AlmizanAlmizan logo
Jum'a 3 ga Rabi'ussani, 1439 Bugu na 1319 ISSN 1595-4474

Rahoto

Tsare Shaikh Zakzaky da Dasuki: Gwamnatin Buhari na zabar umurnin kotun da take bi -Jonathan


 UN

Tsohon Shugaban kasa, Dakta Goodluck Jonathan, ya nuna damuwarsa kan yadda wannan gwamnatin ke zabar irin umurnin kotun da za ta bi, inda ya ba da misali da ci gaba da tsare Jagoran Harka Islamiyya, Shaikh Ibraheem Zakzaky da kuma tsohon mai ba Shugaban kasa shawara kan harkar tsaro, Kanar Sambo Dasuki duk da kotuna daban-daban sun ba da umurnin a sake su.

Ya ce: “Muna so ’yan Nijeriya su lura cewa kotuna sun bayar da umarni ga gwamnati ta saki Kanar Sambo Dasuki da Shaikh Ibraheem Zakzaky, a matsayin beli, amma an ci gaba da tsare su. A fili take cewa gwamnatin APC tana zabar irin biyayyar da za ta yi wa kotu”.

Tsohon Shugaban kasar, wanda ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar, yayin da yake raddi kan kalaman da aka ambato Kakakin jam’iyyar APC, Malam Bolaji Abdullahi, ya yi cewa babu wanda ya sace kudin Nijeriya kamar Jonathan, da kuma wanda Sanata George Akume ya yi cewa PDP ce ta jefa kasar cikin bala’in talauci.

Ya ce munafunci irin na ’yan jam’iyyar APC ne ya sanya mutane irin su Sanata George Akume suka ce PDP ce ta jefa kasar cikin mawuyacin halin da take ciki.

“Sanata Akume (dan Majalisar Dattawa na jam’iyyar APC), kamar Malam Bolaji Abdullahi (tsohon Minista a gwamnatin Jonathan), ya manta cewa PDP ta yi mulkin shekara 16, kuma Akume ya zama Gwamna karkashin PDP na shekara takwas, kana ya zama Sanata a karkashinta shekara hudu. Shin da mutum ya zama dan APC yake zama Waliyyi, ko da kuwa ya kwashe shekara 12 a PDP?”, in ji Mr Jonathan, a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

A cewarsa, “Abin takaici ne jam’iyyar ‘All Progressive Congress’ ta sake yin karya cewa babu wanda ya saci kudin Nijeriya kamar tsohon Shugaba Goodluck Jonathan. “Da farko dai ya kamata su sani babu wata kotu da ta kama shi da laifin sata. Muna son tunawa APC cewa tsohon Shugaban ya taba bayyana cewa ba shi da asusun Banki ko kadarori a kasashen waje.

“Kuma akwai kudirin neman bayanai kan kowane jami’i da Dakta Jonathan ya sanyawa hannu, don haka ina shawartar Bolaji Abdullahi da masu aiko shi su yi amfani da wannan dama wajen binciko hakikanin abin da ya fada”.

Dakta Jonathan ya bayyana cewa idan ma shi barawo ne kamar yadda suka fada, ya kamata su Bolaji Abdullahi su sani cewa su ma barayi ne, domin shi (Bolaji Abdullahi) ya rike mukamin Minista a gwamnatin tsohon Shugaban kasar tsawon shekara uku cikin shekara biyar da gwamnatin ta yi.