AlmizanAlmizan logo
Jum'a 23 ga Ramadan, 1441 Bugu na 1445 ISSN 1595-4474


Rahoto

MUNA NEMAN TABBACIN TSARON SHAIKH ZAKZAKY

Daga Danjuma Katsina


 Shema Ibrahim

Bayanai daga Majiya mai tushe daga gidan yari na Jihar Kaduna, wurin da gwamnatin Tarayyar Nijeriya take ci gaba da tsare Shaikh Zakzaky da mai dakinsa, Malama Zeenah ba bisa ka’ida ba, sun tabbatar wa da Harkar Musulunci a Nijeriya cewa an tayar da wani hargitsi wanda ya yi silar bude wuta tare kuma da rufe dukkanin hanyoyin da za su iya kai jama’a zuwa ga gidan yarin.

Mun kadu kwarai da jin wannan lamari, kuma a yanzu hankalinmu yana a kan wannan batu, don haka muna kira da babbar murya ga dukkanin mahukunta da ke da ruwa da tsaki a kan sha’anin gidan yarin da su tabbatar da bayar da cikakkiyar kariya ga rayuwar Shaikh Zakzaky da

mai dakinsa, Malama Zeenah Ibrahim.

Tabbas za mu dora alhaki a kan gwamnatin Tarayyar Nijeriya idan wani lamari na cutarwa ya same su. Hakkin gwamnati ne ta bayar da cikakken tsaro ga dukkanin jama’ar da ake tsare da su a irin wadannan wurare, musamman a irin wannan yanayi na barkewar Cutar Koronabairos wadda ta addabi duniya, musamman kasancewar yadda doka take kallon wanda ake tuhuma a matsayin wanda bai aikata laifi ba har sai zuwa lokacin da aka iya tabbatar da aikata laifin nasa ta hanyar shari’a.

Lamarin Shaikh Zakzaky a kebe, batu ne wanda ya sha bamban, domin kuwa babbar Kotun Tarayya ta zartar da hukuncin cewa kama shi da kuma tsare shi lamari ne wanda ya sabawa Kundin tsarin mulkin Nijeriya, haka nan kuma lamari ne na tauye masa ’yanci. Dadin dadawa, tuhume-tuhumen da ake yi masa a yanzu, Kotuna guda biyu da ke cikin garin Kaduna sun yi watsi da makamantan su da aka tuhumi wasu ’yan’uwa musulmi kusan 200, suka kuma sallame su tare da wanke su daga aikata irin wadannan laifuka.

Don haka, muna kira da babbar murya da a gaggauta sakin Shaikh Ibraheem Zakzaky da mai dakinsa, Malama Zeenah Ibrahim.

SA HANNU:

IBRAHIM MUSA