AlmizanAlmizan logo
Jum'a 27 ga Shawwal, 1438. Bugu na 1298 ISSN 1595-4474

Rahoto

Harin Sojoji a Zariya: Ban san wanda aka zalunta kamar Shaikh Zakzaky ba - Farfesa Shehu Ahmad Maigandi


Wuyan mai

Farfesa Shehu Ahmad Maigandi, Malami ne a Sashin Kimiyyar Kiwon Dabbobi (Animal Science) a Jami’ar Usman Danfodiyo da ke Sakkwato. A cikin wannan hirar da Aliyu Saleh ya yi da shi, ya bayyana yadda yake kallon harin da Sojoji suka kai wa ’yan uwa a Zariya, tare da yaba irin namijin kokarin da ’yan uwa suka nuna. Ya fayyace irin girman zaluncin da aka yi wa Shaikh Ibraheem Zakzaky, tare da fito da yadda jama’a ke fahimtar hakan cikin gaggawa. Ya fito da irin gazawar gwamnati da yadda yake kallon bijire wa umurnin kotu da ta yi, gami da tabbatar da cewa harin dama tsararre ne. A sha karatu lafiya.

ALMIZAN: Da farko za mu so mu ji cikakken suna?

FARFESA SHEHU MAIGANDI: Sunana Farfesa Shehu Ahmad Maigandi. Ina karantarwa ne a Jami’ar Usman Dafodiyo da ke Sakkwato a Sashen ‘Animal Science’ (Kimiyyar Kiwon Dabbobi).

ALMIZAN: A matsayinka na daya daga cikin Almajiran Shaikh Zakzaky, kuma wanda ya nazarci harin da Sojoji suka kai wa ’yan uwa kusan shekaru biyu da suka gabata a Zariya, me za ka fada wa masu karatunmu?

FARFESA SHEHU MAIGANDI: Ba shakka na ji abubuwan da suke faruwa a Zariya, kuma na nazarce su sosai. Shi kansa wannan ‘program’ din na yi niyyar zuwa, sai Allah bai nufa ba, wani abu ya zo ya gitta. Abin da na fahimta, wadannan mutanen sun gaggauta zuwa da ita wannan waki’ar ne, domin dama muna tunanin zuwan ta. A kowane lokaci Jagoranmu Sayyid Ibraheem Zakzaky (H) na cewa wadannan mutanen suna so su gaggauto mana abin da muke tsammanin zuwan sa, sai ya zama ba zato ba tsammani, domin gaskiya ba wanda ya yi tunanin wannan abin. Sai suka zo suka kawo hari, bisa dogaro da wasu hujjoji da hankali ma ba ya iya dauka. Har gobe sun kasa kare kansu na dalilin da ya sa suka kai harin.

A lokacin da abubuwan ke tafiya, ina biye da su sau da kafa. A lokacin da suka fara kai hari Husainiyya Bakiyyatullahi, na rika tuntubar dan uwa Malam Abdulkarim Danbam. Mun yi ta waya da shi har lokacin da ya ce min “Prof. don Allah a yi mana afuwa, yanzu zan yi shahada.” Kuma bayan minti biyu da na kira wayarsa, tana ‘ringing’ ba a dauka ba.

Ba shakka na rika bin lamarin tun wancan lokacin har ya zuwa yanzu. Lallai sun yi wauta ba karama ba. Wannan tafarkin mun yi imani da shi, mun san cewa jarabawa za ta zo, amma ta yi gaggawar zuwa, kuma ta yi nauyi sosai. Saboda in ka nazarci tarihin duniya ka ga wanda aka jarabta kamar wannan Jagoran namu. Duk cikin wadanda ake jarabta, sai ka ga ko dai ya rasa ’ya’yansa daya ko biyu, amma shi ya rasa komai da yake da shi a duniya, ’ya’yansa, gidansa da komai nasa da ya mallaka a duniya. Mutum ya zauna ya yi nazari a kashin kansa, yana zaune a gida ba zato ba tsammani a kai masa hari, ya zama ko wayarsa bai iya fita da ita ba. Ka ga wannan jarabawa ce mai nauyin gaske. Amma mun san jarabawa tana zuwa ne daidai da karfin imanin mutum. Gwargwadon imanin mutum, gwargwadon jarabawar da za ta zo masa. Wallahi muna da tsaninin yakinin cewa imanin Malam ba karami ba ne, shi ya sa Allah Subhanahu Wa Ta’ala ya jarrabe shi da irin wannan jarabawar ya gani, ko zai iya dauka, ko ba zai iya ba, kuma ya dauka.

Kuma ita wannan jarabawar ta fito da al’umman da ba ka tsammanin su fito fili. Na farko ita wannan Harkar ta yadu a duniya, ba wai a Nijeriya ba. Da Harkar nan za a iya cewa ba ta fita a duniya kowa ya san ta ba, amma yanzu wannan waki’ar ta mai da ita ta duniya. Akwai wadanda muke tare da su, abokaina ne, dukkan su suna yawan fada min cewa an cuci Malam ba karamar cuta ba, an zalunce shi ba karamin zalunci ba, saboda haka ba makawa, Allah zai yi masa sakayya.

Idan ka duba tun farkon Harkar nan duk wani da ya zaluncin Malam, su Allah ya yi masu wani abu na jarabawa a kan kakansu. Za ka ga cewa sun samu wasu matsaloli a rayuwa. Akwai wani abokina babban Soja ya fada min irin halin da manyansu ke ciki sakamakon wannan zaluncin da suka yi wa Malam.

Sannan kuma zan fada maka wani abu shi ma wani abokina Soja ne yake fada min. Ya ce lokacin da suka kama Muhammadu Yusuf suka mika shi ga ’yan sanda, sai aka kashe shi, ba su ji dadin abin da ya faru ba. Don haka lokacin da suka kama Malam, sai suka je wajen SSS don su san halin da Malam yake ciki. Bayan matsin lamba ta kwanaki, manyan Sojoji hudu sun je sun ga Malam, sai suka tarar da shi yana Sallah, sai suka ji yana addu’ar cewa wadanda suka yi wannan aika-aika, ya Allah ka shiryar da su. Wallahi yake fada min dukkan su sai da suka yi hawaye. Ba su yi magana da Malam ba, suka juyo. Ka duba irin rahama ta Malam, wanda aka yi wa wannnan irin zaluncin, amma har yanzu yana neman masu mafita.

Saboda gaskiya ne wannan jarabawar ta zo mana a ba-zata. Mun san cewa wannan Shugaban kasar ya gwada auka wa Harka a lokacin mulkinsa na Soja, amma sai muka yi tsamamnin akalla zaman sa tare da wasu wadanda ke kusa da Harka, ya dan fahimci wasu abubuwa, amma da yake wannan wata kwangila ce wacce aka ba shi, kuma dole ya aiwatar da ita…

ALMIZAN: Ke nan kai ma ka yarda cewa wannan harin da Sojoji suka kai wa Shaikh Zakzaky wani tsararren abu ne da aka tsara aiwatar da shi?

FARFESA SHEHU MAIGANDI: Babu shakka haka ne. Wannan in ka duba ma tafiyar da ake yi a duniya, ba ka bukatar a fada maka cewa tsararren shiri ne da aka aiwatar. Kuma shi Shugaban kasa ko yana so, ko bai so abin da zai yi ke nan.

Akwai wani abokina da yake fada min cewa Obasanjo ya fada masu cewa, duk wani Shugaban kasa da zai hau karagar mulkin kasar nan, sai an ba shi wannan kwangilar, sai dai in ya ki aiwatarwa. Ya fada wa Buhari cewa ya wuce gona da iri, ya shiga gaba daya, ya dulmuya. Kwangila ce wacce ake bayarwa. Abin da zan ce a takaice, wannan lokaci ne na Ahlul Baiti (AS), Shi’a gaba daya duniya ta taso masu. Duk inda ka ce kai mabiyinsu ne, za a taso maka. Don haka tabbas wannan harin tsararren abu ne, ba wata shakka a kansa.

ALMIZAN: Suna kallon Shaikh Zakzaky kamar wata barazana ce a gare su, kuma ya yi fice a Afrika?

FARFESA SHEHU MAIGANDI: Sosai kuwa. Ai ba maganar fice a Afrika ba, ana maganar fice a duniya ne. Imam Khumaini Shugabanmu ne, kuma a kan tafarkinsa muke, kuma shi ya jadadda wannan tafarkin na Ahlul Baiti a wannan lokacin, idan ka dubi muhallin da Imam ya samu kansa, mafiya yawan mutanen mabiya ne na Ahlul Baiti, amma mu nan a lokacin da Malam Zakzaky ya fara kira, da ya fada mana wani abu na Ahlul Baiti, Wallahi za mu gudu ne mu bar shi, amma cikin hikima, sai ga shi Allah ya fahimtar da mu. Ko kai waye, mafarin ka fahimci darajar Ahlul Baiti, albarkacin Malam ne. Don haka ba karamin aiki ya yi ba, ya canza tunanin al’umma gaba daya daga wani tafarki zuwa wani. Wannan ba karamar wahala ce da shi ba. Sannan kuma ya tayar da wani ‘Movement’, wanda ke son dawo da addini ya yi aiki da rayuwarmu kamar yadda yake a zamanin Shehu Usman Danfodiyo. Saboda haka ka ga tunda aikinsa ya girmama, dole jarabawarsa ta girmama. Lallai wannan harin tsararre ne, kuma muna tsammanin zuwan sa, sai dai ya yi gaggawar zuwa ne kawai.

Wani abu kuma shi ne, Wahabiyawa za su yi haukansu su bari. Kwanan nan nake jin wani Minista a Saudiyya yana cewa idan Imam Mahdi ya zo za su yake shi. Ba shakka za su yi din. Mu kuma dama bayyanarsa muke jira. Yanzu sun hada kai da kafircin duniya, don hakkakar da wannan bukatar tasu.

Ka dubi ziyarar da Trump ya kai Saudiyya kwanaki, dubi wulakancin da ya yi masu da ya kai shi. Na ji dadin yadda ya wulakanta su. Na yi amfani da wannan ziyarar na fahimtar da wasu da muke tare da suke ganin Sarakunan Saudiyya a matsayin alamin addini. Da yawansu suna cewa kasa guda ce kawai ba ta daukar wulakancin duniya, sun san ta, amma ba za su fada ba.

Saboda wannan lokacinsu ne, kuma ba shakka, ko ana so, ko ba a so sai an yi. Sai dai kawai mu shirya wa jarabawa. Za ta zo, babu wani shakka a gare ta, kuma har gobe muna cikin wannan jarabawa din.

ALMIZAN: Ka gamsu da irin dakewa da kumajin da ’yan uwa suka nuna a lokacin waki’ar nan kuwa?

FARFESA SHEHU MAIGANDI: Ba wai maganar na gamsu ba, gaskiya sun fid da mu kunya. Ka duba fa an kashe mutane fiye da 1,000 domin su kashe Jagora. Ka san wadannan mutanen sun lura ’yan uwa suna zuwa daga ko’ina za su shiga Zariya, sai suka rurrufe hanyoyin shiga. Akwai wadanda suka kakkashe a kan titi, kamar mota biyu da suka fito daga Kano, suka bude masu wuta a Dogarawa. Don haka gaskiya ’yan uwa sun nuna sadaukarwa. Babu wani Shugaba a wannan kasar da za a ba da rai don kare shi kamar yadda aka yi wa Malam. ’Yan uwa sun ce sai dai bayan ransu za a kai ga Malam. Allah shi ne shaida, na daukar wa raina kullum in na yi Sallah sai na yi wa wadannan bayin Allah da suka ba da rayuwarsu addu’a, tare kuma da sauran Shahidanmu baki daya. Na gamsu kwarai da gaske.

Wani abu da za a duba kuma shi ne; wadanda aka kashe din nan sun kunshi kowane bangaren na al’umma, akwai mata masu ciki, akwai yara na goyo masu shan nono, akwai matasa, akwai dattijai, akwai Malamai irin su Malam Turi da Likitoci irin Dakta Mustapha Umar Sa’id. Za ka ga mutum ya ba da rayuwarsa da kuma ta ’ya’yansa gaba daya, kamar Malam Abdullahi Abbas. Duk sun ba da ransu don kare Jagora. Ni dai a tawa fahimtar na gamsu da irin rawar da ’yan uwa suka taka a wannan lokacin. Muna fatan Allah ya kara tabbatar da mu a wannan tafarkin.

ALMIZAN: Duk wadanda aka kashe din nan, an kashe su ne saboda sun hana Sojojin kai wa ga Shaikh Zakzaky, amma kuma da suka kai gare shi, sai Allah ya tseratar da rayuwarsa, me wannan yake nunawa?

FARFESA SHEHU MAIGANDI: Wannan yana nuna wata irin mu’ujiza ce Allah yake nufin ya fito da ita. Domin su wadanda suka tsara kai harin, sun yi mamakin yadda Sayyid ya tsira da ransa. Wani abokina babban Soja ya fada min cewa shi Sojan da ya bude wa Malam wuta, ya je ya fada masu cewa ya yi aikinsa, ya kashe shi. Sai su manya nasa suka ji labarin ba haka ba ne, shi wannan Sojan sun kashe shi, saboda suna ganin kamar ya yi masu karya. Shi kuma yana mamakin ya aka yi ya harbi Malam a wuraren da yake da yakinin ba zai kai labari ba har sau bakwai, kuma aka bar Malam cikin jini kusan awa 24, amma kuma Allah ya rayar da Malam? Shi da kansa Malam din ya bayyana cewa kwanaki biyar ya yi bai sani ba, a duniya yake, ko a lahira. Dubi ita ma Malama harbi nawa suka yi mata? Ga shekaru, wadanda ko su kadai sukan sa ba tare da an yi wani dogon abu ba, mutum ya rasu. Lallai wannan wata ma’ujiza ce. Allah yana nufin wani abu da wannan bawan Allah, shi ya sa ya ajiye shi don ya zama aya a gare mu. Duk abin da suka yi bai yi nasara, abin da suka yi tsammanin ya faru, bai faru ba, sannan kuma kunya ce sun ji ta, sun rasa yadda za su yi.

ALMIZAN: Duk wannan kashe-kashe da rushe-rushe da suka yi, sun yi ne da nufin murkushe ita Harka din gaba daya, amma kuma sai ya zama abubuwan sun birkice masu, me wannan yake nunawa?

FARFESA SHEHU MAIGANDI: Abin da za a lura da shi, a duk duniya babu inda karfi ya murkushe wani ‘Movement’. Misali Boko Haram, kowa ya san irin ta’addancin da suke yi, amma ga shi da aka yi amfani da karfi a kansu, ba a iya murkushe su ba, yanzu an koma ana tattaunawa. Balle mu mun yi imani da abin da muke yi, babu wani shakka a kansa. Sannan kuma mu ba mutane ne wadanda suka dauki makamai ba, balle su ce suna da abokin gaba da za su yi yaki da su. Mu mutane ne da ke rayuwa a cikin al’umma, kuma suna fahimtar mu, muna taimakon su, kuma suna gane cewa an zalunce mu.

Gaskiya ne sun yi duk yadda za su yi, amma ba su iya kawar da Harka ba. Misali El-Rufa’i ya yi duk yadda zai yi don murkushe Harka, amma kullum karuwa take. A Sakkwato an yi irin wannan, sun yi tsammanin shi ke nan Harka ta mutu, amma ka ga yau kamar ba a yi ba. Babu inda ake murkushe ‘Movement’ na canji a cikin al’umma da karfin bindiga. Saboda haka wannan tafiya ta kafu daram, domin jinin Shuhada da suka zuba, taki ne. Ta hanyar mutum daya da aka kashe, Allah ne kadai ya san iya mutanen da za su fahimta. Yau in abin a ce Malam zai fito, ya kake tsammani? Wannan abin da ya faru ya kara mata karfi ne.

Bayan wannan waki’ar, makiya sun zuba kudade sosai don yin farfagandar karya, amma sai ya zama hankalin mutane ya kasa dauka. Yanzu jama’a sun fara fahimtar irin zaluncin da aka yi mana. Mutane sun fara tambayar cewa in mutanen nan ’yan ta’adda ne, ya aka yi aka zalunce su, amma ba su yi ramuwar gayya ba? Kuma har sun kai kotu. An juyar da hankalin al’ummar nan sosa, amma a hankali sun fara dawowa cikin hayyacinsu.

ALMIZAN: Alkalin wata kotu a Abuja ya nuna cewa an zalunci Malam, kuma bai aikata laifin komai ba, har ma ya ce a biya shi diyyar daurin da aka yi masa ba bisa ka’ida ba, amma kuma gwamnati ba ta bi ba?

FARFESA SHEHU MAIGANDI: Wannan wani karin karfin gwiwa ne. Ba mu yi tsammanin samun wannan adalci ba, daga yadda tafiyar take, domin ai ka ga hukuncin da Alkalin kotun Kaduna ya yi, amma shi na Abuja ka ga hukuncin da ya yi, kuma kiri-kiri gwamnati ta ki bi.

Wannan sai ya nuna abin da suke fada na kare hakkin bil’adama da bin doka da oda, ba gaskiya ba ne. Jama’a sun fahimci fada kawai suke yi. Yanzu gaskiya tana kara fitowa sosai cewa an kai harin nan ne da wata manufa, kuma yin hakan zalunci ne. Yanzu ita gwamnati ta rasa mafita, shi ya sa kullum suke fitowa suna yin karerayi kala daban-daban. Yau su ce suna tsare da Malam ne don ba shi kariya, gobe su ce saboda dalilan tsaro da bukatun jama’a, jibi su ce saboda ba wanda ya yarda ya yi makwabtaka da shi. Saboda haka wannan karin daukaka ne. Da sun sake shi tun wancan lokacin, da yawan matane ba za su fahimci irin zaluncin da aka yi masa ba. Yanzu har makiyan sun yarda an zalunci Malam.

Wata rana muna tafiya a cikin mota, sai wani ya dauko faretin da Harisawa ke yi, yana ta soke-soke. Sai na ce masa ya ji tsoron Allah, wannan abin da yake zargin ’yan Shi’a da shi, kowa yana yi. Sai na dauko masa faretin da ’yan Izala suka yi wanda suke rike da bindigar katako. Nan take sai wani ya amshi maganar, yana cewa shi Wallahi ba dan Shi’a ba ne, amma an zalunci wadannan mutanen, kuma Allah sai ya fitar masu da hakkinsu a kanmu, don haka muke cikin wannan ukubar. Ni sai na yi shiru.

ALMIZAN: Wane abu ya hau kan ’yan uwa a irin wannan lokaci duba da irin halin da suke ciki?

FARFESA SHEHU MAIGANDI: Da yake yanzu ’yan uwa suna cikin wani yanayi marar dadi. Wajibi ne mu yawaita addu’a, kuma mu ci gaba da fitowa muna bayyana rashin amincewarmu da zaluncin da ake yi mana. Sannan kuma a ra’ayina, wannan rashin amincewar zai fi kyau a rika nuna shi a Kaduna da Abuja. In muka ci gaba da haka lokacin da Allah ya ga dama zai kawo karshen wannan zaluncin da ake yi mana. Zai fito mana da Jagoranmu.

Amma dai a kowane lokaci mu rika tuna baya, mu rika tuna tarihin Annabawa da Imamai. Ya rayuwarsu take? Wasu an kashe su, wasu kuma aka ba su guba, wasu kuma aka tsare su a kurkuku. Wani har cire kansa aka yi aka tsire a mashi ana yawo da shi. Wani kuma aka tsarga shi biyu da zarto. Haka tafiyar take. Wannan ita ce Sunnar Annabawa da Imamai. Don haka kai dan uwa a kowane lokaci ka rika tuna wannan.