11 Almizan: A TAKAICE KAI TSAYE
AlmizanAlmizan logo
Jum'a 17 ga Rabi'ussani, 1440 Bugu na 1380 ISSN 1595-4474

A takaice kai tsaye

GYARA KAYANKA

Aliyu Saleh


 Dahiru Bauchi

WANNAN KARYA CE TSAGWARONTA

Na ga wani labari a cikin gidan talabijin na NTA, wai ’yan’uwa Musulmi Almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky suna goyon bayan sake zabar Buhari. Wannan karya ce tsagwaronta. Dama kun kashe mu ne don mu zabe ku? Ina shelanta wa duniya, wannan karya ce, ba za mu zabe ku ba.

Daga Muhammad Sani Birnin Gwari

INA KIRA GA AL’UMMAR NIJERIYA

Ina kira ga al'ummar Nijeriya cewa wannan da’awar Sayyid Zakzaky ita ce mafita gare su. Duk inda wannan al’ummar ta je Wallahi ba za ta samu mafita ba, dole sai ta dawo wajen Sayyid Zakzaky a nan mafitar al'ummar take.

Daga Ali Yakubu Shinge Potiskum Jihar Yobe 0703 289 1462

INA KUKE MASOYA SAYYADATUNA FATIMA (AS)?

Ina kuke masoya Sayyadatuna Fatima (AS)? Kun ji abin da Allah ya fadi a Hadisil Kudsi ta harshen Manzonsa (S)? Ya ce, “na rantse da izzata da buwayata da daukakar matsayina, na yi alkawari ba zan azabtar da masoyinta ba daga wuta ba. Allah ka tabbatar da mu tare da kaunar hasken idon Manzonka (SAWA).”

Daga Sayyid Zulyadaini Potiskum 0703 969 9487

MU GUJI MASU SON HADDARA RIKICI

ALMIZAN ku ba ni dama in bayyana wa ’yan kasa ta Nijeriya mugun nufin da wasu ke yi na neman haddasa fita a tsakanin al’umma. Na farko dai haddasa rikicin akidanci a tsakanin Shi’a da Sunna. Na biyu kuma haddasa rikicin kabilanci da bangaranci a tsakanin Kudu da Arewa. Hakan ya haifar da karuwar cin hanci da rashawa, ga rashin ingantattun harkar tsaro da lafiya da ilimi da tattalin arziki. A kullum sai kara rugujewa suke yi. Ga rashin bin dokokin kasa, da raina kotuna, ga ayyukan ta’addanci sai karuwa suke. Wannan wane irin salon canji ne muka samu? Ko dai jiki magayin ne ke aiki a kan talakawa?

Daga Sadam Aliyu Giade Arrafiidy

’YAN UWA MU GYARA MU’AMALARMU

Shawara ga ’yan’uwa, ya kamata mu kyautata alaka da mu’amalarmu a cikin mutane. Mu yi koyi da Annabi (S) wajen kyautata wa jama’ar da muke tare da ita. Imamu Ali yana cewa; “Ku yi mu’amala da mutane, mu’amala mai kyau, wacce in kun mutu za su yi kuka, idan kuma kuna raye za su yi begen ku”. Shin kana dabbaka wannan magana ta Imam? Shin kana mu’amalar da in ka mutu abokanka za su yi maka kuka? Ko in kana raye ba ka tare da su za su yabe ka? Ka sani kyakkyawar mu’amala takan sa mutum ya yi wa ra’ayinka kyakkyawar fahimta.

Daga Hameed Musa Sara

ZABE YA ZO, WA ZA KA ZABA?

Duk wanda za ka zaba ka yi kokari zabinka ya yi daidai da umurnin Allah. Idan ba ka fahimta ba, ka duba Alkur’ani mai tsarki Suratul Ma’ida Aya ta 44-47, idan ka duba za ka gane. Babu mafita sai kiran Sayyid Zakzaky (H). Ya Allah ka bar mu da shi, mu rayu a haka, mu bar duniya a kan haka, mu tashi a kan haka gobe kiyama. Ilahiy ya Rabbi.

Daga Ummi da Khadija Shehu Kwangi Wangara

ALLAH KA BA MU SABATI DA JURIYA

’Yan’uwa mu kara kaimi wajen ganin an saki ABBANMU (H). Mu daure kar mu gaji, haka hanyar take. Free Zakzaky dole!

Daga Zainab Muhammad Suwidi Katsina.

KOWA DA FIKIRARSA

Kowa da fikirarsa, kai wacce ka zaba? Shaikh Bala Lau ya ce; “A zabi Buhari.” Shaikh Sani Jingir ya ce; “Ni ma Buhari zan zaba.” Shaikh Sambo Rigacukum kuma ya ce; “Atiku zan zaba.” Shaikh Zakzaky ya ce; “A koma wa tsarin Allah, wato Kur’ani.”

Daga Aminu S. Miko Kano, dalibi a Jami'ar Bayero 0812 532 1515

TAMBAYATA ZUWA GA BUHARI

Wai Buhari za ka ci gaba da kama barayi ne, ko kuma za ka ci gaba da daga masu hannu ne suna mulkar mu?

Daga Is’haka A. A. Razak Saminaka Jihar Kaduna 0806 699 2787

KU NEMA WA KANKU MAFITA

Ya ku ’yan Nijeriya! Ku nema wa kanku mafita, amma ba dai Buhari ba, wanda ya kasa tsaya wa al’ummar Arewa game da garkuwa da ake da su, musamman a Zamfara, jihar da aka haifi Ministan Tsaro da Jihar Katsina da aka haifi Shugaban kasa. Wai shi zai tsare al’ummar Nijeriya gaba daya, kai ka san wannan tatsuniya ce.

Daga Abdurrahman Lawal U. Maje Faskari Katsina 0806 244 8231

INA TUNA MAGANAR DAKTA AHMAD GUMI

Har kullum ina la’akari da maganar dan gidan Gumi, Shaikh Ahmad Gumi a kan Buhari, wanda yake cewa mafi yawan masoyansa daga jahilai, sai kidahumai.

Daga Magaji Sa’idu Jahun 0813 761 3124

’YAN SIYASA SUN RAINA HANKALIN ’YAN NIJERIYA

Ka sa ido ka ga idan ana kamfen na siyasa, shi wannan da ake wa kamfen din ba za ka ga dansa ba, ko kanin matarsa, ko kaninsa da suke Uwa daya ko Uba daya ba, sai dai ka ga ’ya’yan talakawa da za a ba su kudi su yi shaye-shaye, ko su yi sare-sare, kai wasu ma fosta za a ba su, wanda yana cin zabe, to ya gama da su ke nan, sai in yana bukatar ta-zarce, ko sabuwar takara. Ko me ya sa haka talakawa? A sa hankali da basira mana.

Daga Dan Umma Birnin Kudu.

KU CANZA TAKEN JARIDAR NAN

ALMIZAN don Allah ku daure ku canza taken jaridar nan, daga jarida don karuwar Musulmi, ya koma jarida don karuwar al’umma. Allah ya fito mana da su Sayyid Zakzaky da gaggawa.

Daga Yahya Tako Maigamji Funtuwa.