AlmizanAlmizan logo
Jum'a 23 ga Ramadan, 1441 Bugu na 1445 ISSN 1595-4474

Rahoto

An gurfanar da Limamai 15 gaban kotu saboda jam’in Sallah

Daga Abdullahi Sambo Richifa


 mallam
A karshen watan Afrilun 2020, Kwamishinan ’yan sanda na Jihar Kano C.P. Sabo ya kira taron manema labarai, inda ya yi bayanin cewa sun gurfanar da Limamai 15 a fadin jihar Kano, a gaban shari’a, bisa zargin saba wa dokar da gwamnatin Kano ta yi na hana zirga-zirga, da rufe kasuwanni da masallatan Juma’a, domin yaki da cutar COVID-19, wadda aka fi sani da koronabairus, kuma tuni aka hukunta su.
Tun bayan da Gwamnan Kano Dk. Abdullahi Umar Ganduje ya sanar da wannan doka don yaki da wannan Cuta, jama’ar jihar Kano suke cikin mummunar damuwa a kan wannan lamari, musamman saboda rufe kasuwanni, da hana su yin sallar Juma’a da hana zirga-zirga. Duk da an shiga Azumi, amma gwamnatin ba ta duba hakan ta sassauta wa al’ummar musulmi ba, wanda yin hakan ya zama sabon lamari ga al’ummar jihar Kano, har wasu suke cewa su ba su taba ganin irin wannan lamari ba a tarihin rayuwar musulmin Kano. Wannan ce ta sa wasu limaman masallatan Juma’ar suka ce ko za a cire su, sai sun yi sallar Juma’ar, wasu kuma daga cikin su suka ajiye limancin, suka ce tunda har lalacewar zamani ta zo da za a iya hana musulmi sallar Juma’a, to su sun hakura da limancin. Gwamnoni su guji yanke albashin ma’aikata In ji Shugaban Jam’iyyar APC Daga A.M. Mahi Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Mista Adams Oshiomole, ya yi gargadi ga Gwamnoni da su guji yanke kudin ma’aikatan jihohinsu, da sunan yaki da cutar korona (COVID-19). Mista Oshiomole ya yi wannan gargadi ne a wata mukala da ya gabatar a Ranar Ma’aikata Ta Duniya, wadda aka saba yin ta duk ranar daya ga watan Mayu na kowace shekara. Oshiomole ya ce, lallai ba daidai ba ne yunkurin da wasu Jihohi ke yi da sunan yaki da korona na fara yanke kudin ma’aikatansu; wasu daga cikin Gwamnonin har shirin rage ma’aikatan suke yi. Oshiomole ya ce, a wannan lokaci da ma’aikata suke cikin damuwa, in dai ba za ka taimaka musu ba, to bai kamata ka rage musu albashi ba, ko ka kori wasu, musamman inda wasu Gwamnonin har yanzu suka ki yarda su yi sabon tsarin albashi mafi kankkanta na Naira dubu talatin. Tun bayan da gwamnatin Najeriya, ta sanar da shirin yaki da wannan cuta ta COVID-19, wasu Gwamnoni suke ta neman hanyoyi na tara kudi da sunan yaki da wannan cuta, wasu daga cikin su har Kwamitoci suka kafa na tara kudin taimakon da suke nema daga al’umma, musamman manyan Attajirai na kasar nan, wasu daga cikin su har da cewa za su tallafa wa talakawa da abinci saboda takurar da al’umma suke ciki na hana su zirga-zirga, da tsai da sana’o’insu, da aka yi tsawon makwanni. Jami’ar Bayero Kano ta samar da na’ura gwajin Korona Daga A.M. Mahi Shugaban jami’ar Bayero (BUK) da ke Kano, Farfesa Muhammad Yahuza Bello, ya sanar da cewa, Jami’ar ta Bayero ta samar da na’urar, musamman don gwajin cutar korona. Farfesan ya ce, sun samar da wannan na’ura ne don amfanin Jihar Kano, da ma kasa gaba daya. Kuma ya ce da wannan na’ura za a iya gwada sama da mutum 100 da ita a rana guda, don gano suna da wannan cuta ko ba su da ita. Tun bayan bayyanar wannan cuta a Kano, Gwamnan Kanon ya sanar da cewa ba su da kayan aikin gwada mutum don gano yana da wannan cuta ko a’a, dole sai an tafi Lagos da jinin wanda ake zaton yana da cutar don a gwada shi ko Abuja. Amma daga baya an yi wasu hikimomi, an samar da wata na’ura a Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano, don gwada jama’a cikin gaggawa. Amma ba a dade ana aiki da ita ba ta tsaya. Za a fara buga wasan kwallon kafa a duniya Daga Sani Hamisu Watanni biyu bayan dakatar da dukkan harkokin wasan kwallon kafa a duniya, sakamakon Coronavirus, yanzu kuma an fara shirye-shiryen dawowa da wasan a kasashe daban-daban. A Ingila an dakatar da wasan PREMIER LEAGUE a ranar 13 Ga Maris, bayan an samu Kociyan Arsenal dauke da cutar Coronavirus. Daga nan kasashen da suka fi amanna da wasan kwallo, irin su Ingila, Spain, Italy, Jamus da Faransa, duk suka auka cikin annobar Coronavirus. Cutar ta kashe dubban mutane a kasar, ciki har da masu harkokin wasan kwallo da iyalansu. Kuma ’yan wasa da dama sun kamu da cutar. Shirye-Shiryen dawowar Premier League: Shugaban shirya Gasar Premier League na Ingila, Richard Garlick, ya bayyana cewa nan ba da dadewa ba dukkan kungiyoyin gasar za su dawo yin tirenin domin shirin ci gaba da gasar. Garlick ya ce, amma an gindaya tsauraran matakan da kowane kulob zai rika dauka kafin da kuma lokacin yin tirenin din, domin kauce wa daukar cutar Coronavirus. Na farko dai kowane dan wasa, tilas ya sa takunkumin kare hanci da baki a lokacin da yake tirenin. Su ma jami’an kula da ’yan wasa har da Kociya, tilas su daura takunkumin. Dole kafin a fara tirenin a yi wa kowane kwallo feshin kariyar cutar Coronavirus. Bayan an gama tirenin ma a tabbatar an yi wa kowane kwallo da raga da sauran kayan tirenin din feshin kariya daga cutar Coronavirus. Kamfanin kula da lafiya na CAT zai bi ’yan wasa ya yi musu gwaji kafin ranar fara tirenin din. Kowane dan wasa zai ajiye motarsa nesa da ta wani dan wasan. Ya kasance an bar filin ajiye motoci uku tsakanin wannan mota da waccan. An haramta wa ’yan wasa tofar da yawu idan ana tirenin. Tuni dai ’yan wasan Arsenal, Tottenham, West Ham da Brighton suka fara fita motsa jiki da na’urar motsa jiki. Kasar Faransa ma ta fara shirin dawowa a cikin watan Yuni, amma Shugaban kasa Edourd Phillipe ya ce, kamata ya yi su dan kara tsahirtawa zuwa nan da watan Satumba. Tuni hukumar kwallon kafa ta Faransa ta ce, ranar 8 Ga Mayu za ta damka wa PSG kofi, duk kuwa da cewa ba a kammala gasar ba. Akwai ratar maki 12 tsakanin PSG da Marsille, wadda ke ta biyu. Sai dai kuma a Ingila ana ganin za a karasa gasar ce ba tare da ’yan kallo ko daya ba a filayen wasa. Sai dai a kalla daga gida a cikin akwatunan talabijin kawai. An sako ’ya’yan fitaccen Malamin da aka yi garkuwa da su Daga Sani Hamisu Masu garkuwa sun saki tagwayen ’ya’yan fitaccen Malamin Musulunci, Taofiq Akewugbafold da ke Ibadan, babban birnin Jihar Oyo. Taofiq din ne da kan sa ya sanar a shafinsa na Twitter cewa a taya shi murna, masu garkuwa sun sako ’ya’yansa da suka tsare tun a ranar da aka fara azumi. Ya ce, an sakar masa ’ya’yan a cikin dokar jeji, misalin karfe 5:30 na asubahin ranar Lahadi. Taofiq ya yi shugabancin Hukumar jin dadin Alhazai ta Jihar Oyo, shekara takwas, tsawon zamanin Gwamna Abiola Ajimobi, wanda ya sauka cikin 2019. Ya kuma gode wa al’ummar da suka taya shi addu’a. Cikin makon da ya wuce ne muka kawo muku rahoton cewa an yi garkuwa da ’ya’yan wani fitaccen Malami. CORONAVIRUS: Jami’an kiwon lafiya 16 sun kamu da cutar a Borno Daga Sani Hamisu. Akalla Jami’an Kula da masu cutar Coronavirus guda 16 ne suka kamu da cutar a Jihar Barno. Kwamishinan Lafiya na Barno, Salisu Kwaya-Bura ne ya bayyana wa manema labarai haka a ranar Asabar, a Maiduguri. Kwamishina Kwaya-Bura ya ce, wannan yana nuna irin shiga halin barazana da sai da ran da Jami’an kiwon lafiyar jihar ke yi wajen sadaukar da kan su domin kokarin dakile Coronavirus a Barno baki daya. Ya ce, daga cikin jami’an kiwon lafiya 113 da suka kamu da cutar baki daya a Najeriya, 16 daga cikin su a jihar Borno ne. Kwaya-Bura ya ce, Gwamnatin Jihar Borno na ta kara daukar tsauraran matakan hana jami’an sake kamuwa da cutar. Ya kara da cewa, yanzu haka gwamnatin jihar ta ba da odar kayan kariyar cuta da jami’an kiwon lafiya za su rika amfani da su, har kaya 2,000 domin rabawa ga jami’an. Kwamishina Kwaya-Bura, wanda kuma shi ne Sakataren Kwamitin Dakile Coronavirus a Jihar Barno, ya ce zuwa yanzu dai mutum 69 ne suka kamu a fadin jihar, yayin da cutar ta kashe mutum 9 a Borno din. Tun da farko dai Mataimakin Gwamnan Jihar Borno, Umar Kadafur, ya bai wa manema labarai hakurin fashin kwana daya da kwamitin wanda ya ke shugabanta ya yi bai yi musu bayanin komai ba. Ya ce hakan ya faru ne saboda ayyukan da suka rincabe wa kwamitin. Daga nan ya ce kwamitinsa na kokarin kara yawan gadajen kwantar da masu fama da cutar, daga 100 da ake da su zuwa 500, har ma 1,000.