Almizan: Jarida don karuwar Musulmi

AlmizanAlmizan logo
Juma'a 1 ga Sha'aban 1435, Bugu na 1131, ISSN 1595-4474


Rahoto

Rikicin kungiyar direbobin tanka reshen jihar Kaduna

Kwamared Nuhu Muhammad ya samu nasara a shari’ar sa da Gambo Tuge

Daga Aliyu Saleh


 PTD
Ranar Litinin ta makon jiya, 19 ga Mayu 2014 ne aka kawo karshen shari’ar da aka kwashe watanni ana gudanarwa a babbar kotun sauraren kararrakin masana’antu da ke Abuja, tsakanin Tsofaffin shugabannin kungiyar Direbobin tanka, PTD ta jihar Kaduna, Kwamared Nuhu Muhammad Marafan Nasarawa, Kaduna da Gambo Ibrahim Tuge, inda kotun ta yanke hukunci, wanda kuma Kwamared Nuhu Muhammad ya samu nasara...

Ita dai wannan kara da Kwamared Nuhun Muhammad ya shigar, yana tare ne da wasu mutum 15, inda suke karar uwar kungiyar ta su, wato NUPENG da kuma Gambo Ibrahim Tuge, tare kuma da wasu mutum 15, inda suke kara bisa katin zama dan kungiyar da su Gambo suka karbe masu ba bisa ka’ida ba, sannan kuma a ba su daman tsayawa zabe, wanda su Gambon suka haramta masu.

Haka kuma su Kwamared Nuhu sun nemi kotun ta sa a tantance su kamar sauran ’yan kungiya a shirye-shiryen zaben kungiyar da ke tafe nan gaba a Kaduna, sannan kuma a sauke Gambo Tuge bisa zargin yana yin haramtaccen shugabanci, wanda wa’adinsa ya kare a watan Junairun 2013, amma bai sauka ba.

To amma da yake mayar da jawabi, Lauyan su Gambo Tuge, Barista A.A Habib ya musanta wadannan zarge-zarge da su Nuhu suka yi. Sannan kuma suka kawo shaidu, wadanda suka hada da tsarin mulkin kungiyar, wanda suka yi nuni da cewa, duk wanda ya shugabanci kungiyar sau biyu, to ba zai sake iya tsayawa takara ba, don haka suka nemi kotu ta haramta wa Kwamared Nuhu yin takara a zabe mai zuwa.

Da take yanke hukunci, Alkaliyar wannan kotu, Mai shari’a N. M. Osoye ta bayyana cewa ta amince da takardun da masu kara suka gabatar a gabanta, inda ta nuna cewa tun farko dakatarwar da aka yi wa Kwamared, ba a yi ta bisa ka’ida ba, bisa laifin cewa ba a kafa wani kwamiti da ya bincike su kan zargin da aka yi masu ba. Don haka sai ta umurci kungiyar ta mayar wa da su Kwamared Nuhu katunansu na zama ’yan kungiya ba tare da bata lokaci ba. Sannan kuma a tantance su kamar yadda ake tantance kowane dan kungiya.

Game da batun da su Gambo Tuge suka kawo na cewa Kwamared Nuhu ya yi shugabancin kungiyar har sau biyu, don haka a hana shi sake takara kuwa, Alkaliyar cewa ta yi, Kwamared Nuhu ya kammala mulki ne a 2009, kuma an yi gyaran tsarin mulkin ne a 2013, don haka Kwamared Nuhu Muhammad yana da ikon sake tsayawa takarar shugabancin kungiyar direbobin tanka reshen Jihar Kaduna, tare da magoya bayansa.

Da take tsokaci game da rikicn da ya dabaibaye kungiyar kuwa, Mai shari’ar ta jawo hankalinsu da su tabbatar da cewa sun zauna lafiya da juna domin kasancewar su ’ya’yan kungiya daya.

Da yake zanta wa da Wakilinmu jim kadan bayan bayyana samakon wannan shari’a, Kwamared Nuhu Muhummad cewa ya yi, “a gaskiya ina cike da farin ciki, kuma ina mai godiya ga Allah Tabaraka wata’ala. Domin tun farko da ma zalunci ne ya sa aka rike mani katin shaidata na zama dan kungiya, wanda kuma na bi hanyoyi domin a sulhunta, tun daga shugabannin yanki, har na kasa, amma abin ya ci tura, saboda wani tunani da wasu ke da shi.”

Shi kuwa daya daga cikin wadanda aka yi kara, kuma daya daga cikin wadanda za su tsaya takara a zaben mai zuwa, Kwamared Abdullahi Haruna 6-3 cewa ya yi ai ita takara, ko mutum nawa ne za su iya fitowa, kuma mai rabo ne zai ci “don haka ba na fargabar ko ma wanene zai fito, ya fito,” in ji shi.

Shi ma Gambo Ibrahim Tuge, tsohon shugaba, daya daga cikin wadanda aka yi kara, kuma daya daga cikin wadanda ke sha’awar tsayawa takara, ya bayyana cewa ba ya shayin yin takara da kowane mahaluki, “dalilina, na san Allah ne ke ba da mulki,” in ji shi.


Sanarwa

Sanarwa
Nan filin duk wani sanarwa ne daga duk bangarorin Harka Islamiyyah

  GAYYATA ZUWA MAKON IMAM KHOMEINI
  Imam KhomeiniDandamalin Dalibai da Malamai na Harka Islamiyyah (Academic Forum) na sanar da dukkan ’yan uwa cewa za a yi Makon Imam Khomeini na bana, wanda za a fara daga ranar:
  Juma'a 30 ga Mayu 2014 zuwa Laraba 3 ga Yuni 2014

  Masu Jawabi: Akwai Malamai da masana daban-daban da za su gabatar da lakca, ciki har da Jagoranmu, Sayyid Ibrahim Zakzaky (H)

  Wannan gayyatar na kowa da kowa ne. Allah ya ba da ikon halarta
  Za mu buga jaddawalin nan gaba kadan in sha Allah.


  Labarai cikin hotuna

  Hotunan YAUMUL MAB'AS na bana

  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asMalam Zakzaky yana jawabi
  • Yaumul Mab'asMalam Zakzaky yana jawabi
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron