Almizan: Jarida don karuwar Musulmi

AlmizanAlmizan logo
Juma'a 1 ga Sha'aban 1435, Bugu na 1131, ISSN 1595-4474


Rahoto

Tabarbarewar Tsaro a kasar nan:

Ba a ba jami’an tsaro abin da ya kamata a ba su

- Sanata Abu Ibrahim


 Kashekashe
Sanata Abu Ibrahim, shi ne Sanata mai wakiltar Katsina ta Kudu a Majalisar dattawa, shi ne kuma Mataimakin Shugaban mai tsawatarwa na marasa rinjaye na Majlisar, kuma shi ne mataimakin Shugaban Kwamitin sadarwa. A cikin wannan tattaunawar da ya yi da Manema labarai a Kaduna, Sanata Abu Ibrahim ya nuna takaicinsa game da tabarbarewar tsaro a kasar nan, inda ya yi zargin cewa shi a ganinsa, ba a ba jami’an tsaro kudaden da ya kamata a ba su don gudanar da ayyukansu. Haka kuma akwai batutuwa da dama da suka shafi harkar tsaro. Wakilinmu, Abdullahi Usman ya rubuto mana cikakkiyar hirar. A sha karatu lafiya...

TAMBAYA: A halin da ake ciki, sha’anin tsaro ya fi jan hankalin kowa a kasar nan, da ma masoya kasar nan. Ku a Majalisar dattawa, ko kun gamsu da matakan da gwamnatin Tarayya ke dauka wajen samar da tsaro a kasar nan? Ko kuna ganin akwai wasu abubuwa da ya kamata a ce an yi, amma ba a yi ba?

SANATA ABU: Alhamdu lillahi. A kwanakin baya, manyan sojoji da manyan masu kula da tsaro a kasa, kamar IG na ’yan sanda da Darakta na SSS, da shugabannin sojojin Ruwa, da na sama, da na kasa, duk sun zo, mu shugabanni na Majalisar dattawa, mun zauna da su, domin kila akwai abubuwan da ba za su so fadi a gaban jama’a ba. Mun ji maganganunsu, mun ji matsalolin su. An kuma koma majalisar sun fadi matsalolion su. A yanzu, babbar matsalar da ta damu Nijeriya ita ce ta Boko-Haram, da kuma maganar wadannan ’yan mata da aka sace, dukkan su sun shafi Boko-Haram.

A fahimtata, su kan su jami’an tsaron nan suna da nasu matsalolin, kudaden da ake ba su na yadda za a biya albashi da alawus din su na soja, sai ka ga sun dade ba a ba su ba. In kuma ba a ba su ba, ba yadda za a yi su ba wadanda ke can kasa. Saboda haka akwai wannan matsalar ta ba a ba su kudin. Na biyu, akwai rashin kayan aiki, wadanda sau da yawa duniya ta ci gaba, yadda akwai na’urorin da ba ma sai an shiga dajin ba, za a iya ganin ko mutum nawa ne ke cikin dajin nan. To, su sojojinmu ba su da irin wadannan abubuwan.

Na uku, sojan yanzu ba irin sojan da ake da su ba ne a da. Na da yana shiga soja ne don yana son aikin soja, da yawa yanzu suna shiga ne don ba su da aikin yi. Saboda haka halayensu daban ne. Wancan wanda ya shiga soja don kashin kansa a can baya, yana iya zuwa ya yi yaki, yana iya zuwa ya yi ko ma menene, wadannan kuwa da suka shiga don neman aiki, to sadaukarwarsu, ko jajircewarsu ba zai kai na wadancan ba. Saboda haka zai yi ta samun dan karamin laifi, ko ba a ba shi alawus ba, da dai sauransu, su yi ta kawo koke-koke. Wadannan su ne matsaloli. Muna nan muna dubawa ta yadda za a yi abubuwa yadda ya kamata.

Yanzu a jihar Borno, akwai mutanen da muke kira Civilian JTF, ’yan sa-kai ne, kuma ’yan cikin garin Maiduguri ne, suke fitiwa da daddare suke kare kan su. Sai muka ce to, me ya sa sojoji ba za su dauke su aiki ba? A dauke su a ba su horo, a dauki kamar mutum dubu biyar, da Yobe da Borno da Adamawa, a ba su horo irin na soja ka ga abin da za su yi maka, ka gani in ba su shiga dajin Sambisa ba. Saboda haka muna nan muna duba wadannan mu gani yadda za a yi.

Sannan kuma akwai zuwan ’yan agaji daga kasashen waje; kasashen waje sun shigo kan wannan abin. Ka ga su ma dole sai sun cike wadansu ka’idoji kafin su yarda su tsaya su yi wadansu abubuwa. To, shi ma wannan ana nan ana dubawa a ga yadda za a yi kan wadannan abubuwa. Wannan abu da ya faru (sace ’yan matan Chibok), yanzu zai kawo a tasar ma Boko-Haram ta ko’ina.

TAMBAYA: A kwanakin baya an samu munanan hare-hare a mazabarka. Shin suna da bambanci da na Boko Haram, ko kuwa iri daya n e?

SANATA ABU: A tattaunawar da muka yi da manyan Jami’an tsaro na kwanakin baya, na lura da cewa akwai wasu ’yan Boko-Haram da aka tarwatsa su, suka shisshiga wadansu wurare. Kila ma har ana tsammani akwai mutanen Mali, wadanda suka shigo Katsina da Birnin Gwari da Zamfara da kila wajen su Benuwe, wadannan ana duddubawa a gani. Amma ga dukkan alamu akwai hannun wadannan abubuwa da suke ciki. Yanzu haka sojoji na can suna tsarkake dajin daga ’yan ta’adda, kuma alhamdu lillahi jama’a na cike da farin ciki, domin na je wurin a jiya (kwana daya kafin wannan tattaunawa).

Makasudin wannan ziyara tawa ita ce, na je in kai masu agaji ne na kayan noma, tunda an karkashe masu shanu, ba su da abin da za su yi, sannan ga damina ta zo. Saboda haka sai na samu irin dan injin nan na noma, wanda ake turawa, inji ne, ba shanu ba, wanda in ka sa lita hudu na mai, zai yi maka mako guda kana aiki. Kuma muna da niyyar sayen 200 ko 300, za mu rarraba a Kananan Hukumomin da ke mazabata, amma yanzu na kai wadanda aka samu, guda 25 a Kananan Hukumomi biyu, kuma mutane sun ji dadi matuka. Kuma alhamdu lillahi, ga alama tsoro ya fita daga zukatan mutane.

TAMBAYA: Ya zuwa yanzu an kasa kwato ’yan matan nan da aka sace, har ma yanzu wasu jami’ai daga kasashen waje sun shigo domin wannan abu. Shin za mu iya cewa abin ya gagari jami’an tsaron kasar nan kenan?

SANATA ABU: Gaskiya, duk da mutane na cewa ba a so a kawo siyasa a wannan lokaci, amma a siyasance gwamnatin Nijeriya ta yi sakaci kwarai da gaske. Kowa ya sani, farkon abin nan, an dauka karya ne, ana so a bata sunan Jonathan, kaza, kaza. Mun ga yadda matarsa ta fito tana ihu, tana yin abubuwan da ba su kamata ba. Tun daga lokacin da abin ya faru, awa 24 ya kamata a san abin da ake ciki, a san yadda za a yi, amma sai ba a yi komai ba, an tsaya ana ka-ce-na-ce, gaskiya ko ba gaskiya ba? Wannan abin mamaki ne, wanda ke shugabancin Nijeriya, yana da jami’an tsaro da komai, amma a ce ba zai iya sanin tabbas na irin wannan abin in ya faru ba?

Saboda haka, kamar yadda na ce, duk da yake ba a so a kawo siyasa a cikin wannan abin, ba siyasa ba ce, gaskiya ce. Kila a ce don ba na cikin PDP ne nake fadin haka, amma gaskiya, gaskiya ce, ko da ina cikin PDP, wallahi zan fadi gaskiya. Saboda ba zai yiwu mu yi shiru ba, zaman mu ne lafiya, sunan mu ne ke baci a duniya. Kawai sai wani ya zo ya ce ba gaskiya ba ne, ai akwai jami’an tsaro, su ne za su iya fada, gaskiya ne ko ba gaskiya ba.

Sai dai kamar yadda na gaya maku, sojojinmu suna da karancin abubuwa. Yaran nan an sace su, ba za ka tashi da soja ya shiga cikin daji ka ce za ka fitar da su ba, ai sai su kashe yaran. Za a iya bi ta na’urorin da za su nuna ina suke, sannan a san yadda za a bi da su, kila ma a sami magana da su don kada su halaka yaran nan.

Saboda haka wannan matsala ce wacce ba mu saba da ita ba ta same mu, kuma ba mu da na’urorin zamani da za su taimake mu mu gano inda suke. Amma ’yan kasashen waje sun zo da irin wadannan abubuwa, yanzu muna iya sani, kila ma yanzu an sani.

TAMBAYA: To a matsayinka na Sanata, ko ba ka ganin wadannan sojojin na kasashen waje idan suka kubutar da wadannan yara, darajar sojojinmu na Nijeriya za ta zube?

SANATA ABU: To, shi dai abu idan ya taso, abu na farko da ake nema ita ce mafita, mafitar nan kuwa ko ta halin kaka dole a neme ta. Kuma dole mu yarda cewa Nijeriya har yanzu kasa ce mai tasowa, abin da sojan Amerika zai yi, ko na Ingila, ko kafarsa ba za mu iya kamawa ba; ya kamata mu fahimci wannan. Wannan zai kara mana kwarin gwiwa, mu ba sojojinmu abin da ya kamata mu ba su, wannan zai nuna mana rashin karfinmu. Ya kamata mu yu kaza a wuri kaza, ya kamata mu yi kaza a wuri kaza.

TAMBAYA: Wadannan abubuwa da ba a ba sojojinmu, shin babu ne, ko kuwa dai ba a ba su ne?

SANATA ABU: To, ka san ita gwamnati akwai inda take ganin ya kamata ta fi mayar da hankalinta, kuma sai ga shi ni ba na cikin gwamnati, amma ina cikin masu bayar da abin da gwamnati ke kashewa. A ganina muna kashe kudade wajen biyan albashin jami’an tsaro da alawus din su, amma ba mu kashe kudi kan ayyukansu na yau da kullum. Misali, ina cikin kwamiti na ’yan sanda, in ka ga abin da ake ba ’yan sanda, DPO, abin da zai kashe ya sha mai a wata guda, bai wuce Naira dubu hudu ko dubu biyar ba, wanda shi ne ke zagayawa ya ga me ake ciki. Ka ba shi kudin mai na kwana daya, sauran cikin aljihunsa zai dauko ya yi? Hatta motocin ma, wasu sun lalace, babu tayoyi, da dai sauransu. Amma ka dauki albashi ka ba shi, iyaka ya yi ta zama ofis. In ba da misali, in ka ce masa ga shi can wajen Machika ko Sabuwa ko Layin Galadima ana kashe-kashe, ba zai iya zuwa ba. To, a wadannan ne nake ganin mun yi karanci, ba a ba su kudin da ya kamata mu ba su. Za ka ga an ce an ba jami’an tsaro Naira biliyan dari takwas da wani abu, duk kudin albashi ne. Saboda haka a yanzu din nan, yadda nake ji daga abokan aiki na, suna cewa ya kamata a kasafin kudi mai zuwa, dole mu kara ma sojojin nan kudade, kafin mu zauna lafiya.

TAMBAYA: Ku ’yan adawa, ya kuka kalli zuwan wadannan sojoji daga kasashen waje, an yi shawarar kawo su da ku ne, ko kuwa Shugaban kasa ne ya yi gaban kansa kawai ya kira su?

SANATA ABU: A’a, ba sojoji aka kawo ba, su kasashen waje za su aiko jami’ansu, wadanda za su taimaka mana da na’urorin da za su taimaka mana, amma babu soja da zai shiga dajin Sambisa a yi yaki da shi. Wannan ne sai an yi shawara da mu. Amma don za ka kawo kwararru da kayan aiki, wannan na gwamnati ne. Kuma wadannan yara, duk abin da za a yi a dawo da su ga iyeyensu, daidai ne.

TAMABAYA: Batun musaya da Shugaban Boko-Haram ya ce za a yi, sannan ya sako wadannan yara. Shin kana ganin ya dace?

SANATA ABU: Ita gwamnati ta san abin da take ciki, ita ke da jami’an tsaro, ita ke da masu leken asirin kasa, ita ke da sojoji, ita ta san me za ta iya yi. Shin ta san inda yaran nan suke? In ta san inda suke, tana iya amincewa don saboda rayuwa su, amma in ba ta sani ba, to ba za ta iya amsawa ba, don ta san maganar banza ce. Saboda haka ina ganin wannan abu ne wanda nake ganin ya kamata a yi taka-tsantsan. Idan gwamnati za ta yi wannan abu, dole ta lura da wasu abubuwa. Na farko, shin ’yan matan nan na nan? Na biyu, ina suke? Na uku, shin Shekau din nan shi ne, ko wani ne daban? Na hudu, shin mai maganar nan da gaske yake yi, ko karya ce? Tunda ka ga hatta ita kanta Alka’ida ta barranta da irin wannan abu da Boko Haram suke yi na kona makarantu, kai hari a kasuwanni, sace mutane da sauransu.

TAMBAYA: Ka jima kana wannan kujera ta Sanata. Shin ko za ka zayyana mana wasu abubuwa da za mu iya cewa ka yi domin inganta rayuwar wadanda suke zaben ka?

SANATA ABU: To, da farko dai zan iya cewa alhamdu lillahi. A ganina an yi hobbasa, a cikin shekara ukun nan, akwai hanyoyi guda biyar ko shida da na samo ana yi daga gwamnatin Tarayya. Akwai Mahuta zuwa Tunburkai, akwai daga Funtuwa zuwa Tafoki, akwai Dayi zuwa Gwarangozai, akwai daga Dabai ta zagayo Sabuwar Kasa, da dai sauran su. Haka kuma akwai dam din Kafur, wanda na iske ana yi, amma mu muka kammala shi, akwai Musawa Dam, akwai Takushe Dam a Faskari. A makarantu, gaskiya ba zan iya zana maku su ba, amma zan ba ku takardun da za su nuna ma wadannan abubuwa, na tabbata babu Karamar hukumar da ba mu yi makaranta ba a cikin Kananan hukumomin 11, wadannan kuwa sun hada da azuzuwan koyarwa, ko na kwamfuta, to babu inda ba mu yi ba, wasu ma an yi masu biyu, wasu kuma uku. Haka kuma mun sayi tiransifoma guda ashirin da uku, kowace Karamar Hukumar an kai. Mun bi kowace mazaba (ward) mun giggina rijiyoyin burtsatse. Kowace Karamar hukuma mun yi rijiyoyin ban-ruwa, kuma an hada kowace rijiya da injin ban-ruwa.

A watanni biyu da suka wuce mun je mun ba yara matasa kayan aiki, wasu mun ba su injin faci, wasu keken dinki, wasu an ba su abin yin taliya da sauransu. Wadannan ayyuka sun hada da nawa na kashin kaina, da kuma wadanda na yi tsaye gwamnatin Tarayya ta zo ta yi, duk zan ba ku wadannan abubuwa a rubuce don ku gani. Haka kuma kamar yadda na gaya maku, jiya na je na bayar da Babura na noma, wadanda ba sai an yi amfani da shanu ba. Wadannan za ka sa masu man fetur ne, ka rike kana turawa kana huda. Muna nan muna kokarin a kawo kimanin 200, amma yanzu mun debo wadanda suka iso, mun kai ma jama’a, sojoji na nan suna zagayawa, mutane sun kokkoma gidajen su.


Sanarwa

Sanarwa
Nan filin duk wani sanarwa ne daga duk bangarorin Harka Islamiyyah

  GAYYATA ZUWA MAKON IMAM KHOMEINI
  Imam KhomeiniDandamalin Dalibai da Malamai na Harka Islamiyyah (Academic Forum) na sanar da dukkan ’yan uwa cewa za a yi Makon Imam Khomeini na bana, wanda za a fara daga ranar:
  Juma'a 30 ga Mayu 2014 zuwa Laraba 3 ga Yuni 2014

  Masu Jawabi: Akwai Malamai da masana daban-daban da za su gabatar da lakca, ciki har da Jagoranmu, Sayyid Ibrahim Zakzaky (H)

  Wannan gayyatar na kowa da kowa ne. Allah ya ba da ikon halarta
  Za mu buga jaddawalin nan gaba kadan in sha Allah.


  Labarai cikin hotuna

  Hotunan YAUMUL MAB'AS na bana

  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asMalam Zakzaky yana jawabi
  • Yaumul Mab'asMalam Zakzaky yana jawabi
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron