AlmizanAlmizan logo
Jum'a 15 ga Sha'aban, 1438. Bugu na 1288 ISSN 1595-4474


Rahoto

Duk mutumin da bai da mataimaki sai Allah, ka ji tsoron fada da shi

Daga In ji Shaikh Halliru Maraya


 Shema Ibrahim

Mai karatu ga ci gaban jawabin da Shaikh Halliru Maraya ya yi a kwanakin baya a Tudun wada Kaduna, wanda muka soma buga muku a Almizan ta 1260. Umar Abubakar ne ya rubuta muku. A sha karatu lafiya.

A bar kowa ya yi addininsa, amma in ya taka dokar kasa a hukunta shi. Shi ne abin da ya kamata. A yi aibi, ka yi shiru; aibinka ya yi na wanda ya yi zaluncin, domin “assumtu ridha’un.” Ma’ana, shiru yarda ne. Saboda haka a yi abu, wanda za a zauna lafiya, shi ne daidai. Ban ga yadda za a yi a ce a hana mutane abu, don gudun za su yi kaza ba. Wai an hana su kar su yi kaza, don gudun za a samu tashin hankali. To, sai ya zamana ku kuma kun zo kun kashe su. To, me ke nan aka yi? Ai ba a gina doka a kan zato. Duk inda ka ji an yi sata, ko an yi garkuwa da mutane, ko an yi fashi, ba kafa ce ta kai mutanen wurin ba? To, shi ke nan yanzun sai gwamnati ta kafa doka ta ce, tunda ana zuwa a yi sata, ana garkuwa da mutane, ana yin fashi, to shi ke nan sai a daina tafiya? A’a, sai a bar kowa ya yi tafiyarsa, amma in kafarka ta kai ka wajen sata, ko wajen garkuwa da mutane, ko fashi, shi ke nan sai a hukunta ka. Don haka sai a bar kowa ya yi addininsa, amma in ya saba dokar kasa, to sai a hukunta shi.

In bin hanya da tare hanya laifi ne, shi ke nan sai a yi gyara a tsarin mulkin Nijeriya. Amma Shugaban kasa ya tare hanya, Gwamnoni sun tare hanya. Nan zabe in ya zo, 2019, za ka gani masu neman takara za su yi ta yin muzaharori suna tare hanya. Amma a ware wasu saboda kahon zuka, a kyamace su, ba daidai ba ne. Wai ai suna zagin Sahabbai, ina ruwan tsarin mulkin Nijeriya da Sahabi? Tsarin mulkin Nijeriya bai san sahabi ba. A wani “police station” an taba kai wani mutum kara. Can da DPO ya ji hayaniya ya ce, kai me ya faru ne? Sai aka ce masa an kawo wani mutum ne yana zagin Sahabi. Sai DPO din ya ce a kawo Sahabin ya rubuta ‘statement’. Sai aka yi masa bayani, sannan ya ce, to wannan shirme ne ai.

Saboda haka don Allah shugabanni su yi adalci, bolo haram da haka suka fara. A shekara ta 2009 kamar wasa, sad da suka fara ba sa kisa. Amma tunda aka kama Muhammad Yusuf da ransa, sojoji suka kama shi, aka mika wa jami’an tsaro suka kasha shi. Tun daga nan suka zama “violent”. Saboda haka, matsi yana sanya dan Adam ya dauki matakin da bai taba zaton zai dauka ba, ko kuma bai son ya dauka. Saboda haka shugabanni su bi a hankali. Ku yi hankali da miyagun Malamai. Kuma babban abin da ya kamata gwamnatin Tarayya ta yi, shi ne kwanan yadda aka yi wa Alkalai, yadda aka dirarwa wasu Alkalan manyan kotuna a kan tuhumarsu da rashawa da sauransu, Malamai ma a yi masu haka, musamman kan kudin makamai. Saboda haka muna kira ga gwamnatin Tarayya da ta bankado bangaren Malamai da Fastoci, duk wanda aka same shi da laifin ya ci kudin makamai, a yi masa hukunci, wanda ya dace.

Da yawa wasu suna lura ne kawai da duk abin da kuka yi sai su ce maku ya dace, don suna so ne kar ku bankado batun kudin makamai. Saboda haka mu yi ta “Hasbunallahu wani’imal wakil” kafa 450, Allah Subhanahu wata’ala ya kare Nijeriya, ya kare mutanen Nijeriya, ya kare duniya baki daya daga sharrin masharranta. Duk duniya babu aibi irin wadannan miyagun mutane. Su kullum burinsu kawai a rabu ne, su-isu ma ba zaman lafiya. Kowa ya ga abinda suka yi a Gusau wajen murnar Zamfara ta cika shekara 40. Suka yi ta aibata junansu.

Ni, na tsaya na yi tunani; ni Malam Zakzaky din nan mun zauna mun yi nagana da shi, mun yi waya, ni ban ga aibinsa ba, wallahi! Sam-sam ni ban ga aibinsa ba. Ko wannan da yake neman mulki, bai je wurin sa ba? Mutane a ji tsoron Allah. Ko da mugun mutum ne, a ce an kama shi tun Disamba a mulkin Dimokuradiyya, a ce har yanzun yana tsare, ba wani maganar hukunci, abin akwai alamun daure kai. Misali yanzun ka dauka Shehunka aka yi wa haka, don haka Ubangiji yake cewa, “wala yajrimannakum shana’ana kaumin ala alla ta’adilu, i’idilu huwa akarabu lit takawa.”

Gwamna ma kirista ya zauna da su lafiya, don haka ne wasu suke cewa sai Musulmi suke fada da shi. Irin wadannan miyagun Malaman, saboda a tunaninsu ne cewa, irin wadannan abubuwan suke so dama. Su je su yi maka bambadanci, kai Ahalus Sunna ne, kana yi wa addini hidima, kana kaza-kaza da sauransu. Kai kuma saboda daman kana son jama’a ne, kuma ga shi sun zo sun gaya maka cewa, kai Ahalus Sunna ne, kana kan Kitabu da Sunna. Shi kuwa ka ga Kirista, yaushe za ka je ka ce masa wani Kitabu da Sunna?

Saboda haka za ka samu koyaushe su suka fara kirkiro irin wannan a nan Jihar Kaduna. Wani zabe a lokacin can da babu Kaduna North ko Kaduna South, Kaduna Local Government ne gaba daya a lokacin, Rabaren Kochi Aboki, lokacin babban Malaminsu yana da rai, suka dage cewan dole kawai sai Musulmi ne zai yi shugabancin Karamar Hukumar Kaduna. Allah ya nuna masu ishara tun a lokacin, Kochi Aboki ya ci zabe. A mazabar Malaminsu kuma, duk da Musulmi ne suka fi yawa a wurin, Kirista mace ta ci zaben Kansila.

Su koyaushe daman abin da suke kokari ke nan, ba wai addinin ne ya dame su ba. Saboda za su je su same ka, wai a matsayinka na Musulmi, su yi maka famfo, su yi maka 419, su kwace maka kudi da dabara. Shi ya sa lokacin Yakowa, da sun zo zan ce a’a, ba wani taimako da Gwamnan nan zai bai wa kungiyarku. Saboda hatta a addinin Musulunci, Ma’aiki (S) ya yi wa kowa adalci. Idan aka je Jihadi, in ba ka je Jihadi ba, kana da ganima? Ba ka da ganima.

Wallahi mu yi hankali. A lokaci na farko, Maulidi da muka saba yi a Murtala Square, a shago muka yi, a ’Yan Tukwane, Maulidin Jiha a baki daya, Maulidin Annabi, alhalin Gwamna yana Musulmi, Shugaban kasa Musulmi, Kwamishinan ’yan sanda Musulmi, amma a shago aka yi Maulidi a karo na farko. To, wata ran a shagon ma ba zai yiwu ba. Ku rubuta wannan, saboda wahabiyawan nan suna zuwa suna yi masu famfo, suna gaya masu cewa Allah ya ba ka mulki, duk abin da yake bidi’a ne ka yi maganin sa. Wallahi abin da suke gaya masu ke nan. Allah ya ba ka mulki, don haka Allah ya zabo ka Ahalus Sunnah ne, kai mai riko da Kur’ani, mai riko da sunnah, saboda haka dama ce Allah ya ba ka shekara hudu ne, a wannan dama ka yi kokari ka ruguza bidi’a. Shi kuma daman bai san bidi’a ba. Ku rubuta, mun fada a baya kuna ganin kamar ba zai yiwu ba, to yanzun ma ku rubuta. Wannan Maulidi da ake yi a shago, wata rana ko da ranmu ko ba ranmu, za a zo a tarar an yarda a yi a shagon, amma a tarar ’yan sanda sun kewaye wurin, cewa ba a yarda ba saboda an sami ‘security report’ cewa za a yi tashin hankali. Daman haka ake fada. Ba za a ce an hana ku ba, a’a za a kawo wani abu ne, a ce an sami labarin za a yi kaza, shi ke nan, saboda haka ku yi hakuri. Allah Ya kiyaye.

Saboda haka, Wallahi masu mulki su ji tsoron Allah! Duk mutumin da bai da mataimaki sai Allah, ka ji tsoron fada da shi. Duk wanda bai da karfi, ba shi da inda zai garzaya a taimake shi sai Allah, to Wallahi, Wallahi, Wallahi a ji tsoron fada da shi. Mulkin shekara hudu, idan ma an zo an yi ta-zarce shi ne shekara takwas, shi ke nan kagama. Duk gatanka, shekara takwas ka gama.

Kuma abin da mutum ya yi a cikin wadannan shekarun har abada zai bi shi. In har akwai wani Gwamna da bai taba rufe hanya ba ya fito ya fada, in akwai Gwamnan da bai yi Muzahara ba ya fito ya fada. Gwamma ma su wadannan Muzahararsu suna yi ne da sunan addini, amma ku kuwa Muzahararku ta neman abin duniya ne. Koyaushe “intent” na mutum za ka duba. Yanzun in mutum ya fito ya bi hanya, yana kuka saboda an kashe Jikan Ma’aiki, soyayya da Ma’aiki ta sa shi haka ko kiyayya? Makiyin Annabi zai fito yana kuka saboda an kashe Jikan Ma’aiki?

Da an yi magana sai su ce zagin Sahabi, amma ga wanda ya kashe Sahabi kuna goyon bayansa. Ai ya zagi Sahabi, ya zagi Sahabi, to wanda ya kashe Sahabi fa? Allah Ya kiyaye. A ce wai iyayen Annabi na wuta, su ba sahabbai ba ne? Akwai zagin da ya wuce ka ce mutum yana wuta? Ina ruwanku da ’yan shi’a sun zagi Sahabi misali, ina ma ruwanka? Allah zai kama ka a lahira da cewar wane ya zagi sahabi, kai a hukunta ka ne? “Wala taziru waziratan ukrah,” balle mutanen nan sun ce ba sa zagin. Mutum ya ce ba ya yi, kai kuma ka dage da cewa, a’a kana yi. Wallahi ba ma zagin sahabbai, a’a kuna yi, a boye kuke yi. Wannan lamarin da daure kai, amma kai naka baro-baro a fili kana yi. Da zagin Sahabi da cewa siyasa ta fi sallah, wane ya fi? Da Sahabi da Sallah wanne ya fi? Akwai zagin da ya wuce ka ce siyasa ta fi Sallah? Wanda ba hadisin da ya taba fadin assiyasatu, ba ayar da ta taba fadin assiyasatu, babu. Amma ummul ibadatu, wacce a lokacin da za a bai wa Ma’aiki Sallah, sai da ya je gurin da ma Mala’ika Jibrilu ma bai isa ya je wajen ba, sannan aka ba shi Sallah. Amma mugun Malamin nan ya ce siyasa ma ta fi ta. Suka ce gaskiyarsa, gaskiya Malam ya yi bayani. To, mai fadin haka ne yake da bakin ya ce ana zagin Sahabi? Allah Ya kiyaye.

Saboda haka don Allah mu ba ruwanmu, bayin Allah din nan suna nan su na Allah ne. Ko Fir’auna ne a zamani, ka yi masa adalci. Babu adalcin da ya wuce, Allah zai tura Musa da Haruna ya ce masu, “fa kula lahu kaulan layyinan”. Amma yanzun duk Jihohi sun fara, ba za su fito fili su ce an hana Maulidi ba, amma sai su ce duk wani taro na addini an hana. Amma abin mamaki kuma shi ne, ai da sai a ce duk wani taro na siyasa shi ma an hana, da duk wani jerin gwano na siyasa an hana. Amma koyaushe za ka ji sun ce duk wani irin taro mai nasaba da addini an hana shi.

Mun sha gaya wa mutane ba su ji ba, suna ganin wasa ne, suka yi ta kashe mutane saboda Musulmi ya yi mulki, to ga Musulmin. Ai ‘system’ din ne ‘matters’ (tsarin ne abin lura), ba mai jan tsarin ba. Musulunci ne ba mu da abin da ya fi shi, amma Musulmi halinka ne zai fisshe ka. Allah ya kiyaye, ya zaunar da kasarmu lafiya. Za mu yi ta addu’a, tunda ka ga an fara kawo wadannan miyagun Wahabiyawan kasar nan. Ina ruwan Shugaban kasa da Limamin Madina? Ga Liman a Abuja, babu ruwansu da shi. ’Yan kungiyarsu suka tattara suka je, suka kai Limamin Madina. Duk “appointment da suke bayarwa yanzun Wahabiyawa ne. Mu ’yan Darika daman mun gaji a tura mota da mu, ta bude mu da kura. Yanzun ba za su dawo ba tukuna, sai 2019, sannan su zo su ce ai daman duk mu ’yan uwa ne, ai mu duk Musulmi ne, ai sai Musulmi kawai. Duk ranar da Batijjane ya tsaya takarar Gwamna, ranar ne za ka gano cewa lallai kai ba Musulmi ba ne a wajensu. Mun kammala.