AlmizanAlmizan logo
Jum'a 15 ga Sha'aban, 1438. Bugu na 1288 ISSN 1595-4474


Rahoto

Zaben Buhari: Mai bata abinai ya bata (1V)

TARE DA M.I. GAMAWA 09071965492


Na ga tafiya ta yi nisa. Kodayake rubutunmu na uku bai rubutu sosai a Almizan ta sati biyu da suka gabata ba. Amma komai ya fito daidai a Dandalin whatsapp da facebook. Na so a sake maimaitawa a ALMIZAN, amma gobe tana kara matsowa dakika bayan dakika, minti bayan minti, yini bayan yini, dare bayan dare. Inda aka tura zababbunmu na kira kamar yadda mai matsoracin Rago ke kama Ragonsa da yaudara, ko karfi. Ka san mai tsoro ba ya tserewa. Ko dai a kama shi da karfi ko da yaudara. A nuna masa masakin da babu komai don ya matso a kama shi. Don haka ya kamata ALKALAMI ya yi gaggawan kammala wannan mukala mai zurfin gaske, don ya jira yadda za ta kaya tsakanin Gwanin kisan ’yan Shi’a da gobe. Dadi na da gobe saurin zuwa.

Lokacin da aka kifar da Gwamnatin Shagari, wa zai gaje shi? Sai ta bayyana Buhari ne, wanda ya rantse wa wakilan Shagari, Soloman Lar da Umaru Shinkafi cewa babu ruwansa a neman kifar da Gwamnatin Shagari. Ya rantse, amma ga shi a Barikin Dodan a kan kujerar Shagari. Daga nan za ka gane cewa, wane irin mutum ne Buhari.

Bayan juyin-mulki sai halin da aka san Buhari da shi ya bayyana a fili ga ’yan siyasar da ya kifar. Sai daurin shekaru dari zuwa sama. Sai wulakanci da cin mutunci. Alhaji Tanko Yakasai ya fada a cikin littafin tarihin rayuwarsa mai suna, ‘THE STORY OF A HUMBLE LIFE’, bugu na 2, shafi na 13: "Alkiblar da addu'armu ta dosa ita ce gun Shugaban kasa Janar Buhari da Birgediya-Janar Tunde Idiagbon. Duk lokaci ba mu da wata addu'a, sai Allah ya sa su fuskanci irin abin da suka fuskantar da mu na wahala ba bisa hakkinmu ba. Watakila addu'o’inmu ne suka jawo kifewar Gwamnatin."

Wulakanci da rashin imanin da aka nuna wa Shehu Shagari ya fi na su Alhaji Tanko Yakasai, nesa ba kusa ba. Littafin ‘Beckoned To Serve’, shafi na 467 ya bayyana yadda Buhari ya tura babban Darakta na NSO, kamar yadda ake kiran su a lokacin, wato Alhaji Lawal Rafindadi, a Marina inda aka ajiye shi. Rafindadi ya nuna masa cewa ya zo ne a madadin Buhari da tabbacin cewa, nan ba da jimawa ba za a mai da shi (Shagari) Sakkwato da alkawura masu yawa, amma daga baya shiru kake ji, wai alkawarin Buhari wa talaka. A shafi na 469 ya fadi yadda aka tsare shi a gida mai lamba 2 a kan titin Ruxton da ke Ikoyin Lagos, aka hana kowa ganin sa. Aka hana hatta masu ba shi abinci magana da shi. Hatta ganin hasken rana, an hana shi; duk bisa umurnin Buhari.

Shaikh Abubakar Gumi, ya fada a cikin littafinsa mai suna ‘WHERE I STAND’, shafi na 206/208 yadda yayi kokarin neman izini a gun Buhari don ya gana da wasu Gwamnonin Shagari da Buhari ke tsare da su, amma Buhari ya ki. Ya ba da labarin yadda Janar Babangida ya kai shi wurin Buhari. A kan hanyarsu ya yi wa Babangida bayanin cewa zai so ganin su Shagari, amma Babangida ya ba shi shawarar cewa, tunda zai ga Shugaba Buhari zai yi kyau ya tattauna da shi a kan bukatarsa. Shaikh Gumi ya gabatar da bukatarsa har sau biyu, amma Buhari na biris da shi. Har ma Gumi ya ce, "ga shi na dawo daga sakon da ya tura ni, amma da na tuntube shi da maganar, sai ya yi shiru." Abinka da Malamin fada, maimakon ya zargi Buhari da laifin hana shi ganin su Shagari, sai ya ce wai ya fahinci mukarraban Buhari ne ba sa son haka. Ka san mai mulki dan gata ne a gun Malaman fada. Komai ya yi za a wanke shi fes.

Manjo-Janar Tarfa mai ritaya, a cikin littafinsa mai suna, ‘Profile In Courage’. A shafi na 325 ya bayyana dalilin kifar da Gwamnatin Buhari. Inda ya nuna ta a matsayin Gwamnatin da ta dakushe kaifin Majalisar koli ta soja. Sai dai 'yan tsiraru ne ke yadda suke so da sunan Gwamnati. Ko a cikin jawabin Janar Babangida na farko bayan kifar da Gwamnatin Buhari, abin da ya zargi Buhari da shi ke nan. Ko cikin littafin tarihin Babangida, ya sake maimaita haka. Littafin tarihin Babangida mai suna ‘Ibrahim Babangida: The military, Politics and Power in Nigeria, shafi na 199,’ ya zargi Buhari da kasancewa “mai tsattsauran ra'ayi, wanda ba ya sassautawa a abin da ya shafi tafiyar da Gwamnati. Idiagbon kuma mutum ne wanda ya daura wa kansa rawanin tsiya da daukar kansa a matsayin wanda ya san mafita ga kowace mas'ala. Mai amfani da mukaminsa a kan abin da bai shafi aikin Gwamnati ba don bukatar kansa." Haka dai maganar take ga duk wanda ya san Buhari.

Wani abin da manyan sojojin da suka yi ruwa da tsaki wajen kifar da Gwamnatin Shagari suka zargi Buhari da shi, shi ne an ci gari da su, amma sun kasa kama ko da kuturun bawa. Haka ma yanzu. Wani abin da ba a saba ji daga cikin gidan mai mulki ba, an ji shi a gidan Buhari. Uwargidansa Madam A'isha Buhari, ita ma ta tabbatar da haka. Inda ta yi masa zigidir a cikin kasuwa. Ta tabbatar wa gidan Radiyon BBC abin da sojojin da suka kifar da shi suka zarge shi a kai.

Masu bibiyar irin shugabancin Buhari da tsarin rayuwarsa, za su fahimci abubuwa hudu daga gare shi. Na Farko HASSADA, na biyu KETA, na uku RASHIN CIKA ALKAWARI, na hudu SON KAI. Wadannan halaye 'yan uwan juna ne. Ko ka ce ubansu ba daya ba ne, da wuya ka ce uwa kowa da tasa. Shakka babu sun hada dangi ta wajen uwa. Ka san dangin uwa suna nan da zumunta, kamar yadda Mamman Shata ya fada a wakarsa ta Gagara Badau.

Wadannan halaye sune suka mai da Buhari mai mulkin kama-karya da ko oh ga duk halin da talakawansa suka shiga. Tabbas duk lokacin da ya samu mulki, dole a wahala, ’yan kasa su shiga halin matsi, talauci, tsangwama, masifa, rashin kwanciyar hankali don karancin kayan masarufi. Za su gamu da zaluncin jami'an tsaro da musgunawa ta kowane janibi. Duk wadannan wahalhalu suna da alaka da halin wannan mutum.

Wani abu da ke damun Buhari shi ne daukar kansa da ya yi a matsayin wanda ya fi kowa gaskiya da rikon amana. Ga shi da rashin godiya ga duk wanda ya yi masa alheri. Ba mamaki da Buhari ya watsar da duk wadanda suka yi wahala da shi, ya dauko na nesa a lokacin da bukatarsa ta biya. Matarsa ma ta tabbatar da haka, kamar yadda muka fada a baya.

Hassada tana daukar juna-biyu har ta haifi keta. Wannan ma akwai shi a wajen gogan naka. Tunda ya dauki kansa mai gaskiya, hassadar da ke zuciyarsa ba za ta yarda akwai wani mai gaskiya in banda shi ba. Don haka kowa barawo ne. Amma in yana bukata a wajenka, zai amsa ba tare da tunanin ta yaya ka samu abin da za ka ba shi ba. Bayan ya karba zai kira ka da sunan da ya dace da kai a mahangarsa, wato barawo. Ko kuma ya bar ka, sai lokacin da kake neman Kura ta saka wa Kura aniyarta, lokacin ne zai tuna kai barawo ne, mai wawushe dukiyar talaka. Kodayake wannan sakayyar ma 'yan Arewa yake yi wa. Don me bai yi wa Rotimi Ameachi da Fashola haka ba?

In ka dau Buhari a matsayin Uba tabbas sunanka maraya. Ubanka na raye, amma matacce ya fi shi amfani, don Ubanka matacce ba zai hana a yi maka dominsa ba. Ba shi da ikon haka, don matacce ne. Amma Buhari tunda yana raye, zai hana a yi maka dominsa. Shi ba zai yi maka ba, ba zai bari a yi maka ba. Lokacin da na ji Buhari ya ce wai ya mai da 'ya'yan Cif Harry Mashal da aka kashe don goyon bayan da ya nuna wa tamfar 'ya'yansa na cikinsa, nan take na ce, aikin banza, wai harara a duhu! Ka sake jin Buhari ya yi maganar su? Tabbas babu ruwansa da su. Ya yi alkawarin siyasa a lokacin da ya je ta’aziyya, alkawarin mai neman kuri’a.

In yana cika alkawari, don me bai cika wa talakawa alkawarin da ya dauka na biyan su Naira dubu biyar-biyar duk wata ba? Don me bai bar kudin man fetur kamar yadda ake sai da shi a lokacin Jonathan ba? Don me bai bar kudin tafiya Hajji a yadda ake biya a lokacin Jonathan ba? Don me bai bar canjin Dalar Amurka a yadda take a lokacin Jonathan ba? Don me ya soke ba da irin shuka kyauta? Don me ya cire tallafin takin zamani, wanda 'yan Arewa ke nema ruwa a jallo?

In mun dawo ta yaki da rashawa, don me bai hukunta Rotimi Ameachi ba? Don me bai hukunta Fashola ba, duk da cewa wadannan tsofaffin Gwamnoni sun yi fachakar da ta wuce misali a lokacin kamfen dinsa? Amma sai aka saka musu da ofisoshi masu tsoka don su maido da kudinsu. Amma aka rika kama tsofaffin Gwamnonin da ba su ba da tasu gudummawa lokacin yakin neman zabensa ba. Me ya sa aka kyale Gwamnoni da yawa da ake da korafe-korafe a kansu, duk da tarin hujjojin da aka gabatar, amma ake kama wasu da babu wanda ya yi korafi a kansu?

ALKALAMI bai gaji da tambaya ba. Me ya sa doka ba ta aiki a kan 'yan lele, kamar su Buratai? Me ya sa ake tuhumar wasu Hafsoshin sojojin sama da na ruwa, amma ba a tuhumar na sojojin kasa, in dai kudin makamai ake nema? Ko dai kabilancin aikin soja ne ya motsa, tunda Buhari tsohon sojan kasa ne?

Me ya sa ba a kama Malaman Izala wadanda suka karbi Miliyoyi don kamfen ma Jonathan ba? Me ya sa ba a binciki zargin da tsohon Gwamnan babban Bankin kasa, Sarkin Kano na yanzu ya yi ba cewa wasu na karbar Dalolin Amurka daga Bankin suna sayarwa da tsada a kasuwar dare? Ya kuma ce 'yan fadar Buhari ne. Me aka yi musu? Me ya sa ba a binciki badakalar MTN ba, wacce ake zargin babban na hannun daman Buhari, Abba Kyari ba? Abin da yawa, wai jami'in tsaro ya ga tattakin 'yan Shi’a.

Masu danganta Buhari da son addinin Musulunci ga tambayoyi kadan. Shin akwai wani masallaci a fadin duniya ba Najeriya kawai ba, da Buhari ya gina? Shin akwai Makarantar Islamiyya daya da Buhari ya gina a fadin duniya? Shin an taba jin inda ya ba da Zakka? In ya taba, wa ya bai wa? Kar ka ce ba shi da abin da zai ba da zakka a kai. Shi ma da kansa ya fadi yawan shanun da ya mallaka. Ko ba a zakkar shanu ne a Sunna? Me ya sa in ya tashi zaben abokan aikinsa, yake zabo makiyan Musulunci masu cin mutuncin Alkur'ani? Misali, kowa ya san yadda riddadde Tunde Bakari ke yi wa Alkur'ani cin zarafi a Cocinsa akai-akai, amma don rashin ruwa da addini, Buhari ya dauke shi mataimaki a karo na biyu na neman zama Shugaban kasa. Dauko Tunde Bakari ya zame wa musulmin Yarabawa abin gori da isgili a gun kiristocin Yarabawa, har su musulman suka yi wa manyan 'yan siyasarsu barazana, sai da suka janye kuri'unsu ga Buhari a wancan lokaci. Kodayake jaridu ba su yayata hakan ba, amma wannan shi ne gaskiyar abin da ya faru.

Me ya sa a duk lokacin da Buhari ya hau karagar mulki, sai ya tsawwala kudin aikin Hajji? Wanda ba musulmi ba ya tausaya wa musulmi, amma shi ya tsawwala. Ina dalili? Wannan shi ne son addini?

Ga wadanda suka zabi Buhari don yana son Arewa, su ma ko za su amsa mana 'yan tambayoyi kadan? Za su iya nuna mana wata masana'anta da Buhari ya yi amfani da mulkinsa ya kawo ta Arewa? Za su nuna mana mutum daya da Buhari ya sama wa aiki a wata Ma'aikata? Za su nuna mana wanda Buhari ya biya wa kudin makaranta in banda 'ya’yansa? Ko za su nuna wata Cibiyar taimako mai zaman kanta, mai taimaka wa 'ya’yan talakawa da Buhari ke da hannu a ciki? ALKALAMI zai yi ta babban mahaukaci, wa ya taba ganin 'yan maula a kofar gidan Buhari suna neman taimako? Za mu ci gaba insha Allah.