AlmizanAlmizan logo
Jum'a 15 ga Sha'aban, 1438. Bugu na 1288 ISSN 1595-4474

Rahoto

Malam Zakzaky (H) a Kaduna!!??


 UN

Jaridun kasar nan, ciki har da Almizan sun ruwaito cewa babban Antoni-janar na kasar nan ya sanya hannu a wata bukata da gwamnatin Kaduna ta nema a rubuce cewa, a ba ta Malam Zakzaky (H) domin su tuhume shi da wasu laifuffukan da suke zargin ya aikata a jihar.

A farko gwamnatin Tarayya ta ki amincewa da wannan bukata. A farko gwamnatin ta Tarayya suna da wani shirin nasu da ba wannan ba, don haka suka ki amincewa da wancan bukatar, kamar yadda wata majiya ta tabbatar mani.

Dalilin da ya sanya suka canza shawara, shi ma wata majiya ta shaida mani, amma hujjojin nasu ba abin kawowa ba ne a yanzu, sai dai kila nan gaba. Amma yanzu, wannan filin ba muhallin kawo su ba ne; watakila sai a wata rana.

Kawo Malam (H) Kaduna wani abin da yake kara tabbatarwa shi ne jihar Kaduna, wadda Gwamnanta yana daga wadanda suke da bayanin da dole wata rana su yi na irin rawar da suka taka a wannan matsala, wadda Allah kadai ya san ranar kawo karshenta.

Wannan kuma na fade shi a wani rubutu na da na yi mai suna KOWA YA YI TANADI MAI TSAWO, wanda ya fito a wannan fili. Na kuma fadi a wani rubuta, mai taken ‘Maitatsine: Gwamnonin Neja-Delta da kuma Nasiru Elrufa’i. Dawo da Malam (H) Kaduna, kamar maido ma gwamnatin Kaduna matsalarta ce, ta kuma fitar da mafita a kanta.

Ni ina da tabbacin yakinin cewa, matsalar da ake ciki ta Harka Islamiyya, da gwamnatin Kaduna karkashin jagorancin El-rufa’i ta yi abin da ya kamata, da lamarin bai kazance a haka ba. Gwamna shi ne babban Jami’in tsaro a jiha. Ba wani aikin tsaro da zai iya wakana ba tare da amincewarsa ba.

Kwanan nan wasu lamurra sun faru wadanda za su zayyana ma mutum karin hasken wannan. Wani Fasto mai suna Sulaiman, ya yi wani wa’azi a wani gangamin wa’azin cocinsa. A wa’azin ya rika cewa a kashe duk Bafullatanin da aka gani kusa da cocinsa.

Wa’azin ya yadu a sakar sama. Daga nan aka fara rubuce-rubuce da kiraye-kirayen a dau matakin shari’a a kan Faston. Faston sai ya kai wata ziyara a jihar Ekiti. Jami’an tsaron DSS suka samu labarin otal din da yake da zama, suka nufi wajen don kama shi.

Da Gwamnan jihar, Fayose, ya samu labarin, sai ya yi maza da motarsa da jami’ansa ya je ya bai wa Faston kariya. Ya hana SSS kama shi. Ya fita tare da Faston ya kai shi gidan gwamnatin jihar. Gwamnan ya ci gaba da ba shi kariya har lokacin da ya bar jihar.

Da Fasto Sulaiman ya koma jiharsu, Gwamnan jiharsa shi ne ya ci gaba da ba shi kariya. Ya rika shiga tsakani a matsayin dan sasantawa da Faston da kuma hukumar tsaron SSS. A lokacin an zargi cewa, an rika daukar nauyin wasu rubuce-rubuce na kira ga gwamnati ta sasanta da Fasto Sulaiman. Kungiyar CAN ta kasa ta fitar da sanarwar manema labarai a kan hakan. Wata kungiyar matasan kudancin Kaduna sun fitar da wata sanarwa, wadda aka buga a jaridu har da jaridar Daily Trust cewa, in aka kuskura aka kama Fasto din, za su fara fasa bututun mai da suka ratsa ta gonakinsu, wadanda ke kai danyen mai zuwa matatar mai ta Kaduna.

Daga baya, wani Gwamna shi ne ya shiga tsakani. Aka kira Fasto Sulaiman har ofis na SSS, aka yi masa tambayoyi, kuma aka sallame shi. A ranar, ko kwana bai yi ba. Wannan shi ne mutumin da har yanzu bidiyonsa yana yanar gizo, kuma kai tsaye yake kira da “a kashe..” Da Turanci ya yi maganar, kuma kai tsaye ya yi ta, amma Gwamna ya hana a kama shi. Wani Gwamna kuma ya shiga tsakani.

Misali na biyu, shi ne a kan rikicin kudancin Kaduna, wanda ya ki ci, ya ki canyewa. An samu hatsaniya, inda Fulani ke fadin barnar da aka yi masu, yayin da kabilun yankin suna fadin nasu. Ana ta zaman gano bakin zaren. An yi zaman sulhu ya fi sau shurin masaki.

Gwamnan ya kai ziyara, inda mutanen yankin suka fusata, suka yi masa rajamu. Gwamnan ya ruga Abuja, inda ya gana da Shugaban kasa. Yana dawowa, aka kara tura jami’an tsaro yankin, aka kuma kuma sanya dokar ta-baci a wasu garuruwan.

A nan duk mai bin lamarin, zai iya fahimta baro-baro cewa, bayan faruwar jifar da Gwamnan ya sha a yankin, sai ya je ya yi ma Shugaban kasa bayani da neman cewa, zai yi amfani da wata damar, wadda ta kunshi jami’an tsaro na kasa. Kuma ya samo damar.

Misali na uku shi ne, jami’an kiyaye hadurran hanya, wadanda jami’ai ne na kasa, amma aka ce korafi sun yi yawa a kanta. Don haka gwamnatin ta yi taron tsaron jiha, ta ce, sun yanke shawarar wannan Hukumar ta bar manyan hanyoyin wasu yankuna a jihar na Kaduna.

Gwamnatin jiha ba karamin karfi gare ta ba, wanda har tana iya sa ido ga aikin wata Hukumar wani bangaren tsaro na hanya, kuma ta hana ta aiki a wani bangaren, kuma Hukumar suka yi sanarwa cewa, duk zargin da aka yi masu karya ne, amma za su yi biyayya ga umurnin na jiha.

Akwai wani hoton bidiyo da shafin Sahara Reporters suka sanya na wani Gwamna yana ka-ce-na-ce da wasu dalibai masu zanga-zanga a daya daga jihohin Yarbawa. Suna zagin sa, yana mai da masu magana. Gwamnan da kansa ya hana jami’an tsaro su taba kowa. Ya daga murya ya ce, “ni ne babban jami’in tsaron jihar, kuma ina ba su kariya, amma duk wanda ya ce min kule, sai na ce masa cas! In kun fadi zan fadi, kuma abin da kuke nema ba a yi.”

Lokacin da tsohon Shugaban kasa Obasanjo yake neman Majalisar Tarayya ta ba shi damar ya kafa dokar ta-baci a jihar Filato, ya fada cewa, dokar ta-baci ne kawai za ta bai wa Shugaban kasa cikakkiyar dama na aiwatar da tsaro a jihar a zamanin mulkin dimokradiyya. Ya ce, in ba haka ba, kowane irin tsari ya yi, Gwamnan na iya dakilewa.

Haka Jonathan ya fada lokacin da ya sanya dokar ta-baci a wasu yankunan wasu jihohi a lokacinsa. Ya ce, in ba dokar ta-baci babban mai tsaro shi ne Gwamna. In aka sanya ta, to an cire masa wannan hurumi, sai abin da gwamnatin Tarayya ta yi.

Gwamna ba karamin karfin ke gare shi ba ta fannin tsaro a mulkin dimokradiyya. Daraktan SSS na Kano, wanda ya mutu kwanan nan, ya taba shaida wa wani babban mutum na kasa wata magana ina zaune. Ya ce yana aiki a wata jiha, sai Gwamnan da wasu suka kawo masa ziyara. Sai yake ce masu da yarensu, “duk abin da za ku yi, ku yi. Za mu ba ku kariya daga Hukumar tsaro da gwamnatin Tarayyya. Ni ne babban jami’in tsaro a nan, kuma da izini na kuke.” Shi Daraktan yana jin yaren, amma bai nuna ba. Ya ce, wannan abin da ya sani, ya sanya shi ma ya yi aikinsa. Inda ya sanya masu ido, duk wani shiri da suka yi, sai ya lalata shi. Da Gwamnan ya dago shi, sai da ya matsa har wajen Shugaban kasa don a ta da shi.

Gwamnatin Kaduna karkashin jagorancin Elrufa’i suna da tambayoyin da za su ba da amsar su masu yawan gaske a kan kisan kiyashin ’yan uwa na Harka Islamiyya a jihar tun watan Disamban 2015. Me ya faru awowin da aka yi carko-carko a Gyallesu da Husainiyya? Me ya faru da Elrufa’i ya zo Zariya ana tsakiyar tirka-tirkan? Me ya sa bayan rikicin, soja suka kai ma gwamnatin Kaduna wasu daga cikin gawawwakin? Me ya sa har yanzu soja ba su yi tsokaci a kan rahoton Kwamitin binciken ba, duk kuwa da cewa rahoton ya ba su wani bangaren laifi? Me ya sa kotu na yanke hukuncin shari’ar Shaikh Zakzaky a Abuja ranar Juma’a, Litinin kuma gwamnatin Kaduna ta fitar da farar takarda a kan ’yan uwa na Harka Islamiyya, ta haramta su, ta kuma kira su da ’yan ta’adda, duk kuwa da ba a taba kama su da daukar makami ba?

Maido da Malam Zakzaky (H) Kaduna, wani sabon Babi ne a yanayin da Harka Islamiyya ke ciki, wanda ke bukatar nazari a tsanake a kan yadda za a fuskaci lamarin, kuma a yi karatun ta-natsu daga wasu kura-kuran da kila aka aikata wajen wannan fadi-tashi na neman hakki da neman a yi gaskiya da adalci. A gyara kure, a kuma yi tsari a tsanake!