AlmizanAlmizan logo
Juma'a 8 ga Sha'aban 1435 Bugu na 1132 ISSN 1595-4474


Rahoto

Yadda aka kashe mutane 36 a Dutsen Ngoshe-Sama da awon gaba da mata 11


kashe-kashe
A ranar Asabar 26/4/2014 ne, ’yan bindiga suka kai hari kauyen Ngoshe-Sama da ke garin Gwoza ta jihar Borno...

Lawan Umaru Gufogo shi ne Lawinin kauyen, ya shaida wa Almizan cewa: “Wannan hari wanda shi ne na biyu a cikin watanni uku, sun kashe mutane 36 da jikkata da dama, kuma ’yan bindigar sun yi awon gaba da mata 11.”

Sai da suka wawushe dukiya kafin su kona gidaje. Kauyukan da aka kona sun hada da Hamsa, Kallambham, Kallahade, Kubo da Bugatha. ’Yan bindigar har kaji ma ba su bari ba.

“Wani abin mamaki shi ne, wadannan gidajen suna makwabtaka da wasu gidajen da ke kasar Jamhuriyar Kamaru, amma maharan ba su kona ko da gida daya ba,” in ji Lawanin.

Ya ce, “a baya babu taimakon da jama’ar kauyen ke samu daga gwamnati, shi ne ya jagoranci gyaran hanyar zuwa garin, inda suka tsaga hanya cikin dutse har tafiyar kilomita 24 zuwa kauyukan, har ta kai yanzu mota na iya hawa da kayayakin more rayuwa. Sabanin bangaren kasar Jamhuriyar Kamaru, inda tuni gwamnatinsu ta yi masu makarantu, rijiyar burtsatse, dakin shan magani, da uwa-uba hanya.”


Sanarwa

Sanarwa
Nan filin duk wani sanarwa ne daga duk bangarorin Harka Islamiyyah

  GAYYATA ZUWA MAKON IMAM KHOMEINI
  Imam KhomeiniDandamalin Dalibai da Malamai na Harka Islamiyyah (Academic Forum) na sanar da dukkan ’yan uwa cewa za a yi Makon Imam Khomeini na bana, wanda za a fara daga ranar:
  Juma'a 30 ga Mayu 2014 zuwa Laraba 3 ga Yuni 2014

  Masu Jawabi: Akwai Malamai da masana daban-daban da za su gabatar da lakca, ciki har da Jagoranmu, Sayyid Ibrahim Zakzaky (H)

  Wannan gayyatar na kowa da kowa ne. Allah ya ba da ikon halarta
  Za mu buga jaddawalin nan gaba kadan in sha Allah.


  Labarai cikin hotuna

  Hotunan YAUMUL MAB'AS na bana

  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asMalam Zakzaky yana jawabi
  • Yaumul Mab'asMalam Zakzaky yana jawabi
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron