AlmizanAlmizan logo
Jum'a 17 ga Rabi'ussani, 1440 Bugu na 1380 ISSN 1595-4474

Rahoto

‘Har yanzu ana kashe mutane a yankin Birnin Gwari’ in Sanata Shehu Sani


Wuyan mai

Sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani ya bayyana wa manema labarai cewa, har yanzu ana ci gaba da kashe mutane a yankin Birnin Gwari.

Shehu Sani, wanda ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Minna ta Jihar Neja, ya ce, “Akalla mutane 21 ne aka bayar da rahotannin an kashe a kauyakun Birnin Gwari ta Jihar Kaduna a tsakanin ranekun Alhamis da Juma’a na makon da ya gabata.”

Ya koka matuka da halin rashin tsaro da ake fama da shi a yankin Birnin Gwari da kuma Jihar Zamfara. “Abin damuwa ne da ban tsoro, domin a kullum mutane ne ake ta yi wa kisan gilla.

“Abubuwan da suke faruwa suna da ban tsoro, hatta wadanda suka je rufe mamatan ma ’yan ta’addan suna kai masu farmaki a makabarta, ana sace su zuwa wasu wuraren da ba wanda ya sani. Sai dai su gudu su bar gawawwakin a watse ba tare da mai rufe su ba, wadanda suka sami nasarar tsira su tsira,” in ji Sanatan.

Shehu Sani ya tabbatar da cewa; “Na sha biyan kudin fansa wajen fansan wasu daga cikin masu yi mani aikin da aka sace. Wannan abin takaici ne,” in ji shi.

Sanata Shehu Sani ya nuna bakin cikinsa na yadda ya kasa zuwa Birnin Gwari ta hanyar Kaduna, har sai da ya biyo ta hanyar Suleja zuwa Minna, ya bi ta Kagara kafin ya isa Birnin Gwari din.

“Mutane masu yawa duk sun bar kauyakunsu. Sun sayar da gidajensu da gonakinsu a yanzun suna zaune ne a wasu wuraren da suke zaton samun zaman lafiya, tabbas wannan zai shafi wannan zaben. Domin ta yaya mutane za su iya yin zabe a wuraren da ba su yi rajista ba? Ta ya za su iya fitowa su yi zabe alhalin kasa babu tsaro?” In ji shi.

Sai dai, a ranar Lahadi, rundunar ’yan sanda ta Jihar Kaduna, ta musanta zargin cewa an kashe akalla mutane 21 a kauyakun a yankin na Birnin Gwari a cikin kwanaki biyu kacal a Jihar.

Kakakin rundunar, DSP Yakubu Sabo, ya shaida wa manema labarai cewa wannan zargin da Sanata Shehu Sani ya yi ba gaskiya ne ba. “Sam ba gaskiya ba ne. Sam rundunarmu ba ta da labarin aukuwar wani abu makamancin haka a tsakanin wannan lokacin,” in ji shi.

A wani labarin kuma, jama’ar garin Rijana da ke hanyar Abuja, sun koka matuka da halin da zaman dardar din da suke ciki, saboda yadda masu garkuwa da mutane. Hakan na zuwa ne kwana daya bayan an sace mutane 50 a kusa da garin nasu.