Almizan: Jarida don karuwar Musulmi

AlmizanAlmizan logo
Juma'a 1 ga Sha'aban 1435, Bugu na 1131, ISSN 1595-4474


Tunatarwa

Ba wata tsiya wai ita Boko-Haram


Shaikh Zakzaky
Wannan wani bangare ne daga karshen jawabin Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), da ya gabatar ga dandazon dubban ’yan uwa da suka halarci taron Yaumus Shuhada a ranar Asabar 25 ga watan Rajab, 1435 (24/5/2014) a filin Polo da ke kusa da Husainiyyah Bakiyyatullah, Zariya. Ammar Muhammad Rajab ne ya rubuto muku. A sha karatu lafiya...

DANGANE DA MASU TSAREWA

To, shi kenan, sai kuma dangane da su masu (tsarewa), tunda na ma fara taba, da tunanin cewa; su ba su da wani aiki illa su yi harbi. Mukan yi muku nasiha, don kuna da hakkin mu yi muku. Su mahukunta, kamar yadda su mahukunta dauri suka yi, ainihin suke ganin da karfin tsiya za su kawar da bayin Allah, haka ma na yanzu suke tunani. Kuma tunaninsu iri daya ne. Ba su daukar darasi daga abin da yake faruwa daga karshe. Ina mulkin Banu Umayya? Ina na Banul Abbas? To, kun ga yanzu me ya rage?

Lokacin da shi wannan Harun din nan zai cika (makashin Imam Kazim), sai ga shi da bakinsa yana cewa; “ma’agna anni maliyya, halaka anni suldaniya.” Da wadannan kalmomin ya cika. Shi da bakinsa ya fada, ya yanke ma kansa hukumci. “Dukiyata ba ta tsinana min komai ba, sarautar tawa ta riga ta kai karshe.” Khalas! Ina sarautar? Shi da kansa, yanzun ga shi ya ga zai mutu, ya kanjame, ga shi yana jiran mutuwa ne. Mutuwa kawai yake jira. Yanzun ana cewa; ranka ya dade ya kaza? Yana cewa; “kai, yanzu ni ta kaina nake. Yanzu dukiyata ba ta tsinana min komai ba, kuma ga shi mulkin nawa ya kare.” Ina dadin da ya sha? Ina shagulgulan da ya yi? Ina hamshakan fadojin da ya gina? Ina sauransu, ina sauransu? Duk ba su tsinana masa komai ba.

An ce wani Sarki na Banul Abbas, ya taba mutuwa, sai ana ma dansa mubaya’a, sabon ‘Suldani’. Aka ajiye gawar, in an gama mubaya’a za a zo a yi jana’iza. Sai wani, ko Zomo ne wanda ake kiwo, ina jin ko kyanwa ce, ko wani abu mai kama da haka nan, wanda suke kiwo a Daji (a lambun Sarki), ya zo ya sami idanun Sarkin ya ciccire ya cinye su. Ko da aka zo, Sarkin Musulmi ba idanu. Shi ke nan zancen. Duniyar ke nan. An gama. Saboda haka ku ma taku haka za ta kare.

Saboda haka kuna da hakkin mu yi muku wa’azi, cewa; ainihin wannan abin da kuke aikatawa, ba zai tsinana muku komai ba. Mulki ne zai gushe ‘lamuhalatan’. Hatta na magidantanku. Dan abin da kuke samu na dukiya, wanda suke ganin ana ba su dukiya su yi komai, shi ma zai kai karshe. Eh, zai kai karshe. Amma Shahidai su ko kuna raya su ne. Amma kuma Harka din da kuke fatan ku ga karshenta, to, kun yi kadan! Dashen Allah ba abin da yake iya tumbuke shi. Wannan al’amari, insha Allahu, Allah ya riga ya ga daman ya kafu, kuma sai ya kafu daram! Saboda haka ku ku yi naku. In da abin in ba ku shawara ne, sai mu ce; ku yi abin da ya fi alheri ne gare ku a lahirarku. Amma in ba ku ji ba, duk abin da za ku yi, ku yi! Duk kulle-kullen da za ku yi, ku kukkulla, kada ma ku saurara mana, ku yi ta ta yi! Insha Allah ba abin da za ku iya tsinanawa, sai abin da Allah ya kaddara! Shi ne!

Kar wani kuma wanda yake da rai, wani abu, wai shahada ta ba shi tsoro. Don Allah an taba maka barazanar za a kai ka Aljanna? Sai a kai ka Aljanna ka ji dadi. An taba maka barazana haka nan? In mutum ya ce; sai in kai ka Aljanna ka sha shagali. Me za ka ce masa? Kai ni! Eh, mana! Har a yi mana barazana da kyakkyawar ‘akiba,’ alhali burinmu ke nan? Kai da kake ma’aikacin tsaro, wanda suke amfani da kai, inda za mu yi maka addu’a, ko da ka zama babba, ko da ko ‘officer’ ne kai, ka kai Janar, inda za mu ce in kai dan Sanda ne, ka kai Kwamishina ko ‘I.G’ ma, mu ce; “Allah ya sa ka mutu kana dan sanda.” Za ka ce; wallahi ba mu son ka. Inda za mu ce; “Allah ya sa ka cika kana Soja.” Zai ce; wallahi ba ka so na. Fatan sa shi ne; ya bar Soja. To, mu ka yi mana addu’a, ka ce; “Allah ya sa mu cika muna gwagwarmaya.” Za ka ji mun ce; Masha Allah! Babban burinmu ke nan! Allah ya sa mu cika muna gwagwarmaya. Yawwa! Ka gani, duk abin da muke so ke nan.

To, in wani dan sanda ya isa, ya ce; Allah ya sa ya mutu yana dan sanda. Inda jami’in tsaro a nan, ya ce; Allah ya sa ya mutu yana jami’in tsaro. Ka ga ba ya fatan haka nan. Ko yana burin wannan? To, kai ina kai, ina fada da abin da, kai naka zai gushe, kake fada da wanda yake zai tabbata? Naka kamar ya zo ya wuce. Amma dai ya rage muku, shi ke nan dai. Nasiha ce, kuma kuna da hakkin mu yi muku. Kuma mukan yi muku.

MAMAYAR AFRIKA

Kun ga yanzu muna fuskantar wani abu a kasar nan. Da ma can na sha wannan maganar cewa; akwai wani abu yana nan tafe. A wa’azuzzuka daban-daban na ambata wannan. To, akwai wani abu na tafe, shi ne; mamayar Afrika. Wanda suka ce, sun yi nazari sun ga cewa; karnin da za a shiga (tun kafin ma a shiga), tun kafin a shiga karnin nan, 2000 din nan. Tun a 1900 suke fada. Suka ce; karni na gaba, sunansa KARNIN AFRIKA. Domin sun yi nazari sun ga cewa, Afrika na da kusan kashi biyu bisa uku na dukkan dukiyan da ake da shi a duniya. Saboda haka za a sake kama Afrika na biyu. Sabon rububi. Abin da aka kira ‘scramble for Africa’. Suka ce za a yi ‘second scramble’. Za a yi sabon rububi. Lokacin rububin Afrika na wancan karon. Tsakanin daulolin Turai, Ingila da Faransa da Jamus da Italiya da Portugal da Belgium, duk kowanne, wannan ya kama nan, wannan ya kama nan, wannan ya kama nan. Har suka je Berlin, suka yi ‘conference,’ aka raba. Kowa ya fadi inda ya kama, aka tsaga, aka ce; kowa ga nasa. To, sun ce za a yi wannan karon.

To, sai kuma Amerika ta zo ta ambata ta ce; za ta yi amfani da ta’addanci wajen sake kama Afrika. To, shi ya sa kuka ga wannan abin da yake faruwa yanzu. Sun yi a Libya. Bayan lokacin da suka ji dagowar Larabawa din nan, da dagowar Misra, abin ya firgita su, suka ce, to, su ma bari su yi nasu. Sai suka yi a Libya. Suka je suka rugurguza Libya din, suka kashe Gaddafi. Yanzu ba komai da ke gudana a Libya banda kashe-kashe da fada na kabilanci tsakanin ‘Militia’ da kabila, da na wariyan launi. Su ko suna diban dukiya.

To, da ma da Libya da Nijeriya, an ce su su ke da mai din da ake ce masa mai zaki, (sweet crude). To, na Libya yanzu da ma nasu ne. Na Najeriya da ma nasu ne, tunda suna samun gaulaye ne su ajiye. Kullum ba su da wani aiki, sai dai su samo wani Gaula su ce shi ne Shugaban kasa, su samo Dolo su ce shi ne Mataimakinsa, su sami Gabo su ce shi ne Gwamna, su samu Wofi su ce shi ne Minista, su sami, ga sunan. Su yi ta tatsan arziki din.

Shaikh Zakzaky

SALON MAMAYAN KASA

To, yanzu kuma sai suka zo da wani salon, mamayan kasa. Saboda haka suka shirya suka mamaye Mali. Yanzu, ko shekaranjiyan nan a labaru suna cewa; an fafata a Kidal da Gawo da wadansu ’yan bindiga. Haka kawai za su bayyana a unguwa, su yi ta zubar da wuta. Ba ka san wa ake harbi ba. A ce ai wasu ne masu kishin Islama ne suka bayyana ana fafatawa. Alhali Mali, Zinariya suka gano a Mali. Zinariyar da ba a san inda take ba tun tuni. Don dama ana da labarin akwai Zinare a Mali. Mansa Musan nan, wanda ya yi tafiya zuwa Hajji, wanda ya shiga tarihi. Wanda aka ce, ya tafi da Rakuma dubu dauke da kayan Zinare da Bayi dubu; kowanne yana dauke da Sandan Zinare. Da ya je Misra, Zinaren da ya kai Misra sai da ya sauke farashin Zinare, da har yanzu bai tashi ba.

Da ya je Makkah ya yi gine-ginen da sai kwanan nan ne, Ali-Sa’ud suka rusa wasu. Suka rurrusa suna gine-ginensu a gewayen Harami. Amma har ya zuwa ’yan shekarun baya gine-ginen Mansa Musa abin kallo ne. To, Gwal din nan ba a san inda yake ba. An san akwai Gwal. A ina ne ma Mansa Musa ya yi fada? Ba a sani ba. Ko su ce, NAR ne, ko su ce Niani, ko su ce kaza ne, Bil ne, a je Bil a shafa ba a gani ba. A ce wannan garin ne, a je ba za a gani ba. To, yanzu sun gano Gwal din, saboda haka, suka tsara yadda suka mamaye Mali. Suka ce ’yan kishin Musulunci ne suka fada daga Aljeriya. Ba dan Mali ko daya a cikin su. Wai sun kama rabin Mali, fiye ma da rabi, sun kafa daula wai sunanta ‘Azwad’. Sannan sai Faransa, maza wuf ta shiga, wai ta fatattake su. Ta riga Amerika shiga. Don Amerika ita ta shirya shiga. Wai sun fatattake su.

Bayan wannan, sai Faransa, akwai ‘Diamond’ a Central Africa, shi ne; sun je diban ‘Diamond’ ne sai suka hada fada. Wadansu mutane da ba a san ko su wanene ba, wai su Saleka, suka shiga cikin Central Africa Republic, suka yi ta kashe Kiristoci, suna kona Cocina da sunan wai su Musulmi ne. Sannan su ba ’yan Central Africa Republic ba ne. Suka fita kasar. Bayan sun fita Afrika ta tsakiya, sannan sai suka kawwana Militia na kirista wai su Anti Balaka. Sai suka bi suna kashe musulmin da suke zaune a kasar. Wai suna ramuwar gayya. To, in ma wadancan Saleka sun zo sun kashe ku, ’yan kasar ku ne? Daga wani wuri fa suka shigo, suka kuma fita. Wai ma su suka fara.

Kamar yadda suka yi juyin mulki a Mali, suka yi wani wai shi Sanogo ya zama Shugaba. Wai shi ya yi juyin mulkin a kan cewa, shi Sulaimanu Traore ya kasa ima ’yan tawayen Arewa. Sai kuma aka ce, ’yan tawayen Arewa din ma sun kwace kasar gaba daya ma a karkashin shi Sanogo din. To, nan ma na Jamhuriyar Afrika ta tsakiya, sai aka ce, wai wani musulmi ya yi juyin mulki na soja. Wai sunansa Michael Djotodia. Kun taba jin sunan musulmi Michael? Wai Musulmi ne, amma sunansa Michael Djotodia. Wai Djotodia Michael ya kwace mulki. Wai shi musulmi ne. Ya za a yi Musulmi ya zama Shugaban kasar da mafi yawa Kirista ne? (Haka suke cewa). Ashe haramun ne Kirista ya zama Shugaban kasa a kasar da yake mafi yawan su Musulmi ne. Shi ne har aka samu Kiristoci suka zama shuwagabanni a Najeriya? Da wannan suka fake, suka je suka shiga cikin Central Africa suna ta kashe Musulmi, musamman Fulani makiyaya wadanda ba su ji ba, ba su gani ba. Diamond suka je diba.

Kudancin Sudan da suka ga ba zai yiwu su kai ’yan kishin Islama ba ne, sai suka hada fadan kabila tsakanin Dinka da Noer. Amma shi ne, hana ma China Mai. Ya zama tunda dama Kudancin Sudan suna dasawa da China, ya zama ba su tare da China.

Najeriya kuwa, shi ne suka bullo da wani abu wai shi Boko-haram, wanda tuntuni wasu ba’adin Amurkawa sun riga sun ambata, sanannen abu ne cewa, ba wani abu wai shi Boko-haram, kirkiran Amerika ne.

To, yanzu ga shi wai Boko-haram sun sace wasu ’yan mata a wata Makaranta, amma su ’yan matan da iyayensu sun san su wa suka sace su. Sun sani sarai, gwamnatin Jonathan ce. An ce ana ta zanga-zanga, na ce; wai ana zanga-zangar me ne? Har da jan kaya. Ina jan kayan ya fito? Wai ku ba mu ’yan matanmu. Wa zai ba ku? Jonathan ko Shekau? Idan Jonathan ne zai ba ku ’yan matanku, eh, to, ku yi masa zanga-zanga ya fito da ’yan matan inda ya san ya ajiye. Don ya san Barikin Sojan da ya ajiye su. Idan ko Shekau ne, kun san a wacce sheka yake? Yaushe yake jin ku? Yana nan shi ma suna tsare da shi a wani Barikin Soja. Don kayansu ne duka. Ba wata tsiya wai ita Boko-Haram, karyar tsiya ce kawai. Wannan iskanci din ba mu za a yi wa ba. Idan kuna so ku zo ku diba Mai, ku diba Zinariya, ku diba arziki, ku zo a yi ciniki. Ko da cinikin ‘Muzabanah’ ne. Mu ba ku kwai, ku ba mu kaza. Ko, mu ba ku Rakumi, ku ba mu Rago. Mun yadda gara haka nan. Amma kwa zo ku yi mana iskanci da addininmu. Ku ce mana muna fama da musulmi masu kishin addini, kun zo ku cece mu. Alhali mun san kun zo ku cuce mu ne.

Shaikh Zakzaky BOKO-HARAM SUN SHIGO NA SOSAI, SU NE AMERIKA

To, ga Boko-haram din sun shigo na sosai, su ne; Amerika. Suna shigowa ko, yalai sai kashe-kashe. Sai tashe-tashen bama-bamai. To, kuma wannan irin sa fa suka yi a Afghanistan ko kuma suke yi har yanzu. Kuma irin sa suke yi har yanzu a Irak. A Afghanistan suna da filaye gomomi ne na filayen jirgin sama suna kwasar dukiyoyi, da sunan suna yaki ne. Asali sun shiga da cewa; suna neman Bin Laden ne. Ba a san inda Bin Laden yake ba. Can kuma suka ce; Bin Laden din ma sun kashe shi a wani wuri ma ba a Afghanistan din ba. To, suna mene ne a Afghanistan? Har yanzu suna nan.

Irak ko suka shiga suka ce akwai WMD (Makaman kare dangi). Suka rugurguza Irak. Suna ta cewa; za a ga WMD din. Har suka kamo Saddam ma, har cocila suka kunna suna kallon bakinsa, in ma WMD din yana cikin bakin Saddam ne, duk sun dudduba. Sai suka juya kuma wai suna kai musu Dimokradiyya ne. Yanzu kuma sun ce ba WMD, amma ba su bar Irak ba. Suna nan suna tatsar dukiya. Kullum sai tashe-tashen bama-bamai da kashe-kashe. Kuma su suke yi. To, yanzu tunda suka shigo nan, mu ma abin da suka yi mana shiri ke nan. Haka kawai mun wayi gari abin da muke jin labari a wasu kasashe ya zo mana bagtatan. Mun tabbatar ba wata kungiya wai ta kishin Islama, wai wadda ake ce mata wai Boko-Haram. Mun tabbatar ba ta. Ba ta da wujudi sam-sam. A ina? A wane gari? A wane titi? A wace unguwa? Amma bama-bamai na tashi. Su suke sa bama-baman nan. Ko su haka rami wawukeke su saka, su binne ko su matsa ‘remote,’ ko su zo da Mota su ajiye su danna. Aikin kenan. Ko mutane su bayyana, su bude wuta. Saboda mene? Dukiya suka zo diba.

A tsakanin Zamfara Zinare ke kwance, suna so su share Eriyan da Zinare yake ne, ya zama ba mutum ko kadan, su yi filin jirgin sama, su yi sansanin Soja, su rika kwasan Zinariya. Nan tsakanin Zariya da Birnin Gwari, Zinare ne yake kwance da duwatsu masu daraja. So, suke su share mutanen wurin, su kafa filin jirgin sama su kwasa. Tsakanin Sakkwato har zuwa Borno, daga Uranium sai Zinare sai Platinum. Shi suka zo diba.

To, ku zo mana a yi ciniki. Ko da ma ku ba mu Kaza mu ba ku Rakumi, amma ku bar mu da ranmu, kuma ku kyale mana addininmu. Amma mene ne na cewa; za ku shigo ne, da yi ma mutane wayayyu babarodo. Ina ku kuke da wayon? Yaushe aka yi Ba’amurke? Yaushe aka yi Bature ma tukunna? Wani wayo yake da shi? Eh mana. Dauko tarihin Bature ka karanta mana, badaje, maye, dan bori! Yaushe ya waye har da zai mana wayo? Rashin kunyan banza kawai. Ku zo a yi ciniki. Kuna da Bindiga mun sani, kun iya kisan kai, amma a kyale mana addininmu.

To, yanzu abin da ya kawo su kenan kuma yanzun musiban yana rutsawa nan da nan tsakanin ’yan uwa. Kun san a Gwoza, har ma sun rutsa da garin Gwoza, sun ce, ba za su shiga ba, saboda suna jin tsoron ’yan Shi’a. Don akwai wani dan uwa da suka kama suka cire masa kai, suka fille kansa sosai, amma sai suka ji kalma, kan na Kalmar Shahada. Suka duba, ga Kai yana ‘la ilaha illallah Muhammadur Rasulillah,’ ga gangan jiki din. To, shi ne suka ce; suna jin tsoron garin saboda ’yan Shi’a.

To, wannan abin da muke fuskanta ke nan. Kuma na san sun riga sun ambata tun tuni, abin da suke jin tsoro kawai ita ce; wannan Harka din. Don sun san ita ce kawai za ta taka musu burki. Amma muna ma kira ga su wadannan mutanen, mun ji an kira ka ba ka ci zabe ba, an ce kai ne kake da mukami, mun ji ba ka cancanta ba, mun ji kai Gaula ne, ko Gabo ne ko Sakarai ne ko Shashasha ne, ko Wofi ne, to, mun ji kai ne. Yanzu ko a haka nan, ka yarda yanzu a ba ka kudi a kashe mutanenka? Kai ba ka da tunani? Shi ke nan an ba ka mukami, an ba ka kudi shi ke nan a kashe mutanenka. Shirun ya isa ga al’umma. Kuma ba kyale ka za su yi ba; in sun gama da kai, in ka zama fanko, kashe ka za su yi. Haka suke yi. Saddam din nan da suka kashe, kayansu ne. Gaddafin da suka kashe, kayansu ne. Duk su suka yi su. Suka kama su, suka kawar da su. Kai ma in sun gama da kai, za su yanka ka ne, an gama.

Na san wannan, a munasabar Yaumus Shuhada muna da magana da yawan gaske ganin cewa; wannan abin da ya kunno kai a kasar nan lallai fa ya shafe mu. Kuma lallai kam fuskantar wannan da duk iyan abin da muke iyawa, aiki ne ga addinin Musulunci. Kuma wanda duk suka kashe a cikin mu sunansa Shahidi! Ban ce muku tunda su suna daukan Bindiga ne, mu ma za mu dauki Bindiga ne ba, amma muna da makamai irin namu. To, su zamu dauka insha Allahu.

Allah Ta’ala, muna rokon ka, ka nuna mana Yaumus Shuhada na badi cikin koshin lafiya da yalwar arziki. Allah Madaukakin Sarki ka kare mu da kariyarka, ka taimake mu da taimakonka, ka dora mu birbishin makiya.

Wasallahu ala Muhammadin wa alihid dayyibinad dahirin. Wassalamu alaikum warahmatullahi.


Sanarwa

Sanarwa
Nan filin duk wani sanarwa ne daga duk bangarorin Harka Islamiyyah

  GAYYATA ZUWA MAKON IMAM KHOMEINI
  Imam KhomeiniDandamalin Dalibai da Malamai na Harka Islamiyyah (Academic Forum) na sanar da dukkan ’yan uwa cewa za a yi Makon Imam Khomeini na bana, wanda za a fara daga ranar:
  Juma'a 30 ga Mayu 2014 zuwa Laraba 3 ga Yuni 2014

  Masu Jawabi: Akwai Malamai da masana daban-daban da za su gabatar da lakca, ciki har da Jagoranmu, Sayyid Ibrahim Zakzaky (H)

  Wannan gayyatar na kowa da kowa ne. Allah ya ba da ikon halarta
  Za mu buga jaddawalin nan gaba kadan in sha Allah.


  Labarai cikin hotuna

  Hotunan YAUMUL MAB'AS na bana

  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asMalam Zakzaky yana jawabi
  • Yaumul Mab'asMalam Zakzaky yana jawabi
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron