AlmizanAlmizan logo
Jum'a 3 ga Rabi'ussani, 1439 Bugu na 1319 ISSN 1595-4474

Rahoto

Farfesa Soyinka ya yi tir da Buhari: Saboda ci gaba da tsare Shaikh Zakzaky


Wuyan mai

Sanannen marubucin nan dan Nijeriya na farko da ya karbi kyautar Nobel a fannin adabi, Farfesa Wole Soyinka ya ce, shi bai ga “dalilin da ya sa za a ci gaba da tsare jagoran 'yan Shi’a Shaikh Ibraheem Zakzaky ba.

Ya kuma bayyana ci gaba da tsarewar duk da umurnin kotu na a sake yi da cewa "hakan kuskure ne."

Kimanin shekara biyu ke nan da gwamnatin Buhari take tsare da Malamin bayan auka wa almajiransa da sojojin kasar suka yi a Zariya.

Ya bayyana hakan ne lokacin da yake zantawa da Jimeh Saleh, Editan sashen Hausa na BBC, yayin da ya kawo ziyara ofishinsu na Landan, kwanakin baya.

Farfesan ya yi amfani da kalmar “kisan kiyashi” wajen bayyana irin kisan gillar da aka yi wa musulmi tsiraru mabiya mazhabar Ahlul bait a watan Disamban 2015 a Zariya.

Ya kuma ce, “Ya saba wa hankali, kuma ba dabara ba ce, ci gaba da tsare Jagoransu. Ban san dalilin da ya sa shi (Buhari) yake ci gaba da tsare Shugabansu ba. Wannan bai dace ba kuma keta masa hakkinsa na dan’adam ne.”

Farfesa Wole Soyinka ya ce, Shugaban Najeriya Muhammad Buhari har yanzu bai zama "cikakken farar hula ba, ta halayyarsa ga sauran al'ummar kasar."

Ya ce shugaban ya gaza wajen shawo kan matsalar kiraye-kirayen raba kasar da kungiyar IPOB ke yi.

Farfesan ya ce, har yanzu kasar tana amfani ne da kundin tsarin mulki wanda ya samu asali daga sojoji. "Kudin tsarin mulki ne da sojoji suka yi wa kansu," a cewarsa.

Ya ci gaba da cewa: "Har yanzu sojoji suna rike da manyan mukamai a kasar, ciki har da kujerar Shugaban kasa."

"Fata muke su mayar da kansu fararen hula ciki da bai. Kuma wannan yana daya daga cikin gazawar Shugaba Buhari," in ji shi.

Shugaba Buhari ya taba zama Shugaban mulkin sojin Najeriya a tsakanin shekarar 1983 zuwa 1985, kafin ya lashe zabe a shekarar 2015.

Sai dai ya ce, duk da cewa, akwai fannoni da dama da gwamnatin Buhari "ta tafka kurakurai wadanda suka cancanci suka, akwai kuma fannonin da ya kamata a yaba mata".

Ya ba da misali da yadda gwamnati ta yi aiki wajen gano kudin da aka sace wadanda aka kai kasashen ketare.

Da kuma yadda aka sa "wadansu manyan jami'an gwamnati suka amayar da kudin da suka sace".

Hakazalika farfesan ya ce Shugaban zai iya cewa ya cika aikin da aka zabe shi, wato aikin yaki da cin hanci da rashawa da kuma shawo kan rikicin Boko Haram da kuma makamantanta.

A wani labarin kuma, tsohon Ministan sufurin jiragen sama, kuma sanannen mai sukar wannan gwamnati, Mista Femi Fani-Kayode (FFK) ya yi Allah wadai da gwamnatin Buhari kan irin mummunan musgunawar da sojojin Nijeriya suka yi wa Shaikh Zakzaky a Zariya cikin watan Disamban 2015.

Yayin wani rubutu da ya yi wanda ya samu yaduwa sosai, FFK ya ce, “Shaikh Zakzaky, Jagoran ’yan Shi’a a Nijeriya an harbe shi a ido, wanda hakan ya sa ya rasa ido daya, aka jefa shi a baro, kuma ana tsare da shi ba bisa doka ba tun kimanin kwanaki 700 da suka wuce bayan kotu ta ba da umurnin a sake shi. Haka ma matarsa. Wannan rashin imani ne, kuma ba abin da za a amince da shi ba.”