AlmizanAlmizan logo
Jum'a 23 ga Ramadan, 1441 Bugu na 1445 ISSN 1595-4474

Rahoto

Mahara sun kashe mutum 50 a kwana 14 a Katsina -Masari

Daga Dakta Shu'abu Musa


 UN

Gwamna Aminu Bello Masari, ya tabbatar da cewa mahara sun kashe fiye da mutum 50 a cikin kwanaki 14 a Katsina.

Da yake jawabi a lokacin da karbi bakuncin jami’an tsaro da suka kai masa ziyara a gidan gwamnati shekaranjiya Laraba, Masari ya ce; “Rahoton da nake samu an kashe sama da mutane 50 a cikin kwana 14 da suka gabata, kuma an sace dimbin dabbobin mutane da jikkata wasu da dama”. Ya ce, tura ta kusa kai bango, jama’a sun fara fusata suna neman daukar matakin kare kansu. “Al’ummar yankin Karamar Hukumar Faskari har sun yi yinkurin daukar makamai domin tunkarar wadannan ’yan bindigar a cikin daji da karfe 3:00nd”. Masari ya ce; “Ko daren jiya (Talata), ’yan bindigar sun kai wasu tagawayen hare-hare a Karamar Hukumar Sabuwa da Faskari, inda suke kashe mutum biyar nan take. DPO mai kula da Karamar Hukumar Faskari, ACP Aminu Abdulkarim, sun harbe shi, yanzu haka yana kwance a asibitin kashi da ke nan Katsina rai a hannun Allah. “Har ila yau, Kantoman riko na Karamar Hukumar Danmusa, Yahaya Musa Sabuwa, sun sace shi har da dansa, yanzu haka suna hannunsu. ’Yan bindigar sama da 100 suka je. Haka kuma sun shiga wani kauye a Sabuwa sun kashe mutane biyar, sun sace masu dabbobi,” in ji Gwamnan. Ya ce abin nan fa kara ta’azzara yake; “Mutanenmu na shiga mawuyaci hali, saboda yadda ’yan bindigar nan ke kai hare-hare, kusan kullum ana kashe su, ba ta cutar Korona suke ba, ta annobar cutar ’yan bindigar suke,” ya ce. Ya kara da cewa, ko jiya sun je kauyen Lallaba da ke Karamar Hukumar Batagarawa, sun kashe Mai Unguwar garin, tsoho mai shekara 80, Malam Lawal Auta. Bayan sun faffalla masa mari, kuma suka kashe. Sun kashe wani ma’aikacin Hukumar Alhazai ta Jihar Katsina, Faruk Lawal Bakiyawa a gidansa. ’Yan bindigar na cin karensu babu babbaka ne a Kananan Hukumomi Batsari, Safana, Danmusa, Jibia, Faskari, Sabuwa, Batagarawa da Dutsinma. Kusan kullum sai an kai masu hari an kashe su duk da sasanci da aka yi da su. Rundunar ’yan sanda ta Jihar Katsina, ta bakin Kakakinta, SP Gambo Isa ta ce, suna bincike kan wadannan tagawayen hare-hare.