AlmizanAlmizan logo
Jum'a 17 ga Sha'aban, 1441 Bugu na 1440 ISSN 1595-4474

Rahoto

Jama’a na dandana kuda sakamakon rufe hanyoyin shiga Sakkwato

Daga Abubakar Usman


 UN

Jama’a na shan wahala sosai sakamakon rufe hanyoyin shiga cikin garin Sakkwato da gwamnati ta yi a kokarinta na dakile yaduwar cutar Koronabairus.

Wannan matakin na rufe Sakkwato ruf da gwamnatin Aminu Waziru Tambuwal ta yi, ya biyo bayan wata ganawa ne da ya yi da Sultan Sa’adu Abubakar, Malaman addinin Musulunci, Sarakunan gargajiya, jami’an kiwon lafiya da bangorin jami’an tsaro na Jihar domin daukar matakin hana shigowar cutar COVID-19, wacce ke yaduwa tamkar wutar daji.

Jim kadan da kammala zamansu, Tambuwal ya bayyana wannan matsaya da suka cimma, wanda kafafen yada labarai na Jiha da masu zaman kansu suka sanar.

A cikin jawabin nasa, Gwamna Tambuwal ya bayyana cewa; “Duk da har yanzu ba mu da wani a cikin wannan Jihar da ya kamu da wannan cutar, amma ya zama wajibi gare mu bisa ga shawarar Likitoti da kuma tanadin addinin Musulunci mu dauki matakin hana shigowar wannan annobar.”

Ya kara da cewa; “Gwamnatin Jihar Sakkwato ta kafa kwamitin kula da yakar wannan cutar da kuma ba da shawara a kan daukar matakin kare lafiyar al’ummar Jihar Sakkwato a karkashin shugabancin Dakta Ali Inname.”

Ita dai wannan dokar, wacce ta fara aiki tun daga ranar Juma’a 27/3/2020 zuwa yau Juma’a 10/4/2020, ta tanadi hana jama’a shigowa garin Sakkwato ta bangarorin da ake shigowa garin. Sai dai dokar ba ta shafi masu dauko kayan abinci ba da kuma magunguna.

Wakilinmu ya lura da yadda jama’a a kan iyakar shiga Sakkwato daga Zamfara ke dandana kudarsu, sakamakon yadda jami’an tsaro suka killace hanyar shiga Jihar tun daga garin Bimasa da ke kusa da Lambar Tureta da ke da nisan kilomita 60 da shiga garin Sakkwato.

Jama’a na keta daji ne suna yin tafiyar fiye da kilomita 10 a kafa dauke da kayansu kafin su isa wajen da za su hau abin hawan da zai shigar da su cikin garin Sakkwato.

Jami’an tsaro ba su barin kowa ya shiga, ko ya fita, a kafa yake ko a kan abin hawa, sai dai in masu kayan abinci ne, ko magunguna, ko kuma masu aiki na musamman kamar ’yan jarida da masu aikin kiwon lafiya. Su ma sai an gwada zafin jikinsu, an dauki sunaye da lambobin wayarsu, bayan sun wanke hannaye da kuma ba su abin da za su shafa a hannunsu don gudun kamuwa da cutar Kornabairus.

A lokacin da Wakilinmu ke zantawa da daya daga cikin jami’an tsaron da ke aikin kula da shige da ficen, ya bayyana cewa sun dauki tsattsauran matakin hana shiga garin Sakkwato ne don gudun kar a shiga a yada masu cutar Koronabairus.

Jami’in, wanda ya bukaci mu sakaya sunansa, ya musanta zargin da ake yi masu na amsar na-goro kafin su bar mutane su wuce. Ya ce; “Allah yana ganin aikin da muke yi a nan, ba ma amsar cin hanci, amma an je ana ta yadawa cewa muna amsar na-goro kafin mu bar mutane su wuce”.

Sai dai yayin da aka rufe kan iyakokin shigowa Jihar Sakkwato, amma a cikin garin an bar kowa yana walwalarsa, ba tare da takurawa ba, sabanin yadda abin yake a Kaduna, wacce ita kuma ta bari ake a shiga a fita, amma ba zirga-zirga ko bude masallatai, coci-coci, makarantu da kasuwanni.

Wakilinmu ya lura ita ma Jihar Zamfara ba ta hana shiga da fita ba, amma duk wanda zai shiga ko fita, sai an gwada zafin jikinsa, sannan ya je ya wanke hannunsa da ruwan da aka tanada, a shafa masa maganin kariya daga cututtuka kafin ya wuce.