AlmizanAlmizan logo
Jum'a 17 ga Rabi'ussani, 1440 Bugu na 1380 ISSN 1595-4474


Rahoto

Cutarwar 'yan Izala ga 'yan Shi’a a Najeriya (xiii)

TARE DA M.I. GAMAWA 09071965492


Mun dan runtsa a satin da ya gabata kan rikicin Sunna Clinic. Da sunnar ce ta Manzo, tabbas babu mai ikrarin mallakar ta har a tashi bai wa hammata iska domin ta. Amma sunna ce da aka rikidar da ita ta zama asibiti, dole a yi warwaso wajen mallakar ta. Wannan dai shagube ne kawai. Bari mu shiga aiki.

Rikicin Sunna Clinic da wasu masu kama da haka sun kara fadada tsoho da sabon alkawari masu manyan birane a Jos da Kaduna. Garuruwa biyu da wani Sufi mai ganin badini ya ce, "Duk wanda ya dimanci zama a cikin su zai zama shakiyi mashayin giya mai yawan sabo, sai dai kariyar Allah." Amma wani abu da wannan Sufi ya boye mana don tausayi shi ne zaman garuruwa biyun sansanin da za a yi amfani da su wajen wargaza hadin kan musulmi.

Abubuwan da muka ambata a satin da ya gabata a matsayin sanadin rabuwar kan 'yan Izala kadan ne daga cikin abubuwa masu tarin yawa. Ba mu yi maganar hassada da jin kai da ba su da magani a gun Likitan asibiti ba. Wadannan laifuka da muka ambata sun yi katutu a gun Malaman Izala har da na kai wa kasuwa don nemo riba. Su kuma wadannan cututtuka maganin su yana wajen Malaman tarbiyar ruhi. Su kuma sune abokan gaba na farko a gun Izalawa.

Dole aka bar wa Mu'assis Sunna Clinic. Dole ba don dadi ba. Darewar Izala gida biyu ya kara yawan masallatai da mahautu. Ya kuma kara wa magabta dandalin ayyana gaba da juna. Kowa ya kama gabansa da abincin da ya ci a cikinsa. Duk inda ya je zai zubar da abin da ke cikin sa ne. Kiyayya ga Darika da Shi’a sune suka hada tsoho da sabon alkawari.

Wannan rabuwa ba ta bai wa uwargijarsu, wato Saudiyya wata mas'ala mai yawa ba. Sai dai ta nemi a sasanta, amma abin ya ci tura daga baya. An yi bukin sasantawa, sai dai kafin a yi bikin, bakin alkalami ya bushe. Wasu da ke jagorantar bangarori sun soma jin dadin shugabanci, don haka da wuya su dawo su rika zaman bi-ta-zai-zai.

Dole rarraba ta zama ciwon ido, sai hakuri. Aka gwammace a tafi a haka. Bukatar maje hajji aikin hajji, kamar yadda Hausawa ke fada. Bukatar kafa Izala tun farko ita ce farraka musulmi. Ga shi an farraka mai farrakawa. Dadi kan dadi, wai kunama ta harbi gyambo.

Bari mu dawo ga rasuwar Mufti Gumi. Idan ganga ta cika zaki, tabbas ta yi kusan fashewa ke nan. Rasuwar Mufti Gumi ta sake sabbaba wa Izala wata baraka mai yawa. Na farko da Gumi zai tafi asibiti Ingila ya mika duk abin da yake karantarwa da shi a masallacin Sultan Bello ga Shaikh Sunusi Gumbi. Gumbi ba bako ba ne a wannan aiki. Ya saba ya daure. Duk lokacin da Gumi zai yi tafiya, shi ke karatun hadisi ko tafsiri. Ashe masu hankoron Gumbi sun yi likimo ne kawai.

Ganin ido na hana cin fuska, kamar yadda Bahaushe ke fada. Rashin sanin tahakikin halin da Mufti Gumi ke ciki a Ingila, ya sa magabtan Sunusi Gumbi sun daga masa kafa. Amma da aka samu labari maras dadi na rasuwar Mufti Gumi, sai maitar mayu ta bayyana a fili. Suka fara farautar kurwar Sunusi Gumbi a bayyane. Bayan jana'izar Mufti, sai rigimar wa zai gaje shi? Mutane biyu sune suka kallafa wa rayukansu haye wa kujerar Mufti. Na farko Shaikh Sunusi Gumbi. Na biyu Mu'assis Is'ma'ila Idris. Sai dai ’yan fada suna da nasu da suke so ya gaji Mufti Gumi.

Tabbas Gumi ya bar wa Gumbi karatun da ya saba gabatarwa a masallacin Sultan Bello, amma bai bar wasiyyar wa zai gaje shi in rai ya yi halinsa ba. Gama zaman makoki ke da wuya sai neman nesanta wadanda ake ganin sune ke kaiwa kujerar Mufti bara ya kankama. Wani rikici sabo fil ya sake yi wa Izala kamun kazar kuku. Da Mu'assis ya fahimci cewa kifi ya yi wa kaska nisa, sai ya goya wa wanda aka jaza wa hawa kujerar baya a fakaice. Wanda 'yar canken ta fada kansa shi ne Shaikh Lawal Abubakar, tsohon almajirin Mufti Gumi.

Daga nan Shaikh Sunusi ya kama gabansa, ya zura na mujiya. Ba za mu shiga dalilan da suka jawo hana Shaikh Sunusi hawa kujerar Mufti Gumi ba, duk da yake Gumi da kansa ya ba shi dani na lokaci zuwa lokaci a sa'ad da yake raye.

Rashin Shaikh Gumi ya mai da Izala mareniya a kasar Saudiya na wasu lokuta. Da a ce Gumbi ya gaji Gumi, da zai yi wuya a ce kawance da Saudiyya ya samu tsaiko. Amma nada Malam Lawal a matsayin magajin Gumi ya sabbaba wa Izala shiga wani kullallen dakin da ba a jin muryarta a inda ba a san ta ba kafin tafiyar Mufti Gumi. Na daya tafiyar ta mai da ’yan boko saniyar ware, ba wai don an kore su ba, sai dai don suna ganin Malam Lawal Abubakar a matsayin tsohon yayi. Rashin iya Turanci ta janibin Shaikh Lawal ya kara jan ragamar Izala baya a siyasar Najeriya. Wato ya kara maida ta a matsayin kayan mutanen Arewa Hausawa kawai. Da ma Saudiyawa ba su san Malam Lawal Abubakar ba. Rashin sanin sa gare su na da dalilai masu yawa. Ga kadan daga cikin su:

Malam Lawal ya shagalta da abin da ya shagaltar da shi - Limanci da wa'azozi ta rediyo. Ya tsaya a matsayinsa. In Mufti ya gayyace shi tafiya, su je. In ba a gayyace shi ba, yana inda aka tsai da shi. Malam Lawal ba shi da shisshigi. Ba shi da son a sani. Kadimi ne ta wajen biyayya ga Malamansa da yadda yake tafiyar da almajiransa. Bai taba yarda da kafirta masallata ba. Kuma yana mu'amala mai kyau da Maluman da babban Malaminsa Mufti Gumi ke takun saka da su.

Fakam da yawa fahimtarsa, kan saba da ta Mufti, amma sai ya nuna iyakar dabara wajen bijire wa matsayar Mufti. Misali, lokacin da Mufti Gumi ya ce, "Siyasa ta fi salla," da aka tambayi Malam Lawal don karin bayani, nan take ya ce, "A je wajen Malam, ni ma ban fahimci maganar ba, balle in kara bayani a kanta." Malam Lawal ya yi rayuwarsa baina-baina ne a duk tsawon rayuwarsa da Izalawa. Ba ya zuwa wa'azin kasa balle na jiha. Wata rana an je wa'azin kasa Kaduna. Ganin Malam Lawal a wurin ke da wuya, sai aka ba shi maudu'in magana kan Shi’a da illolinta. Malam Lawal na hawa kan mumbarin wa'azi ya ce. "An ce in fadi Shi’a da illolinta. To, ban sani ba." Yana fadin haka ya sauka daga mumbari ya je ya zauna.

Tabbas Malam Lawal, sabanin Malaman Izala, ya dauki maganar hisabi bayan mutuwa da muhimmancin gaske. Sabanin yadda da yawansu ke ba da labarin Shi’a, alhali ba su taba karanta ko littafi daya na Shi’a ba, domin rashin daukar ranar hisabi da gaske ko shagaltar su da ita ranar. Shi Malam Lawal yana tsananin taka tsantsan wajen ba da fatawa. Yakan tabbatar ya taka dutse, kafin ya ce a yi wasan jifa. Wato ba ya fadin abin da bai sani ba, don mutane su dauke shi Malami.

Haka ne halin Malam Lawal. Amma me ya sa duk da haka aka zabe shi ya gaji Mufti Gumi sabanin Sunusi Gumbi? Yawan magabtan Sunusi Gumbi a fadar Mufti shi ne abu na farko. Na biyu rufe wa mu'assis Isma'ila Idris kofar kujerar halifanci. Na uku rike wa da daya tilo na Mufti Gumi da ya tafi bidar ilimin addini a kashin kansa, wato Dakta Ahmad Gumi. ’Yan fada na ganin cewa, in Ahmad ya dawo ya haye kujerar Babansa, to uwar daki Saudiyya za ta dawo da tallafi kamar yadda take yi a lokacin Mufti.

Halifantar da Shaikh Lawal Abubakar ke da wuya, sai wata barakar ta sake kunnowa. Shaikh Sunusi bai ce komai a bayyane ba. Amma ta ciki na ciki. Sai dai ya kauracewa tafsirin da Shaikh Lawal ya fara a mazaunin marigayi Mufti Gumi.

Shi kuma Mu'assis ya taba fada a fili cewa, "dan Darika ya gaji Malam. " Bai taba kiran Malam Lawal dan Darika ba, sai a wannan karon. Ya dai taba kiran Malam Lawal matsoraci a lokacin da yake ba da labarin dalibtarsu a wajen Gumi a lokacin da Maluma suka mai da shi Gumin saniyar ware. Su kuma ragowar almajiran Mufti da suka surfa suka nika, sai suka kame bakunansu suka yi shiru, kamar an samu kayan sata a gidan maroki.

Da 'yan takara biyu suka rasa kujerar Mufti, sai su biyun suka koma inda suka fi wayo. Mu'assis ya koma Jos inda ya fi wayo. Da ma Mu'assis yana neman cika burinsa ne da samun kujerar Gumi, amma da haka ba ta samu ba, sai ya koma Jos ya ci gaba da fadada tsohon alkawarinsa. Shi kuma Gumbi sai ya koma zauren gidansa ya rika ba da karatu. Da ma can bai kutsa cikin Izalawa kwansa da kwarkwatarsa ba.

Za mu ci gaba insha Allah.