AlmizanAlmizan logo
Juma'a 2 ga Zulhijjah 1435 Bugu na 1150 ISSN 1595-4474


Tunatarwa

Raya Ashura da Tattaki ibada ne

In ji Shaikh Zakzaky


Shaikh Zakzaky
An bayyana taron Ashura da duk abin da ya shafe shi, kamar majalisi, tattaki da sauransu, a matsayin ibada a cikin addinin Musulunci. Shaikh Ibraheem Zakzaky ne ya bayyana haka ranar Asabar da ta gabata a Husainiyya Bakiyyatullah, Zariya a lokacin da yake gabatar da jawabinsa wajen taron kwana daya da aka shirya domin shirye-shiryen tarukan Ashura da tattaki na bana da ke tafe...

“Tattaki da zuwa taron Ashura duk Ashura ne. Mu a wurin mu ibada ne. Saboda yana daga cikin raya al’marin Ahlil Baiti, ‘rahimallahu man ahya amrana’. Kuma sun umurce mu ne da yin jaje na Ashura da yin kuka, domin shi a karan kansa ibada ne, wanda ana yin sa domin kashin kansa, ba domin wata manufa ba, yin kuka saboda kukan, da jajantawa saboda jajantawa, da bakin ciki saboda bakin cikin, shi a kashin kansa, ba domin ya biya wata bukata ba, domin shi a karan kansa ibada ne,” in ji Shaikh Ibraheem Zakzaky.

Ya ci gaba da cewa jajen Ashura umurni ne, “an umurce mu daidai wannan lokacin mu tuna, mu yi kuka. Kamar yadda aka samu wani iyali a cikin garin Zariya, nan gidan Alhazawa. Aka ce su a gidansu sukan rinka haduwa, mutanen gidan, kwana 10 na Almuharram a jere, su hadu su zauna su yi kuka. Da aka tambaye su, sai suka ce su abin da suka gada daga wajen kakaninsu ne; aka ce masu in Almuharram ya kama har ya kai 10, su rika zaunawa ana kuka, shi ke nan kuma suna yi. Haka aka gada a gidansu kuma ana yi.”

Shaikh Zakzaky ya kuma bayyana cewa, bayan yin kukan bin umurni ne, kuma yana da lada mai yawan gaske, “ya zo a riwaya cewa digon hawaye na kokawa saboda Abi Abdullahil Husaini (AS), digon hawaye ya isa ya bice wutar jahannama. Kuma da cewa kurar da ta tashi ta kakkaba a kafar da aka yi tafiya domin jajanta Abi Abdullhil Husaini, wannan kurar ba za su taba haduwa da wutar jahannama ba.”

Haka kuma Shaikh Zakzaky ya bayyana cewa wadannan taruka na Ashura, bayan ladan da suke da shi, akwai kuma wani hadafi na musamman da ke tattare da shi. Ya ce, “manufarsa shi ne raya wannan al’amari a zukata. Idan zuciya ta rayu da jin abin da ya faru da Ahlul Baiti, wanda ya tattaru, ya alamtu da waki’ar Karbala, da dacinsa a zukata, yana hada mutane da tarbiyyar wannan gidan, da wannan addini na Manzo (S), wanda aka yi kokarin a kawar.”

Shaikh Zakzaky ya ce shi ya sa wadannan makiya addini suke damuwa da yadda ake taruwa ana kuka game da wannan abu da ya faru. Ya ce suna damuwa ne domin sun san cewa, idan ana wannan taruwa ana kuka, to tamkar raya al’amarin ne, alhali su kuma suna so a manta da shi ne, domin in ba haka ba, meye nasu na damuwa idan ana kuka?

Sannan kuma Shaikh Zakzaky ya ce, akwai wasu amfanunnuka da dama wadanda mutum cikin hikimarsa zai iya ganowa, “lokacin da ake yi, lokacin ake fahimtar abubuwa da dama, daga wannan mutane za su fara tambaya, shi ya sa ma akan debo kowane irin nau’in mutane a tafi tare, sai ya zama abin ya ba su sha’awa, sai ya zama kofar fahimtar abubuwan da suka faru ke nan,” ya ce.

Shaikh Zakzaky ya ci gaba da cewa yadda al’amarin Ashura ke daukaka cikin dan gajeren lokaci, abin na bayar da mamaki, “wanda yake ’yan shekaru kadan baya babu shi ne samsam.”

Tun farko a cikin jawabin nasa, Shaikh Zakzaky ya fara ne da kawo wani hadisi na Imam Ali, inda yake cewa, ‘na yi maku wasiyya da tsoron Allah da tsara al’amuranku’.

Shaikh Zakzaky ya ce, “tsara al’amura wani abu ne da aka san al’ummar musulmi da shi. Lokutansu tsararru ne, suna da hamsu salawat wadanda suke tsararru, kuma duk sallolin nan suna da nizami, nizamin raka’o’i, har da yadda ake gyaran kuskure. Kuma komai na rayuwar musulmi wani abu ne tsararre, za ka gan shi tiryan-tiryan. In mutum ya ga musulmi suna huldodinsu na addininsu, zai ga wani tsari ne zaunanne.”

Daga nan ya ci gaba da bayyana cewa, cikin ikon Allah sai ya sanya a cikin musulmin ma, ’yan uwa da ke wannan gwagwarmaya, suna gudanar da al’amuransu cikin tsari, ta yadda hatta makiya ma suna yabon mu da cewa mun iya tafiyar da harkokinmu cikin tsari, “alal misali, shekarun baya da wasu ba’adin ’yan uwa da suka zo daga Iran, suka yi musharaka da mu a Nisf Sha’aban. Da aka fito sun yi ta mamakin yadda suka ga mutane ba sa turereniya, kowa na tsaye a inda yake, ana wucewa. Har suna cewa in su ne, ai da wuyan gaske a tsaya.”

Ya ci gaba da cewa, idan aka kwatanta yadda muke da tasari, da kuma yadda sauran al’umma ke gudanar da harkokinsu, lallai mu kam muna da tsari, “ko wadannan da suka zo maulidin Imam Ridha (AS), sun yaba da abin da suka gani tun a taryar da aka yi masu a filin jirgin sama, har suka kwatanta da Hizbullah. Suka ce wannan tsari kamar na Hizbullahi? Taryar filin jirgin sama ke nan. Da kuma suka zo suka ga sauran abubuwa, duk dai abin ya bubburge su.”

Sai dai kuma Shaikh Zakzaky ya bayyana cewa duk da an san mu da nizami mai kyau, amma har yanzu mu kuma ba mu ganin mun kai yadda ya kamata a ce mun kai, “abin da ya kamata ya zama shi ne, shi nizami, ba sai an ce maka ka yi kaza ne ba, ya kamata ka san abin da ya kamata ka yi ne, shi zai zama abu ya tafi yadda ya kamata. In kowa ya san abin da ya kamata ya yi, kamar yadda nake ba da misali da salla, ba sai an zauna an koya wa mutane yadda za su yi ba.”

“Idan ka zo za ka bi salla, babu bukatar ka ce Liman a raka’a ta nawa yake, za ka kabbara ne kawai ka bi, lokacin da Liman ya sallame ka san meye ya rage maka, za ka tashi ka yi abin ka. Saboda tsararren abu ne, kowa ya riga ya san abin da ya kamata ya yi, ba sai an gaya masa ba. To, haka nan ya kamata ya zama duk al’amuranmu, ba wai sai an tsaya an ce maka yi kaza, bar kaza ba, sai ya zama kawai kana yi ne, ka riga ka san abin da ya kamata ka yi ne.”

Shaikh Zakzaky ya ci gaba da cewa, yana da muhimmanci mutane su sani cewa ya kamata ne su yi abin da ya kamata su yi, ba wai sai abin da aka umurce su ba, “nakan ji wani lokaci sai in ga in ta gini, ana wargaza mani da ‘MALAM YA CE’. Ba Malam ya ce ne ake yi ba, kai ba ka san abin da ya kamata ka yi ba ne? Kana da hankalinka, ka san abin da ya kamata ka yi, shi ya kamata ka yi, ba a ce maka Malam ya ce ba.”

Ya ci gaba da cewa shi mutum ya kamata a ce ya san abin da ya kamata ya yi a kowane yanayi, ya zama jikin mutum cewa ya san abin da ya kamata ya yi, “kowane lokaci, da hankalinka da komai, in abu ya taso ka san abin da ya kamata. Kuma wannan ginin tarbiyya ke koyar da shi.”

Ya ci gaba da cewa shi ya sa wani lokaci su mahukuntan kasar nan idan suka ga muna taro, su kan dauka kamar mu ‘crowd’ (taron kawai) ne , “jami’an tsaronsu, abin nasu yana ba ni mamaki, kullum suna mana kallon mu ‘crowd’ ne. ‘Crowd’, su ne wadanda suka tattaru a kan titi. Kamar idan mutum ya zo yana wasa da maciji a bakin hanya, yana buga ganga, yanzun nan za ka ga jama’a sun taru. In ka duba a taron nan, kowa abin da ya fito da shi daga gida da inda za shi, daban ne. Wani za shi cefane ne, sai ya ga maciji sai ya tsaya, wani kuma ya fito kasuwa za shi gida sai ya ga maciji sai ya tsaya….”

Saboda haka su wadannan, taron su ne ‘Crowd’, ba ainihin tsararren taro ba ne, kowa da inda ya fito da inda za shi, ba su da hadafi daya, kawai a nan ne dai aka ci karo da maciji aka tsaya ana kallo. Komai yawansu, ba al’umma ba ne su, ba tsararrun jama’a ba ne, ba kungiya ba ce, ba su da nizami. To, in sun gan mu muna taro, sai su dauka wai ‘crowd’ ne.”

Shaikh Zakzaky ya ci gaba da bayyana ‘crowd’ da cewa wani abu ne da ba shi da jagora, kuma abu ne da ya fizgi mutane, “saboda haka idan mutane suna zanga-zanga, to wadanda a kan titi suka hadu ne. Don haka mu ba zanga-zanga muke yi ba, muna muzahara ne, muna bayyana wani abu ne. Zanga-zanga an rude ne kawai aka hadu a bakin titi, to wanda ya iya yanka ihu, shi zai jagoranci tafiyar. In ana cikin tafiya wani dan sanda ya zo, sai ya ce ‘a buge shi!’ Nan da nan sai ka ji kakakau. Wani ya ce ‘ku daina ya isa haka nan!’ Wani ya ce ‘kashe shi ya kamata a yi!’ Wannan shi ne ‘crowd’, shi kawai ba shi da jagora, ‘Emotional’ ne kawai, kana iya juya shi yadda ka so ka juya.”

Sai Shaikh Zakzaky ya ce abin takaici, “su jami’an tsaro har yanzu suna kallon mu ‘crowd’ ne, sai su zo yanka ihu, ta nan ne ma muke gane jami’in tsaro. In ka ji mutum ya yanka ihu, ‘Malam ya ce, a yi kaza ne!’ to dube shi da kyau, za ka gan shi, ko da gemun roba, ko kuma ba shi da shi ya share, wato dama daga bariki ya zo. Wai shi ya dauka ‘crowd’ ne zai ja ‘crowd’ din ya fizge shi ya bi inda ya ga dama.”

Daga nan sai ya bayyana cewa, mu duk inda aka gan mu, to ba haduwar wannan ranar ba ce, haduwa ce da ta kwashe shekara da shekaru ana samun tarbiyya, “saboda za ka ga taro ne kowa ya san abin da ya kawo shi, ya san me yake yi.”

Haka kuma Shaikh Zakzaky ya bayyana cewa duk yabon da ake mana na cewa muna da tsari, to ba wai ba mu da matsaloli ba ne, muna da matsaloli, “daga ciki akwai cewa muna karuwa, karuwar kuma da yawan gaske. Baki na shigowa, suna shigowa kuma da yawa ne, kuma za su zo ba su da tarbiyya. Idan aka samu mutane suna da tsari, kamar su 20, sai aka samu baki guda 2 suka shigo, to su baki biyun nan za su yi abin da suka tarar da ashirin din nan suna yi ne, ba za su fita daban ba, za su yi kokari ne su saje da ashirin din.”

“Amma idan ana da ashirin, sai arba’in suka zo baki, to yanzu za su zama jagorori, saboda su wadannan ashirin din za su zama kalilan. In an zo, wannan arba’in za a gani. Saboda haka zuwa da mutane suke yi da yawa, suna zuwa da rashin tarbiyya, tunda su ba sun tarbiyyantu ba ne da abin da ake yi ba,” in ji Shaikh Zakzaky.

A nan ne ya kawo misali da batun tattaki, inda ya nuna dole za a kwashi wasu ne a hanya, kuma za su shigo ne da wani abin da sai an yi ta fama da shi, ana gyara masu tare da nuna masu abin da ya kamata a yi, tun da ba sun gogu da abin da ya kamata a yi ba ne. “Kuma in suka yi yawa suna iya haddasa wasu abubuwa, za su yi wani abu wanda in aka gani, sai a ce su wadannan da suke wannan tattakin, su suka yi wannan abin,” Shaikh Zakzaky ya ce.

Ya ci gaba da cewa, akwai kuma matsala irin ta masu suka, wadanda ya ce su dama ba abin da suke nema illa su ga an yi kuskure, su yi suka a kai, “kullu yaumin su kuma, abin da mutum daya daga cikin mu ya yi, shi ne duk cikar mu muka yi, kodayake na san wannan rashin adalci ne. Da za a ce zai zo ma mutane fes-fes-fes, sai ya ga kazami guda daya, sai ya ce duk kazamai ne, saboda dama ba ya son abin. Suna yi mana wannan, in mutum daya ya yi abu, sai su ce duk cikar mu muka yi,” in ji Shaikh Zakzaky.

Ya kuma ce, wani lokaci wasu abubuwan da suke fada da gaske ne, amma ba abin da ake yi ke nan ba, amma saboda dama su sharri suke nema, sai su mayar da hankalinsu wajen sharri, su ki kallon alherin da ake aikatawa, “wani lokaci ma sukan ce, Shi’a kaza suka ce. Sai a shafa ka ce yaushe suka ce haka nan? In abu kaza suka ce, ya kamata ya zama ko duk cikarsu haka suke cewa, ko mafi yawansu, amma sai ka samu wani ne kawai ya ji ya fadi maganar, sai ya dauka kawai ya dora ma kowa da kowa,” ya ce.

Saboda haka sai Shaikh Zakzaky ya ce, amma duk da haka bai kamata a ce an ba da wata kafa ta yadda mai suka zai samu abin suka ba, “na san ba za mu iya ma masu suka ba, domin su kullum duk abin da muka yi suna suka ne, amma daidai gwargwado bai kamata ya zama shi mai sukan, kai ma ka ba shi damar ya yi suka ba. Kamar yana sukan wani abu, a zo a ga wani abu mai kama da haka nan ba. Amma in ba a samu ba, in ya yi suka, shi kenan ya yi abin shi, babu damuwa. Idan mutum ya soke ku da kazanta alhali kuna da tsafta, ai bai kamata ku damu ba.”

Saboda haka sai Shaikh Zakzaky ya ce lallai a shirya, shiri mai kyau domin za a kwaso mutane a kan titi, “in aka kwaso su, to sai kuma an zauna da su, an koyar da su, lallai akwai bukatar zama da mutum wajen tarbiyyantar da shi,” ya ce.

Shaikh Zakzaky ya ce, don cimma nasarar wannan abu, akwai bukatar tsararren aiki, wanda daga cikin sa akwai rarraba ayyuka, ‘division of labour’, “wannan muhimmin abu ne, ya zama kowane aiki akwai mas’ulan sa. Akwai wani mas’uli da mataimakansa, ta yadda ba zai zama akwai wani na aikin wani ba, ko a yi karo ba.”

“Alal misali idan aka ce kula da tsaftar muhalli, sai ya zama a ce su wane ne da dakarunsa masu kiyaye tsafta, kamar yadda ake da bangaren kula da kiwon lafiya. Aka ce misali, samar da ruwan sha, sai a ce wane ne masa’uli, idan ba mu samu ruwa ba za mu ce wane, an san cewa wane ne aka dora ma alhakin. Abinci kuma wane ne masa’uli, kaza wane ne, kaza, kowane abu, kowane abu ya zama akwai masa’ulinsa, shi kuma da mataimakansa. Yana da muhimmanci ya zama kowane abu an tsattsara ne,” in ji Shaikh Zakzaky.

Sannan kuma ya ci gaba da cewa idan an ba mutum aiki, ya zama an ba shi kayan aiki, ta yadda zai hada dabararsa da wannan kayan aikin, domin a samu nasarar aikin da aka ba shi. Ya ce, “akwai kuma nizamin tsaro, tsaro din kuma iri-iri ne, akwai na boye, akwai na bayyane, duk za a sassa ido ya zama kowanne, tunda yake akwai makiya, akwai masu son su kurda su yi wani abu, akwai masu… ga sunan dai.”

Za mu soma kawo cikakken jawabin Shaikh Zakzaky a taron Mu’utamar na Ashura da Tattaki a mako mai zuwa.


Sanarwa

Sanarwa
Nan filin duk wani sanarwa ne daga duk bangarorin Harka Islamiyyah

  GAYYATA ZUWA MAKON IMAM KHOMEINI
  Imam KhomeiniDandamalin Dalibai da Malamai na Harka Islamiyyah (Academic Forum) na sanar da dukkan ’yan uwa cewa za a yi Makon Imam Khomeini na bana, wanda za a fara daga ranar:
  Juma'a 30 ga Mayu 2014 zuwa Laraba 3 ga Yuni 2014

  Masu Jawabi: Akwai Malamai da masana daban-daban da za su gabatar da lakca, ciki har da Jagoranmu, Sayyid Ibrahim Zakzaky (H)

  Wannan gayyatar na kowa da kowa ne. Allah ya ba da ikon halarta
  Za mu buga jaddawalin nan gaba kadan in sha Allah.


  Labarai cikin hotuna

  Hotunan YAUMUL MAB'AS na bana

  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asMalam Zakzaky yana jawabi
  • Yaumul Mab'asMalam Zakzaky yana jawabi
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron