AlmizanAlmizan logo
Jum'a 17 ga Rabi'ussani, 1440 Bugu na 1380 ISSN 1595-4474

Rahoto

Kwankwaso ya bayyana babban kuskuren da Buhari ya yi a Kano

Daga Sani Hamisu


 UN

Tsohon Gwamnan Kano, Rabi’u Musa Kwankwaso ya yi hira a gidajen rediyon Kano inda ya tattauna a kan manyan batutuwan da suka shafi zaben 2019 da yake kusantowa a Najeriya.

Rabi’u Kwankwaso ya bayyana cewa, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi kuskure mai girma na fada wa Duniya cewa a sake zaben Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, wanda ake zargin sa da karbar rashawa ta makudan Daloli.

Kwankwaso, wanda ya nemi takarar Shugaban kasa a PDP, inda ya sha kashi wajen zaben fitar da gwani, ya bayyana cewa, ko kadan ba zai ki Abba Yusuf ya nada shi cikin masu ba shi shawara idan ya zama Gwamna a zaben 2019 ba.

Injiniya Kwankwaso ya ce, ba aibu ba ne don ya zama mai ba Gwamnan Kano shawara a kan harkar ilimi ko aikin ruwa, domin a nan ne ya samu kwarewa.

Kwankwaso ya kuma ce, dole a mai da hankali kan ilimi, domin fetur ya kusa daina rana.

Abba Yusuf wanda shi ne dan takarar Gwamna a PDP ya samu tikiti ne a dalilin Rabi’u Kwankwaso, wanda hakan ya sa wasu manyan ’yan Kwankwasiyya suka koma APC, bayan sun rasa tikitin Gwamna a karkashin jam’iyyar adawar.

Tsohon Gwamna Kwankwaso ya ce, bai ki gobe wadanda suka sauya sheka su dawo a ci gaba da tafiya a jam’iyyar PDP ba.

Sanatan na Kano ya kara da cewa, "dama can wadannan manyan ’yan siyasa sun koma APC ne saboda hana su takara a PDP.”

Haka kuma Kwankwaso ya ce, PDP za ta ci zabe, inda ya ce, ba sai ma ya daga kafar wandonsa wajen yakin neman zabe ba, domin rigar Gwamna mai-ci za ta sa ya sha kasa a zaben da za a yi saboda zargin karbar rashawar da ke kansa."