AlmizanAlmizan logo
Jum'a 16 ga Sha'aban, 1445 JBugu na 1445 ISSN 1595-4474


Tsokaci

DANDALIN IYALI - An yi walkiya

Daga Sakina I. Gwadabe (sakinatgwadabe30@gmail.com)


Ya Mahadi

Godiya marar adadi daga Amatul-Jaleel, zuwa ga Rabbil Jaleel, wannan da Ya sanya ni cikin bayinsa da Ya so jarabta a wannan takaitacciya, kuma rudaddiyar rayuwar duniya marar tabbas.

Ban mallaki wasu muhimman kalaman da zan yi amfani da su wajen nuna tsantsar godiyata ga Alhakeem, wannan da bisa tarin hikimarsa ne Ya aiko mana da waki’ar da ta yi sanadin gane masoyanmu na hakika da baragurbi, masu harshen damo da munafukai, algungumai, kinibabbu da kuma manyan makiya.

Hakika walkiya ta haska mana abokan cikin dangi, a lokaci guda kuma mun gano wadanda har abada mun yi hannun riga da su, tunda idanunmu na zahiri da badini a bude suke karr! Kuma ba mu daga cikin dolaye masu tafiya da ka!

Ku sani ya ku taron danginmu na jini, masu ikirarin bin Sunnah, wadanda kuke tausaya mana sakamakon batan da kuke zargin muna kai, ku ke jefa mu cikin wuta da bakunanku, ku ke jifan mu da kaulasan da shim-meruwa, ku ke mana kallon biyu-ahu, daga yau, mun yafe tausayawanku, ku ji da kanku! Ku shagalta da matsalolinku, ba mu bukatar tausayawanku, don muna da cikakken yakini a kan akidarmu, kai, ku saurara! Wallahi mu mu ke da tabbas da hakika! Idan kuma Aljannar taku ce, ba mu fatan ku tausaya mana ku sanya mu a cikinta, a lokaci guda kuma, kada ku yi sanyin jiki wajen jefa mu cikin wuta ranar mahshar, in har kuna da ikon hakan.

Walkiya ta haska, mun gane cewa ba wata da’awar Sunnah ta hakika cikin zukatanku, balle tsantsar ’yan uwantaka! A wace irin Sunnah ce, kuma sunnar waye ta koyar da ku kafirtawa, zargi, sharri, yada karya da murna a kan bala’in da ya aukar wa Musulmi? Kodayake kun ce gara Kirista da mu, duk da cewa mun yi imani cewa Allah daya ne, kuma shi muke bautawa. Mun yi imani da cewa Annabi Muhammad Manzon Allah (S) ne, Ramadhan muke azumta, tare da ku muke aikin Hajji, muna fitar da hakkin Allah (T) cikin dukiyoyinmu. Mun sha jaddada wannan, shin wane sharadi ne ba mu cika ba har ya sa kafiri ya fi mu a wajenku?

Bayan waki’ar 12/14/12/15 da wata guda cur, na je ga Mahaifiyata da nufin warware mata dukkan kullin makiya da suke ta yadawa (kamar da ma jiran waki'ar suke yi ta auku). Don ni kadai ce a zuri’arta nake bin tafarkin Sunnar Manzon Allah (S) da Iyalan Gidansa Tsarkaka. Na yi mata tambayoyi kamar haka: Hajiya ina ’yan uwana mazansu da mata? Ina zumuncin da ke tsakanin mu? Ina kyautatawa da tausayawar da ke tsakanin mu? Waye a cikinsu bai san bala’in da ya same mu a Zariya da lokacin Tattaki ba? Mutanen da ban taba zata ba sun min jaje, sai sune ban cancanta su yi min jaje ba? Ashe dama Hajiya hannunka na rubewa ka yanke ka yar?

Yanzu Hajiya da rashin kulawarsu gare ni ne zan fahimce su, na fahimci batan da suke zargin ina kai? Kuma na gano gaskiyarsu na fahimce su?

Ai Hajiya na yi zaton ko Kirista nake aure (Allah ya tsare ) aka ce an dasa bom, ko an kai hari a cocin da muke zuwa bauta, lallai ina sa ran za su bincika, kuma su tuntuba su ji ko harin ya rutsa da ni, a matsayina na ’yar uwarsu shakikiya.

Wadannan tambayoyi da ma wasunsu, sun sanyaya jikin Hajiyar, tare da kara tausaya mana fiye da tausayawar da ta nuna lokacin waki’ar. Kuma ta nuna rashin jin dadinta game da rashin kulawarsu gare ni.

Ganin irin karerayi da sharrukan da ake lika wa Shi’a, musamman dai bayan waki’a, kuma na san ba za su kasa isa kunnen mahaifiyata ba, hakan ya sa na bijiro mata da dukkan sharrin da ake jingina su gare ni, har ma wanda ba ta ji ba, na yi mata fashin baki, tare da kore dukkan shakkunta a kanmu, ta hanyar kawo mata kwararan hujjoji na shari’a da hankali, wanda a karshe muka rabu tana sa min albarka tare da ba ni hakuri.

Babban kirana cikin kakkausan lafazi da kakkarfar murya a gare ku ya ku danginmu cikin Sunna, shi ne, zagin wani ko wasu, ba ya daga cikin koyarwar addininmu. Kafirta Musulmi, bai cikin manufarmu. Fasikanci kuwa, shi ne babban abin kyamarmu. Mu matan Shi’a kuwa, wasu halittu ne masu tsadar gaske da tarin daraja ga mazaje! Shi ya sa ma kullum za ku gan mu cikin hijabi baki, ta yadda babu abin da wani namiji zai gani a tare da mu ya yaba, ko mu ba shi sha’awa, don ba mu fatan burge kowa sai mazajen aurenmu. Don haka adonmu ga mazanmu ya kebanta kadai, bisa koyarwar Manzon Rahma (S) da Iyalansa. Don haka mu matan Shi’a na musamman ne sabanin wasunmu.

Walkiya ta haska, na hango wani dan uwana na jini mai da’awar Sunnah, wanda a da nake girmama shi kafin ya fadi warwas, ya je ga mahaifiyata ya gurfana yana ba ta shawarar cewa lallai a yi kokarin raba aurena da mijina, don shi ne sanadin Shi’ancewa ta! Wannan shi ne bonono wai rufe kofa da barawo. Haba Yayana, ai ka makarkaro, ka bar kari tun ran tubani, bakin alkalami kuwa tuni ya gama bushewa! Ba ka san cewa duk da na halal bai iya juya baya ga shiriya ba? Barin tafarkin gaskiya (Shi’a) haihata Yayana! Ko da a ce za ku yi nasarar raba aurena da dan Shi’a, kamar yadda ka ambata, Wallahil Azeem (ba kaffara) ba za ku yi nasarar raba Shi’a da jinin jikina ba, don tuni zuciyarta, ta yi nisan da ba ta jin kira. Sai dai in za ku riskar da ni ga ruhin shuhada mai tsarki, ba makawa zan yarda don hakan ne matukar burina.

Abin da kuka kasa ganewa shi ne, mu matan Shi’a, ba muna addini don mazanmu ba ne, ku gane masu girma mazajenmu sun dora mu bisa turbar tsira ne kadai, amma ko da ba mu tare, ba za mu iya sauka daga layin da suka dora mu a kai ba, don mun riga mun mika wilayarmu ga ma’abocin cancanta, wannan da muke fatan Allah Ya sa kuna da rabon gane hakikaninsa kafin a tsallake siradi ranar mahshar! Kun ga kuwa mafarkinku na raba zukatanmu da Shi’anci, ba zai taba tabbata ba ilal abadi insha Allah.

An yi walkiya, na gano wani kanin Maigidana, mai kama da kububuwa don fusata, bayan waki’a, ya sa mahaifiyarsu gaba ya yi ta tunzura ta a kan Shi’a har ta so yi wa danta(Maigidana ke nan) mummunan baki saboda waki’ar da ta auka mana a Zariya.

Abin dariya, wai yaro ya tsinci hakori. A yayin walkiyar, na ji ya umurci Mahaifiyar Maigidana da ta kirawo Yayana (ni mai magana) ta kai karar Shi’ancinmu gare shi.

Sam-sam alamu sun nuna kamar ba ka tare da koyarwar Shugaba Amirul Jaishi, kuma ba ka kwatanta tarbiyyar da mai Ashabul Kahfi, Sarki Abduljabbaru ke kokarin ba ku. Eh mana. In ba haka ba, ta ina dan Wahabiyya zai iya warware matsalar ma’abocin wilaya ga Shugaban Wasiyyai, mai sitamfin da in ya buga maka ka rabauta? Wallahi wutsiyar rakumi ta nesanta da kasa! Na san kana ji na mai sunan manya, sai fa hakuri, matsalar, mu an horar da mu rashin jin tsoron kowa sai Allah, don shi yake da yadda zai yi damu, ba mutum marar katabus ba!

Za mu ci gaba insha Allah.