AlmizanAlmizan logo
Jum'a 8 ga Muhammaram, 1439 Bugu na 1308 ISSN 1595-4474


Rahoto

Labbaika yaaaaa Husain!

TARE DA M.I. GAMAWA 09071965492


Amincin Allah ya kara tabbata a kan gwarzon da ya ceci Addinin Musulunci. Imam Husaini, Jikan Manzon Allah, kanin Hasan, wanda ba ya shayin duk wani karami ko babban azzalumi.

Yau Alkalami zai yi magana a kan Gwarzon gwaraza. Tsayayyen tsayayyu. Dakakken dakakku.

Namiji a cikin mazaje. Jarumin jarumai. Mai bijire wa wanda ya bijire wa Allah. Mai tawaye ma wanda ya yi tawaye ma Allah. Wanda ya ba da wuyansa ga masu sare wuya don tsananin gabarsu da Allah. Mai kuncin da Manzo ya sumbanta. Mai jikin da ya fito daga cikin 'yar Manzon Allah. Mai jikin da ya hau gadon baya da kafadun Manzon Allah. Wanda kafafuwansa suka taka gadon bayan Manzon Allah, amma Manzo ya yi farin ciki da haka. Wanda babu Uwa kamar tasa a fadin duniya. Babu Uba irin nasa a fadin duniya. Babu kaka irin nasa a fadin duniya. Wanda ke da Uba mai surikin da ya fi kowa. Mai Uwar da Mahaifinta ya fi na kowa. Jagoran masu tawaye ga maki Allah komai zaluncinsa.

Jajircaccen da ya jajirce don kare Musulunci. Tsayayyen da ya ba da wuyansa da duk abin da ya mallaka, kama daga 'ya'ya da mata da mabiyansa don kare addinin Kakansa. Mai bakin da ya sumbanci bakin Manzo. Mai tsananin zuciyar fuskantar makiya addinin Kakansa. Mai tsananin ibada da rikon amana. Mai tsananin tausayi ga duk wata halittar Allah. Mai adalcin da ya kere masu adalci. Mai hikamar da ta kere masu hikima. Mai fasahar da ta kere masu fasaha. Mai kyautar da ta kere masu kyauta. Mai hakurin da ya kere masu hakuri. Mai juriyar da ya kere masu juriya. Abin kaunar Manzon Allah. Dan abin kaunar Manzon Allah. Kanin abin kaunar Manzon Allah. Ina wani in ba shi ba?

Shekaru sittin da daya bayan hijira, Imam Husaini ya nuna wa duniya yadda ake takun-saka da azzalumi dan azzalumi jikan azzalumi. Yazidu dan la'anannu ya nemi mubaya'ar Imam Husaini. Tun ran gini, ran zane. Babu rabon Yazidu da Ubansa Mu'awiyya har zuwa ga babban Kakansu Shaidan a cikin mubaya'ar Imam Husaini. Tabbas babu rabon tsuntsu a goruba. Kamar yadda giya ta haramta a gidan Liman, ko da na Izala ne. Haka mubaya'ar Imam ta haramta wa kazamai irin su Yazid.

Sai dai sakamakon bijire wa azzalumi yana da daci da kuna har da tsananin radadi fiye da radadin garwashin wuta. Duk da haka, Imam bai yi gezau ba wajen bijire wa Mal'uni Yazidu, mashayin giya, mai wasa da birai da karnuka.

Kamar yadda makircin Uban Yazidu, Mu'awiyya ya tilasta babansa Imam Ali (as) fita Madina, ya koma Kufa, haka Yazid ya tilasta wa Imam Husaini barin Makka don hijira. Babu koma wa Madina daga aikin hajji. Madina ta fi karfin Imam Husaini da iyalansa. Abin da ya biyo bayan hijira shi ne aikata abin da ba a taba aikatawa a tarihin Larabawa ba. Aka tozarta jarumtaka. Runduna mai mayaka dubu saba'in ta auka wa mutane saba'in. Gwanayen yaki masu makamai suka yaki mata da yara. Kisa kadai bai ishe su ba har da amfani da wuta. Duk wannan a kan dan Annabin rahama da iyalansa. Babu kunya. Babu ragowa. Babu tsoron wanda ya aiko Manzon, balle tunanin abin da za a riska a lahira.

A ranar, Manzon Allah ba komai ba ne a gun su, balle zuriyarsa. Kur'ani mai tsarki ba komai ba ne a gun su balle su tuna cewa an yi kashedin kisa a cikin sa balle su fasa kisa. Hadisin Annabi ba komai ba ne a gun su, balle su tuna amanar da Manzo ya bar musu na iyalansa, balle su fasa kisan iyalan.

A ranar da suka aikata wannan danyar babu imani ko ragowa a zuciyar ko mutum daya daga cikin su. In ka kira su maguzawa a rigar musulmi, duk daya. In ka kira su bakaken arna, duk daya. In ka kira su mushirikai a cikin rigar Musulunci, duk daya. In ka kira su yan wuta, duk daya. In ka kira su dakarun Shaidan, duk daya. Kowane suna ka kira su ya dace da su, in banda musulmi.

Sun fi mahaukacin zaki barna. Sai dai ka kwatanta su da sojojin Najeriya. Sun fi mugunta da kanta iya mugunta. Sun fi duk wata halittar Allah lalacewa. Shakka babu, Shaidan ya yi Wawan kamu a ran nan, inda ya fisge imanin ya'yan sahabbai. Tabbas da ma ba su da imani ko na kobo. Ba su damu da wacce zuriya suke neman kawarwa daga doron kasa ba.

Hakika ko da Annabi ya dawo a ran nan, tabbas za su hada da shi. Imaninsu ya bace. Hankalinsu ya gushe. Fariyar kabilanci da maye daga giya, sun zama sune suka maye duk abin da hankali zai doru a kai. Don haka aika-aikarsu ta rasa iyaka.

Falalin Karbala ya zama wajen da masu tausayi da fada da zalunci za su rika tunawa da shi har duniya ta nade. Ba gangar jikin Imam Husaini kawai aka nemi rabawa da duniya ba. A'a an so raba duniya da gaskiya dungurungum ne har tashin kiyama. Imam na wakiltar gaskiya, Sojojin Yazid na wakiltar karya.

Imam Husaini na wakiltar adalci, Yazidu na wakiltar zalunci. Imam na wakiltar tausayi da danadamtaka, Yazidu na wakiltar dabbanci da rashin mutumta danadamtaka. Na'am, haka abin yake har rana mai kama da ta yau. Yau Yazidanci ya shimfida daularsa a fadin duniyar da Allah Mai kowa da komai ya shimfida wa halittunsa bisa adalci. Amma wannan akida da ke wakiltar Shaidan ta jibge duk sharrinta a wannan duniya.

A yau an mai da ran Husainawa kamar abin da ya zama wajibi a kawar a doron kasa. Duniya ta yi nisa da gaskiya, ta barranta da duk wani abu da ke da alaka da gaskiyar da Imam Husaini ke wakilta. Duniyar kafirci ta mai da fari ya zama baki a duniya, kamar yadda ta mai da baki ya zama fari. Duk don nesanta danadam da Husainanci.

Dacin daukar Husainanci a kafada ya zarce fadawa cikin wuta mai tsananin kuna. Fajirai, fasikai sun zama sune masu watayawa da sheke ayarsu ta duk yadda suka so. Ko dai ka tafi da su ta yadda suke so, ko ka zama saniyar ware, a mai da jininka da kadarorinka abin halakawa da barnatawa. A irin wannan hali ne Shaidan ya daina fitowa neman wadanda za su taimake shi zama a jahannama gobe kiyama, ganin cewa ya samu kowa da kowa in banda Husainawa ’yan kalilan.

Misali, abin da Yazidawa suka yi wa Malam Zakzaky da mu almajiransa a nan kasar, kusan shekaru biyu da suka wuce ta mahukuntan Najeriya karkashin Yazidu Buhari ba su manta aikin kakansu ba. Wannan ya tabbatar da cewa, duk wanda ya dauki hanyar Imam Husaini, dole ya gamu da rashin tausayin Yazidawa. Na'am, Yazidawa ba su kona mata ba. Amma jikokinsu karkashin Buhari bisa jagorancin Hamanansa Buratai, sun aikata abin da ya fi haka.

Mutum ba ya zama Bayazide sai ya rasa imani da tausayi. Sai ya dauki kansa a matsayin wanda ba shi da tunani ko na sisi. Wanda ya dauki zaman kabari da hisabi ko tashin kiyama a matsayin almara, kamar yadda kakan Yazidawa Abu Sufiyan ya fada a gaban Khalifa na uku.

Abin tambaya shi ne Husainawan Najeriya sun yi saranda bayan aika-aikar Yazidu Buhari? Amsa ita ce har abada babu saranda! Tun kamawar Muharram Husainawan Najeriya suka bi sahun ’yan uwansu Husainawan duniya don zaman makoki da juyayin aikin zaluncin da Yazidun farko ya aikata a kan Husaini da Husainawa.

Husainiyanci ya dawo ke nan babu komawa. Yanzu Husainanci ya tashi daga bakon abu a cikin kasar nan. Sai dai marasa rabon duniya da Lahira su yi ta haushi a shagunansu da suke kira masallatai. Ka rinka jin maganganun da ko a gidan giya ba a jin su daga bakin mai gemu da dagaggen wando.

Su kuma kazamen mahukunta a karkashin Buhari da Nasiru Sarkin Bokaye, wanda ya kashe ’Yar'aduwa, ya hana Jonathan cin zabe sun shirya tsaf ta hanyar wawayen jami'an tsaronsu don zubar da jinin Husainawa. Mutane irin su Nasiru ba sa tunanin mutuwa ko abin ke iya faruwa kafin mutuwa. Su dai komai ta fanjama fanjam. Yau mulki na hannunsu, ba sa tuna cewa gobe mulki na iya komawa wajen wani, kamar yadda jiya mulki na hannun waninsu.

Barazanar kisa, ko kisa tunda sun saba ba zai hana Husainawa bumbuntowa kamar kudan zuma don la'antar Yazidu da jijokinsa ba. Su yi ta shirin kisa, wata rana mulki da makami tabbas za su fita daga hannuwansu. A lokacin ba su san wanda mulki da makaman za su komawa ba. Watakil mai tausayi ko mamugunci kamar su, ya yi musu fiye da abin da suka yi mana.

A yau mutane, hatta cikin wadan da suke turowa don kashe mu, suna tausaya mana. Dole mai hankali ya tausaya mana, don ba mu kashe kowa ba. Ba mu doki kowa ba. Amma mutane irin su Nisuru, babu mai musu irin shaidar da ake mana. Sun kashe mu, sun binne mu a rami guda, ba tare da wanka ko sallah ba. Randa Allah ya juya abubuwa a kansu, tabbas tarihi ba zai manta wannnan danyen aikinsu ba. Mun ce su bi a hankali, sun ce a'a. Mun ce su rika sara suna duban bakin gatari, sun ce a'a. Mun ce musu duniya juyi-juyi ce, sun ce a'a. Mun ce marar karfi na iya samun karfi wata rana, sun ce a'a.

Hankalinsu ya bace. Tunaninsu ya bace. Basirarsu ta bace, don kawai sun samu mulki na shekaru hudu. Sun manta cewa shekaru hudu kamar minti hudu ne ga mai rai. Kamar kiftawa da Bisimillah a gun zamani. Buhari da Nasiru dukkanin su sun dandani zafin rabuwa da mulki, amma babu wanda ya koyi darasi a cikin su.

Wajibi ne yan uwa su fito ran goma ga Muharram. Fitowa ta kasaita don la'antar la'ananne dan la'anannu, da jikokinsa da ke fadin duniya, da nan gida Najeriya. Mun tabbatar wa Buhari da karnukansa cewa bakunanmu ba za su taba shiru da la'antar wanda Allah da Manzonsa ya la'anta ba. Mu yi zaman makoki, sa'annan mu hadu ran goma ga wata mu la'anci Yazidu da jikokinsa na yau. Mu fada, mu maimaita, mu kara fada da babbar murya “LABBAIKA YAAAAAA HUSAIN!”