AlmizanAlmizan logo
Jum'a 15 ga Sha'aban, 1438. Bugu na 1288 ISSN 1595-4474

Rahoto

Yaushe Buhari zai dawo daga London?

Daga Danjuma Katsina


 mallam

A yayin da Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya sake koma wa London domin neman magani, wata zazzafar muhawara ta kaure a tsakanin jama’a game da lokacin da ake ake tunanin zai kwashe kafin ya dawo gida.

Fadar Shugaban kasa dai ta bar abin a rufe, kamar yadda ba ta bayyana ciwon da ke damun Shugaban kasar ba, haka kuma ta yi gum game da ranar da zai dawo gidan Nijeriya.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Shugaban kasa, Femi Adesina ya fitar, ta ce Shugaban zai gana da Likitocin ne a wani bangare na ci gaba da jinyar da ya je a watannin baya. Sai dai ya ce, babu tabbacin ranar da Shugaban zai dawo, domin Likitoci ne kawai za su fayyace hakan. Amma ya ce kada ’yan kasa; “su tayar da hankulansu domin babu wani abin damuwa”.

Tuni dai har ya hannunta ragamar tafiyar da kasar a hannun Mataimakinsa, Yemi Osinbajo domin ci gaba da mulkin kasar a matsayin Mukaddashin Shugaban kasa. “Tuni Shugaban ya aika wasika ga Majalisar Dattawa domin sanar da su cewa Osinbajo ne zai ci gaba da lura da al’amura”.

Sashe na 145 (1) na Kundin tsarin mulkin ya ce; “A duk lokacin da Shugaban kasa ya aika wa Shugaban Majalisar Dattawa da Kakakin Majalisar Wakilai wasika cewa zai tafi hutu, ko kuma wani dalili zai sa ba zai iya zuwa ofis ba, to mataimakin Shugaban kasa ne zai ci gaba da jan ragamar kasar, har sai lokacin da Shugaban da kansa ya sake aika wata wasikar da zai bukaci a janye hakan”.

A cikin sanarwar, Femi Adesina ya ce Shugaba Buhari ya jinkirta tafiyar tasa ne domin ya gana da ’yan matan Chibok 82 da Boko Haram ta saki.

A makon da ya gabata ne wasu ’yan kungiyar farar hula suka yi kira ga Shugaban da ya koma asibiti saboda ya kula da lafiyarsa, in ba haka ba za su fito zanga-zanga ba ji ba gani.

Fargaba kan yanayin lafiyar Buhari ta kara ta’azzara ne bayan da aka ga bai halarci taron Majalisar Ministoci ba sau uku a jere, inda kungiyoyin fararen hula suka dinga kiran sa da ya koma London don a sake duba shi. Sai dai mai dakinsa, Hajiya A’isha ta ce, ana zuzuta batun rashin lafiyar Maigidan nata.

Yanayin lafiyar Buhari dai ya zama wani babban abin damuwa a kasar, inda ake cike da tsoron samun gibi a wajen jagorancin kasar zai iya shafar farfadowarta daga matsin tattalin arzikin da take fuskanta.

Kafin Buhari ya bar kasar nan ya gana da Mataimakinsa, Farfesa Yemi Osinbajo da Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Bukola Saraki da Kakakin Majalisar Wakilai, Yakubu Dogara.

’Yan Nijeriya suna nuna matukar damuwa kan rashin lafiyar Shugaban bisa fargabar kada a maimaita irin abin da ya faru a shekarar 2009 a lokacin da Marigayi Shugaba Umaru Musa ’Yar’adua ya yi ta fama da rashin lafiya, al’amarin da har ya sa aka kai shi kasashen Saudiyya da Jamus don neman magani. An bayyana rasuwarsa a ranar 5 ga Mayun 2010.

Kuma saboda bai mika ragamar mulki ga Mataimakinsa ba, kuma ga rashin bayyana wa ’yan kasar halin da yake ciki, hakan ya jawo ce-ce-ku-ce sosai.

A lokaci jinyar Buhari a London dai, Mista Osinbajo ya samu yabo ta bangarori da dama saboda yadda ya tafiyar da mulkin kasar a matsayinsa na Mukaddashin Shugaban kasa. Matakan da ya dauka na gaggawa wurin tunkarar matsalolin da kasar ke fuskanta bayan tafiyar Shugaba Buhari hutun jinyar na farko, sun bai wa masu sharhi mamaki.