AlmizanAlmizan logo
Jum'a 17 ga Rabi'ussani, 1440 Bugu na 1380 ISSN 1595-4474

Rahoto

Hako mai a Bauchi: Masu filin sun ce ba a biya su kudin diyya ba

Daga Ukasha Idris


 mallam

A 'yan kwanakin da suka gabata ne Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da fara hako mai a Kogon Kolmani II da ke kauyen Baranmu a Karamar Hukumar Alkaleri a jihar Bauchi.

To, sai dai kuma fa, duk da ci gaban da kasa take daf da fara samu daga wannan dimbin albarkatun a wannan yankin, mazauna kauyen da aka shiga gonakansu sun koka sosai a bisa rashin samun kudaden diyya na filayensu da gwamnatin ba ta ba su ba har zuwa yau, inda suka nemi agajin Gwamnati ta hanun kamfanin NNPC da su yi wa Allah su biya su diyyar kudadensu domin su rage radadi.

Wasu masu filayen da muka zanta da su jim kadan bayan da Shugaban kasa ya kammala kaddamar da aikin, sun shaida cewa sun so su samu damar da Shugaban kasar zai ji korafinsu, amma sakamakon hana su ketara layi, muryarsu bai kai a ji ba, inda suka nemi 'yan jarida da su taimaka musu domin a san halin da suke ciki.

Daya daga cikin masu filin, Haruna Adamu, wanda manomi ne, kuma mai kiwo a kasar Barambu, ya ce, “Wannan filin da ake aiki yanzu haka a ciki, filayenmu ne da muke noma a ciki. An samu albarkatun kasa a wannan wajen, masu wannan aikin sun ki biyan mu diyya har zuwa yau. Sannan ana aikin nan, mu jama’an wannan kauyen an mai da mu ba mu da wani amfani, domin ba mu cin gajiyar aikin da ake yi, sai dai wasu su zo su ci arziki a wajen. Ba su neman mu a ciki, ko da leburanci ne, sun kuma hana mu noma a filin.”

Ita kuwa Altine Alesha, wacce ta koka da bayanin halin da suka tsinci kansu, ta yi kira da babbar murya ga wadanda abin ya shafa domin agaza musu. A cewarta: “Gonakinmu da mazajenmu suke nomawa, an share wajen, an dauki wajen, an kama aikin mai a filayen, ba tare da duba halin da za mu shiga ba. Ko a bana ma, an hana mu yin noma gaba daya a wajen. Sannan kuma bara sun zo sun sare filayen, suka ce za su biya kudin diyya idan an fara aikin, ga shi an jima da fara aikin, amma har yanzu sisi, ba mu gani ba. An kai takardunmu, an shigar da shi can wajen, an ce mana za a biya, amma har yanzu ba a biya mazajenmu ba."

Da yake mai da martani kan wannan zargin na mazauna kauyen, daya daga cikin masu kwantiragi a wajen, da ya nemi 'yan jarida su sakaye sunansa, ya shaida cewa, jama’ar yankin su kara hakuri, za a biya su hakkinsu. Batun biyan kudin diyya na wannan filin na hanun APS da ke karkashin NNPC. Don haka kudin na hannun kamfanin NNPC. Amma gaskiya ko mu muna jin zafin rashin biyan su kudinsu, amma su kara hakuri, za a biya su.”