AlmizanAlmizan logo
Jum'a 17 ga Sha'aban, 1441 Bugu na 1440 ISSN 1595-4474

Rahoto

Rimi: Shekara 10 na rasuwar Limamin Canji

Haruna Uba Jahun


Wuyan mai

Kamar yadda na saba yi duk bayan na yi Sallar Asuba da kuma sauran ayyuka na ibada, nakan kama rediyo domin sauraron labaran duniya, musamman a shekarun baya lokacin da babu ci gaba na kafafen sada zumunta na zamani a waya, idan ban makara ba, nakan fara da sauraron tashar Hausa ta Muryar Amurka. Daga nan idan sun kammala sai na koma sashin Hausa na BBC.

Ba na manta ranar Litinin 5/4/2010 ina kama Muryar Amurka da safe, babban kanun labaransu na ranar shi ne; “Jiya Lahadi 4/4/2010 Allah ya yi wa tsohon Gwamnan Kano, tsohon Ministan sadarwa, kuma jigo a jami’iyyar PDP, wato Alhaji Mohammadu Abubakar Rimi rasuwa.”

Bai yi wata jinya ba, illa iyaka kamar yadda mutane da dama ke hasashe ya hadu da bugawar zuciya ne sakamakon tare su da ’yan fashi da makami suka yi a hanyarsa ta dawowa Kano daren wannan ranar. Sannu a hankali yau shekara 10 ke nan da faruwar wannan lamari.

Marigayi Alhaji Muhammadu Abubakar Rimi dan siyasa ne gogagge, wanda ya cancanci a ambace shi da dukkan kalmomin yabo a siyasa. Ga shi ɗan sarauta, amma da kishin talaka. Hakikanin dan dimokaradiyya ne wanda ya ba da lokacinsa domin tabbatuwar dimokaradiyyar. Mutum ne wanda yake da tabbacin abin da ya sa a gaba, sannan yake yakin ganin ya cimma wannan manufa tasa ba tare da jin tsoro ba. Saboda iya kalamansa na rashin jin tsoro ya sa gab da karshen jamhuriyya ta biyu, sai da Rimi ya zama sautin muryar da shi ake sauraro a kan sauran Gwamnonin Nijeriya.

Lokacin da aka zabe shi farkon Gwamnan Jihar Kano a shekarar 1979 a jamhuriyya ta biyu, gwamnatinsa ta ba da himma da fifiko a kan ayyukan da za su taba rayuwar talakawan da suka zabe shi. Wannan ne ma ya sa tun ranar rantsar da shi a Gwamnan Kano bai yi wata-wata ba ya soke biyan haraji da jangali da Sarakuna suka kakaba wa talakawan kasa. Rimi ya kira wannan da ci gaba da zaluncin da ake yi wa talaka, shi ya sa kuma ya soke shi.

A gwamnatinsa ya tattaro masana masu shaidar karatun Digiri a fannoni daban-daban, kuma ya bai wa kowa fannin da ya dace da karatunsa domin ya kawo gudummawarsa wajen gina Jihar Kano. Sannan ya ba su dukkanin irin dama da kuma ’yancin da suke bukata wajen aiwatar da aikinsu. Kodayake shaidar Digiri a Jami’a ba shi ne ke da tabbacin cewa mai rike da wannan shaidar zai yi abin da ya cancanci a yaba masa ba, amma a gwamnatin tasa an yi nasarar hakan.

Kuma bincike ya nuna cewa a duk Gwamnonin jamhuriyya ta biyu babu Gwamnan da ya fi shi kokarin aiki da kuma cimma nasarori a bangarori daban-daban na shugabanci. Batun ayyuka masu muhimmanci da nagarta, za a iya bugar kirji a ce, a tsohuwar Jihar Kano ta da wadda ta hada da Jihar Jigawa ta yanzu, babu bangaren da Alhaji Abubakar Rimi bai taba ba. Kiwon lafiya, samar da ruwan sha ne, gina sabbin titunan mota, da kuma ayyukan kyautata rayuwar mutanen karkara.

Sai dai duk wadannan babu inda Rimi ya fi cira tuta kamar bunkasa ilimi da ba shi dukkan kulawar da ta kamaci a ba shi. A zamanin mulkinsa aka farfado da ilimin manya ta hankar kunna wutar yaki da jahilci a dukkan fadin Jihar. Allah ya ji kan Alhaji Mudi Sipikin, shi aka danka wa wannan Hukuma. Wannan ya taimaka ainun wajen samar da mutanen da suka koyi karatu da rubutun zamani sakamakon wannan shiri. Sannan shi ne ya fito da tsarin fitar da dalibai hazikai wadanda suka ci jarabawarsu sosai zuwa kasashen waje karatu, musamman karatun Likitanci kasantuwar a lokacin Jihar Kano tana matukar bukatar Likitocin.

Duk da a gwagwarmayar siyasa da kokarinsa na tabbatuwar dimokaradiyya an kama Rimi, an kuma daure shi a zamanin Buharin soja da kuma Janar Sani Abacha, wadannan ba su zama abin da-na-sani a tattare da rayuwar siyasara ba, kamar sabanin su da Malaminsa na siyasa, wato Malam Aminu Kano ba.

Rigima ce da asalinta zai yiwu Rimi ne da gaskiya, amma sakamakon zafafan kalamansa gami da irin balahirar adawar da ya nuna wa Malam din, sai ya lullube duk irin kokarinsa da nasarorin gwamnatin tasa. Domin duk irin hidimar da za ka yi wa jam’iyyar PRP a Kano da Kadunan, matukar za ka daga wa Malam Aminu yatsa, to za ka fada kwandon tarihin siyasa. Wanda a wannan yanayi shi ba yatsa kawai ya nuna wa Malam ba, har da lakacar hancinsa da yatsan duk ya yi.

Duk wanda ya san rikicin Santsi da Tabo zai tabbatar da cewa wasu wayayyun ’yan siyasar birni ne wadanda suke kewaye da Malam Aminu, suka mai da shi kamar fursunanan da za su dinga aron bakinsa suna ci masa albasa. Wadannan ’yan siyasar birni sune domin biyan bukatar kansu suka kunna wutar fitinar tun daga nada Kwamishinoni zuwa shigar Gwamnonin taron babbar jam’iyyar maja ta PPP, wanda jam’iyyun adawa na lokacin wato UPN, GNPP, PRP da kuma NPP suka so kafawa. Sannu a hankali sun yi ta rurata wutar gaba tsakanin Malam da Rimi har ta kai ga korar Rimi daga jam’iyyar PRP.

Babbar matsalar da siyasar Nijeriya ta samu a yau shi ne rushewa da komawa siyasar neman abin duniya ta hanyar karya, yaudara da kuma cin amana. Wannan rashin manufa da akida shi ya haifar da samun makiya dimokaradiyya a jiya, su zama shugabanni karkashin siyasar a yau. Galiban din ’yan siyasar yanzu, suna rudin mutane da dimokaradiyya ne lokacin yakin neman zabe, a ranar zabe su tafka magudi. Idan sun hau kujera, maimakon su yi wa al’umma aiki, sai su koma farautar ’yan adawa da cin amanar wadanda suka zabe su.

Wannan shi ne bambamcin siyasar akida ta gidan Malam Aminu Kano, wanda dalibinta Rimi ya aikata ta a aikace. Kuma da a ce Rimi ya samu shugabancin Nijeriya lokacin da ya fito takarar neman tsayawa a shekarar 1999, da mai yiwuwa sai ya fi duk shugabannin da aka yi kataɓus. Saboda aikinsa yana nan har yanzu ana morar sa. Sabanin na yanzu masu yaudarar mutane da sunan canjin da babu komai a cikin sa ban da farfaganda, bakar wahala da mugun talauci da dasa muguwar gaba a tsakankanin al’umma. Allah ya ji kan Rimi, Limamin canji.