11 Almizan: A TAKAICE KAI TSAYE
AlmizanAlmizan logo
Jum'a 15 ga Sha'aban, 1438. Bugu na 1288 ISSN 1595-4474

A takaice kai tsaye

SHAWARATA GA SHUGABAN KASA

Aliyu Saleh


 Dahiru Bauchi

Ina da muhimmiyar shawara ga Shugaban kasa, Malam Muhammadu Buhari. Kwanakin baya ka je London neman magani saboda rashin lafiya, kuma ka samu murmurewa ka dawo gida, iyalai da masoya sai murna. Ka gode wa Allah da sakin Zakzaky, wanda duk jikinsa miki ne na harbin bindiga da baraguzan bom da Sojoji suka jefa masa, domin ya je ya nemi magani ko Allah ya tausaya maka a yinin kiyama. Ka san cewa muna da hakkin nasiha gare ka tunda na zabe ka. Ka yi watsi da ra’ayi, ka rungumi kasar duka, ka zama Shugaban kowa da kowa.

Daga Saleh Ibrahim Mi-Yetti Allah Secretary 0803 833 9921

ALLAH KA TABBATAR DA MU

ALMIZAN don Allah ku isar min da gaisuwa ta ga Wakilin ’yan uwa na Shall, Malam Hamza Idris, wanda aka saki kwanan nan bayan ya share watanni a tsare ba tare da an same shi da laifin komai ba. Da fatan Allah ya kara ba shi lafiya da kariya ta musamman daga sharrin makiya, kuma Allah ya tabbatar da mu a karkashin jagorancin Sayyid Zakzaky. Ilahy.

Daga Yahaya Abu Sumayya Yalwan Dass 0802 382 2770.

IN KA KI SHARAR MASALLACI KA YI TA KASUWA

Allah Sarki! Wasu sun ce mu saki Shehu mu kama Ubangijin Shehu, sai su kuma suka kama wasu ’yan siyasa. Su wadanda suka kama tsani ne zuwa fadawa cikin fushin Allah, domin suna ketare iyakokin Allah, su kuwa Shehunnai tsani ne zuwa ga Allah. Don haka mu kara rike Shehunnai, kuma mu kira ’yan uwanmu su zo mu rike Shehu, tsani zuwa ga Allah.

Daga Abu Nusaib Dan Shanono

MA’AUNIN GANE GASKIYA DA KARYA

Hankali shi ne ma’aunin gane gaskiya da karya. Ya al’umma mu sa hankali wajen dukkanin ayyukan addinin Musulunci na fahimtarka ko ba na fahimtarka ba.

Daga Sharafuddeen Muhammad Hadejia

JAN HANKALI ZUWA GA AL’UMMA

Abin takaici jami’an gwamnati sun zama wasu gungun mutane ne marasa imani. Don haka ba sa son duk wani da zai wayar da kan al’umma. Shi ne dalilin ya sa suka yi kisan kiyashi a Zariya. Malam Zakzaky jarumi ne da ya tsaya don tabbatar da adalci. #Free Zakzaky.

Daga Abubakar Madugu Hayin Ojo

WACE SUNNA CE WANNAN?

Amurka ta kai wa Musulmi hari a Syria, wasu Musulmi suna murna da sunan Sunna. In kun ce Shi’a ba Musumi ba ne, Yahudawa fa? Annabawa ma haka aka yi masu.

Daga Musa Kutama 0803 951 6952

KARSHEN ALEWA KASA

ALMIZAN ni dai na fada na maimaita karshen alewa kasa. Zalunci ba ya dorewa. Na yi imani da haka. Mu je zuwa. Allah ya kara wa Malam Ibraheem Zakzaky lafiya.

Daga Sani Sharif Lokoja 0806 493 8666

MENE NE NA BOYE-BOYE?

’Yan uwana Sistoci da Burazu zan yi wani karambani na dan yi jan kunne ga wadansu ’yan uwanmu. Akwai wadanda za ka gan su ’yan Harka ne, amma kuma suna wani boye-boye kamar marasa gaskiya. Mun san cewa a kan tafarkin daidai muke, ba da kowa muke koyi ba sai Manzon Allah da Iyalan Gidansa Tsarkaka. Mene ne abin boye-boye?

Daga Mujahid Aliyu ’Yantsire Gama, (B) Karamar Hukumar Nasarawa a jihar Kano

DUK KASAR CE TA SANKARE

Tabbas annobar ciwon SANKARAU ta addabi wani sashi na kasar nan, amma idan muka fadada nazari sai mu ga ai duk kasar ce ta SANKARE sakamakon taba Mujaddadin wannan karni. RIGAKAFI da MAFITA kawai shi ne amsa da’awarsa. LABBAIKA YA EL-ZAKZAKY! #FREE ZAKZAKY DOLE!

Daga Mustafa Liman Lere 0703 456 6251

WATAN RAJAB BA NA BARCI BA NE

Akwai Hadisin da Imam Ali Al-Hadi (AS) ya ce; “Duniya kasuwa ce, wasu kan ci riba, wasu kuma su yi hasara”. To ’yan uwa ku ci ribar rayuwarku! Ka kasance mai neman lahirarka kafin ka tad da Ubangijinka. Don haka mu yi amfani da wannan watan na Rajab da ya shigo don mu ribaci abin da za mu samu. Ba watan barci ba ne, ba na tsofaffi ba ne, amma na masu wayo ne.

Daga Zainab Dauda Hadejia.

A SAKI SHEIKH ZAKZAKY!

Muna kara jaddada kira ga gwamnatin kasar nan ta sakar mana Jagoranmu, Shaikh Ibraheem Zakzaky (H). Kwanaki 488 ke nan gwamnati na tsare da shi, duk da cewa Babbar Kotun Tarayya ta ba da umurnin sakin shi da mai dakinsa Malama Zeenatudeen tare da biyan su diyya na tsare su da aka yi. #Freedom4Zakzaky!

Daga Amina Hasan Yola.

’YAN UWA MU DAGE DA ADDU’A

’Yan uwa mu dage da addu’a ita ce za ta ceto mana Maulanmu da sauran ’yan uwa baki daya.

Daga A’isha A. Tankari Katsina.

DUK WANI CI GABA NA CIKIN ALKUR’ANI

A kowane lokaci addinin Musulunci sabo ne ba tsoho ba. Abin da ya kamata al’umma su gane shi ne, duk wata wayewa da ci gaba da neman sauki yana cikin Alkur’ani. Duk wani abu da muka rasa ta dalilin kin bin maganar Allah ne, in muka koma ga Allah wallahi duk abin da muke so sai mun samu.

Daga Mudansir Usman Malumfashi 0812 539 8142, 0706 717 4966

KU RIKE NAKU, MU RIKE NAMU

ALMIZAN a gaya wa Assalafi su rike Mu’awiyya da Banu Umayya, mu kuma Shi’a mu rike Imam Ali da Ahlul Baiti (AS).

Daga Isa M. Yola

KUN YI BAKUWA

ALMIZAN kun yi bakuwa. Don Allah ku fada wa ’yan uwa su dage da addu’a a watan nan na Rajab. Allah ya gaggauta kwato mana Jagoranmu Sayyid Ibrheem Zakzaky. Ilahy!

Daga Safiyya Bashir Kano

MU ZAMA MASU GASKIYA DA RIKON AMANA

Ya zama wajibi a kanmu masu gwagwarmayar shimfida adalci a doron kasa, mu zama daban da sauran al’ummar da muke son kawo gyara a cikinta. Wajibi ne mu zama masu kamun kai, riko da addini, gaskiya da rikon amana da taimakon al’umma. In mun kasance haka, muna kan tafarkin da Sayyid Zakzaky ya bar mu ke nan, in kuwa mun kauce, mu daina rudar kanmu da cewa mu Almajiransa ne.

Daga Husaini Muhammad da Khadija Maraba Abuja

GASKIYA ’YAN SHI’A AN CUTAR DA KU

ALMIZAN ina maku fatan alheri. Allah ya kara daukaka amin. Ni ’yar Darika ce amma ina da Kawa ’yar Shi’a. Gaskiya an cutar da ku, kuma an zalunce ku, kuma duk Musulmi na kwarai da Kirista na kwarai ba zai ji dadin abin da aka yi maku na kisan da aka yi maku a Zariya ba. Allah ya yi maku sakayya.

Daga A’isha Ibrahim Funtuwa

DA WANE DALILI AKE TSARE DA SHAIKH ZAKZAKY?

Sun ce wai Shaikh Ibraheem Yaqoub El-Zakzaky ya karya dokar kasa. To, don Allah a gabatar da shi a gaban Kuliya domin a hukunta shi bisa ga laifinsa, in kotu ta same shi da laifi. Amma ga makiyan Shaikh Ibraheem Yaqoub El-Zakzaky su ci gaba da kiyayya, amma ire-iren mu son sa muke da zuciya daya. Muna amfani da wannan dama, muna kira ga Shuganinnmu na kasa da na Arewa da su yi adalci a kowane mataki.

Daga Pastor Yohanna Y D Buru of Peace Revival And Reconciliation Foundation Of Nigeria, Kaduna Nigeria. 0806 871 8181

LALLAI SAYYIDA ZAHRA (AS) TA DABAN CE

Wata rana Manzo (S) ya ce mata; “Na aura maki wanda ya fi kowa ilimi, wanda shi ne farkon musulunta, wanda kuma ya fi kowa hakuri”. Allah ya sa mu dace.

Daga Fatima Mahmud M/fashi.

WAJIBI NE MU KULA DA IYALAN SHAHIDAI

Shuhada kun cika alkawari, kun ba da rayuwarku da lokacinku don ba da kariya ga Jagoranmu lokacin harin da aka kai masa. Wallahi kun rabauta. Mu da muka saura ba a kashe mu ba, wane abu ya kamata mu yi? Wajibi ne mu kula da iyalansu. Matasan Sharifai na kira da babbar murya a kan a saki Sayyid Zakzaky.

Daga Sayyada Fatima Abubakar Halkar Kawo Giginyu Kano

HABA ’YAN UWA MU DAGE MU BIYA HAKKIN SHUHADA

Don Allah mu dage, duk wanda bai biya hakkin Shuhada ba ya biya, mu sani fa hakki ne da a ranar lahira za a tambaye mu a kansa.

Daga Fatima Salisu Maradun jihar Zamfara.

MUHIMMANCIN SADA ZUMUNCI

’Yan uwana, mu sadar da zumunci ga makusanta, domin sada zumunci yana daga cikin mafifitan ibadu, kuma yana kara tsawon rayuwa da dukiya. Hadisai sun yi nuni cewa, mai yanke zumunci abin wajabta wa azabar lahira ne. Kin yin sa (zumunci) yana sa talauci da saukar balai da karancin rayuwa. Allah ya ba mu ikon sada zumunci.

Daga Bara’atu Tahir Katsina.

BAMBANCI FAHIMTA TSAKANIN SUNNI DA SHI’A

Ahlus Sunna sun ce Halifofi bayan Manzon Allah guda hudu ne. Na farko Khalifa Abubakar, sai Umar, sai Usman, sa Ali (RA). Su kuma Shi’a sun ce Khalifofi a bayan Annabi 12 ne. Na farkonsu Ali da na karshensu Mahdi. Sai kuma ga Hadisi a cikin littafin Buhari ya ce Manzon Allah (S) ya ce Khalifofi a bayansa 12 ne, dukkansu Kuraishawa ne, na farkonsu Ali na karshensu Mahdi. To hujja Shi’a ke nan, to Sunna ina taku hujjar?

Daga Nura Gwadabawa 0813 369 9801

WACE CE ZAHRA?

An haife ta ranar Juma’a 20 ga Jimada Sani shekaru takwas bayan aiko Annabi. An haife ta a Makkatul Mukarrama. Mahaifinta shi ne Annabi Muhammad bin Abdullahi. Mahaifiyarta ita ce Khadija Bintu Kulaid. Mijinta shi ne Aliyu Bin Abi Dalib. Ta yi aure ranar 1 ga Zulhajji shekara biyu bayan hijira. Ita ce Shugabar Matan Duniya. ’Ya’yanta Hasan da Husaini sune Shugabannin Samarin Aljanna. Sayyida Fatima Azzahra Ma’asuma.

Daga Abida Hassan Kuta Jihar Neja

MU CI GABA DA ADDU’A

Kotu ta ba da umurnin a saki Malam Zakzaky, amma gwamnati ta ki bin umurnin. Mun san sun bijire ne saboda ba kotu ce ta ba su umarnin auka wa su Malam ba, iyayen gidansu ne suka sa su. Mu dai mu ci gaba da addu’a, lokaci muke jira.

Daga Muhammad Sabon Garin Fafa 0813 210 4151

ILIMI SHI NE GISHIRIN RAYUWA

Shawarata ga ’yan uwa ita ce mu rike ilimi, saboda shi ne gishirin rayuwa. Mu nemi ilimi, kuma mu yi aiki da shi. Kun san cewa ilimi ba aiki da shi, to barin shi ya fi. Mune ya kamata a ga addini a gare mu. Da an gan mu an ga ilimi, an ga masu aiki da ilimi. Mu ya kamata a gani a ga tarbiyya tattare da mu, ba wai a gani ga wasu ba.

Daga Khadijatul Kubra Bintu Bukhari Abdullahi Katsina

MUN SAN FALALOLIN WATAN RAJAB KUWA?

Watan Rajab wata ne na Allah, yana daya daga cikin jerin watanni masu albarka. Shi ne watan da ake son mutum ya zamto mai kamewa daga munanan dabi’u, kuma ya yawaita azumomi tun daga Rajab, Sha’aban har Ramadam. Shi ne wata ne da ake son mutum ya yawaita addu’o’i da zikirori da karatun Alkur’ani mai girma da kyautata wa mutane. Allah ya taimaka mana.

Daga Fatima Aliyu Al-mizan.

INA BAYAN KI SISTER KHADIJA SUFIYAN ABUJA

Ra’ayin Sista Khadija Sufiyan Abuja da na gani ya tuna min wata rana da Malam Yakubu Yahya Katsina yake cewa, Amawa suna cewa ’ya’yanmu na birge su. Sai ya ce, to kwalelanku ba za mu bayar ba. Kin ga ko bai kamata a ce Sista, abin kunya a ji ta auri Ba’ame. Wannan ai ci baya ne, domin ba ya taimaka maki a kan al’amarn da ya shafi Harka da kika tashi a cikinta ba. Ya kamata mu duba, kar fa mu rusa ginin da Shaikh Zakzaky ya dade yana yi nana. Domin ni dai gaskiya ina ganin auren Ba’ame rusa gininsa ne. Allah ya bar mu a kan tafarkin Jagoranmu.

Daga Hawwa G. A. S. Katsina

ABIN DA BAN MAMAKI

Gaskiya da mamaki a ce an samu Hadisai da yawa daga Nana A’isha (RA) da ta rayu da Annabi a Madina, amma na Sayyida Fatima (SA) ya boyu da ta rayu da shi tun daga Makka har aka yi hijira zuwa Madina. Ko dai akwai wani abu da ake son boyewa ne? Amma dai da mamaki.

Daga Ja’afar Dan K/gana Birnin-kudu 0817 308 5160

FREE ZAKZAKY DOLE!

Duk da gallazawar da azzalumai suke yi mana, Wallahi ko dar ba na yi, ina da yakinin Allah zai cika haskensa ko munafukai da azzalumai ba sa so.

Daga Umar Takai.

MU KASANCE MASU YI WA JUNA UZURI

Don Allah ’yan uwa mu kasance masu yi wa juna uzuri, yayin da ka ga dan uwa ko ’yar uwa ta yi abin da bai dace ba, ko wani ‘group’ a cikin garinku ka ga suna abin da bai dace ba, to ka kira su guri guda, ka gaya masu cewa, abin da suke bai dace ba domin a samu gyara.

Daga Z. U. Abukur