AlmizanAlmizan logo
Jum'a 27 ga Shawwal, 1438. Bugu na 1298 ISSN 1595-4474


Rahoto

Kayyutu kayyu, wani mai madarar baki

TARE DA M.I. GAMAWA 09071965492


Yau Alkalami zai yi magana a kan Kayyutu. Mun sha magana a kansa. Ba za mu fasa ba, kamar yadda shi ma bai fasa ba! Ko can dan halas ba ya fashi, sai shege. Dole mu tona asirinsa har na kusa da nesa su gane shi.

Tilas mu yaye labulen da ya boye mugun halinsa. In yana sa hula mu fizge ta don a gane cewa yana da sanko. Ba sanko ba kawai, har a gano cewa yana da kora a ka. Kusan shekaru uku kacal ya yi da Ubansa, Malamin madara a duniya. Don haka ba dole ne ya koyi da’a da tausayi ba, balle girmama na gaba da shi. Haka tsohon Shugaba Obasanjo ya ce masa, lokacin da Obasanjo ya ga tsageran cinsa ya wuce wuri.

Wannan magana ta Obasanjo ta bayyana kadan daga halin wannan Kurege, uban barna. Kwanaki ya yi tinkaho, inda ya ce wai addu'a ba ta kama shi. Ya manta cewa zara ba ta barin dami. Wanda ke tashi da tsakar dare yana fada ma Allah kukansa, bayan an zalunce shi, daban yake da wanda ya auri duniya, Wanda ko salloli biyar suna ba shi wahala.

Yau Kayyutu ya zama kamar annoba, babu wanda ke son sa. Ya zama kamar Maye, babu mai abota da shi. Ya zama kamar mugun labari, babu wanda ke son ya ji shi. Ya zama kamar asara, kowa neman tsari yake da shi. Ya zama kamar talauci, kowa addu'ar neman Allah ya raba shi da shi yake yi. Duk a sakamakon addu'o’inmu. Kayyutu ya zama tauraruwa mai wutsiya, ganin ki ba alheri ba. Da karbar bakuncin sa a kudancin Kaduna, gara su karbi bakuncin annoba. Don annoba tana barin masu nisan kwana. Da karban bakuncinsa a mahaifarsa Zariya, gara su karbi ciwon Ibola. Tabbas ciwon Ibola zai rage wasu. Mutuwa ta rena mai gajerun kwana ne kawai. Amma shi gubar Nukiliya ne, wanda ba shi barin babba ko yaro.

A yau Kayyutu ya rasa komai, in banda kiyayyar da talakawa ke masa. Mu shaida ne ga "Ba ma so! Barawon Gwamna!" Wannan ita ce taryar da aka yi masa a garin Kudan, a cikin satin da ya gabata. Da kyar ya tsira. Ko in ce katakau ya tsere kamar zomo. In ka ce yana da mutumci a idon jama'a? Sai mu ce mai yi wa mata fyade ya fi shi mutumci. In ka tambaya ko yana da sauran farin jini a gun talakawa? Sai mu ce maka ya fi yunwar dare bakin jini a gun su. In ka tambaya, ko talaka na dokin ganin sa a yanzu? Sai mu ce da yawa sun gwammace su ga Na'uwale Aljanin matan kulle. In ma ba su ce gara su ga Azara'ilu ba.

Shin akwai wanda ya kai shi bakin jini a fadin jihar Kaduna? Sai mu ce maka, inda zai tsaya takarar Gwamna a zabe mai zuwa a jihar Kaduna, da Evans, gawarceccen mai garkuwa da mutane, tabbas zai ka da Kayyutu ko a cikin gidan Sir Kashim. Duk kuwa da cewa Evans dan kudu ne kuma mugun mutum. Tabbas mutanen jihar Kaduna sun san muguntarsa ba ta kai ta Kayyutu ba. Musulmai da Kiristoci na neman tsari da Kayyutu. Suna fatan shekaru biyu su yi sauri, irin saurin walkiya, don su kori dan mitsitsin Kaduna daga gidan Sir Kashim.

Tabbas ya gane cewa shi ba Sarki ba ne balle ya tursasa talakawa su bi shi. Shi kuma ba soja ba ne, balle muzurensa ya tsorata talakawa. Kowa ya dawo daga rakiyarsa. Yara ba sa so. Tsofaffi ba sa so. Ya zama kamar kayan sata. Duk mai mutumci ba ya son ta'ammuli da shi. Daga shi sai mugun halinsa da mugun tunaninsa. Zuciyarsa ta sawwala masa cewa, shi ya fi kowa sani. Amma a kashin gaskiya ya jahilci komai har da dalilin zuwansa duniya. A cikin tarihinsa da ya rubuta da kansa, wanda wasu daga iyayengidansa suka kira "Ayoyin Shaidan." Ko ba komai Kayyutu ya zama kamar cutar kuturta, kowa gudunsa yake. Shakka babu an kusan maida wa Abu-Lahabi abin da ya yi.

Kwanan nan mai girma Sanata Shehu Sani ya sace wa Kayyutu iska. Lokacin da Sanata ya je wakiltar Shugaban Majalisar dattawa wajen bikin bude ofishin Hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) a Kaduna. Bai zaci cewa Shaidan ne da kansa zai zo wannan muhimmin aiki ba. Shaidan na isowa, sai Sanata ya fita da gaggawa. Dama al'adar mutanen kirki, in sun ga Shaidan a wuri suna gudu. Nan take ya bai wa rigarsa iska daga ganin Kayyutu ya iso wajen. Ya san ba maganar mutumci za a yi ba, tunda maras mutunci ya shigo. Ba maganar gaskiya, tunda ga makaryaci ya zo. Makaryacin da ya fada wa duniya cewa, wai yana tare da Malam Zakzaky a Jami'ar Ahmadu Bello kafin a kori Malam. Da fadar haka, wanda a da bai san Kayyutu a matsayin kasurgumin makaryaci ba, dole ya tabbatar da haka. Babu wanda ya kori Malam a Jami'ar Ahmadu Bello. Amma Kayyutu ya shara ta. Ko a jikinsa, wai Buhari ya yi karya wa talaka!

Nan take sanata ya nuna cewa haske ba ya zama wuri daya da duhu. Mutumin kirki ba ya zama wuri daya da akasin sa. Haka maketaci ba ya zama wuri guda da mai tausayi. Mai kunya ba ya zama wuri daya da marar kunya. Mai taimaka wa al'umma ba ya zama da wanda ke kwace abin da suke da shi. Duk wadannan halaye suna wajen Kayyutu. Abin da kawai ba za ka samu a wajensa ba, shi ne rikon amana. Don shi Kurege ne, yana cin nasa ya cinye na wasu. Shi annoba ne mai kashe mutane. Shi ne bakin ciki mai munanawa kowa. Shi yunwa ne, mai ramar da jikkuna. Shi hassada ne, mai kore alheri.

Don me jama'a ba za su kara guje masa ba? Ya kashe wasu ta hanyar rusa musu muhallai. Ya kashe wasu ta hanyar korar su daga wajajen aikinsu. Ya kashe a Zariya, ya binne a Mando, don Addininsu, tunda shi makiyin Addinin Musulunci ne. Ya biya wadanda suka kashe ’yan kudancin Kaduna don su ji karfin kisa. Ko shi da kansa ya tabbatar da haka. Don shi makiyin Kiristoci ne. Ya ce a kama wadanda suka kare Arewa daga shegantakar 'yan Biafra don shi makiyin Arewa ne.

Wannan Kurege bai amfani jihar Kaduna da komai ba. Duk abin da talaka ke nema, ko dai wannan Kurege ya hana, ko ya kwace wanda ke hannun talaka. Shi ne masifa. Shi ne bala'i, kuma annoba ga wannan al'umma, akalla a Kaduna da inda hannayensa za su iya kaiwa. Dan mitsitsin da wadanda suka san shi sani na hakika ke kira Butulu. Wadanda suka san shi sanin shanu, ke kiran sa Mugu sai mai shi.

Wannan karamar sallar da ta wuce, Zazzagawa sun shirya jifan Shaidan ran salla, amma Kayyutu ya bata musu harka. Watakila ya samu labarin abin da zai auku gare shi. Dole ya sake wuri, kuma ya sake gari. Yadda za ka fahinci cewa, addu' armu ta karbu a kan Kayyutu shi ne karbar sarautar da ya yi a kauyen da ya je gudun Hijira ran salla karama. Irin sarautun da ya rusa, sai ga shi ya karbi sarautar Dan Dukununu, babu kunya, ba tsoron Allah. Abin da ya ba ni haushi shi ne don me za a bai wa Kayyutu sarautar Dan Dukununu bayan watan Ramadan ya wuce? Wannan sarautar ta fi dacewa da a ba shi ita ran da azumi ya kai kwana goma sha biyar. Da a wannan lokaci za a daura masa igiya a kugu, don shiga gidaje neman tsaba, amma ba a jihar Kaduna ba.

Ko ya gudu bai tsira ba. Mutanen Kaduna sun yi jinga da Gwamna mai zuwa cewa, dole ya amince zai mai da Kayyutu, Na'uwale Aljanin matan kulle kafin su ba shi kuri'arsu. Ko kuma in ya aminta cewa zai gina gidan Zuu a Kaduna don ajiye Dabba daya tilo da ta taba zama Gwamna. Wannan zai farkar da talakawa cewa, akwai dabbobi a cikin mutane, kuma dole a lura da haka a lokacin jefa kuri’a don maganin gaba.

Allah na nuna mana cewa azzalumai ba za su taba galaba a kan masu neman a yi adalci a bayan kasa ba. Masu gaskiya za su yi rinjaye, kamar abin da ke faruwa a wannan lokaci. Yanzu dogon Daura dan London na can gida yana murmurewa, babu murya, balle hoto. Wannan karon ba mu ga hotonsa tare da Limaminsa kuma Jagoransa na duniya da lahira, mai masa addu'a ta musamman, Paparoman Ingila kuma Bishop na Cantabury ba. In ba a manta ba lokacin da Tsoho zai dawo Najeriya da "kwari," Bishop ne ya yi masa addu'ar karshe, kamar yadda hotuna suka nuna.

Masha Allah. Allah na zaban yadda zai saka wa 'yan Shi’a. Ashe Allah na kowa ne. Allah na 'yan maula, masu ci da Addini, kaskantattu masu tozarta sakon Manzon Allah, shi ne kuma Allah na 'yan Shi’a. In sun yi addu'ar Allah ya tsare mulkin iyayengidansu Trump, Natenyahu, Salman da Buhari, mu kuma mu roki Allah ya bai wa namu Jagoran Sayyid Zakzaky lafiya a sakamakon harbin da matacce a cikin rayayyu, Buhari dan London ya yi masa. Watakila ba da jimawa ba mu yi murnar kada Bushiya mai dauro. In haka ta samu, sai addu'armu ta fuskanci Kayyutu. Mu zaro Nukuliyoyinmu na addu'o’i don antaya wa wannan dan jaririn bera mai sace daddawa a tukunyar kowace tsohuwa.

Don tsananin jabberanci yanzu Kayyutu ya kirkiro Shi'arsa da Malaminta, wai don ya yi maganin abin da ya kira Shi'ar Zakzaky. Abin da bai sani ba shi ne, shi da Malamin da ya kawo dukkanin su gwanayen yi wa wanda ya yi musu dare, rana ne. In ba ka gane ba dukkan su kwararrun maciya amanar wanda ya maishe su mutane ne.

Tabbas ya kafa Malaminsa na Shi’a. Muna jiran mu ji yadda za ta kaya tsakanin maciya amana biyu. Aiki ne na wanda ya ci amanar Ubangidansa Obasanjo da wanda ya ci amanar Malaminsa Sayyid Zakzaky. Muna jiran mu ga yadda sakamakon aikin zai kasance. Don masu dariya su yi, masu kuka su ma su yi. Akwai karin maganar Fulani mai cewa "In wayonku ya zo daya, randunanku za su kwana babu ruwa a cikin su." Girman kai, nuna sani da hassada, duk ayyukansu ne. Dole mu gayyato Dan Anace ya buga musu kawu ko za mu ga wanda zai gama da wani a cikin kasa da shekaru biyu, kafin sabon Gwamna ya gama da su dukkan su.

Ta daya jinibin kuma muna jin dadin abin da ke gudana tsakanin azlamu da masassara a London. Ko yaya za ta kaya? Sanin gaibu sai Allah. Muna ji, muna gani, muna kuma sauraro! Amma shi Kayyutu gabarmu da shi tana nan. Dole mu ci gaba da harba masa abin da muka fi kwarewa a kai. Shi ne kai karar katafaren azzalumi irin sa wajen Allah. Mu ci gaba da fatan Allah ya nuna mana karshen wannan mugun makiyi. In ba ka san shi ba. Shi ne Kayyutu kayyu, wani mai madarar baki, kuma mai kircin baki.