AlmizanAlmizan logo
Jum'a 15 ga Sha'aban, 1438. Bugu na 1288 ISSN 1595-4474

Tunatarwa

Jawabin Shaikh Ibraheem Zakzaky na karshe kafin kisan kiyashin Zariya 111

Shaikh Zakzaky


Shaikh Zakzaky

Wannan shi ne jawabin da Shaikh Ibraheem Zakzaky (h) ya yi ga Miliyoyin al’ummar da suka taru a filin Polo daura da Husainiyya Bakiyyatullah, Zariya a ranar Alhamis21 ga watan Safar, 1437daidai da 3 ga watan Disamba, 2015 a taron Yaumu Arba’in na Imam Husain (a.s). Ammar Muhammad Rajab ya rubuta muku.

Don haka ne ma aka ce lokacin a Birnin Kufa, a lokacin Hajjaj yana ta kisa ba-ji-ba-gani, ana ta kawo masa Sahabi yana kashewa, a ce can gidan akwai wani Sahabi, ya ce; a kawo a yanka, kafin ya shigo jama’a suka ce; ya Jabir, mu bar garin nan, domin wannan mutumin ba za mu amince masa ba. Ya ce; a’a shi ba inda za shi, duk ko aka watse sai aka bar shi. Sai aka ce akwai wani tsohon Sahabi a gida kaza, sai ya ce a kawo shi, sai aka zo da shi. Ya ce; zan kashe ka (in ji Hajjaj). Ya ce; “ba ka isa ba, saboda ni dan sakon Manzon Allah ne. Ni Manzon Manzon Allah ne, kuma ban isar da sakon ba, kuma sai na isar. Tunda Manzon Allah ya gaya min cewa zan isar da sakon, sai kuma na isar.” Hajjaj ya ce; “kawo sakon.” Ya ce; “kai ne, Manzon Allah zai aiko ni ya zuwa gare ka, kazamin ka da kai? Manzon Allah ya aiko ni ne ya zuwa ga Jikansa Muhammad, wanda za a kira Bakir, kuma ba a haife shi ba.” Sai ya ce; “ku kashe shi!” Zuwa can sai ya ce; “wannan tsohon banzan, ku fitar min da shi. Ba na son ganin sa. Sai ya ce; “da ma ba ka isa ka kashe ni ba.” Saboda mene? Jabir yana da yakini, saboda Manzon Allah ya ce zai ga Bakir, zai gan shi ne. Haka ko ya faru.

Lokacin da aka haifi Imam Bakir, da ya shigo shi bai san ma an yi haihuwar ba. Da ya shigo, sai Imam Zainal Abidina ya ce; “gai da Maigidanka.” Kamar yadda na ce ma ku ya tsufa, ba ya gani. Ya ce; gai da shugabanka, ya mika hannunsa ya ce; “Assalamu Alaika Ya Maulaya, ya Sayyadi, ya Muhammad Al-Bakir. Manzon Allah (saww) ya ce na ce maka ‘Assalamu Alaik.” Sannan Imam Bakir yana jariri ya ce; “wa alaihis salam, wa alaikas salam ya Jabir.” Jabir bai dade ba bayan wannan ya bar duniya. Ya ko isar da sakon. Na kawo muku labarin Jabir ne don a san waye Jabir. Labarin Jabir na da tsawo.

Kun san a kissar Umar bn Khattab, ya kasance yana ba mutane kason Dirhami, yana raba musu ko Dinare ne goma-goma, idan ya zo kan Jabir sai ya ba shi ashirin. Duk lokacin da idan ya ba kowa goma-goma, idan ya zo kan Jabir, sai ya ba shi ashirin. Sai Abdullahi dan Umar, ya ce; “Ya Baba, na ga kana fifita wani a kan danka. Yanzu ka ba Jabir ashirin, ni ko goma ka ba ni. Ya ce; “ya Dana ba zan manta da ranar da Babansa ya dake, Babanka ko ya gudu ba. Ranar Uhud, Babanka ya gudu, shi ko Babansa ya dake. Don haka duk lokacin da na gan shi, sai na tuna da Babansa. Shi ya sa nake ba shi kaso biyu.” To, idan kai Ahlus sunnah wal jama’a ne, kana da ‘uswa’ daga ziyarar Jabir, ballantana kuma ga Imam Zainul Abidina ya zo, wanda shi Jabir yake kallon sa a ‘Sayyadi wa maulahu’. Suka kwana uku (3); shi ne arba’in na farko. To, tun daga nan ake Arba’in har ya zuwa yau.

ZIYARAR ARBA’IN NA DAGA CIKIN ALAMOMIN MUMINI

Kuma ya zo a ruwayarmu daga Imam Hasanul Askari ya ce; alamomin Mumini guda biyar ne. Daga ciki sai ya ambaci Ziyaratul Arba’in. Ziyarar Arba’in na daga cikin alamar Mumini. Ta yiwu a wancan lokacin, mutane ba za su gane me yake nufi ba, amma yanzu za mu iya ganin Arba’in yadda ya canza. Yanzu arba’in ya zama ma’auni na gane ina wulayarka take. Idan dama can Ashura ta riga ta raba duniyar Musulmi biyu, Yazidawa da Husainawa, babu dan ba ruwanmu, ba dan baina-baina. Duk wanda ya ce; shi dan ba ruwansa ne, karya yake yi, Bayazide ne. To, sai ya zama ga shi Imam Hasan Askari (s.a) yana cewa ainihin; daga cikin alamomin Mumini akwai Ziyaratul Arba’in.

To, Ziyaratul Arba’in ya shiga kambama, ya yi ta fadada, ya yi ta fadada, shekara da shekaru, tun wannan shekara ta farko ake yin sa, har ya zuwa yau din nan. Kamar kwana uku da suka wuce, a irin ‘net’ din nan, ‘site’ din AL’ALAM na ga sun sanya wani hoto, suka ce masa ‘sura nadira’, tafiyar masu tafiya a kafa ne zuwa arba’in a shekara ta 1916 miladiyya. Ba yanzu muna da, mun kusa shiga 2016, ko? Kun ga kimanin, kidayar Shamsiyyah, kun ga kimanin shekara nawa ke nan? Ku ce min dari (100) cur, 1916 ba? Muna iya cewa ma dari (100) tunda nan da kwanaki kadan za mu shiga 2016. To, wannan hoton 1916 aka dauke shi, kuma mutane hululu suna tafiya da kafafuwansu za su je ziyarar Arba’in, saboda haka wannan abu dadadden abu ne ake yi.

ZIYARAR ARBA’IN MU A NAN SHI NE KARO NA 17

Na’am na san a nan dinmu Ziyarar Arba’in ya zama bako, domin wannan taro namu da muke yi na Ziyarar Arba’in, mu a nan shi ne na goma sha bakwai da muke yi. Ina da hotunan na farko din da muka fara yi. Idan mutum ya gani, zai gan mu ’yan gomomi ne. Muka yi ma ba wutan NEPA muka dauko irin fitilar nan mai Batir, muka kwana da shi muka yi. Muka karanta Ziyarar Arba’in, amma Ziyarar Arba’in ya shiga habaka, ya shiga habaka, ya shiga habaka, har ya zo abin da yanzu kowa ya san ana Ziyarar Arba’in.

ZIYARAR ARBA’IN SHI NE TARO MAFI YAWA NA BIL’ADAMA A DORON KASA

Kuma Ziyarar Arba’in ya zuwa kabarin Abi Abdullahil Husain, yanzu ya zama taro mafi yawa na Bil’adama a doron kasa. Duk shekara kara yawa yake yi, sai dai a kiyasta mutane, ba a kidaya su ba. A bara an yi kiyasin a kan Miliyan Arba’in suka je, to bana kuma… ni ban ji kiyasin ba, amma na san tun kwanaki da yake akwai wasu canaloli da suke nuna yadda ake tafiya, an kwashe wajen kwana arba’in ana tafiya da kafa zuwa kabarin Imam. To, kun ga an sami tafiyar da ta fi kowanne tsawo, wanda mutane suka taso daga Mashhad da kafa, nisan kilomita 1700. Da ana ganin Basra ita ta fi nisa, nisan kilomita 600, yanzu an samu wanda ya nunka dari shida din, har ya dora. Taron arba’in ya zama taron da ya fi kowanne yawan Bil’adama a doron kasa yanzu. Don haka ne ma muka ce; mu a nan ya kamata mu ma mu nuna akwai magoya bayan Imam Husain.

Na’am na san yanayi na rayuwa ya sa mutanenmu ba su tafi da yawan gaske zuwa ziyarar Imam Husaini a Karbala ba, kadan sun tafi. Abin takaici shi ne; bana ba a nunka na bara ba a wadanda suka tafi, sai ya zama kamar wanda suka je ne, kamar na bara ne, kamar mutum dari da hamsin (150) suka tafi daga nan suka hadu da ’yan Nijeriyar da suka je daga sauran kasashe, suka kai dari biyu da wani abu. To, kuma da yake kowane gungu ana ba su dama su shiga cikin harami din, kodayake ba sun tafi duk gungu daya bane, akwai wanda aka ba su dama suka shiga jiya karfe goma sha biyun dare a can, karfe goma ke nan a nan, yau ma akwai wanda suka shiga yau, suka kuma ziyarci Abul Fadl Abbas, har ma sun aiko da sako cewa; yanzu suka fito (dazun nan da safe). To, haka nan, amma a nan na san yanayi ne ya sa ba a iya zuwa ba. Har wani lokaci a nan Husainiyya nake cewa; da za a ce za a zo da Jirage, a ce; to, Bismillah, wanda za shi Karbala, da ya ka gani Malam? Ya yiwu yanayi ne ya sa ainihin ba a iya zuwa ba. Amma da da hali, kowa zai so ya je.To, insha Allahu mu ma a nan kamantawan da muka yi na tattaki zuwa taron arba’in, muna fatan Allah ya sa mu yi musharaka da wadanda suka taka zuwa Karbala.

Za mu ci gaba insha Allah.