AlmizanAlmizan logo
Jum'a 23 ga Ramadan, 1441 Bugu na 1445 ISSN 1595-4474


Tambihi

Tare da Malam Muhammad Sulaiman

Kusantowar Bayyanar Imam Mahdi (AF)


Ya Mahadi

Kasantuwar wannan wata da muke ciki na Sha’aban aka haifi Hujjar Allah a doron kasa, kuma Shugaban wannan zamani, wato Imam Mahdi (AS), kuma rubutu ya gabata a shekarun baya dangane alamomin bayyanarsa da kuma ladubban zamanin gaiba. Haka kuma Darussa 12 daga rayuwarsa. To, a wannan shekara, insha Allah rubutun zai kasance kan kusantowar bayyanarsa, musamman idan muka yi la’akari da hali da yanayin da duniya take ciki yanzu, wato na wannan annoba ta ‘coronavirus’.

Kasantuwar wannan wata da muke ciki na Sha’aban aka haifi Hujjar Allah a doron kasa, kuma Shugaban wannan zamani, wato Imam Mahdi (AS), kuma rubutu ya gabata a shekarun baya dangane alamomin bayyanarsa da kuma ladubban zamanin gaiba. Haka kuma Darussa 12 daga rayuwarsa. To, a wannan shekara, insha Allah rubutun zai kasance kan kusantowar bayyanarsa, musamman idan muka yi la’akari da hali da yanayin da duniya take ciki yanzu, wato na wannan annoba ta ‘coronavirus’.

Idan mutum ya yi bincike cikin littaffan Hadisai zai ga ruwayoyi masu yawa da aka ruwaito daga Manzon Allah (SAAW) da kuma A’imma na Ahlul bayt (AS) da suke bayani dangane da alamomin bayyanar sa, wanda mutum zai iya kasa su gida uku. Na farko akwai alamomin da za su kasance gabanin bayyanarsa. Na biyu akwai alamomin da za su kasance gab da bayyannarsa. Na uku akwai alamomin da za su kasance idan ya bayyana.

Idan mutum ya dubi na farkon, wato alamomin da za su kasance gabanin bayyanarsa, mutum zai ga cewa da yawansu sun bayyana. Misali yawan fasadi a bayan kasa, yawaita zalunci a doron kasa, da dai sauransu. Yanzu abin da ya rage shi ne alamomin da za su kasance gab da bayyanarsa, wanda kusan shi muke ciki yanzu. Alal misali ya zo a Hadisai cewa gabanin bayyanarsa za a yi Annoba wadda za a samu mace-mace da yawa a cikin ta. Gabanin bayyanar sa za a samu kaura ce wa masallatai, wato ya zamanto an bar su. Gabanin bayyannarsa za a samu karyewar tattalin arziki na duniya da samun tsadar kayayyaki, kamar yadda yake gudana a yanzu na cewa tattalin arzikin duniya ya karye. Gabanin bayyanarsa za a samu tsoro da yunwa ya mamaye duniya. Gabanin bayyanarsa za a hana aikin Hajji, da dai sauransu.

Wadannan ababe da aka ambata duk akwai Hadisai a kai da aka ruwaito daga Manzon Allah da A’imma na Ahlul bayt, gabanin zuwan wannan hali da muke ciki. Ire-iren wadannan Hadisai, in mutum ya karanta, ba zai fahimce su sosai ba, saboda bai ga abin a aikace ba. Misali na kaurace wa masallatai. Yanzu ga shi a aikace, musamman ma mu nan Kaduna. Ka ga lokacin Sallah ya yi, a kira sallah ma domin fadakar da wadansu cewa lokacin sallah ya yi, ba za ka ji ba. Wato kamar yadda ake yi a wasu kasashe ko garuuwa. Wani lokaci idan lokacin sallah ya yi, saboda sabo da jin kiran sallah a masallatai, yanzu ko shiru, sai in ce wannan unguwa tamu kamar ta Maguzawa.

Amma idan muka dubi kasar Saudiyya da Kuwait da sauran kasashen Larabawa, duk da ba a zuwa masallatan, amma akalla Ladan yakan zo ya kira sallar a masallaci, har daga karshe a cikin kiran sallar sai ya kare da cewa “SALLU FI BUYUTIKUM.” Wato ku yi salla cikin gadajenku. Shi ne nake cewa, to ita wannan jumla da suka kara a cikin kiran sallah, ina suka samo ta har da suka mai da ita yanzu juz’i na kiran salla? Alhali “hayyi ala khairal Amal,” da suke ka-ce-na-ce a kai akwai ta a Hadisai.

Ga wasu daga cikin Hadisai da aka ruwaito na alamomin gab da bayyanar Imamuz Zaman (AS). An ruwaito daga Imam Ali (AS) ya ce, gab da bayyanar Mahdi, za a samu abin da ake ce ma Mautul Ahmar da kuma Mautul Abyab. Mautul Ahmar shi ne yake-yake da kashe-kashe. Mautul Abyab shi ne Annoba da za a samu mace-mace a ciki. Wannan Hadisi, hatta Malaman Sunna sun ruwaito shi. Wannan ma da na kawo a cikin ruwayar Ahlus Sunna na ciranto shi daga Suyudi.

A kuma wani Hadisi da aka ruwaito daga Imam Sadik ya ce, “Ba makawa gabanin bayyanar Imam Mahdi za a samu Annoba, wanda mace-mace za su auku a cikin ta. Game da kuma kaura ce ma masallatai, an ruwaito daga Imam Ali ya ce, “Idan aka wofintar da masallatai, to ku saurari babban al’amari. ” Amma su a ruwayar Ahlus Sunna sun kawo shi a cikin alamomini tashin kiyama ne. Wani abin da na lura da shi a littafan Hadisai na Ahlus Sunna, in dai abu ya shafi alamomin bayyanar Imam Mahdi, galibi akan jirkita shi da cewa, alamomi ne na tashin kiyama. Ba mamaki a lokacin Bani Umayya aka samu wadannan canje-canje din, da yake a lokacin akwai Hadisai masu yawa da suka kago, akwai masu yawa da suka jirkita su, musamman ma idan sun shafi Ahlul bayt.

Na shi kuma hana Hajji, ita ma ruwayar daga Imam Ali aka ruwaito ta, yana cewa, ku yi dakon yankewar aikin Hajji. Idan duk alamomin suka cika, to Mahdi zai bayyana. Su kuma a ruwayar Ahlus Sunna, kamar yadda ya zo a cikin Littafin Hadisi na Buhari, Manzon Allah ya ce, “Ba za a yi tashin kiyama ba har sai an kai lokacin da ba za a yi aikin Hajji ba.”

Kwanakin baya da suka wuce, Ministan aikin Hajji na Saudiyya ya fito karara, ya fada ma kasashen musulmi cewa, su dakatar da amsar kudin zuwa Hajji, saboda kila baza a samu yin aikin Hajjin ba. Da dai sauran Hadaisai da suka zo kan wadannan Alamomi na gab da bayyanarsa, kamar na karyewar tattalin arzikin duniya, wanda ba za a iya kawo su ba saboda gudun tsawaitawa.

A takaice dai yanzu duniya ta shiga wani hali, wanda ba ta taba shiga ba. Misali annoba an yi da dama a tarihi, amma in mutum ya bincika zai ga irin wadannan annoba ba su game mafi yawan kasashen duniya ba kamar wannan. Wato za ka samu cewa annobar ta shafi wani yanki ne na duniya. Misali kamar annobar ‘Lassa fever’ da ta auku a wannan kasa. Haka nan kuma ire-ire annobar da suka auku a tarihi ba su tsai da harkokin mutane na Duniya ba. Amma in muka duba yanzu kusan fiye da rabin mutanen Duniya harkokin yau da kullum sun tsaya cak, suna zaune a gidajensu.

Kuma abin mamaki, ga cuta ta bayyana, amma kuma wai ba maganinta, sai komawa ga Allah Ta’ala. Hatta Shugabannin kasashen yamma, misali Shugaban kasar Italiya, an nuno shi yana jawabi, yana kuka cewa, duk matakan da za su dauka domin magance wannan annoba, sun dauka. Yanzu mafita kawai sai ga Ubangiji.

Haka nan Shugaban Amerika, sai da ta kai ya sa aka gayyato masa Limaman Kirista da na Musulmi da na Yahudawa, ya ce kowa ya yi addu’a, yana zaune yana jin su. Da na ga abin sai da na ji mamaki cewa, ashe Trump ya san a koma ga Allah.

To, tambaya, yanzu menene abin yi, musamman ga mu mabiya Ahlul bayt? Amsa, babban abin yi shi ne kowanne mu ya ga cewa ya kyautata alakarsa da Imam Mahdi. In mun ci sa’a kila ya bayyana a wannan karnin da muke ciki insha Allah, domin ko a cikin wasiyyar Shehu Usman Dan Fodiyo, ya yi hasashen cewa kila ya bayyana a karni na sha biyar. A lura da kyau, wannan hasashe ya yi, ba wai ya ayyana lokaci ba ne, saboda akwai Hidisai da suka zo kan hani na ayyana lokacin da zai bayyana, amma gini kan hasashe da tsammani da kuma fata, wannan ba matsala; inda matsalar take, mutum ya ayyana, ya ce zai bayyana lokaci kaza.

Dawowa ga bayani dangane da kyautata alaka da Imam Mahdi. Wannan maudu’i, maudu’i ne, wanda wasu daga cikin Malamai na Imamiyya sun yi bayanai da kuma rubuce-rubuce a kai. Alal misali idan mutum ya duba littafin ‘Uswatul- Arifin,’ littafi ne da ya yi bayanin Tarihin Ayatullahi Bahjati da kuma wasu bangarori na rayuwarsa. To, a cikin littafin, Fasali na 12, zai ga an kawo irin wadannan hanyoyi na kyautata alaka da Imam Mahdi. Haka kuma a wani littafi mai suna ‘Fi Madrasati Ayatullah Shaikh Bahjati,’ shi kuma littafi ne da aka kawo darussa dabam-dabam na koyarwar Ayatullahi Bahjati. To, a cikin littafin, a fasali na 7, shi ma bayanai dabam-dabam sun zo a kai. Saboda haka a nan za a kawo wasu sassa na bayanan Ayatullahi Bahjati da ke cikin littafan biyu da suke da alaka da wannan maudu’in.

Kuma kamar yadda wasun mu suka sani, Ayatullahi Bahjati yana daya daga cikin manya-manyan Urafa’u na wannan zamanin. mu duba matsayin Imam Khumaini a fagen Irfan, amma duk da haka, wasu ababe da suka shafi Irfan, yakan mai da su ga Ayatullahi Bahjati. Akwai ma lokacin da wasu suka tambayi Imam Khumaini ya fada masu wani Malami da za su dinga komawa gare shi dangane da abubuwan da suka shafi Irfani, sai ya ce ga Ayatullahi Bahjati. Kuma maraji’ai da dama, a lokacin yana raye, musamman wadanda suke cikin birnin Kum, suna kwadaitar da mabiyansu da yin sallah a bayansa, domin yin sallah a bayansa, kamar yadda da yawa suke cewa, yana gusar da bushewar zuciya.

Shi ya sa ga wadanda suka san masallacinsa, masallaci ne wanda in kazo awa daya ko biyu gabanin lokacin sallah, to ba za ka samu waje ba a ciki, saboda da yawa kafin lokacin sallar wani zai zo ya zauna, wani kuma ya aje wata alama, misali littafi ko jaka a sahun, ya tafi harkokinsa, sai lokacin sallah ya yi ya zo. A takaice dai a wannan zamani namu, bayin Allah Arifai, wadanda Allah Ta’ala ya bayyanar, ba wadanda suke boye ba, to ba kamar Ayatullahi Bahjati. Mutum na iya duba wancan littafi na tarihinsa da aka ambata a sama mai suna Uswatul-Arifin, zai ga haka. Saboda haka bayanan da za a kawo nan na hanyoyin kyautata alaka da Imam Mahdi (AS), bayanai ne wadanda suka fito daga wanda yake da alaka da Imam Mahdi (AS), alaka ta zahiri da badini.

Ayatullahi Bahjati ya ce, “Ya hau kan kowane mutum, shi a kashin kansa ya yi tunanin hanyar da zai kyautata alaka da kuma dangantaka da Imam Mahdi (AS), ko da ko bayyanar Imam Mahdi (AS) tana kusa ne ko nesa. Domin alakantuwa da Imam Mahdi (AS), wani abu ne da yake karkashin zabinmu da kuma ikonmu, sabanin bayyanarsa, shi a hannun Allah yake. Saboda haka me ya sa ba mu damuwa mu ga cewa mun hakkakar da wannan alaka da kuma dangantaka da Imam Mahdi (AS)? Me ya sa muke gafalallu ga wannan maudu’i? Kawai abin da ya dame mu bayyanar Imam Mahdi (AS) ko kuma haduwa da shi? Tare da sanin cewa idan ba mu himmatu ba wajen gyara kawukanmu, domin mu alakantu da Imam Mahdi ba, to akwai abin tsoro a kan hakan, domin muna iya guje masa in ya bayyana.”

A nan Ayatullahi Bahjati yana nuna mana muhimmancin kowannen mu, namiji ne ko mace, ya yi tunanin hanyar kyautata alaka da Imam Mahdi (AS), domin shi wannan abu ne wanda in mutum ya sa kansa zai iya yi, sabanin bayyanar Imam Mahdi (AS), shi yana hannun Allah Ta’ala ne. Saboda haka mufi damuwa da kyautata alaka da shi fiye da bayyanarsa, domin idan ba haka ba, ko da ya bayyana, muna iya barin sa. Saboda kafin bayyanar sa ba mu da kyakkyawar alaka da shi.

Tabbas akwai Hadisai da suka zo daga A’imma na Ahlul bayt (AS) cewa, akwai ’yan Shi’ar da idan Imam Mahdi (AS) ya bayyana, za su yi inkarin sa. Wannan abu ko akwai ban tsoro a ciki.

A wani waje kuma Ayatullahi Bahjati yana cewa, “Ina bayin Allah wadanda suke da alaka da Imam Mahdi suka tafi? Mu ga shi ba mu da irin wannan alaka. Idan kuka ce mu ba za mu iya isa ga Imam Mahdi ba? Amsarku ita ce, to me ya sa ba zaku lizimci ayyukan da’a ba, kuma ku nisanci ayyukan zunubi, domin barin ayyukan da’a da kuma aikata ayyukan zunubi sune shamaki da suka shamakance mu daga haduwa da Imam Mahdi.”

A wani waje kuma yana cewa, “Kasantuwar bayyanar Imam Mahdi (AS) yana kusa, saboda haka ya wajaba ga kowane mutum ya gyara kansa domin waccan ranar. Daga cikin abubuwan da mutum zai soma yi, shi ne ya tuba daga zunubai. Muna rokon Allah Ta’ala kada mu kasance cikin wadanda suke addu’ar Allah ya gaggauta bayyanar Imam Mahdi da harsunansu, amma kuma da ayyukansu suna jinkirtar da bayyanarsa.”

Za mu ci gaba insha Allah.


Sanarwa

Sanarwa
Nan filin duk wani sanarwa ne daga duk bangarorin Harka Islamiyyah

  GAYYATA ZUWA MAKON IMAM KHOMEINI
  Imam KhomeiniDandamalin Dalibai da Malamai na Harka Islamiyyah (Academic Forum) na sanar da dukkan ’yan uwa cewa za a yi Makon Imam Khomeini na bana, wanda za a fara daga ranar:
  Juma'a 30 ga Mayu 2014 zuwa Laraba 3 ga Yuni 2014

  Masu Jawabi: Akwai Malamai da masana daban-daban da za su gabatar da lakca, ciki har da Jagoranmu, Sayyid Ibrahim Zakzaky (H)

  Wannan gayyatar na kowa da kowa ne. Allah ya ba da ikon halarta
  Za mu buga jaddawalin nan gaba kadan in sha Allah.


  Labarai cikin hotuna

  Hotunan YAUMUL MAB'AS na bana

  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asMalam Zakzaky yana jawabi
  • Yaumul Mab'asMalam Zakzaky yana jawabi
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron