AlmizanAlmizan logo
Jum'a 17 ga Rabi'ussani, 1440 Bugu na 1380 ISSN 1595-4474


Rahoto

Kasar nan ba ta ga canji na alheri ba -Sanata Mamman Abubakar Dan Musa

Daga Danjuma Katsina


 Shema Ibrahim

Daya daga cikin Dattawan Katsina masu mutunci, Alhaji Mamman Abubakar Dan Musa, wanda yake tsohon Sanata ne, kuma tsohon Kakakin Majalisa a tsohuwar Jihar Kaduna, kuma gogaggen Lauya ya ce; “Sam kasar nan ba ta ga wani canji na alheri ba a hawan jam’iyyar APC kasarkashin jagorancin Muhammadu Buhari”.

Sanata Dan Musa, wanda ya bayyana haka a taron manema labarai da aka yi a dakin taro na gidan Abba Saude a Katsina, ya ce, lokacin shiru ya kare, dole ne Dattawa irin su, su fito su yi magana.

Ya kara da cewa; “Tsaron da ake maganar an samu, a kwanan nan Gwamnan Katsina sukutum ya fito ya ce masu satar mutane da barayin daji sun yi wa Jihar kawanya. A jawabin na Gwamna ya ce, hatta shi kansa bai tsira ba. Sa’annan kuma kwanan nan ne aka tare Galadiman Katsina, Hakimin Malumfashi, aka tafi da mai masa hidima.”

Sanata Mamman ya ce garinsu na Dan Musa ya zama kullum waje ne na hari da sata, wanda ta kai dole ne sai da jama’a suka hada kansu don kare kansu daga hare-haren mabarnata.

“Kasuwar Dan-Musa, wadda tana daya daga cikin kasuwanni mafi girma a Katsina, yanzu ta zama kufai, an kaurace mata saboda tsoron ’yan fashi da masu satar mutane,” in ji shi.

Dan Musa ya kara da cewa, saboda wannan ta’annati, yanzu matasanmu sun zama ’yan gudun hijira a garuruwan kudancin kasar nan a Jihohin Benin, Lagos da Osun, sun bar gonakinsu da barayin shanu suka hana su nomawa, sun koma Kudu da kuma Yammacin kasar nan neman abinci.

Dan Musa ya ci gaba da cewa; “Ya za ka ce mu yi shiru, wannan bala’in da ya shafe mu? Kalli abin da ke faruwa a Jihar Zamfara makwabciyar Jiharmu, da kuma abin da ke faruwa a Kananan Hukumomin Jibiya, Batsari, Safana, Dan Musa, Kankara, Faskari, Dandume da kuma Sabuwa na kisa da satar mutane. Kuma har yanzu an ki fada wa jama’a cewa ga mafita.”

Sai Dan Musa ya ce; “Ranar Asabar mai zuwa za a yi zaben Shugaban kasa, kuma ni Mamman Abubakar Dan Musa na yi wa Muhammadu Buhari, kamfen a shekarun 2007, 2011 da 2015, amma gaskiyar magana bayan zaben na Buhari a matsayin Shugaban kasa ba a abin da na gani a yankina, sai rashin tsaro mafi muni. Kuma tsaron da ake magana an samu an mai da hankali ne kawai a Jihohin Arewa maso Yamma. Wato tsohuwar Jihar Barno. Amma mu a Jihohinmu inda Shugaban kasa ya fito, yanzu muke a cikin tashin hankali.”

Dan Musa ya ce hatta nasarar da ake ikirarin an samu na tallafa wa manoma, tatsuniya ce kawai, duk mai so kuma ya je ya tambayi manoman Jibia, Batsari, Safana ko Dan Musa za su fada masa gaskiyar halin da suke ciki.

Ya ce; “A kan karyar an farfado da masana’antu, duk Katsina a fada mana masana’anta daya da aka farfado da ita, wadda matasanmu suka samu aikin yi a cikinta? Amma a kudancin kasar nan irin su Jihohin Ogun da Abia, duk sun ga hakan. Kuma masana’antunsu, na ta daukar matasansu aiki.”

A kan maganar yaki da cin hanci da rashawa kuwa, Sanata Dan Musa ya ce; “Yaki ne kawai wanda yake kamawa da hukunta duk wadanda aka dauka a matsayin makiyan gwamnatin da ke kan mulki.”

Ya ce; “Da farko gwamnatin ta sama ta ce, za ta bayyana sunayen wadanda ake tuhuma da kaddarar da aka kwace a wajensu, amma har yanzu saura kwanakin zabe kaza, amma ba su yi hakan ba. Kuma kwanan nan kungiyar da ke sa ido ga kasashe a kan cin hanci a duniya (TIN), ta ce yakin da Nijeriya ke yi da cin hanci takaitacce ne.”

Dan Musa ya kara da ce wa, masu rike da mulkin nan su sani, yadda yanzu suke tuhumar wadansu haka wata rana za ta zo a kansu, don an yi irin haka a kasashen kudancin Koriya da Birazil. A kasar Birazil, tsaffin shugabanin kasar biyu aka kama da laifi, kuma yanzu haka duk suna gidan yari.”

Ya ci gaba da cewa; “A kasar Koriya kuwa tsohon Shugaban da abokan kasuwancinsa, duk suna gidan yari. In lokacin ya zo komai tsufan mutum sai ya fuskanci hukunci. Don haka ta faru ga shugabanni kamar Ruz a kasar Kambodiya.”