AlmizanAlmizan logo
Jum'a 23 ga Ramadan, 1441 Bugu na 1445 ISSN 1595-4474

Rahoto

Kotu ta daure Dattijon da ya zagi Buhari

Daga Danjuma Katsina


Wuyan mai
Wata kotu da ke zamanta a Jihar Katsina a ranar Talata ya yanke wa wani Dattojo mai shekaru 70, Lawal Abdullahi Izala, hukuncin daurin watanni 18 a gidan Yari, bayan ta same shi da laifin zagin Shugaban kasa, Muhammad Buhari da kuma Gwamnan Jihar, Aminu Bello Masari.
Jami’an tsaro ne suka kama Lawal Izala da wasu mutum biyu, bisa zargin zagin Shugaban kasa Buhari da Gwamnan Jihar Katsina, Masari a cikin wani faifan bidiyo da ya yi yawo a kafofin sada zumunta na zamani. Sauran mutane biyu da aka tuhuma tare da Lawal Izala, sun hada da Bahhajje Abu da ya dauki zagin da kuma Hamza Abubakar da ya yada zagin a kafofin sada zumunta. Dukkan su suna zaune a unguwar Gafai da ke cikin garin Katsina. SAHARA REPORTERS ta ruwaito cewa, an gurfanar da Lawal Izala da mutanen biyu ne a gaban Kuliya ana tuhumar su da furta kalaman da ka iya tayar da zaune tsaye da kuma rashin yi wa Hukuma da’a ta hanyar furta maganganu na cin mutunci. A lokacin da yake magana da manema labarai bayan an kama shi ranar Talata, Lawal Izala ya ce ya yi furucin ne a cikin fushi lokacin da ya ziyarci kauyensu ya gano cewa ’yan bindiga sun kashe wasu ’yan’uwansa, sun kuma sace masu shanu 15. A cewar Lawal Izala; “Ina cikin tafiya aka tsayar da ni aka tambaye ni ya rayuwa? Lokacin na dawo ke nan daga kauye bayan ’yan bindiga sun kai hari, sun kashe ’yan’uwana, sun sace min shanu 15. “Sai na ce shugabanninmu; Buhari da Masari, sun ci amanar mu. Shi ne na yi zage-zage cikin fushi da bacin rai ba tare da sanin cewa ana nada a bidiyo ba. Ni kawai ina fadin gaskiyar abin da ke raina ne. Bayan faifan bidiyon ya zagaya a dandalin sada zumunta, sai ’yan sanda suka kama ni. An zarge ni da aikata laifi a karkashin kundin tsarin mulki.” A Hukuncin da ya zartar, Alkalin kotun ya ce an samu Lawal Izala da laifuka biyu na assasa fitina da rashin da’a ga Hukuma, don haka an yanke masa hukuncin daurin watanni shida a gidan gyaran hali na laifin farko. Sai kuma na shekara guda na laifi na biyu. Sai dai an bai wa Lawal Izala zabin biyan tara ta Naira dubu 10 a laifin farkon da kuma Naira dubu 20 a laifin na biyu. SAHARA REPORTERS ta ruwaito cewa wasu mutane masu tausayi a Jihar Katsina sun biya wa Dattijon kudin tarar da aka ci shi ta Naira dubu 30. Tun farko da da yake magana yayin baje kolin mutanen uku da aka kama, Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Katsina, SP Gambo Isah, ya ce an ankarar da su ne a kan wani faifan bidiyo da wani da aka fi sani da Izala, inda yake zagin Buhari da Masari a cikinsa. “A saboda haka, Kwamishinan ’yan sanda na Jihar Katsina, CP Sanusi Buba, ya ba da umarnin gudanar da bincike, wanda ya kai ga kama mutanen uku. A yayin da muke tuhumar su, wadanda ake zargi sun amsa laifinsu.” Ya ci gaba da cewa; “Duk wanda aka samu yana amfani da dandalin sada zumunta domin zagin wani mutum ko wasu mutane, zai fuskanci fushin doka, kamar yadda aka tanada a karkashin dokokin hukunce-hukuncen manyan laifuka a yanar gizo.”