AlmizanAlmizan logo
Jum'a 23 ga Ramadan, 1441 Bugu na 1445 ISSN 1595-4474


Rahoto

NANKARWA A JIKIN BELBELA (VI11)

TARE DA M.I. GAMAWA 09071965492


Watakila wanda ya karanta mu a satin da ya gabata ya sha mamakin rashin imani da tausayi na shuwagabannin Arewa idan ta zo ga hada kan Najeriya ko mu ce tabbatar da ita Najeriyar a matsayin kasa daya dunkulalliya. Amsa a nan ita ce, shugabannin Arewa sun ta'allaka rayuwarsu da tabbatuwarsu a doron duniya da wanzuwar Najeriya a matsayin kasa daya, al'umma daya. Abin da ya ci Doma bai barin Awai. Wannan akida ita ta shigi talakawan Arewa.

Don wannan mugun abu ya dawwama a zukatan shugabanni da talakawan shi ne ya sa aka buda wa shuwagabannin Arewa hanya a Turai, aka ba su damar ajiya a bankuna, wasu kuma suka zama 'yan kasa. Sai dai kayan aro na aro ne. Giji kuma lahira ne. Yanzu lokaci ya fara canzawa, an fara samun tawaye daga gida. Addinin da Bature ya kawar don tabbatar da tsarinsa ya fara dago kai. Kuma ga dukkan alamu karfin gwuiwa da kumajin masu addinin ya fi na wadanda suka mika wa Bature kai domin bori ya hau. Yaran Turawa a Arewacin Najeriyawa suna ayyuka don abubuwa biyu ne kadai, babu na uku. Na farko don su rayu. Na biyu don su rayar da tsarin da Bature ya kawo. Kana iya kiran na farko da abin da Bahaushe ke kira "da ruwan ciki kan ja na rijiya. Wato sai an ci an sha a biya wa Bature bukata. Har ma abin ya wuce haka. Yanzu kusan kashi casa'in na abin da suka sata ba ya zama a gida Najeriya sai dai Turai.

Na biyun kuma shi ne tsayin daka don kada tsarin Bature ya rushe. Don kuwa a bisa tsarin Bature suka gina 'ya'yansu da jikokinsu. Wannan ya koyar da su cewa duk wanda zai kawo wa tsarin hukuma sabanin abin da Bature ya kawo a matsayin makiyi wanda babu wata nau'in azaba da ba ta cancance shi ba.

Da zarar Bature ya mai da mulkin Nijeriya hannun 'yan Kudu, Yarabawansu ko Ibonsu ko kananan kabilunsu don karbi-in-karba, tabbas za a samu sauyi mai ban mamaki a Arewa. Don duk wanda za a dauko daga Kudu, da wuya a ce musulmi ne, sai dai ya zama musulmi bisa hadari. Imma haka ta samu, to dole ya zama musulmi mai mata kirista, kuma dolensa ya nuna wa musulmi 'yan'uwansa bambanci don kada kiristoci su koka da shi.

Wannan domin abubuwa biyu ko fiye da haka. Na farko shi ne Turawa sun mai da Arewa yankin Musulmi, Kudu kuma yankin Kirista. In dai mutum ya ta'allaka da kafofin yada labaran Turai zai zaci cewa babu Musulmi ko daya a kudancin kasar nan. Amma suna nuna akwai kiristoci a Arewa da Musulmi ke zalunta. Amma ba sa maganar musulmin Kudanci, balle su fadi zaluncin da Kiristoci ke musu. Tabbas zalunci ya kare a kan musulmin Kudu, Yarbawansu da Ibonsu daga kiristocinsu. Sai dai duk dan siyasar Arewa komai son musuluncinsa dole ya yi shiru in yana da gurin tasiri a siyasar Najeriya. Da zaran Musulmin Arewa ya yi magana a kan danninyar da ake wa Musulmin Kudu, to jaridun Kudu za su yi masa fentin mai tsattsauran ra'ayin Musulunci, kuma mutum mai tsananin hadari ga wanzuwar Najeriya. Sabanin yadda kowane dan Kudu ke da 'yancin zargin musulmin Arewa da danne wa kiristocin Arewa hakki.

An wajabta wa 'yan Arewa nesa da 'yan'uwansu musulmi na Kudu. Da zaran 'yan Arewa sun samu aikin gadi, wato shugabancin kasa, sai su fara nesa da musulman Kudu. Kamar an ba su umarni daga Turai cewa kar su yarda su bai wa musulmin Kudu mukaman gwamnati, hatta a jihohin da musulmi suka fi yawa.

Misali akwai Musulmi masu yawa a jihohin Ibo, amma sai Musulmin Arewa su guje su kamar yadda 'yan'uwansu ke gudunsu ko ma fiye da haka. Sai su zama ba su da masoyi a gida da waje. Haka masu mulki 'yan Arewa suka yi tun daga zamanin Sardauna har yau. Amma su 'yan Kudu da sun samu mulki, sai su ga kamar sun samu damar kwato wa Kiristocin Arewa 'yanci ne kawai. Wannan an gani a wurin Obasanjo a dawowarsa ta biyu. A duk shekaru takwas da Obasanjo ya shafe yana mulki bai taba yarda ya bai wa musulmi mukamin babban Hafsan Sojan kasa ko ruwa ko na sama ba.

Wani abu da ya dace talakawan Arewa su daina shi ne murna don suna mulkin kasar nan. Ya kamata su gane cewa wannan mulki tamkar rawa ne da maciji a aljihu. Mulkin dan Arewa, mulki ne na rashin 'yanci da takura. Mulkin ga koshi ga kwanan yunwa. Mulkin dulmuya talakawan Arewa cikin tekun jahilci da talauci ne.

Watakila mulkin Buhari ya koya wa talakawan Arewa hankali in dai akwai sauran hankali a jikinsu. Shakka babu wanda ya kasa fahimtar me ya sa mulki ya shekara kusan arba'in a hannun 'yan Arewa, amma Arewa ne yankin da ya fi kowane yanki talauci a Najeriya, to ya fi kowa jahilci a duniya. Me ya sa ma'aikatar ilmi ta kasa ta shekara kusan arba'in a hannun Ministoci 'yan Arewa, amma kusan kashi arba'in da biyar na mutanen Arewa ba su da ilmin boko? Me ya sa jami'oin Arewa suka cika da 'yan kudanci sabanin jami'o'in kudu da ba ka samun 'yan Arewa a cikin su? Me ya sa aka rika kawo wa Arewa muggan akidu na rashin tausayi da sunan addini? Me ya sa fadace-fadace suka zama ruwan dare dama duniya a Arewacin kasar nan sabanin Kudanci?

Me ya sa har yau talakawan Arewa suka makale wa shugabanninsu duk da bayyanannen zaluncin da shugabannin ke yi musu dare da rana? Me ya sa 'yan Arewa suka kasa gane wanda ya zo musu da hanyar da in sun bi za su kubuta daga wannan zalunci, kaskanci da bautar kattin da suka rasa mutunci da karamci har abada? Sai dai duk wanda ya mutu a cikin su a ce, "Ya bautata wa kasarsa Najeriya." Yaushe talakan Arewa zai daina bauta wa mai bautar kasar da za a nade a ranar tashin kiyama? Me ya sa musulmin Arewa zai kafirce wa gunki, amma ya buge da bautar mai bautar kasa?

Zaman Najeriya kasa daya bai taba amfanar musulmin Arewa ba. Kuma ba zai taba amfanar sa a nan gaba ba. An tsara wanzuwar kasar da zub da jinninsa da guminsa ne. Hatta mutumcinsa, don kuwa duk da wannan asarar rayuka da talauci, dan Arewa ba shi da mutumci a gun shungun 'yan Najeriya. Duk da cewa wanzuwar kasar ya samu ne da jininsa da aka zubar, amma har yau shi ne mas'alar kasar a wajen wadanda ya ceto daga masifar abin da ka iya tasowa bayan rabewar kasar. Wannan shi ne dora wa kiyashi kayan rakumi, kayan bai dauku ba, ya kashe kansa. Da ma balbela ba ta da nankarwa a jikinta. In kuwa ka gan ta da nankarwa, to ka duba da kyau watakila farin Borintinke ne. Intaha.

ASHE BINDIGAR BUHARI NA KASHE WANDA BA DAN SHI'A BA?

Yau gobara ta cinye masakar masaki. Masaki bai cika alaka da wuta ba, sai dai abin da ba za a rasa ba, kodayake ana dafa tuwo a gidansa. Talakawan Arewa na ganin tasku kamar magidancin da ya gaza biyan haraji kafin zuwan gwamnatin PRP a Kano.

Yau abin ya dawo kansu bayan sun yi biyayya, sun yarda, sun aminta, sun sallama wa Buhari. Kai wuce nan! Sun kona, sun kashe duk wanda ya ce ba zai so Buhari ba. Sun kasa, sun tsare, sun raka, amma duk da haka cinnaka bai san na gida ba, har su ma bai kyale su ba.

Da ya kashe mu da lafin 'Dukan kirjin Janar,' abin da ya fada a gida Najeriya ke nan. Amma da ya je hadaddiyar daular Larabawa cewa ya yi, "Na auka wa Zakzaky da mutanensa don in rage tasirin Iran a Afrika."

Ko ma don mene ne babu wanda ya zaci zai auka wa masoyansa masu kashe wadanda ba su zabe shi ba. Wadanda suka ba da rayukansu domin sa. Mutuwa ta dauki wasu saboda shi. Masu rabo cikin su kuma Allah ya bar su a raye don su gane ko shi waye, su fahimci cewa duniya ta dade ba ta ga mayaudari, maketaci kamar sa ba. A yau rana ba ta haska mugu kamar sa ba. Ba ta haska mai bakin hali kamar sa ba, kamar yadda ba ta haska mahassadi irin sa ba. Watakila rabon da a samu mutum irin sa tun zamanin Sarki Hasidin-iza-hasada.

A cikin wannan wata talakawan kasar nan sun ga bakin ciki, kari a kan wanda suka saba gani. Da ma rabon talakan da ke son Buhari da farin ciki tun ran da ya ci zabe a karo na farko. Da ma sunansa "Kashe mai son ka." Sai kuma ga cutar Korona. Ganin haka gogan naka ya fake da haka ya kafa dokar hana fita da sunan killace jama'a. Yanzu an killace Abuja, Legas da Ogun. karyar yau daban da ta gobe. Labarin da 'yan kasa ke ji a kullum shi ne wai an kashe musu biliyan kaza ko tiriliyan kaza. Da ma ba a taba gwamnatin da sata ya zama kamar farilla a gun ta kamar wannan gwamnatin ba. Talaka bai ga komai ba sai karya a gidajen rediyo, wai an ciyar da shi.

Wata arangama da aka yi ta gwabzawa ita ce killace masallatai da kasuwanni har da wajajen ibadar 'yan kasa coci-coci. Sai dai wannan bai zo wa gwamnatin Tarayya da ta jihohi da sauki ba. A satuka biyu da suka gabata mutane hudu sun sha dalma har lahira daga 'yansandan Mai rusau Nasiru don bijire wa dokar hana Salla a Masallatai. Shin me ya sa talakawan Arewa ba sa tambayar me ya sa jininsu ya zama arha kamar rake a garin Sara a duk tsawon mulkin 'yan'uwansu Arewawa? Ana saba dokar killacewa a Kudu, amma babu wanda aka harba. Wasu ma da 'yansanda suka taba lafiyarsu, sai da hukumar 'yansanda ta kama 'yansandan, kuma aka kafa kwamiti don ladabtar da su. Amma wadanda aka kashe a Kaduna, ko maganar ba a yi. An kashe banza, banzar ma ta bazara.

Ba kowa ke tsammanin cewa Musulmin Arewa masu murna da kisan 'yan Shi'a samun nasu harsashin daga 'yan sandan Buhari da rana a tsaka ba. Ga shi su ma sun samu nasu kason. Ashe jinin kowa halas malas ne a gun jami'an tsaron Buhari, madamar mutumin dan Arewa ne.

Yanzu killacewa ta kara tsawo. Jihohi sai kara daukar matakan killacewa suke yi. Jami'an tsaro kuwa sai gyara bindigogi da albarusai suke yi don maganin masu zuwa masallaci don khamsus-salawatu ko sallar Juma'a. Abin tambaya a nan shi ne mutane nawa Buhari zai kashe a Arewa kafin ya sauka daga mulki?

A farkon wata shidansa a karo na farko ya kashe sama da mutum dubu, maza da mata, yara da manya don biya wa Saudiyya da Yahudawan duniya bukata. Su kuma talakawa a lokacin sai murna suke, wai an kashe musu 'yan Shi'a. To, yanzu ya fara kashe masu bijire wa dokar killacewa, su ma 'yan Shi'a ne? Ya fara kashe masu zuwa salla masallatai su ma 'yan Shi'a ne?

Dole talakawan Arewa su sake tunani sosai a kan Buhari, su tambayi kansu, shin wa Buhari yake wa aiki duk da cewa su suka zabe shi? Su suka wahala domin ya samu shugabanci, amma sune abin kashewa da bindiga da uwa-uba yunwa. Yanzu wane suna masu kiran sa gwarzon Musulunci za su kira shi a nan gaba? Bayan kashe 'yan Shi'a yanzu ya fara kashe su don sun je salla a masallatai. Shin gwarzon Musulunci zai rika kashe musulmi Shi'arsu da Sunnan su? Ina kazamen Maluma masu rigar Shaidan da suka wanke Buhari, suka mika wa talakawan da suka dauke su a matsayin magada Annabawa?

Dole musulmin Arewa su sake tunani madamar suna fatan samun rabon duniya da lahira. Yanzu kam duniyar ba ta samu ba duk da makauniyar biyayyar da ake wa shugabannin Dagutu. Da'a ma Dagutu kafirce wa Allah Mai ba da sakamako a lahira ne, shin talakawan Arewa sun shirya wa asarar lahira ne? Tabbas kisa kan killacewa yanzu gwamnatin Buhari ta fara. Sanin kowa ne ko Korona ba ta kashe ba, yunwa za ta kashe na kashewa. Duk dai alhakin nasa ne. Amma duk da haka har yanzu ana samun wasu bayi a motar Buhari. A nasu tunanin, shi za su bautatawa komai wuya komai dadi. Kash! Inda asarar take shi ne Buhari ba shi da abin da zai ba su a lahira in mun tafi. Shi ma ta kansa zai yi a wannan rana. Wayyo! Ina amfanin badi ba rai? Wa iyazubillah!