AlmizanAlmizan logo
Juma'a 8 ga Sha'aban 1435 Bugu na 1132 ISSN 1595-4474


Rahoto

Batun gurfanar da Janar 10 Na Soja

*Bisa zargin taimaka wa Boko Haram

*Hedikwatar Tsaro ta karyata

Daga Mahadi Muhammad


 Sojoji
A ’yan kwanakin nan ma, rundunar sojojin kasar nan da Ma’aikatar tsaro ta Tarayya sun bayyana cewa akwai alamun da ke nuni da cewa wasu manyan da kananan hafsoshin sojojin kasar nan na da hannu wajen fallasa asirin tsaro ga ’yan ta’adda, kuma har an samu kame wasu daga ciki, an gabatar da su gaban kotun soji a wasu barikoki da ke Arewacin kasar nan...

Cikin wadanda suka shiga hannu, kuma aka gabatar da su gaban kotun sojojin, akwai wasu manyan jami’an soji 15, wadanda suka hada da Janarori 10, kuma duk an same su da laifin fallasa asirin da ya shafi tsaro da kuma sayar da makamai ga Boko Haram.

Wata majiya ta sojojin ta tsegunta cewa wasu daga cikin wadanda aka gurfarnar din a barikokin su, ba su cire tsammani ba, domin ba za a iya yin komai ba har sai hukuncin karshe da babbar hedikwatarsu da ke Abuja za ta yanke.

“Akwai jami’an soji da dama da aka kama, wadanda ake zargi da hana ruwa gudu game da yakin da ake yi da ’yan ta’adda. Baya ga kananan sojojin da aka kama bisa zargin hana ruwa gudu ga wannan aiki da muke yi, akwai kuma Janarori 10, da kuma wasu manyan Hafsan. Yanzu haka an gurfanar da su gaban kotun soji, an kama wasu da laifi, wasu kuma har yanzu ana tuhumar su. Da zarar kotunan sun yanke hukunci, za a aika da shawarwarin da suka bayar zuwa hedikwatar tsaro, ko ta soja da ke Abuja domin daukan mataki na gaba,” in ji majiyar.

Haka kuma wata majiyar ta shaida wa Wakilinmu cewa, an kama wasu manyan jami’an sojin da laifin rashin biyayya da kuma taimaka wa Boko-Haram. “An gurfanar da wasu Janarori gaban kotun sojoji bisa laifin fallasa muhimman bayanai ga ’yan wannan kungiya. An same su da laifin fallasa dabarun soji ga ’yan Boko-Haram, wanda kuma wannan ne musabbabin da ya sa ’yan Boko-Haram suka yi wa wasu sojoji kwanton bauna, suka kashe da dama daga cikin su,” in ji Majiyar.

Majiyar tamu ba ta bayyana mana sunayen wadannan sojoji ba, amma ta ce, akwai wani yanki a kasar nan, wanda ke da hannu dumu-dumu a cikin wannan aiki na cin amanar kasa. “An same su da laifin hada baki da wasu miyagun ’yan siyasa domin hargitsa kasar nan, kawai don biyan bukatun son ran su. Ana nan ana garambawul a rundunar sojojin, za a yi gaba da Janarori da dama. Za a gurfanar da wasu a gaban kotu, wasu kuma za a tilasta masu yin ritaya,” in ji majiyar tamu.

Haka kuma majiyar ta ci gaba da shaida mana cewa abin takaici, ’yan Boko Haram suna sane da duk wani motsi da sojojin mu suka yi. Ta ce, “wasu da dama daga cikin abokan aikin mu suna tsegunta wa ’yan Boko Haram duk wani motsi da sojojinmu ke yi a Arewa maso Gabas. To amma ma’aikatar tsaro ta gano wannan barnar, kuma ta dauki matakan da suka dace wajen canza wasu daga cikin manyan ofisoshin da ke yankin Arewa maso Gabas.”

Manema labarai sun yi kokarin jin ta bakin Kakakin rundunar sojin, Manjo Janar Chris Olukolade, abin ya ci tura, amma wani Janar a hedikwatar sojin ya bayyana cewa ana nan ana ci gaba da shari’a da dama a kotunan sojin, “ana gurfanar da duk wanda aka zarga. Wannan zai sa abin da wahala mutum ya gasgata wannan labarin, ko ya karyata. Amma dai na san da zarar an yanke hukunci a wadannan kotuna, za a sanar da manema labarai yadda ta kaya.”

*Hedikwatar Tsaro Ta karyata labari

Ga dukkan alamu, wannan labari bai yi wa hedikwatar tsaro ta kasar nan dadi ba, inda ta fito ta karyata wannan batu, ta Kakakinta, Manjo Janar Chris Olukolade. Tana mai musanta cewa babu wasu Janarori da suke fuskantar wata shari’a a halin yanzu.

Hedikwatar tsaro ta ce tana karyata wannan labari da babbar murya, “cewa an gurfanar da wasu manyan jami’an soji, ciki har da Janarori 10 bisa zargin hannu a taimaka wa ’yan ta’adda. Wannan labari da wasu kafafen yada labarai da wasu cibiyoyin labarai na sakar sama suke yadawa, babu danshin gaskiya a ciki, kuma abin takaici ne, wanda aka yi domin a ba sunan runduna da sojojin kasar nan.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, ai batun a ce an gurfanar da Janarori a gaban kotun soji ba karamin abu ba ne, wanda kuma ba ya boyuwa. “Muna tabbatar wa jama’a cewa in dai har akwai wata shari’a da ake yi wa wasu jami’an soji, to za a sanar da jama’a. Bilhasali ma ai an saba cewa ba a boye duk wata shari’a ake yi wa wani soja, kamar yadda aka sani cewa ana sanar da duk irin wadannan abubuwa da aka yi a baya.”

Daga nan sai ta jawo hankalin masu yada irin wadannan labarai da ta kira marasa tushe balle makama, su guji yin haka, musamman a wannnan lokaci da kasar ke fuskantar matsaloli na tsaro. “Abin kunya ne ga soja a ce an yanke wa Janar daya hukunci a irin wannan laifi, kamar yadda yake a labarin, ballantana ma a ce har Janarori goma. Rundunar sojin Nijeriya kwararru ne, kuma wadanda suka san abin da suke yi, ba za a taba samunsu da irin wannan kazafi ba,” in ji Hedikwatar tsaron.

Saboda haka sai ta jawo hankalin al’umma da cewa su yi watsi da wancan labari.


Sanarwa

Sanarwa
Nan filin duk wani sanarwa ne daga duk bangarorin Harka Islamiyyah

  GAYYATA ZUWA MAKON IMAM KHOMEINI
  Imam KhomeiniDandamalin Dalibai da Malamai na Harka Islamiyyah (Academic Forum) na sanar da dukkan ’yan uwa cewa za a yi Makon Imam Khomeini na bana, wanda za a fara daga ranar:
  Juma'a 30 ga Mayu 2014 zuwa Laraba 3 ga Yuni 2014

  Masu Jawabi: Akwai Malamai da masana daban-daban da za su gabatar da lakca, ciki har da Jagoranmu, Sayyid Ibrahim Zakzaky (H)

  Wannan gayyatar na kowa da kowa ne. Allah ya ba da ikon halarta
  Za mu buga jaddawalin nan gaba kadan in sha Allah.


  Labarai cikin hotuna

  Hotunan YAUMUL MAB'AS na bana

  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asMalam Zakzaky yana jawabi
  • Yaumul Mab'asMalam Zakzaky yana jawabi
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron