AlmizanAlmizan logo
Jum'a 8 ga Muhammaram, 1439 Bugu na 1308 ISSN 1595-4474

Tunatarwa

Bature bai zo kasar nan saboda mu ba

Shaikh Zakzaky


Shaikh Zakzaky

Wannan shi ne jawabin da Shaikh Ibraheem Zakzaky ya yi a garin Lokoja. Ammar Muhammad Rajab ya rubuta.

MAKASUDIN ZUWA NA

’Yan uwa Musulmi, assalamu alaikum warahmatullahi ta’ala wabarakatuhu. Duk da an yi bayanin makasudin zuwana, ina ganin ba zan bata lokaci ba, in ni ma na yi bayanin makasudin zuwa na din. Ko ba komai, kila na dan dada kwakkwafawa.

’Yan watanni uku kamar da suka wuce, ba’adin ’yan uwa na wannan sashe na Kudu maso Gabas da Tsakiya da wannan ‘area’ din, suka shirya wani taro irin wanda ake ce ma na kara wa juna ilmi din nan (semina) a garin Ayingba. To, aka yi wannan taron, kuma ’yan uwa da dama na wannan shiyya sun halarta, musamman ma wadannan dai yankuna na bangaren wannan jiha ta Kogi. To, kuma a daidai wannan lokacin da ma sun shirya cewa; za a yi abubuwa kamar a gari biyu ne; da can Ayingba da kuma nan Lokoja.

To, sai muka nuna musu cewa; lallai zai yi wahala a ce za a yi wadansu tarurruka a garuruwa biyu a lokaci guda, a dai dauki daya dai kawai. To, sai aka tsaya a kan cewa; a Ayingba za a yi, amma kuma suka kawo batun cewa; akwai wasu ’yan ayyuka da ’yan uwa suka gabatar a nan Lokoja din, wadanda suke bukatar a zo a gani. Wannan ko shi ne na gyaran wadansu makabartu (kaburbura) na wadansu Sarakuna da Turawa suka firfitar suka tara a nan, kuma wadanda yau da kullum tarihi ya ambace su, ana tunawa da su, har ma wasu kaburburan ma wuraren sun zama juji, inda ake zubar da shara, kuma har ma inda ake dan zagayawa a tsuguna. Wurin dai an kazantar da shi haka.

Wannan dai ya nuna maganar wannan ya taso tun wani lokacin da wadansu ba’adin ’yan uwa suka kawo ziyara, suka ga wannan. Har ma suka rubuta cikakken rahoton su a ALMIZAN, wanda yake ya jawo hankulan wasu, wanda yake suka ga lallai ya kamata a dauki wadansu matakai. To, ba’adin ’yan uwa su suka dauka wa kansu yin wannan, da cewa a madadinmu suke yi, suka zo suka dan yi gyare-gyare, suka dan tsaftace wuraren, suka dan gyaggyara dai, daidai gwargwadon wanda za su iya yi.

To, kuma su mutanen garin sun rika tambayar su, suna bayyana musu ainihin dai su ga su ma’abota wannan Harka ne, su kuma suna cewaMalam ne ya sa su, da sauran su, da sauran su dai. To, kuma dai wasu suka ce; da an kammala aikin a daidai lokacin da muka je Ayingba din nan, da sai mu zo mu ga wurin, amma sai suka ce a lokacin ba a gama ba, ana fata za a gama a Disamba.

To, shi ke nan, ana nan, ana nan dai har dai ya zuwa wannan lokaci Disamba din ya yi. To, kuma sun so har wala yau ya zama mako mai zuwa ne za a zo, to mu kuma har wala yau muna da wani taro, saboda haka sai muka tsaya a kan wannan cewa a dai yi a daidai wannan lokacin. Suka ce; wannan lokaci ana samun cinkoson motoci a Lokoja duk shekara, amma dai muka yi fatan a dai zo wannan lokacin ba dai laifi. Haka nan dai an zo din, an yi fama da cinkoson, amma alhamdulillahi dai, insha Allahu ga shi dai an zo din. GARIN LOKOJA

To, wannan gari da ake ce ma Lokoja, wanda mutanen garin, wanda yake galibansu suke gaba na, sun san abubuwa da dama fiye da mu dangane da tarihin garin su. Da ma dai ba ina ‘tawakku’in’ cewa; da ma can zuwan Turawa ya samar da garin ba, da ma akwai garin, tunda da ma can mahadin koguna ne biyu, na Binuwe da Neja. Kuma da ma zai kasance tuntuni, ba ina ce muku na san tarihin garin ba ne, dama zai kasance garin akwai shi da mutane. Sai dai abin da sauran al’umma suka fi sanin garin da shi, shi ne; nan ne mazauni na ’yan mulkin-mallaka na farko lokacin da suka shigo kasar nan.

Saboda haka tun lokacin da Lugard ya zo karkashin ‘Royal Niger company,’ ya ajiye hedikwatarsa a nan, kuma har aka mai da wannan kamfanin ainihin aka ba shi izinin ya mallaki wannan shiyya. Daga nan ne kuma ya buga har ya mallaki sauran sassa na Arewacin kasar nan a madadin gidan sarautar Ingila. Har kuma daga nan ne har wala yau ya kafa daularsa, ya zama kamfani mai zaman kansa. Ya zama gwamnatin Birtaniya ta karbi ko kuma na ce gidan Sarautar Ingila ta karba ma kansa cewa; yanzu shi ne yake mallakar wannan shiyya. Kuma yana karkashin Ofishin mulkin-mallaka ne. Wanda ainihin daga nan bayan ya kafa gwamnatinsa, wanda daga nan ya tashi saboda wani dalili nasa ya koma da Hedikwatar Zungeru a lardin Zariya na wancan lokaci. Kuma daga nan Zungeru, bayan wannan lokaci ya koma Zariya da Hedikwatarsa. To, daga baya kuma ya ta da Hedikwatarsa zuwa Kaduna.

To, har wala yau a Jamhuriyya ta farko lokacin mulkin Sir Ahmadu Bello sun yi ta hankoron cewa; su dawo da Hedikwatar Nijeriya daga Lagos zuwa Lokoja. To, kuma muna iya cewa kusan Abuja wannan mafarkin nasu ne. Ko ba komai, kodayake Abuja ba Lokoja ba ne, amma dai kusa-kusa ne, kuma abin da suke nufi ke nan. Sai kuma wani mafarkin da suke nufi nan gaba ya yiwu shi ne na maishe da wannan gari ya zama mashigi na ruwa, wanda za a rika fitar da kayayyaki, kamar yadda ake yi a Lagos da Fatakwal. Wato wannan tsohon mafarkinsu ne, amma yanzu ake shirin. Tana iya yiwuwa wata gwamnati nan gaba ya zama ta tabbatar da wannan ta hanyar yashe Kogin Neja da mai da wannan gari ya zama wurin da za a rika sauke kayayyaki, ya zama manya-manyan jirage suna saukewa, ana sauke kayayyaki. Wannan yana iya yiwuwa nan gaba.

MULKIN MALLAKAR BATURE

To, fakam da yawa idan ana magana dangane da mulkin-mallaka, mutane suna masa hange daban-daban, suna ganin Bature ya zo nan kasar ya samu Sarakunan kasashen nan suna mulkin danniya. Kuma ya samu wadansu mutane, musamman na Kudancin kasar nan ainihin wadanda ba su da zaunannun dauloli suna rike da wadansu da ‘takalidai’ da al’adu wadanda suke wadansu ainihin abin da suke su daidai ne a wurinsu, amma Bil’adama ko ma mu ce; kanunan duk duniya yana ganin wannan abin ba daidai ba ne. Kamar kashe tagwaye da daukar su miyagun Alkhaba’is, da wadansu abubuwa da suke yi irin wannan.

Fakam da yawa mutane sukan ta kawo batun cewa kamar Bature shi ya zo ne ya kawar da wadannan abubuwa ya kawar da zalunci ya kawo tsari na adalci a kasa. Kuma ko ba komai shi ya samar da kasar da yanzu ake ce mata NIJERIYA; shi ya kafa ta. Ba wai shi ne ya yi kasar ba, ba kuma shi ya samar da mutanen da suke zaune a kasar ba, a’a amma shi ne ya shata kan iyaka wanda yake daidai nan wurin sunan kasa ce guda, sunanta NIJERIYA. Ya fara da wurin da ya kira ‘colony of Lagos,’ sannan ya kama Kudu ya ce masa ‘southern protectorate,’ sannan ya kama Arewa ya ce masa ‘Northern protectorate.’

Kasashe uku daban-daban, daga baya ya hada ‘colony of Lagos’ da ‘Southern protectorate’ a matsayin kasa daya, sannan kuma a 1914 ya hada wadannan bangarori biyu (‘Southern protectorate’ da ‘Northern protectorate) a matsayin kasa daya. Aka saka wa wannan kasa suna Nijeriya, wanda yanzu aka bar mana gadonta. Yanzu mu nan sunanmu wai NIJERIYAWA ne. Kuma kasarmu sunanta Nijeriya, mu kuma sunanmu me? Wai Nijeriyawa. Kuma abin da yake gabanmu shi ne; mu ciyar da kasarmu gaba.

Mene ne ci gaba? Na ji kun yi shiru ne. Wato ke nan mu yi gine-gine, mu yi dogaye daban-daban, mu yi titunan motoci; ga su nan dai. A samu garuruwa ana ta karakaina, ana ta harkoki, a yi ta rayuwa, kodayake kuma a yi ta mutuwa kuma. Tunda ana rayuwar ana mutuwa, shi ke nan. Sai ya zama Nijeriya din nan ta zama tsarar wadansu kasashe fitattu a duniya kila kamar irin su; Misra da Libya da Moroko da Aljeriya. Kila ma idan aka yi hobbasa ma a goga kafada da Malesiya da Indonesiya, kila ma a ce ke Singapore ke ma sai mun kamo ki, kila ma a kama Indiya. Wato a ci gaba sosai. Kila ma ana nan, ana nan sai a ci gaba sosai a shiga ajin kasashen nan da suka ci gaba. Domin yanzu kasashe a duniya an raba ta gida uku ne; da ci gababbu, da masu ci gaba da cibayayyu.

To, Nijeriya tana cikin jimlar cibayayyu. Saboda haka yanzu za ta zo ta shigo cikin ajin masu ci gaba, wata rana ma sai ta ci gaba. Ta zama kasa wadda take mai manya-manyan masana’antu wadanda take kere-kere na motoci da jiragen sama da jiragen kasa da sauran su. Ta yi kafada da kafada da sauran kasashen duniya irin ci gababbu irin su; Italiya da Birtaniya da Faransa da Jamus da sauran su.

To, sai dai ita Nijeriya tana da nata matsalar, amma kafin na kawo ga nan bari na zo ga cewa samar da kasa din. Ina iya ce mana wannan magana da nake yi kyanta da a ce bara ne na zo na yi a nan, domin kuwa bara wancan shekara biyu da suka wuce, lokaci ya wannan ina jin a Disamba ne ko? Mun je garin Bormi, inda shi ne aka yi fafatawar karshe tsakanin ’yan mulkin-mallaka da dakarun Sarkin Musulmi na wancan lokacin, Attahiru (Attahirun Amadu), wanda suka kashe mutane da daman gaske, ciki har da shi Sarkin Musulmi din, shi Attahiru din da ’ya’yansa da wadansu mutane. Suka yi ma abin da ake ce ma Dala din nan (gini) da gawawwakin wadanda suka karkashe kafin su tabbatar da ikonsu.

To, shekaru dari bayan wannna, wannan sun yi shi a 1903 daidai. To, da shekara dari suka kammala a 2003 ke nan, ‘yan uwa sun yi taro na karawa juna sani, ba’adin ’yan uwan da ake ce ma ’yan Academic forum, galibansu Malaman Jami’o’i ne da kuma dalibai, sai suka shirya Semina a can garin Bajoga, wanda ke kusa da Bormi din. Yanzu Bormi ta zama kango. Kodayake yanzu garin Bajoga shi ne, da ma su ’yan Bormi din ne suka dawo Bajoga, tsakanin su kuma, kamar dai wuri daya ne kawai. A wancan lokacin sai muka je aka yi bikin cika shekara dari (100) bayan kafuwar ’yan mulkin-mallaka da kawo karshen gwagwarmayar Attahiru. To, kuma muka ziyarci shi kabarin Attahiru din. A wancan lokacin shekara dari ke nan, kun ga yanzu shekara dari da biyu (102).

Na san maganar da na yi a can na faduui abin da ya faru a nan birnin Lokoja a watan Afrilu na 1904, wanda yake nuna shi Bature, su mutane suna ganin cewa kamar ya zo da adalci, ya kuma samar da kasar da ba ta, ya kuma samar mana da harshen da da ba mu da shi. Kila ma ya ba mu ilimin da da ba mu da shi. To, amma kila suna kallon abin da suke son su yaba masa da shi ne kawai. Amma akwai wani abu guda, Bature bai zo kasar nan saboda mu ba. Wannan tambayi kowane Bature zai iya gaya maka wannan. Bai zo kasar nan saboda mu ba. Bai zo domin ya wayar da kan masu duhun kai ba. Bai zo domin ya kafa kasa ta ci gaba ba. Bai zo domin ya kyautata rayuwar mutanen da suke wannan wuri ba. Bature ya zo ne domin kashin kansa. Ya zo sata ne; barawo ne, dan fashi ne! Ya zo ne ya dibi arziki, ya ci gabantar da kansa, ya kuma sallada ikonsa a kanmu, kuma ya bautar da mu bautar din-din-din. Wannan abin ya kawo Bature ke nan, kuma har yanzu zancen ke nan.

Za mu ci gaba insha Allah.