AlmizanAlmizan logo
Jum'a 8 ga Muhammaram, 1439 Bugu na 1308 ISSN 1595-4474

Rahoto

An daure Dagacin Gyallesu saboda satar awaki

Daga Aliyu Saleh


 mallam

Wata kotun Shari’ar Musulunci da ke Tudun Wada, Zariya ta daure Dagacin Gyallesu da wasu masu unguwaninsa a kurkuku saboda samun su da laifin hada baki wajen satar awakin jama’a a unguwar.

Alkalin kotun Mai shari’a Aminu Sa’ad, ya ba da umurnin a ingiza keyar Sarki Bello Aliyu Danmasani, Dagacin Sabon Garin Gyallesu zuwa gidan kukuku, tare da Yusuf Aliyu Fulana Maidawa, Sarkin Fulanin Gyallesu, Mai Unguwa Ibrahim Umar Sabo Gyallesu, Salisu Maiwada Galadiman Dagacin Sabon Garin Gyallesu da Mataimakin Jami’in tsaro na Kwalejin Ilimi ta Tarayya da ke Zariya, Mista Bitrus Sabo da wani da ake hada baki da shi yana sayar masu da awakin mai suna Tsalhatu Muhammadu Gyallesu.

An ruwaito cewa; dan sanda mai gabatar da kara, Saje Adamu Yahaya ya shaida wa kotun cewa, wadanda ake tuhumar sun hada baki ne suka rika satar awakin jama’a har 16, inda suka sayar da takwas a kan Naira dubu 45, suka ba matamakin jami’in tsaro na Kwalejin FCE, Bitrus Sabo Naira dubu 20, su kuma suka raba Naira dubu 25 da sauran awaki takwas a tsakanin su.

Saje Adamu Yahaya ya ce aikata hakan laifi ne da ya saba wa sashi na 139 da na 140 na kundin manyan laifuffuka na Jihar. Wadanda ake tuhumar duk sun amsa laifinsu, inda Alkalin Kotun Mai shari’a Aminu Sa’ad ya tura su zaman wakafi na mako biyu kafin ya yi nazari, tare da yanke hukunci a kan karar.

Wata majiya ta ce mutanen unguwar sun yi fama da sace-sacen awaki, lamarin da ya sa ’yan sintiri da jama’a suka sanya ido, inda a ranar 30 ga Agustan da ya gabata aka sanar da ’yan sintiri cewa an ga wata akuya a gidan Tsalha Muhammad, inda suka je gidan suka samu daya daga cikin awakin da aka sace, suka kai wa ’yan sanda.

Majiyar ta ce da ’yan sanda suka fara tuhumar Tsalha ne sai allura ta tono garma, inda ya ambaci Dagacin da masu unguwannin da mataimakin jami’in tsaro na Kwalejin FCE da hannu a lamarin.

Shugaban sashin tsaro na Kwalejin FCE, Malam Adamu Yalwa ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya shaida wa majiyarmu cewa; “DPO din Tudun Wada ya gayyace ni ofishinsa domin in yi masa bayani a kan lamarin, na kuma yi masa bayani cewa awakin jama’a sun dame mu da lalata wurare tare da cinye mana shukar da muka yi domin kawata makaranta, kuma wani lokaci awakin suna shiga har cikin aji da sauran wurare su bata, don haka na yi doka cewa duk ma’aikacin da yake da gida a cikin makarantar kuma yake kiwo, to ya daure abin kiwonsa, kuma na tara masu unguwannin Gyallesu da muke makwabtaka da su na roke su kan su yi shela ga jama’arsu domin su daina barin awakinsu suna shiga makarantar, amma duk da haka awakin na shiga.”

Ya ci gaba da cewa; “Idan suka kama awakin sai su sanar da masu unguwanni domin su kira masu awakin su ja masu kunne, kuma ya hada su da abokin aikinsa domin ganin cewa jama’a sun bi dokar. To shi kuma sai ya hada baki da Sarakunan suna bin wata hanya ta daban ba tare da sani na ba, kuma da ’yan sanda suka gayyace shi a ofishinsu ya amsa laifinsa har aka kai su kotu”.

Ya ce Sarakuna amintatu ne na jama’a, don haka makarantar ke neman su kai-tsaye, don yin shawara da su a samu mafita kan duk abin da ya taso, amma sai aka samu akasi.

Lokacin da Wakilinmu ya leka unguwar ya fahimci ba matsalar satar awaki kawai jama’a ke kuka da shi ba, mutane suna bayyana cewa yanzu unguwar ta zama wajen da ake fama da rashin tsaro; “Sace-sace sun zama ruwan dare. Muna kwana da ido daya ne. Yanzu sai ka ji an hauro maka gida an yi maka sata, ko kuma a fasa shago a washe shi. Matsalar ta addabe mu a wannan unguwar ta Gyallesu,” in ji wani mazaunin unguwar.

Har yanzu ba mu samu tabbacin ko sauran sace-sacen da ake yi wa jama’a a unguwar ta Gyallesu, akwai hadin bakin Sarakunan da aka samu da hannun dumu-dumu a sace akwakin mutane ba.