AlmizanAlmizan logo
Jum'a 8 ga Muhammaram, 1439 Bugu na 1308 ISSN 1595-4474


Rahoto

HANTSI: In ba ka da sani, ka tambaya

Daga Danjuma Katsina


 Shema Ibrahim

Ya zo a cikin Alkur’ani mai tsarki wata aya saukakka daga Allah na cewa: “Ku tambayi masana in ba ku da sani.” Wannan aya an yi mata fassara mai yawa, kuma an rubuta dimbin littattafai a kan ayar. Masana wadanda ba Musulmi ba sun yi rubutu da yawa a kan wannan ayar. An kira ayar da ita ce mabudin duk ilmi, kuma wanda ya rike ta yake amfani da ita, shi ne ya fi kowa sani a duniya.

Duk wanda ya nakalci ayar, ba abin da zai shige masa duhu. Kuma ba wani abin da zai bata masa rai. Aya ce wadda kan zama mabudin farin ciki. Ita kadai ta ishi kowa jarin duniya da lahira.

A irin labaran ban dariya na raha da faranta rai da akan bayar, an ce wai wani Bafullatani ya sawo sabon yadinsa ya kai dinki, kafin ya bar shagon telan, sai ya ga an sanya almakashi an tsaga tsakiyar kayan! Bafullatanin nan ya danne. Sai ya ga an kara ketawa da almakashi. Ya ga telan ya sanya hannu ya kara faskawa. Sai ya kasa hakuri, ya yi kukan kura ya rarumi sauran yadinsa ya ce, ba ya son dinkin, tunda abin ya zama wulakanci. Me ya jawo haka? Bai sani ba, bai kuma tambaya ba! Sai ransa ya baci ya kuma fusata da yin fushi. Ko da labarin nan ba gaskiya ba ne, ana yin sa ne don raha, amma gaskiyar magana hakan yakan faru ga wanda bai sani ba, bai kuma tambaya ba, ya kuma yanke hukunci ga abin da tunaninsa ya ba shi.

Daga labaran Raha wadanda kan yi yawo, amma akwai darasi a cikin su shi ne labarin wani Babban Ofisa da Masinjan ofis nasa. Shi dai Masinja sai ya lura tsawon lokaci, kullum idan Maigidansa ya zo ofis tun safe har Azahar, lokacin kawo abincin rana Maigidan nasa ba ya cin komai, sai aiki. Sai kuma kadan-kadan sai ya danna kararrawa, in ya shigo sai ya ce, miko mani ruwa. Sai ya miko ruwa. A takaice Maigidansa ba ya cin komai sai shan ruwa har Azahar.

Masinja sai ya yi tsammanin cewa, lallai akwai wani sirri a shan ruwan safe har Azahar ba tare da an ci komai ba. Don haka sai ya yi niyyar ya dan fara gwadawa ya ji me ake ji? Don haka a ranar da ya fara, idan ya kai ma Oga ruwa, shi ma sai ya fito waje ya kurbi nasa daga butarsa.

A ranar farko cikin ya yi tatil da ruwa, idanuwan suka yi wuru-wuru, ya kai da kyar. Amma gogan naka sai ya ki daukar haske. Sai ya dauka wahalar ranar farko don kila ya fara ne. Yana sabo, shi ya sanya. A rana ta biyu sai ya dasa, a ranar aka wuce da shi asibiti. Don kuwa

jiri ya kwashe shi, ya fadi a some sai asibiti. A asibitin aka ce yunwa ce. Bayan ya sha wahala ya sha jinya, ya wartsake shi ne yake shaida wa abokansa cewa ai ga silar abin da ya faru. Nan da nan aka shaida wa Oga cewa ga abin da ya faru. Shi ne ya kira shi yana masa dariya. Ya ce, gobe ka zo gidana mu yi kalaci.

Da safe Masinja ya je gidan Oga. Ya ga kayan alatun da suka karya kumallo da su. Duk kayan maski ba sai an jero lissafinsu ba. A ranar Masinja ya sha ruwa da hujja, kuma ya karu da ilmin da ya samu ta hanya mai wahala.

Wani misali da nake da shi, wanda da ni abin ya faru da wani Maigidana wanda na watsa labarin na ji an canza masa salo da kama da yawan gaske ,kuma na ji ya watsu a duniya sosai.

Mun baro Kano a wata marsandi mu hudu- ni da direba a gaba shi da abokinsa a baya. Sai motar nan ta yi cak a daidai garin Dakatsalle. Aka yi, aka yi motar ta ki motsawa. Aka yi ta kiran Kanikawa suka kasa gano matsalar. A lokacin Dakatsalle ba service na kowace waya, muna da kan wata Thurayya, amma babu kati a ciki.

Ana tunanin ni in dawo Kano in taho da wata motar, sai ga wani yaro bakanike, dudu shekarunsa ba sa wuce sha biyar ba a lokacin An zo wucewa da shi bisa Babur. Sai zuciyata ta ce bari a jarraba sa’a. Sai na tsai da shi na fada masa. Sauran ’yan motan na yi man dariya. Yaron nan ya zo ya ce a kunna, ya saurara. Ya je ya samo wata waya, ya taho da wata kusa ya kwanta karkashin motar. Bayan kamar mintuna goma ya fito ya ce a kunna. Sai ga mota ta tashi.

Maigidana ya ce, me za a ba ka? Ya ce, “Naira dubu daya da dari biyu.” Yallabai mutum ne mai raha da son wasa. Sai ya daure ya ce, “kudin sun yi tsada, har sai ka yi mana bayani daki-daki.”

Yaron ya kalli dattijon nan ya ga lallai ya yi jikoki da shi. Sai ya ce, to Baba ga bayanin. Ita kusar can Naira dari na sawo ta. Amma don riba halas ce, dari biyu na sai da maku ita. Ladar aiki, Naira dari biyar. Ilmin da ya gano matsalar Naira dari biyar. In kun lissafa nawa ke nan? Ai babu kwara ko?”

Maigida ya fashe da dariya, ya ce, ya sayi duk farashin yadda ya sanya shi, amma ilmin da ya gano, ya kara masa kudi daga Naira dari biyar zuwa dubu biyu da dari biyar. Haka aka ba shi. Daga baya na zo na gano yaron can, dan wani kauye, ya sanya an kai shi wani kamfanin hada motoci don ya cigaba da aiki a wajen.

Duk wani abu da ka gani a duniya bisa ilmi ya ginu. Za ka iya ganin shi da sauki, kuma kana iya daukar sa da sauki, kana ma iya jarraba aikata shi babu ilmi, ka dan yi ’yar nasara. Amma da ka nemi masanansa suka yi masa aiki, sai ka ga fasalinsa ya canza. Misali, za ka iya sayen fili ka fadi yadda kake son aikin, kuma a yi maka. Amma da za a ce ka samu masani ya auna maka, ya sanya ilmi a ciki, da za ka ga aikin na ginin naka ya dau fasali mafi kyau da inganci.

A duniyar ci gaba da neman ingatacciyar nasara, duk abin da za ka sanya a gaba, sai ka tabbatar da masana fannin suna ba ka shawara, kuma suna dora ka hanya ingantacciya, kai ma kana hadawa da taka kwakwalwa da basira, wadda Allah ya ba ka kana aiwatarwa.

Shekaru da yawa na taba tattaunawa da Aliko Dangote, mutumin da yanzu ya fi kowa kudi a Afrika. A bakin teburinsa wata karin magana ce a rubuce, wadda ke da take da Turanci, “NOTHING IS IMPOSIBLE.” Ma’ana babu wani abin da bai yiwuwa. Na tambaye shi, mene ne babban sirrinsa? Ya ce, komai zan yi sai na tambayi masana a kan lamarin. Zan tambayi

kwararru, zan tambayi gogaggu. Zan tambayi manazarta, kafin nazarin fara duk abin da zan sa a gaba.

Ko ka san cewa, hatta a kukan jana’iza ta nuna takaicin cewa wani masoyi ya mutu akwai kwararru? A kudancin kasar nan akwai wajen ajiye gawa masu zaman kansu da shirya ma gawa jana’iza daidai kudinka da daukar hayar masu yin kukan daidai nauyin aljihunka. Kukan ma kala-kala ne akwai na a fadi kasa, a yi birgima farashinsa daban ne. Na kukan ruri, shi ma kudinsa daban ne. Sai na zubar da hawaye, sai kuma na bata rai.

Talla don gamsarwa a saya ilmi ce. Karatu ke gare ta har digiri na uku. Haka yekuwar fahimtar wani hali da yanayi shi ma ilmi ne. A aji za a koya maka shi. Shi kan sa da matakansa, ka fahimci cewa ana iya yi da ka, amma da an sanya ilmin ya fi tsari da tasiri.

Sakon da nake son isarwa shi ne, komai da ka gani ya ginu bisa ilmi. Kuma idan ka samu wadanda suka san ilmin lamarin za su saukaka maka aikinka. In kuma ka daukar wa kanka tafiyar kwanaki, sai ta koma ba a san rana ba. Hakika Jagora (H) da kuma Harka na bukatar wannan daukar dora jinka a yanayin da ake ciki, tuntuni. Allah ya sanya mu dace.