Almizan: Jarida don karuwar Musulmi

AlmizanAlmizan logo
Juma'a 1 ga Sha'aban 1435, Bugu na 1131, ISSN 1595-4474


Rahoto

SSANU ta raba filaye 104 a Jami’ar Ahmadu Bello Zariya

Daga Sabo Ahmad


ABU Zaria
Kungiyar manyan ma’aikatan Jami’o’i ta Nijeriya reshen Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya ta raba filaye guda dari da hudu ga ’ya’yan Kungiyar don su samu damar mallakar muhallin kansu, ko da kuwa bayan sun gama aiki a Jami’ar ne...

Daga cikin mutum dari da hudu da suka samu wannan fili, wanda yake a wata unguwa mai suna Tukurwa, kusa da kauyen Biye da ke makwabtaka da Jami’ar, kowannensu ya samu fili mai fadin kafa hamsin da kuma tsawon kafa dari a kan kudi Naira dubu dari hudu da hamsin.

A jawabin da Shugaban Jami’ar, Farfesa Abdullahi Mustafa ya gabatar, wanda Mataimakinsa a bangaren gudanar da harkokin mulki ya wakilta, Farfesa Na’iya Sada, ya tabbatar da kokarin da Jami’ar take yi wajen ganin ta taimaka wa dukkan ma’aikatanta, don su samu ingantacciyar rayuwa, ko da kuwa bayan sun bar aiki da Jami’ar ne.

Saboda haka, sai Shugaban ya shawarci wadanda suka samu nasarar samun wannan fili da su tabbatar sun yi kyakkyawan amfanin da ya kamata su yi da shi. Sannan sai ya yaba da kokarin da shugabannin wannan kungiya suka yi na ganin cewa, wannan mafarki nasu ya kai ga tabbata.

A jawabin da ya yi wa Wakilinmu a ofishinsa, Shugaban Kungiyar manyan ma’aikatan, Kwamared Iliyasu Abdul Bello, wanda Shugabar mata ta Kungiyar ta wakilta, Halima Abubakar, ya bayyana jin dadinsa bisa wannan nasara da suka samu ta raba wadannan filaye ga ’ya’yan Kungiyar a karkashin wani shiri na musamman na samar da filaye ga ’yan Kungiyar manyan ma’aikatan Jami’o’i na Nijeriya.

Ya ci gaba da cewa, da yardar Allah, wannan shiri zai ci gaba da gudana a wannan Jami’a har sai kowane babban ma’aikaci ya kai ga mallakar nasa filin. Saboda haka ya yi kira ga wadanda ba su samu damar mallaka ba a wannan lokacin da su yi hakuri zuwa wani lokaci, su ma za su kai ga mallaka.


Sanarwa

Sanarwa
Nan filin duk wani sanarwa ne daga duk bangarorin Harka Islamiyyah

  GAYYATA ZUWA MAKON IMAM KHOMEINI
  Imam KhomeiniDandamalin Dalibai da Malamai na Harka Islamiyyah (Academic Forum) na sanar da dukkan ’yan uwa cewa za a yi Makon Imam Khomeini na bana, wanda za a fara daga ranar:
  Juma'a 30 ga Mayu 2014 zuwa Laraba 3 ga Yuni 2014

  Masu Jawabi: Akwai Malamai da masana daban-daban da za su gabatar da lakca, ciki har da Jagoranmu, Sayyid Ibrahim Zakzaky (H)

  Wannan gayyatar na kowa da kowa ne. Allah ya ba da ikon halarta
  Za mu buga jaddawalin nan gaba kadan in sha Allah.


  Labarai cikin hotuna

  Hotunan YAUMUL MAB'AS na bana

  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asMalam Zakzaky yana jawabi
  • Yaumul Mab'asMalam Zakzaky yana jawabi
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron