AlmizanAlmizan logo
Jum'a 8 ga Muhammaram, 1439 Bugu na 1308 ISSN 1595-4474

Rahoto

Yanzu ne aka fi bukatar samun hadin kan ’yan’uwa - Shaikh Abdullahi Zango

Daga Bala Musa Minna


Wuyan mai

A kwanakin baya ne aka gudanar da daura ga ’yan’uwa almajiran Sayyid Zakzaky da ke Minna da kewaye, inda Shaikh Abdullahi Zango da ke karatu a Jamhuriyar Musulunci ta Iran ya gabatar.

Daurar ta karatu ta samu halartar ’yan’uwa da dama daga sassan jihar Neja. Inda aka karantar da su littattafai daban-daban na Musulunci.

A karshen karatun da aka yi na kwanaki hudu, Shaikh Abdullahi ya gabatar da nasiha ga ’yan’uwa don neman hadin kansu ga Harkar Musulunci. Ya ce, "Sayyid Zakzaky ya tarbiyyantar da ’yan’uwa hadin kansu ga Harkar Musulunci, don hana makiya samun kafar yin wata barna.

Ya ce, "yanzu ne aka fi bukatar samun hadin kan ’yan’uwa almajiran Sayyid Zakzaky. Don makiya na ganin tunda Sayyid Zakzaky ba shi nan, za su yi amfani da wannan damar wajen rarraba kawunann ’yan’uwa, ta yadda za su sanya damuwa ga su Sayyid in ya fito daga hannun

azzalumai. Saboda haka ya dace ’yan’uwa su rika bin jagorancin da Sayyid Zakzaky ya dora su a kai, ta yadda duk wani bakon abu da zai zo, za su iya ganowa.

Ya kara da cewa, "duk da a yanzu Sayyid na hannun azzaluman mahukunta, amma akwai bayin Allah da almajiran Sayyid Zakzaky ne, wadanda suke tafiyar da komai na Harka babu wata matsala. Ya wajaba mu rika ba su hadin kai don hana makiya samun nasara a kan Harkar Musulunci. Su fa wadannan makiya a kullum neman yadda za su rusa Harkar Musulunci suke yi tare da taimakon Yahudawan duniya.”

Malam Abdullahi ya ce, ko a Jamhuriyar Musulunci ta Iran sun natsu kwarai da yadda Sayyid Zakzaky ya tarbiyyantar da su Shaikh Yakub Yahaya Katsina. Saboda ko bayan waki'ar watan Disamba na shekarar 2015 da ta faru a Zariya ya je Iran. Kuma su Sayyid Khamne'i sun yaba da dabi'unsa da ilminsa da kokarinsa. A nan, Shaikh Abdullahi ya ce, "ya dace ’yan’uwa su kasance masu basira. Su rika girmama na gaba wadanda wakilan Malam ne, da suka tsayu dare da rana suna kokarin taimaka wa kiran Sayyid Zakzaky don ya yi nasara. Harka ko da'awar Sayyid Zakzaky ta zama ta duniya. Saboda ko da aka yi waki'ar Zariya, kasashen duniya sun nuna tausayawa ga su Sayyid Ibraheem Zakzaky da almajiransa da aka zalunta.

A karshe Shaikh Abdullahi Zango ya nemi ’yan’uwa da su ci gaba da tsayuwa kan jagorancin da Sayyid ya tarbiyyantar da su na koyi da Manzo da Iyalansa tsarkaka (As).

Bayan kammala jawabinsa ne, Wakilin ‘yan’uwa na Minna, Malam Ibrahim Khalil ya yi jawabin godiya ga Malamin, ya yi fatan Allah Ta'ala ya karba addu'o'in da aka yi da samun albarkar karatun da aka koyar. Kuma ya nemi ’yan’uwa da su yi riko da nasihar da aka yi masu don ya amfanar da al'umma.