AlmizanAlmizan logo
Jum'a 17 ga Rabi'ussani, 1440 Bugu na 1380 ISSN 1595-4474

Tunatarwa

Ninanci ke tafi da kasar nan

Shaikh Zakzaky


Shaikh Zakzaky

Saboda haka wannan rana ce da ta nuna sasantawa tsakanin musulmi da Kirista. Har ma akwai ayar da take cewa, za ka ga wadanda suka fi kusa da son muminai, wato in na ce musulmi za a fi ganewa, sune wadanda suka ce mu Kirista ne. Allah (T) ya ce, saboda a cikin su akwai Malamai akwai masu ilimi, ku su ba su da girman kai. Wannan yabo ne ga Kiristoci, cewa cikin su akwai masu ilimi, kuma ba su da girman kai. Shi ya sa suka fi kusa da son musulmi.

Na san akwai wadansu abubuwa da wannan ba shi ne muhallinsu ba, wani lokaci in muna taron kirista da musulmi ma yi wannan. Amma na san akwai wadansu ayoyi da wadansu sukan yi musu fassara wani iri. Alal misali akwai “La tattakhizul Yahuda wannasara auliya.” Na taba ganin wani fassara da wani ya rubuta da Turancin Ingilishi. Ya ce “do not take Jews and Christians as friends.” Sai ya ce, ai addininku ya ce kar ku dauko kowa a matsayin aboki. Sam ba abin da ayar ke cewa ba ke nan. Kuskure ne a fassara shi da ‘friends’; ba ‘friends’ yake nufi ba.

A lokacinsu akwai yake-yake. Akwai kasar Khaibar da Fadak, su Jews ne. Akwai Najran da wasu kasashe, su kuma ‘Christians’ ne. Akwai su kuma musulmi a Madina, akwai kuma Kuraishawa masu bautar gumaka. To, lokacin da ake wadannan yake-yake su Kuraishawa, sai suka hadu da Kiristoci da Yahudu, suka hada kai ‘against’ Annabi. Sai aka ce wannan ayar ba ‘friends’ take magana ba, tana magana ne a wannan ‘wad’i’ din. Da an ce ‘ally’ da hakan ya yi. Kamar ‘allies’ a ‘war.’ Ma’ana kar ku dauki mutanen Fadak da Khaibar da kuma Najran a matsayin ‘allies’ din ku domin su ‘allies’ din ‘one another’ ne, ba ‘friends’ ake nufi ba. Ga Fasto Buru abokina ne, kodayake ya ce wai ni Maigidansa ne. Wancan ‘wrong’ fassara ne. ‘Situation’ ne na wancan lokacin tsakanin kasa da kasa.

Kamar yanzu da aka yi ’yan yake-yake, aka ce ‘allied forces,’ wadannan sun hadu da wadancan. To, kar ku dauke su ‘allies,’ in mutum yana ‘ally’ ‘to enemy’ dinka. Don lokacin su Kuraish mutanen Makka ‘they are against the Prophet in Madina’, suna kawo masa yaki. Sai ya zama su Fadak da Khaibar, kasashen Yahudu da Najran sun yi ‘allying’ da su. Sai aka ce, to ku kuma kar ku zama ‘ally’ din wanda yake ‘ally’ ga makiyinku. Wannan ‘situation’ ne wanda daga baya ya zo ya wuce. Ya zama yanzu Makka ma din ta yi ‘falling’ Khaibar din ma haka, Najran kuma an sasanta da ita. Saboda haka wannan ayar ke nan. Sam ko kadan ‘wrong’ fassara ne a ce mutum ya fassara da cewa “don’t take them for friends,” ba abin da yake nufi ba ke nan. Ya kamata ka ga ‘situation’ da ake magana a kai ne.

Har wala yau rana mai kama ta gobe, rana ce ta wani buki na daban. Shi ne ran da Amiril Muminin da kansa da 'family' dinsa su ma suka yi wata sadaukarwa. Sadaukarwar a kimarsa na ‘monetary value may be little,’ amma ‘sacrifice’ din is ‘much.’ Shi ne inda suka yi azumi, suka zauna za su yi buda baki, sai mai bara ya kwankwasa musu kofa, sai Amirul muminin ya tattara ‘sufra’, kyallen da ake tattara abinci a kai, da burodin da komai a lokacin ya mika wa shi wannan almajirin. Sa ya zama ran nan sun kwana ba tare da sun ci abinci ba. Suka kuma ci gaba da azumi babu buda baki. Wato sai suka sha ruwa kawai. Kashegari suka sake azumi. Sun zauna za su ci abinci ke nan, na farko wanda ya fara zuwa miskini ne aka ce, wato 'poor person'. Sai na biyu kuma yatim, wato maraya, wanda shi kuma ba shi da iyaye. Shi kuma ya zo ya roke su ko suna da abinci. Sai shi ma aka tattara aka ba shi. Sai kuma rana ta uku, sai wani Asir, kamamme ko ribatacce ko 'prisoner’ shi ma sai ya zo ran nan. Kamar ‘test’ ne Allah ya yi musu, shi ma suka sake ba shi. Sai ya zama kwanaki uku a jere suna azumi amma ba su cin abinci. In za su ci abinci, sai a roke su, sai su mika. duk 'family' din kuma. Ya hada da shi Imam Ali da matarsa Fatima ‘yar Manzon Allah da ‘ya’yansa Hasan da Husain da yarinyar gidansu, ma’aikaciyarsu sunanta Fiddha. Sai da ta kai ma sun kanjame saboda yunwa na kwana uku a jere. Aka ce wannan aikin nasu Allah ya gode har ya saukar musu da Ma’ida daga sama, kamar shigen wadda aka saukar wa Annabi Isa. Muna da sura sunanta Ma’ida. Ma’ida na nufin teburin da aka jera abinci, kamar dai nan da aka jera abinci. Aka saukar musu da Ma’ida daga sama, wato abincin Aljanna ke nan suka ci a wannan dare saboda sadaukarwarsu. Har aya ta sauka tana yaba musu sune suka ciyar da miskini da yatim da asir. Suka ce mun yi muku ne saboda Allah, ba domin godiya ko don ku biya mu ba.

To, shi ma wannan aiki ne wanda ya cancanci, kamar sadaukarwar Annabi Ibrahim na yanka da, shi ma a yi bikinsa. A tuna da cewa wadansu mutane sun fifita wasu a kan kansu. Na’am kana da bukatar abinci, kana jin yunwa, amma ga wani ya fi ka jin yunwa, sai ka sadaukar ka ba shi, kai ka hakura. Wannan sadaukarwa ce da Allah ya yaba. A kansa ne ya saukar da ayoyi, ya yi musu alkawarin Aljanna saboda wannan aikin. Duk wadannan abin da nake fada in an lura abin da yake nufi shi ne ka sadaukar don wani, ka sadaukar don wani. Kuma wannan shi ne ainihin koyarwar dukkanin Annabawa, wadanda suke sadaukarwa domin wasu.

Mu yanzu mishkilolin da muka samu kanmu a ciki, kowa kansa yake so. Ina jin bara wancan akwai wata kalma da ni na yi 'coining' Dinta da Hausa na ce mata ‘ninanci,’ ‘egocentrism’ ke nan. Kowa ni, ni, ni. Ga abinci ba zai ishi kowa ba, wa zai ci? Ni, ni, ni. Ga riga, ba yawa. Wa zai sa? Ni, ni, ni! Ana sanyi yanzu, ga rigar sanyi, ba yawa. Wa zai sa? Ni, ni, ni! Ga gidaje ba yawa. Wa zai shiga? Ni, ni, n! Ninanci ke gudanar da kasar nan, kowa kansa kawai. Saura kuma 'let them go to hell, none of my business.' Wasu har suna fadin haka nan.

Ina tsare a 'prison' din Fatakwal, na ga wani abu haka nan. Ana ba da abinci, ana 'measuring' abinci ne. har ma a nan Arewa suna ce masa laba, ma’ana 'pounds'. Kowane 'prisoner' ana auna abinci 'per pound' ne. In da za a ba ka 'pound' din garin rogo ba za ka iya cinyewa ba, amma kowane 'prisoner' haka za a auna masa. Suna karbar 'full measure' ne. Sai ma an sa sikeli. A lokacin suna amfani da tsohon sikeli, irin wanda akan zuba kawai ana tura wadansu duwatsu. To irin sa suke amfani da shi. Sai sun dauka 'full'. Amma ana gama awo, har da wani wai shi ‘weigh man’, ana gama awon za ka ga ana fita da abincin buhu-buhu da katon-katon na kifi; duk ana waje da shi. Jarka-jarka na manja duk ana waje da shi ne. Na wane kaza, na wane kaza ne. Sai ya zama a wurin, a idonmu sai ka ga 'prisoner' yana mutuwa saboda yunwa, alhali an karbi 'share' dinsa.

To, wani Wader a nan 'prison' din wanda ya shahara, ban sani ba, kila yanzu ya mutu ko yana da rai, don ko lokacin ya manyanta, wani mutumin Benin, sunansa Obaseki, amma suna ce masa 'Law there'. Don kowane lokaci yakan ce 'The law is there'. Tun ana ce masa 'The law is there, sai sunansa ya zama 'Law there.' Wasu ma ba su iya faDa ba, sai su ce 'Lozaya. Sai ya zama sunansa kawai. Na san in ya ji wannan maganar ba sharri nake masa ba, ya faru ne. Da kunnena na ji shi yana fadin "I don’t care, prisoner can die as long as" ni zan ci. Su debi abinci su fita da shi. Shi da yake cewa 'The law is there', in ka ci abincin 'prisoner' sata ka yi don na 'prisoner' ne.

Don an taba wani mutum duk suka ki shi, ni ban gan shi a 'prison' Din ba, wasu sun ce mutumin Filato ne, ni ba mu zauna da shi ba, da ya je ya rike 'prison' din, to shi sai ya hana a fitar da komai. Sai ya zama su 'prisoners' suna ci suna koshi. Aka ce wata rana ma saboda tsoron sa da suke yi, wani 'Warder' ya taba Daukar soyayyun kifaye, an soya da manja da ya gan shi sai ya bude hularsa ya saka. Da yake an soya ke nan, da dan zafi. Sai manjan ya shiga gangarowa. Sai ya ce 'Warder' yana 'sweating' mai. Ya daga hular sai ga kifaye tutsa. Ya ce a mayar 'kitchen'. Su Fursunoni sun yi murna, amma sauran su ba su ji dadin zamansa ba. Saboda shi ya tsaya kan za a yi gaskiya ne.

To, wannan irin 'mentality' na mutanenmu cewa shi kansa kawai ya sani, sai aka rasa su wane ne za su sadaukar? Domin kowa zai ce abin da kake fadI gaskiya ne, amma akwai hadari. Don na san a lokacin ina prison din Enugu, har na fara rubuta littafi, littafin da bai ga hasken rana ba. 'Title' din littafin shi ne 'Mission of man on earth'. 'Based on' wata lacca da na saba yi ne. Amma wannan na yi rubutu ne. Kuma akwai bambanci tsakanin magana da rubutu. Rubutun da na yi yana da dan tsawo. To sai shi mai rike da kurkukun, wani mutumin Akwa Ibon din nan, Akibi, ya ce yana son ya ga abin da nake rubutawa. Sai na dauka na ba shi. Bayan da ya karanta sai ya ce a kira ni, ya ba ni kujera na zauna ya ce wannan abin da ka rubuta gaskiya ne, amma lallai akwai hadari, domin a kan wannan mutane ba kyale ka za su yi ba. Amma ya ce gaskiya ne abin da ka fadi. Mutum ga abin da ya kawo shi a doron kasa, amma kuma wani abin daban yake yi.

Za mu ci gaba insha Allah.