne ya koma Irak. Ya koma birnin Najaf. Shi ma birnin karatu irin shigen na Kum ne. Bilhasali ma Najaf ta fi Kum, don nan ne kabarin Amirul muminina yake, don nan ne babbar cibiyar karatu. Kum karamar cibiya ce in aka kwatanta da Najaf.

Nan ma Malamai, duk da dai wasu sun je sun gaggaishe shi, amma su ma irin wadanda suke karatun ne dai kawai. Wasu kuma ba su so zuwansa nan ba, don kada ya zo nan ma ya fara magana, ya kawo musu abin da su ba su saba ba, neman karatu kawai ake yi. Ba a san ana magana dangane da siyasa ba. Wato ya zama kamar wani laifi. Kamar yadda na karanta a wata Magana ta Imam Khumaini, yake cewa ‘Akhum siyasi,’ wato Malami mai siyasa. Wato kamar wani laifi ne idan Malami yana magana dangane da abin da ke faruwa a duniya. Sai su ce masa Malami mai siyasa. Ba za mu ce masa Malamin siyasa ba, Malam mai siyasa ke nan. Wato shi Malami kawai, ‘spritual’ kawai, ba ruwansa.

Shi ko ‘Politics’ bangaren rayuwarmu ne, ko ba haka ba ne? Ba suna yin dokoki su shafe mu ba? Ba suna daukar matakai su shafi rayuwarmu, su tattakura mu? Yanzu abubuwan da suke yi daban-daban din nan, in wani ya sace kudi, zai yi sanadiyyar mutane masu yawan gaske su mutu. Yanzu saboda yawan satar kun ga yadda ake ta mutuwa. Ba magunguna a asibiti. A kan N3000 ma ko kasa da haka ma, sai mutum ya mutu. Ko ka ga wani ‘operation’ dan karami, wanda yake za a iya yi, amma sai su ce wai ba su da kayan aiki. In ka je asibiti, sai a ce ba za a iya yin ‘operation’ din ba saboda ba su da ‘instruments’ din sai dai ka je Ghana. Yanzu an fara zuwa Nijar ma. Akwai wani ‘test’ za a yi masa, aka ce masa a Kano kawai ake da ‘machine’ din. Ya je aka ce layi za a bi, sai ya jira nan da wata uku. Sai ya je Maradi aka yi masa, ya kawo nan take kawai. A Maradi akwai. Ka gani yanzu an fara zuwa Nijar. Yanzu za ka ga ‘operation’ dan kankani, Likita zai ce ma zai iya, amma ba kayan aiki a Asibitin. Kasar nan babu? Sai a ce duk ko’ina babu, sai dai ka je Ghana, ko in abin ya yi kamari ka je Nijar. Yanzun nan sai ka samu biyan bukata. To, wannan sanadiyyar sace kudin al’umma ne da suke yi.

A kan dan abu kankani, shi ke nan. Ga sace kudi, ga kajagogi, ya kamata a ce muna kera motoci ne, amma kajagogi muke shiga. Sai an yi amfani da mota an yar da ita, sannan sai a tattaro a kawo nan. Taya ma har akan wurgar don su suna da ka’idar in taya ta shekara uku dole ka canza, saboda haka guda biyar din za ka canza har da ‘spare.’ In ka canza sai ka ba da biyar din, ka ba da kudi a kona. To, dan Nijeriya sai a ba shi kudin konawa, sai ya tattara ya kawo Nijeriya ya sayar a matsayin sababbi. Har sai a taya ka murna, ashe ka sai taya. Kwana biyu a yi hadari ya kashe mutane, ga ramuka a hanya da sauransu. Mace-macen da ake yi a kan satar kudi ba kadan ba ne, amma kar ka yi magana, kai ka yi magana kan ‘spirit’ kawai, ka ce a kiyayi Shaidan kawai, alhali ga Shaidanu, ka yi shiru. Ga Shaidanun mutane da suke wa Shaidan Aljani aiki.

Ba mu ce kar a yi karatu ba; a yi karatu. Amma kuma ba zai yiwu mutum ya zama a ce ba ruwansa da abin da ke gudana a al’umma ba. To, shi Imam dai ya fita daban. Maganarsa kan abin da ke faruwa a al’umma da yadda Sha ya sayar da kasa, ya tsaya kyam a kan wannan. Don haka ma a Najaf din ya ga mutane sukan je Najaf su ziyarci Imam, kuma su dawo da bayani ga al’umma lafiya lau, sai ya ce a kore shi ma daga Najaf din. Shi ne aka kore shi ya je Turkiyya.

Turkiyya kuma a lokacin suna da ka’ida, kuma suna neman su zama Turawa, saboda haka ana yin ‘national dress.’ Tun lokacin da Ataturk ya fito da ‘national dress’ ana sa malfa ne. Bature yana sa malfa ne, saboda haka ya yi doka kowa ya rika sa malfa don ya zama Bature. Kuma kowa ya canza sunansa ya zama irin na Turawa. Ya zama sunansa biyu, da ‘surname’. Shi ma sai ya yi wa kansa ‘surname’ din. Da sunansa Mustafa Kamal. Sai ya canza wa kansa sunan zuwa Kamal Ataturk. Ataturk, ma’anarsa baban Turkawa. Ata, baba ke nan. A nan Nijeriya ma akwai wasu kabilu da Ata ke nufin baba. Ataturk Uban Turkawa.

To, shi ke nan wasu sai ka ga suna sa suna Oglu, Ozal, Turgut, wai sunaye ne, wai ka zama Bature ke nan. Kamar yadda Turawa kan sa Fisher, Thatcher ko Smith ko Bush. Ya zama ‘surname’ kowane ‘family’ na da shi. Shi ne ya ba kansa, ya zama Kamal Ataturk. Ya zama kowa dole ya yi suna irin wannan. Sannan kuma dole ya sa malfa. To, Turawa sai suka yar da malfa. Lokacin da Bature ya zo nan, yana da wata irin malfa mai tulluwa. Daga baya ya daina mai tulluwa, yana mai shimfidadden kai. Ya dawo kuma ya wugar da malfar ya ce kai ba hula. A Turkiyya kuma, sai aka ce yanzu kai ba hula.

Lokacin da Imam ya je, doka ta hana sa hula, dole ya cire rawani, ya yi ‘national dress’ kuma. Sai ya sa doguwar ‘over all’ kansa ba hula, ya zauna a Turkiyya. Daga nan ma Turkiyyan Sha ya fara cewa a kore shi, ya dawo Irak. Da abu ya yi tsanani aka kore shi gaba daya daga Irak, ya nemi ya je Kuwait ta mota. Har ma sun je Boda, Kuwait ta hana shi shigowa. Aka rasa yadda za a yi. An kore shi ba a san ina za shi ba. Sai ya zama akwai jirgin sama zuwa Faransa, sai kawai ya hau jirgin France air, sai Paris.

ZAMAN IMAM A PARIS

Faransa suka karbe shi, amma da sharadi; ba zai sa baki a siyasa ba, kuma ba zai yi hira da ’yan jarida ba. Amma mutanen Iran da tasu dabarar, sai suka yi ta tudada ‘embassy’ din Faransa a Tehran, suna nuna godiya, suka yi ta yin muzaharori na nuna godiya ga Faransa da ta karbi bakuncin Ayatullah Khumaini a kasarta. Kuma cikin abin da suka yi, suka yi mata dadin baki, suka ce sun san Faransa kasa ce mai ’yanci, saboda haka suna ganin ba za su takura wa Imam ba. Shi kuma Charles Deguille sai ya ji dadi an kambama shi, sai ya ce yana iya ma hira da ’yan jarida. Sai ya zama yanzu Imam yana iya hira da ’yan jarida. Sai ya zama yana maganarsa ana turawa Tehran.

Maganar da yakan yi, yakan tafi masallaci ne a yi sallar azahar da la’asar da ’yan Iran da suke can. Galibinsu dalibai ne ma, yara samari, wadanda suke karatu a can. Sai su je, in an yi salla, sai ya yi magana da su, sai a dauka da dan karamin kaset rikoda. Sai a zo gida, lokacin kayan ‘communication’ din ke nan, sai a buga waya, irin na ‘dial’ din nan. A ce Tehran ne, to saurara, yau ga abin da Imam ya ce. Sai a matsa kaset din. Shi kuma can sai ya danna kaset ya dauka. Sannan sai a yada kasetocin. Ya zama lokacin ana ta farautar kaset. In aka gan ka da kaset din Imam Khumaini, kai ka mutu.

Sai ya zamana ainihin an yi dabarbari iri-iri na boye kaset. Akwai wani saurayi da yake cewa, a lokacin, da yake sun fi damuwa da samari, ba su damu da tsofaffi ba. In ka shiga mota, in ka ga tsoho sai ka zauna kusa da shi, ka zama abokinsa, ka samu ka jefa masa kaset din. In aka je ‘check point’ aka ce kai yaro sauko, ina kaya? Sai a shafa ba kaya. Alhali kaset yana aljihun Baba ko a kayan Baba. In an sauka, sai mutum ya ce sannu Baba, sai ya dauki kaset dinsa ya tafi. Magana dai ta dinga ‘circulating,’ jama’a har dai aka dago, aka tashi. Shi Imam yana Paris, can kuma ga yadda al’amari ke gudana, Iran ta juye, al’umma sun dago, ana cewa, “Mutuwa ga Sha! Mutuwa ga Sha!”

Shi kuma Sha din nan an dade ana boye masa abubuwa, ba ya sanin me ke faruwa, ana nuna masa komai lafiya lau. Sai a ce masa akwai wadansu suna bore, amma mun yi maganin su. Wasu ’yan tsiraru ne, amma an kore su. Sai da abu ya yi kamari, wata rana shi Sha ya hau helikofta, ya ga tituna iyakar ganinsa sun cika da mutane, sai ya juyo ya ce wa Janarori biyu da suke bayansa, ya ce duk wadannan mutanen ba su so na ne suka fito? Sai suka sunkuyar da kansu. Shi ne da ya sauka ya ce, ba zai sake amince wa kowa ba, har matarsa ma ba zai sake amince mata ba. Ashe duk sun san abin da ke faruwa suka boye masa. Haka dai Sha al’amari ya yi kamari har ya san inda ya nufa.

To, kuma duk yunkurin da Amerika ta yi na ta zaunar da Sha ya gagara ko kuma ta yi juyin mulki na soja. Kamar littafin da wani Janar dinsu ya rubuta, Janar Huyser, ‘Mission to Tehran’, sunan littafin nasa. Shi Janar ne da aka tura don ya ga yiwuwar yadda soja za su kwaci mulki, idan ya zama dole Sha ya kife. Kuma suka sa ya je ya yi ‘liason’ da sojoji ne, kar ya yi hulda da sha’anin siyasa; sha’anin siyasarsu kuma na hannun Ambasada dinsu Sullivan. Amma shi ma Ambasadan ya yi littafi, kuma littafin Huyser kamar raddi ne ga littafin Sullivan. ‘Mission to Iran’ shi ne na Sullivan, shi kuma Janar Huyser sai ya yi ‘Mission to Tehran’.

Don shi Sullivan Ambasada din su yana ganin shi ya karanta rubutu a bango, yana ganin ba yadda za a hana ‘revolution.’ Ya ba su shawarar cewa, abin da ya kamata Amerika ta yi shi ne, ta yi kokari ta ga gwamnatin da za a kafa ba abokiyar gabar Amerika ba ce. Amma abinka da masu ‘arrogance’ suna ganin a’a, sai sun hana. Ya ce, ba zai yiwu ba, ku kyale kawai, Imam kamar ya kafa daula, ba yadda za a yi a iya hanawa, saboda duk al’umma suna tare da shi; ba zai yiwu ka iya hanawa ba. Amma dai su sun tsaya tsayin daka.

Har dai karshe dole Sha ya gudu, kuma juyin mulkin soja bai yiwu ba. Ya kafa wani wai shi Bakhtiar Firaminista. Har ya rubuta wa Imam Khumaini takarda, “da dukkan girmamawa zuwa ga mai girma. Na san manufarka ita ce a samu adalci da sauransu. Kuma ina iyan kokari na in ga an yi adalci kamar yadda kake so kaza, kaza. Kuma a shirye nake in ziyarce ka a Paris don ka ba ni umurnin yadda kake ganin ya kamata a yi, kuma shi zan bi.” Sai Imam ya ce a ba shi amsa. A ce masa yana iya zuwa ya gan shi a Paris, amma sai ya sauka daga Firaminista.

An ce wani lokaci har wadansu daga cikin mabiya Imam sun ga kisan da Sha yake yi ya yi tsanani, suka je suka sami Imam suka ce, wannan al’amari kisan da yake yi fa zai iya karar da al’umma, ba yadda za a yi a dan sassauta? Kisan ya yi tsanani. Suna wannan maganar, sai ya ce musu su kawo masa ‘list’ na mutanen da za su iya gudanar da gwamnati in an kafa. Suka ce su suna kokarin yadda za a samu sassauci, shi yana cewa a kawo ‘list’. Ya ce musu wannan al’amari na Allah ne, kuma zai tabbatar da shi. Ka ji wannan al’amari irin na Imam! Tsayuwa kyam.

Shi ma Janar Huyser a cikin littafinsa yake cewa, su sai su ga mutumin nan ya dauki wani ‘dangerous step’, wanda ba yadda za a yi mutum ya dauki wannan ya yi nasara, shi kuwa sai ya yi nasara. Alal misali su soja suna harbin mutane; abin da aka saba in soja suna harbin mutane, me za ku yi? Kila ku samu duwatsu ku harbe su. To, shi Imam sai ya ce a ba su Fulawa ne. Shi kuma fulawa na da daraja a wurin mutumin Iran. Mu nan ba mu san ma’anar fulawa ba. ’Yan Iran su sun san ma’anar fulawa. Akwai wani gari ma Bahallati, garin fulawa ne ma. Har duk duniya suna aika wa don a samo musu fulawa, don duk gonaki fulawa ne iri-iri. Kuma su Fulawa na da ma’ana a wurinsu. In za ka je gai da mara lafiya, akwai fulawar gai da mara lafiya. Za ka gani a kofar Asibiti ana sayarwa. In ba ka sani ba, kai ‘novice’, za ka ga fulawa ce kawai, amma akwai fulawar gai da mara lafiya. In fulawar mutum ya dawo gari ne, ya tafi tafiya ya dawo, akwai fulawar da ake tarban sa a ‘airport.’ Kuma fulawa mai rai, ba kamar wannan na roba ba, na sosai, wanda yake ana zuba masa ruwa, in ya kwana ya yini shi ke nan, sai ya fara yankwanewa.

Saboda haka bizines din fulawa babban bizines ne a wurinsu. To, fulawa tana da ma’ana, kowacce akwai abin da take ‘expressing’. To sai aka samu fulawar kauna da so, sai ana ba soja. Shi yana harbi, ana wurga masa fulawa. Su suna ganin kamar wannan ba zai yi aiki ba, amma sai ya fara tasiri a cikin sojojin. Suna harbin mutum yana ba su fulawa, sai suka fara kuka. Cikin ‘slogans’ dinsu har da cewa “Haba sojojinmu! Me ya sa kuke harbin mu?” “Haba sojojinmu me ya sa kuke kashe mu?” Shi kuma Imam sai ya fara jawabi yana cewa, “Haba soja! Haba soja! Yanzu ka yarda ka zama bawan wata kasa, maimakon ka zama kana wa kasarka hidima? Yanzu mutanenka za ka kashe maimakon ka yi musu aiki?”

To, su ba su dauka wannan maganar, soja zai ji ba? Sai ya ce, “ka yar musu da ‘uniform’ dinsu tunda ka bar musu barikin. Gudu kawai ka koma kauyenku.” Sai sojoji suka fara jin wa’azi. In an je ‘demonstration,’ sai kawai su jefar da bindiga, su yar da ‘uniform’, sai su shiga mutane. In an tura su su yi harbi, in an tura kamar dari shida, in aka dawo, sai a ce hamsin ba su dawo ba. In aka sake zuwa, sai a ce yanzu kuma dari ba su dawo ba. Sai suka fara cewa yadda za a yi, da yake ba su sa hula, da wuyan gaske ka ga mutum da hula a cikin mutanen Iran in dai ba Malami ba, galibi mutane ba su sa hula, kansu a waje. Sai suka ce sojoji su rika aski. Suna musu wani aski, su bar tsakiya da gashi. Su mutane sukan je da ‘shirt’ ne da wando, kana durowa cikin su, ka ce “na zama naku,” sai ka cire ‘uniform’, sai su ba ka ‘shirt’, sai ka zama dan gari. Sai suka ce daga yanzu duk soja ya yi aski, ta yadda da an hango wani ya zama dan gari ne sai a harbe shi.

To, da samarin gari suka ji haka nan, kowa sai ya yi askin soja. Ko soja ya duro kan sa iri daya da na mutanen gari, ba wani bambanci. Yana durowa daga mota, sai a ba shi ‘shirt’ da wando, ya cire ‘boot’ a ba shi takalmi ‘normal’, shi ke nan sai ya zama mutumin gari. To, wannan ya daure musu kai, sai soja ya shiga kuka ya fada cikin mutane. Wannan wane irin mutum ne ya dauki matakin da ba a san ana samun nasara da daukar sa ba, amma shi sai ya yi nasara?

Shi Huyser a littafinsa yana cewa, wai rai goma yanzu, zai maganin rai dari nan gaba. Ya yi ta maimaita wannan. Wato a kashe rai goma yanzu maimakon a kashe dari nan gaba. Wato ya yi ‘justifying’ kashe mutane da suka yi. Domin kashe su yanzu za a kashe kadan ne, amma in aka bari, za su yi karfin da sai an kashe da yawa. Kai ka ce ‘the only thing’ da za su yi shi ne duk mai ra’ayin ‘revolution’ su kashe.

To, kuma abin yana zama in kana ganin ra’ayin daidaiku ne, yanzu sai dai in za ka kashe al’ummar ne gaba daya, ka mallaki itatuwa. Shi ne wannan mutumin ke cewa ‘cantankerous,’ ya ki ‘compromise.’ Ya tsaya kyam a kan cewa kasarsu ce, a fita a ba su wuri, a bar musu kayansu. Har ma Imam da kisan ya yi yawa lokacin Bakhtiar ya ce, shi ma zai zo, ga shi nan a kashe shi. A hada har da shi a kashe.

To, wannan cewa fa zai koma Tehran, abin fa ya firgita su. Ga Imam nan fa zuwa. Suka yi mitin, to yaya za a yi ne? A hana shi sauka a Tehran ne, a ce ya sauka a wani gari. Aka ce mutanensa ba za su yarda ba, sai dai a yi rigima. Aka ce, to a rufe ‘airport’. Aka ce, to ai ba zai rufu ba.

Sannan mutane suka fara cewa, da can muna ‘compromise,’ amma yanzu in kuka hana Imam dawowa, za mu fito da bindigogi. Sun san dama akwai bindigogin, amma ba a yi amfani da su ba. Zai zama yaki ne sosai. Kuma ko ba komai da yawan sojoji sun balle. Ana cikin haka kuma ‘airport’ suka balle. Soja kana iya samun wanda bai yi makaranta ba, ya je ya zama soja. Amma da ka ji an ce mutum ‘airforce’ ne, dole sai da ya yi karatu. Sojan sama wasa ne? Ka san dole ya san kan gadon jirgi ko? Ba za a ce maka kai sojan jirgin sama ne, alhali ba ka san komai ba. Kafin ka zama sojan jirgin sama, dole sai ka yi karatu. Saboda haka sojojin jirgin sama a cikin ‘military’ su suka fi ilimi, don su wayayyu ne, don su ‘minimum qualification’ da za ka zama ‘airforce,’ dole ilimi ne mai zurfi, sabanin zama ‘ordinary soldier in the army,’ wanda kila ko firamare ka yi ko sakandare, ko ma ba ka iya rubutu da karatu ba, kana iya yi. Amma banda ‘airforce.’ Su tun a lokacin suka sallama, suka je suka yi mubaya’a kawai. Suka ce sun bi.

Ya zama shi Sha ya rasa ‘airforce,’ saboda haka ya nemi sojan kasa su far wa ‘airforce.’ Lokacin ya sa wani ‘curfew’ tun Imam yana Paris. Kun san yadda ake sa ‘curfew’ a nan kasar, suna yi su ce sun hana kowa fita. To, nan ma sun yi haukar da ba mu taba jin an yi ba a duk duniya. Suna yin 24 hours ‘curfew’. Ba mu taba jin wannan ba. A tarihin bil’adama ba mu taba jin an yi ‘24 hours curfew’ ba, sai a Nijeriya, mahaukata ke yi; wai kuma gwamnatin da aka zaba take yi. Wannan hauka har ina? The ‘biggest’ hauka shi ne wanda Sha ya yi, ya ce 12-4. Daga 12:00 midday zuwa 04:00 na yamma. Wato ya ba da awa hudu ke nan. Ka fito karfe 12:00 na rana, karfe 4:00 ka bace. To, ba a taba jin irin sa ba kafin wannan. Imam yana Paris ya ce kar su bi wannan dokar. Sai ya zama don biyayya ga Imam, to ba ma wanda ya kwana a gida. Ba ma ‘curfew’ ba, a kan titi aka zo ana kwana. Duk da ko a lokacin ana ma sanyi, amma duk da haka mutane kowa ya fito ya kwana a kan titi.

Sai ya zamana lokacin da ya so ‘army’ su far wa ‘Airforce,’ sai ya zama ba ta inda za su bi, duk mutane ne a kan tituna. Kuma da ‘Airforce’ din da mutanen gari suka bi suka fafata da ‘Army’ din. Dole ‘Army’ din aka yi ‘confining’ dinsu a bariki.

GAGARUMAR TARBAR DA AKA YI WA IMAM

Kama-kama ana nan dai al’amari ya kai dole suka kyale Imam ya koma, kuma aka yi masa gagarumar tarba. Taryar da ba a taba yin irin sa ba a tarihi ya zuwa yanzu. Tarihin da muka sani dai, an san ana tarya iri-iri. Na’am an san Manzon Allah ya shiga Madina da gagarumar tarba ta ‘Dala’al badaru Alaina min saniyyatul wada..’ da kuma Isa Almasihu, ya shiga birnin Kudus a kan jaki wanda suka rika cewa “Hossana dan Dawuda..” har duwatsun gari sun amsa tare da su. Lokacin da Malaman Yahudu suka rika cewa “ka ji abin da mutanen nan suke cewa, ka hana su fadi!” Sai duwatsun gari ma suka fadi. An ga tarya irin wannan. Akwai shi a Bayibul a Huzaiya, inda ya ce, an nuna masa mahayin jaki da mahayin rakumi. To mahayin rakumin shi ne Annabi Muhammadu. To, ban sani ba ko Huzaiya an nuna msa mahayin jirgin sama ba. Kila ya ga wani ya sauka a jirgin sama, ya ga tarya gagaruma. Shi kuma Imam Khumaini da jirgin sama ya sauka.

Wani abin mamaki dangane da halin da ake ciki din nan, ana zaman dar-dar, ga jirgi ya dago daga Paris, ba a san abin da zai faru ba; za su harbi jirgin ne, za su hana shi sauka ne? Shin me zai faru? Duk mutane suna firgice. Wani ke ba da labara ya ce, shi da ya ji an ce jirgin ya taso, firgita ya yi. Yaya za a yi ne, yanzu Imam yana sama? Aka ce da Imam ya hau jirgin ya je ‘first class’ inda suka yi masa ‘reserving’, sai ya kwanta ya yi barci abinsa. A natse kawai shi yake.

Haka nan ya sauka, aka yi wannan gagarumar tarya, aka sa shi a mota. Na takaita muku labari, kafin zuwan Imam kusan komai ya tsaya a Tehran, a Iran gaba daya, kusan komai ya tsaya. Sun tsai da komai. Masu sai da kananzir sun ki sayarwa. Masu kwashe shara, ba kawai kwashe sharar ne ba su yi ba, sun ma zuba sharar ne a kan titi. Ko’ina biji-biji. Komai ya tsaya cak. Amma da aka ce Imam zai dawo, to ko lomar tuwanka ya fadi a kan kwalta kana iya dauka ka ci abinka, saboda tsaftace muhallin da aka yi, aka sa sabulu da soso aka wanke tituna. Ko’ina fes-fes, aka dora fulawowi. Gagarumar tarya, a lokacin suna cewa wadanda suka tarbe shi sun kai kimanin miliyan shida, wasu hotuna suna nan, wasu black and white, wasu kala, za ka ga gagarumar tarbar da aka yi wa Imam.

Da ya sauka, ya yi nufin ya tafi Bahesti Zahra ne, makabartar Shahidai, saboda haka hanyar ta gagara tafiyuwa daga ‘Airport’ zuwa Baheshti Zahra saboda dafifin mutane, kowa yana so idonsa ya hango masa Imam. Wasu ma don zari har sun hau kan motar ne suka zauna, da kyar ake hango Imam. Mota ta gagara tafiya cikin dandazon mutane. Titi ya cika da mutum, ba zai yiwu ta yi tafiya ba. An rasa yadda za a yi da mutane, sai aka ce bari a zo da helikofta. Aka yi ta korar mutane, sannan aka samu inda helikoftan zai sauka. Ya hau helikofta ya tafi. Ko da ya je can ma mutane sun isa can. Mutane suna jin cewa Baheshti ya nufa, suka nufi can a guje. Aka rasa inda helikofta zai sauka. Mutane aka yi ta kora, sannan aka samu wurin da helikofta zai sauka.

Za mu ci gaba insha Allah.