AlmizanAlmizan logo
Jum'a 15 ga Sha'aban, 1438. Bugu na 1288 ISSN 1595-4474

Rahoto

Shekaru 40 cur na Harka Islamiyya: Jarabawowi da nasarori

Daga Muhammad Suleiman


Wuyan mai

Da farko muna godiya ga Allah Ta’ala da ya nuna mana wannan lokaci na cikar wannan Harka shekaru 40 cur. Idan mutum ya bibiyi tarihin wannan Harka, zai ga cewa Sayyid Zakzaky (H) ya faro Da’awa siriyya ne a watan Afrilun 1977. Wannan abu ya faru ne a garin Katsina a wata makaranta da ake ce ma Katsina Teachers College, a wani IVC da aka gudanar a lokacin, wato Islamic Vacation Course, kamar yadda dan uwan da ya kasance a wannan IVC ya taba ba mu bayani, wato babban Yayanmu a wannan Harka ta Musulunci, Shaikh Muhammad Mahmud Turi. Ina ce masa haka ne, da yake duk wani dan uwa da yake cikin wannan Harka a yanzu, to a bayansa ya zo.

Yake cewa a wannan IVC, Sayyid Zakzaky ya yi gayyata ta musamman. Sayyid ya ce za a yi wani taro na musamman da tsakar dare, lokacin da idanuwa suke barci, amma yana son duk wanda zai halarta ya kasance ya yi nufin ba da rayuwarsa baki daya a tafarkin Allah Ta’ala. Lokacin da aka zo wannan taro da tsakar dare, sai Sayyid Zakzaky ya ga dalibai da yawa sun zo, shi ne har yake cewa anya wadannan duk sun yi nufin ba da rayuwarsu a tafarkin Allah? A takaice dai haka aka yi wannan taro. Kuma wanda ya wanzu a cikin wannan Harka na mahalarta taron shi ne Shaikh Muhammad Turi. Kuma ya ce, wannan shi ne karon farko da ya soma ganin Sayyid Zakzaky.

Ya kuma faro Da’awa Jahariyya shi ma a watan Afril 1980. Wannan ya faru ne a garin Funtuwa. Lokacin da wannan Harka ta cika shekaru 25, akwai taro da aka yi a garin Zaria, wanda a lokacin Sayyid ya yi bayanai na tarihin wannan Harka, wato yadda ta faro da kuma jarabawowin da aka fuskanta a cikin shekarun da kuma nasarori da aka samu. To, a yanzu idan mutum ya lissafa daga lokacin da aka faro Da’awa Siriyya wato a watan Afrilu 1977 zuwa yanzu, wato watan Afrilu na 2017, zai ga cewa shekaru 40 ke nan cur.

Idan muka dubi jarabawowin da suka auku tun daga faro wannan Da’awa zuwa yanzu, za mu ga cewa suna da yawa. Kuma sun auku ne ta fuskoki dabam-dabam, a wajaje dabam-dabam, a kuma lokuta dabam-dabam. Saboda haka kasantuwar jarabawowin na da yawa, za mu dauki jarabawowin da Sayyid Zakzaky ya fuskanta a tsawon wadannan shekaru 40 ta fuskacin gwamnatoci dabam-dabam da aka yi tun lokacin da ya soma Da’awar zuwa yanzu.

Ga wanda ya san tarihin wannan Harka, zai ga cewa, Sayyid ya fara Da’awa ne a zamanin mulkin soja na Janar Obasanjo, saboda haka kamun farko da aka yi ma Sayyid Zakzaky ya auku ne a zamanin Gwamnatin mulkin soja, karkashin shugabancin Janar Obasanjo. Wannan abu ya faru ne a 1979, wato lokacin Sayyid yana dalibi a Jami’ar Ahmadu Bello. Yana ma shekarar karshe ne na karatunsa. Kai a lokacin ma yana rubuta jarabawarsa ta kammalawa ne aka kama shi. Saboda haka a lokacin akwai Faifofi da bai samu rubuta su ba, sai daga baya. A lokacin da aka kama shi an tsare shi ne a Police-Station na ‘Yan Sanda a Zaria. Wani abin mamaki ma shi ne da suka tsare Sayyid, sai da suka kwana uku ba su ba shi abinci ba. Bayan kwana uku da suka fito da Sayyid cikin ‘Cell’ domin su yi masa tambayoyi, su kansu ’yan sandan abin ya ba su mamaki, domin duk tambayoyin da suka yi masa ya ba su amsa. Kuma suka bukaci ya rubuta ‘statement,’ to sai da ya rubuta masu har shafi goma. Shi ne har suke cewa, “duba rubutunsa da kyau, kamar wanda bai sha yunwa ba”; wanda yake nuna ashe da gangan suka hana shi abincin.

Akwai lokacin da Sayyid yake ba da labarin wannan al’amari, yake cewa, wani ikon Alah cikin wadannan kwanaki da ba su ba shi abinci ba, bai ji wani abu da ake ce ma yunwa ba, ballantana ya bukaci su ba shi abinci. Allahu Akbar! ’Yan uwa mu dubi yadda wannan gwagwarmaya ta faro.

Bayan haka kuma an tsare Sayyid Zakzaky a garin Sakkwato a 1981, aka kai shi Kotu aka yenke masa hukunci na zuwa Kurkukun Inugu na tsawon shekaru hudu. Saboda haka daga 1981 zuwa 1984 Sayyid Zakzaky yana kurkukun Inugu ne. Kuma wannan shi ne karon farko na zartar ma Sayyid Zakzaky dauri na zaman Kurkuku a tarihin wannan Harka. Wannan waki’a ta faru ne a zamanin Gwamnatin farar hula karkashin jagorancin Alhaji Shehu Shagari.

Bayan haka kuma a shekarar da Sayyid Zakzaky ya fito daga Kurkukun Inugu, wato a 1984, wato a karshen shekarar, aka sake kama shi. Wani tarihi a nan shi ne, a cikin wannan shekara ta 1984 Sayyid Zakzaky ya yi aure. Saboda haka bayan aurensa da kimanin watanni biyar ne aka kama shi. A lokacin da aka kama shi, sai aka kai shi Lagos aka tsare shi a Kiri-kiri. Wannan ya auku ne a zamanin Gwamnatin mulkin soja, karkashin shugabancin Janar Muhammadu Buhari.

Sayyid Zakzaky ya kasance a Kiri-kiri har ya zuwa 1985. Shi ya sa ko lokacin da aka haifa masa da na farko, wato Sayyid Muhammad yana Kiri-kiri ne. Wani tambihi a nan, kuma abin lura shi ne, wannan da nasa na farko da ba ya nan aka haife shi, to yanzu ma a lokacin aurensa ba ya nan a karkasin shugabancin wanda ya tsare shi a wancan lokacin.

Ta yiwu wasu su yi tambaya kan Kiri-kiri. To, kamar yadda Sayyid Zakzaky ya taba bayani a kansa cewa, waje ne da idan ana so a musguna ma mutum, ko a azabtar da shi, to akan kai shi wajen. Har yake cewa, ba a yarda mutum ya shiga wajen da riga ko wando, sai dai a shigar da mutum daga shi sai Fant. To, lokacin da suka kai Sayyid Zakzaky, sai suka ce ya tube rigarsa da wando. Ya ce ba zai yiwu ba. Haka dai aka yi ta ja-in-ja. Daga karshe suka bar Sayyid Zakzaky ya shiga da rigarsa da wando. Har ma Sayyid yake cewa, yana ganin shi ne mutum na farko da ya shiga wajen da kayan jikinsa. Kuma ya ce yawancin dakunansu a karkashin kasa suke, saboda haka a lokacin ya ce gane lokacin Sallah yana yi masa wahala sosai, musamman ma ya ce Sallar Asuba, da dai sauran abubuwa na cutarwa da Sayyid Zakzaky ya fuskanta a wannan zama nasa na Kiri-kiri.

Bayan haka kuma, a shekarar 1987 aka kama Sayyid Zakzaky aka tsare, daga karshe aka kai shi Kurkuku na Fatakwal, ya fito daga Kurkukun a 1989. Wannan waki’a ta faru ne a zamanin Gwamnatin mulkin soja karkashin shugabancin Janar Ibrahim Babangida. Sai kuma a 1992 aka sake kama Sayyid Zakzaky a filin jirgin sama na Kano, lokacin zai yi tafiya zuwa Ingila kan wani taro na Addinin Musulunci da aka gayyace shi. Bayan an kama shi, aka kai shi Lagos. Kai tsaye aka wuce da shi Kiri-kiri, amma tsarewar, Alhamdu-lillahi ba ta tsawaita ba, kimanin mako guda ne. Wannan shi ma ya auku ne a lokacin mulkin Babangida, wato dai Babangida sau biyu yana kama Sayyid da kuma tsare shi.

Bayan haka kuma sai a shekarar 1996, aka sake kama Sayyid Zakzaky aka tsare a Kurkukun Fatakwal. Wannan ya kasance a lokacin Gwamnatin mulkin soja, karkashin jagorancin Janar Sani Abacha. Ya fito daga kurkukun ne a shekarar 1998, wato bayan mutuwar Abacha. A takaice dai daga shekarar 1981 zuwa shekara 1998, Sayyid Zakzaky ya kwashe sama da shekaru goma a gidajen kurkuku dabam-dabam na kudanci da kuma arewacin kasar nan. Akalla kurkuku sun kai guda tara da ya zauna a cikin su.

To, tun daga 1998 har ya zuwa 2015 ba a sake kama Sayyid Zakzaky aka tsare ba. Amma fa a lura cewa haka ba yana nufin Gwamnatocin da suka biyo bayan na Abacha sun hakura daga makirce-makirce ko kullu-kulle ga Sayyid da kuma ita Harkar ba ne. A’a sun lura ne cewa, duk kame-kame da kuma tsare-tsare da suka yi ma Sayyid Zakzaky yana habaka da kuma tambatsa Da’awar da yake yi ne kawai, saboda haka yanzu abin da suke ganin mafita gare su shi ne su kashe shi. Shi ya sa in muka duba za mu ga cewa gwamnatoci kamar irin ta Alhaji Musa ’Yar’aduwa ta yi yunkuri na kashe shi ta hanyar jefa Bom a gidansa, kamar dai yadda Sayyid Zakzaky ya yi bayani a kai a lokacin da aka yi wannan yunkuri.

Haka nan mu dubi lokacin Gwamnatin Jonathan, shi ma an yi ta yunkuri kala-kala, ta kuma fuskoki dabam-dabam, a kuma lokuta dabam-dabam, amma ba su samu nasarar haka ba. In ma mutum bai san wadancan ba, to ya dubi abin da wannan Gwamnati da muke ciki ta yi masa na nufin kashe shi, amma Allah Ta’ala bisa ikonsa ya kare shi, ya kuma nuna ma wadanda suka ba da umurnin haka cewa, shi ne Mai iko a kan komai.

Lokaci ya yi da mutanen kasar nan, musamman masu tafi da iko za su fahimci cewa, al’amarin wannan bawan Allah, al’amari ne na Allah Ta’ala. Shehu Usman Dan Fodiyo ya yi albishir da bayyanarsa. Haka nan ’yarsa mai suna Asma’u. In mutum na so ya ga wannan bushara, to ya nemi littafin Shehu Usman Dan Fodiyo mai suna “BUSHRAL-AHBAB.” Shi wannan littafi ya kunshi bayanai na Shehu Usman kan wadansu bayin Allah Waliyyai da suka kasance a zamaninsa da kuma wadanda za su zo bayansa. Amma a cikin littafin Shehu Dan Fodiyo ya karfafa bayani ne kan Imam Mahdi (AF) da kuma Sayyid Zakzaky. Wani abin lura, idan mutum ya karanta littafin, zai ga yadda Shehu Usman Dan Fodiyo ya kawo wasu bayanai dangane da Sayyid, wanda duk wanda ya san Sayyid, ko yake tare da shi, zai tabbatar da su. Ga misalan wasu ababe da ya kawo:

1- Fadin sunan Sayyid, wato Ibrahim. 2- Fadin shekarar haihuwarsa, shekarar da ya fada ita ce 1370 ta Hijira.

3- Fadin cewa Sayyid zai zo daga yamma shi ya sa a cikin littafin ya yi masa lakabi da ‘Ibrahimul-Magribi’. 4- Fadin cewa Sayyid zai yawaito ziyarar Manzon Allah a Madina, duk wanda ya dade a cikin wannan Harka, zai ba da shaida cewa lalle a shekarun baya, baya ga aikin Hajji da Sayyid yake zuwa kowace shekara, to duk watan Ramadan a birnin Madina yake yin sa, wato a Masallacin Manzon Allah, kuma ya fi zama a Rauda, kamar yadda ya taba fadi. 5- Fadin kamannun Sayyid, misali ya yi bayanin idanuwan Sayyid da goshinsa, da dai sauransu.

In ma mutum bai yarda da wadannan ababe ba, to karamomin da suka bayyana gare shi, kuma suke bayyana sun isa su tabbatar da cewa ko shi wane ne. Alal misali wannan waki’ar da aka aukar ta Zariya, Sayyid ya jima yana bayanin cewa, akwai ‘plan’ na yin kisan kiyashi. Ya kuma ce, idan sun yi haka, to za su tambatsa Da’awar, ta inda ba su tsammani. Kuma sai sun yi bakin ciki a kan haka, wato bakin cikin ba su samu nasara ba. Ya ce kuma za su yi hasarar duniya da kuma lahira. To, mu duba fa mu gani.

A takaice, duk wadanda suke tare da shi za su tabbatar maka da abubuwa masu yawa na karamomin da suka shaida daga wajensa. Cikin ’yan uwan da suka ziyarce shi kwannan yake ce min Sayyid yana tsare ba a waje ba, amma ya fi mu sanin abubuwan da suke faruwa a ciki da wajen kasar nan. Shi ne nake ce masa, haka al’amarin Waliyyan Allah yake, suna gani ne da hasken Allah Ta’ala. Shi ya sa ni ko da wane lokaci, in na ga wani ko wasu suna fada da Sayyid ko wannan Harka ta Musulunci, to ina tausaya masu, saboda fada ne da al’amarin Allah, wato dashen Allah Ta’ala.

A tarihin dan Adam kuma, babu wani wanda ya yi fada da Allah, ya samu nasara. In ma mutum bai san haka ba, to ya yi tunanin duk wadanda suka yi fada da shi, yadda karshensu yake kasancewa. Kuma ma mutum ya yi tunani. Duk Gwamnatoci dabam-dabam da aka ambata, tun lokacin da ya faro Da’awar, matakan da suka dauka kan Sayyid Zakzaky da mabiyansa da kuma ita kanta Da’awar domin ganin sun kau da su, to tambaya a nan sun ci nasara? Kai ba ma kawai ba su ci nasara ba ne, sun ma taimaka wajen bunkasa Da’awar ne da kuma daukaka shi Sayyid Zakzaky.

Bari in ba da misali. Duk wanda ya kasance cikin wannan Da’awa ta Sayyid Zakzaky sama da shekaru 30 da suka wuce, zai tabbatar maka da cewa, Da’awar nan lokacin da ta faro ta fi karfi ne a makarantu, musamman ma manyan makarantu, kamar Jami’o’i da sauransu. Amma sakamakon kamun Babangida ga Sayyid Zakzaky, sai Da’awar ta tambatso zuwa cikin gari, wato ta soma shiga cikin birane. Haka nan sakamakon kamun Abacha da matakan da ya dauka kan Da’awar, sai Da’awar ta nausa ta yi cikin kauyuka, kai har ma da rugage na Fulani a cikin dokar daji. In ma mutum bai fahimci haka ba, to ya dubi wannan waki’a da muke ciki, sakamakon abubuwan da aka yi ma Sayyid da mabiyansa, yanzu Da’awar ta tambatsa a sassan duniya dabam-dabam.

Ta wani labari da na ji cewa, Shugaban kasar Indiya, ya ga lokaci bayan lokaci, wasu daga cikin Musulmin kasarsa suna fitowa Muzahara a kan a saki Zakzaky, shi ne yake tambaya wai “waye wannan Zakzaky? Ya ce, ina son in san wani abu dangane da shi.” Haka nan wadanda suka samu ziyara zuwa Karbala ta wannan shekara da muke ciki, wato ta Arba’in din Imam Husain, in an gan ka bakin mutum, ana tambayar ka daga wace kasa? Kana cewa daga Nijeriya, sai ka ji an ce “Zakzaky?” Wato sakamakon waki’ar, sunan Sayyid Zakzaky ya tambatsa a duniya. Akwai ma wani da muka hadu da shi a Birnin Najaf a haramin Imam Ali (AS), to sai yana son ya tambaye ni cewa, Zakzaky har yanzu yana tsare ne a hannun hukuma, ko an sake shi? To, kasantuwar mutumin ba ya jin Turanci ko Larabci, sai dai harshen kasarsu na Turkiyya, to sai ya kama hannuna ya matse, wato yana nufin yana tsare? Sai na kada masa kai na cewa iye. To, kawai sai na ga hawaye suna zubowa daga idanuwansa. Saboda haka irin wadannan matakai da hukumomi suke dauka na cutarwa da kuma gallazawa, suna taimaka ma Da’awar ne, amma su ba su sani ba. Wato suna tallata Da’awar sakamakon abin da suke yi, amma su ba su sani ba. Shi ya sa ci gaba da tsare Sayyid Zakzaky yana dada fadakar da mutane Musulmi da wadanda ba Musulmi ba, na cikin kasar nan, da ma wajen kasar nan cewa, lalle abubuwan da aka yi, kuma ake kan yi, to akwai lauje cikin nadi, kuma tabbas tarihi zai ba da shaida a kai.

Sai kuma abin da ya shafi nasarori da wannan Harka ta Musulunci ta samu a tsawon shekaru 40 da ta kwashe, wadannan nasarori suna da yawa, wato sun kai haddin ‘La tu’addu wala tuhusa, amma ga wasu daga ciki:

1- Tsayuwa da kuma wanzuwar Da’awa, wanda ko da ba a fagen addini ba, a ce a fagen duniya, ga wani abu ka tsaya kyam a kan sa tsawon shekaru 40, ai ko za a yabe ka, to ballatana tsayuwa a fagen addini, wanda yake tattare da jarabawowi masu yawa, amma duk da haka mutum ya tsaya kyam. Tabbas wannan babbar nasara ce.

2- Adadin wadanda suke Da’awar yanzu ana maganar miliyoyi ne. Mu duba fa mu gani Sayyid Zakzaky shi kadai ya soma wannan kira, aka fara samun daidaiku suka amsa masa, suka soma kai wa daruruwa, suka soma kai wa dubbanni, yau ga shi sun kai miliyoyi, a takaice dai wadanda aka faro wannan Harka da su, to yanzu suna matsayin kakanni ne, wato sun haifi ’ya’ya a ciki; ’ya’yan da suka haifa su ma sun haifa duk a cikin Harkar, wanda in mutum na da tunani, zai fahimci cewa, lalle wannan abu ya kafu daram, kau da shi ba zai taba yiwuwa ba. Shi ya sa ko wannan kashe-kashe da aka yi, to ko daya bisa dari na ’yan uwa ba a kashe ba, wato in ka kwatanta adadin da suke cikin Harkar.

3- Aikata addini a aikace, ba wai a karance kawai ba. Daga cikin nasarorin da wannan Harka ta samu akwai wannan, wato dabbaka addini a aikace, wanda hakan kuma ya yi tasiri sosai a cikin wannan kasa da muke a ciki.

4- Jawo mata a fagen addini. Gabanin fara Da’awar Sayyid Zakzaky a wannan kasa tamu, ba a san mata a fagen addini ba. Amma sakamakon Da’awar, yau Harkoki na addini, duk da mata ake yi, wato dai kamar yadda yake lokacin Manzon Allah (S) cewa, gwagwarmayar addini tare da mata aka yi.

5- Hada kan al’ummar Musulmi. Daga cikin nasarorin da wannan Harka ta samu akwai sa’ayi wajen hada kan al’ummar Musulmi, da kuma kusanto da wadanda ba Musulmi ba jika, wato dai kyautata alaka da su, wanda kuma ana ganin tasirin hakan. A takaice dai akwai nasarori masu yawa da aka samu a tsawon wadannan shekaru 40. Ga mai bukatar karin bayani kan tarihin wannan Harka da Sayyid Zakzaky, yana iya duba littafin da na rubuta a shekarun baya mai suna ‘TARIHIN SAYYID IBRAHEEM YAQOUB AL-ZAKZAKY DA HARKAR MUSULUNCI’.

Daga karshe, nasiha ga masu fada da wannan kira na Sayyid Zakzaky (H) da ya kwashe shekaru 40 a kai, mutum ya tambayi kansa, in shi mai mulki ne ko jami’in tsaro, shekaru 40 da suka wuce yana wane mataki ne a rayuwar sa? Kila ma wani zai ga cewa ko haihuwarsa ba a yi ba a lokacin, ko kuma an haife shi, amma yana firamari ne. To, saboda Allah ka tausaya ma kanka, ka yi ma kanka adalci. Abin da ake yi tun gabanin a haife ka, ko tun kana yaro, yau ka zo ka ce za ka kau da shi, alhali in kan mulki mutum yake a kai, bayan wasu shekaru, in wa’adin ya kare zai sauka ne, shi da abubuwan da ya aikata su zama tarihi.

To, da a ce shi kenan, da sauki. To, kiyama tana gabanka, kuma akwai hisabi a can na duk abubuwa da ka aikata a wannan gida na duniya. Saboda haka lahira ita ce abin ji. Saboda haka duk abin da mutum ya shuka a wannan gida na duniya, kyakkyawa ko mummuna, to shi zai girba a gobe kiyama.