AlmizanAlmizan logo
Jum'a 23 ga Ramadan, 1441 Bugu na 1445 ISSN 1595-4474

HANTSI

KARFIN IKON ALLAH, KWAYAR KORONABAYIRUS 11

DANJUMA KATSINA


 Dahiru Bauchi

A tsawon sama da shekaru dubu da dari hudu da suka gabata, kabarin Manzon Rahama (saw) da ke Madina ba a taba fashin zuwa kusa da shi don ziyara ko neman tubarraki ba, sai a wannan shekarar. Hukumomin kasar Saudiyya sun kulle wajen da kuma rauda da makabartar Baki’a. Sun yi hakan a abin da suka kira daukar mataki na tsare al’umma daga masifar cutar annobar koronabayirus.

A karon farko tsawon shekaru sama da dubu biyu an dau tsawon kwanaki dimbin jama’a ba a dawafi a Dakin Ka’abah. Mahukumta a kasar Saudiyya sun killace dakin mai tsarki, sun nesanta al’umma daga yin dawafi a kusa-kusa da ginin mai daraja da albarka. Balle har mai dawafi ya iya shafa ko sumbaci dutsen Hajral Aswad, ko addu’a a kasan Indararo, kamar yadda hadisi ya aminta a yi.

Bakin ciki da damuwa ya ratsa al’umma lokacin da suka ji wata murya ta ladanai a kasar Makka da Madina masu tsarki tana cewa, ku yi sallah a cikin gidajenku. Lamari mafi muni da ya faru a tarihin Musulunci.

Wannan bakin ciki na hana sallah ya watsu a duk kasashen duniya, wanda ya sa a wasu kasashe suka hana sallah a masallatan Juma’a. Wasu kuma suka haramta sallah a masallatai na cikin gari da sallolin rana rana. Dukkanin wannan na faruwa ne a kan wata cuta da aka sanya ma suna Covid-19 ko kuma Koronabayirus.

A kasar Vatikan fadar Fafaroma, a karon farko filin bauta, wanda mabiya dubbai kan cika kowace ranekun bauta, yanzu filin fayau an ba da umurnin cewa kowa ya yi aikin bautar sa daga gidansa ta hanyar sako da kuma bi na intanet.

Duk wani wurin kasuwanci da safarar hannun jari da ke birnin New York na kasar Amurka da kuma Ingila da Paris ya zama fanko, mutane sun kauracewa wajen, an koma komai a bisa intanet ake saurare kuma ake bi.

Dandalin nishadi da holewa da ke birnin Las Vegas da Hollywood sun zama kwarangwal, gidajen rawa da caca an rufe su. Masu rayuwa da masha’a sun shiga halin zaman dole a mazaunansu.

Tattalin arzikin duniya yana ta tangal-tangal. Babu mai wani tabbas a kan ya gobe za ta kasance a alkiblar gobe? Mutane a wasu kasashen suna ta sayen abinci a adadi mai yawa domin adanawa don ba wanda zai iya cewa me gobe zai faru?

Shugabannin kasashe suna ta jawabai na daukar matakin kare kai da kuma kira ga al’ummarsu su zama cikin shirin ko-ta-kwana, cutar har ta kashe wasu manyan jami’an wasu kasashe, ta kuma sanya killace wasu.

A karon farko a tarihi, ko’ina a duniya ta zama fursuna. A karon farkon a tarihin Bil’adama da wata kwayar cuta ta girgiza duniya, kuma ta nufi manyan masu tafiyar da kasa da kasa da kuma nahiya-nahiya da ma duniya baki daya. An ruwaito cewa an gwada sama da shugabanni ashirin na manyan kasashen duniya domin tabbatar da ko sun kamu ko a’a, cikin su har da Shugaban kasar Amurka da Jamus da Najeriya da Ingila, wanda aka tabbatar da ya kamu, wanda har ma ya kebe kansa yanzu haka yana amsar magani. Daga cikin manayan duniyar yamma da suka kamu har da babban Yarima mai jiran gadon sarautar Ingila, wanda ake kira da Dan Sarki Charles.

A kasar Iran manyan Likitoci da jami’an gwamnati sun kamu, wasu sun riga mu gidan gaskiya, wasu kuma sun killace kansu suna amsar magani. Duk duniya baki daya ta killace kanta, ba shiga, ba fita. Kowa ya zauna a inda yake; abin da ya fara faruwa a karon farko a tarihin Bani Adam.

Yanayin yana shirin jefa tattalin arzikin duniya baki daya cikin tsaye cak. Ba abin da ke shigowa, sai dai abin da za a ci da kuma ririta abin da aka tanada aka ajiye don wata bukata ko jiran ko ta kwana a irin wannan yanayin.

YA ABIN YA FARU?

Wani Likita a kasar Chaina, a birnin Wuhan yana nazari akan marasa lafiya da wasu gawawwakin da suka mutu, sai ya lura da wata irin cuta da bai gane kanta ba. Ya kuma fara nazari a kan ta, sai ya gano tana da hatsarin gaske, don haka sai ya yi rubutu a kai.

A rubutunsa sai ya jawo hankali cewa, ga wata musiba fa da ya lura da ita, don haka yana kira ga Hukumomi su dau hannu da daukar mataki kafin al’amarin ya kauce hanya. Maimakon a kula da sakonsa, sai aka kama shi aka gargade shi da kar ya kuskura wannan maganar ta fita, don kuwa za a tuhume shi da laifin yada labarin da zai ta da hankali, kuma hukuncinsa yana da tsanani a kasar ta Chaina. An gargade shi da cewa, idan labarin ya fita zai iya taba huldar kasuwancin kasar Chaina, kuma ga shi kasar tana asakala da kasar Amurka.

Likitan sai ya yi shiru, amma ya rika taskace rubutunsa a ma’ajiyar bayanansa na intanet. Ya kuma ci gaba da lura da yadda cutar ke yaduwa a hankali, a hankali. Bai ankara ba, shi ma sai ya kamu. Lokacin da ya san yanzu yana ciki, kuma ba fita, sai ya fara maganar cewa lallai ko dai kasar ta dau mataki ko kuma wata Annoba da za ta mamaye duniya daga Chaina tana kyankyasa, kuma tana yada ’ya’yanta a duniya lokacin da za a farga wuri ya kure.

Yana wannan rubutun aka rufe shafinsa na intanet, aka cire duk abin da ya rubuta a baya, aka kuma nisanta shi daga samun wata dama ta isar da sako a intanet. Sam aka daina ji daga gare shi. A daidai lokacin sai kasar ta yi niyyar bincike da nazari a kan zargin da ya yi. Ina! Kamar yadda ya rubuta, lokacin da za a farga, lokaci ya kure.

Nan da nan kasar suka fahimci cewa, lallai wannan matsalar gaskiya ce, kuma a daidai lokacin dubbai sun kamu a garin Wuhan, kuma kullum tana karuwa kamar wutar daji. A daidai lokacin kuma, cutar ta ci karfin shi Likitan. Nan da nan aka dauko shi don ba shi kulawa ta musamman da kuma ji daga gare shi. Ina! Bakin alkalami ya riga ya bushe. Daga nan ya bukaci a ba shi damar ya yi sakon bidiyo, inda ya isar da wani bayani mai ban tausayi. Daga baya ya mutu, aka yi masa janaza ta ban girma da kuma sanya shi cikin gwarazan kasar.

Abin farko da kasar Chaina ta yi shi ne shelanta ma duniya cewa, cutar ta bulla kuma gaskiya ce, ba ta kuma da magani. Sannan ta fara bayyana ma duniya alamunta da yadda ake gane ta. Sannan duk birnin na Wuhan baki dayansa ta kulle shi, ba shiga, ba fita. Daga baya kuma ta kulle duk illahirin mutanen garin. Daga nan ta fara daukar matakai ba ji ba gani! Ina! Lamarin ya riga ya fantsama, domin birnin Wuhan a kasar Chaina gari ne wanda ke da baki masu yawa daga ko’ina a duniya. Kafin a je ko’ina, cutar ta yadu kuma tana ci gaba da yaduwa a duniya.

Wasu na cewa cutar ta samo asali ne daga wani yakin makaman sinadari, wanda dama an san kasashen da suka ci gaba sun san saba da irin wannan makida. Shi wannan ra’ayin hasashe ne, babu wani binciken kimiyyya da ya tabbatar da shi. Kuma wani ko wata bai fasa kwai ba cewa ga abin da ya faru, yana da masaniya ko kuma da shi aka shirya. Don haka wannan zai iya zama hasashe har lokacin da wani karin haske ya bayyana.

Masana tarihin da ya shafi jin kai da rayuwar dan’adam kuma suna da nasu bahasin a kan wannan cuta da ta bayyana. Sun ce duk lokacin da dan’adam ya yi wani rashin imani a kan dan’uwansa mutum, kuma babu abin da ya wakana na gyara, ko tuba ko hukunta wadanda suka jagoranci ta’addacin, to Allah kan yi fushi, kuma ya dau mataki. Mafi yawan matakan Annoba ko yake-yake ko kashe-kashe ne.

Masu wannan ra’ayin na cewa ta’addacin da aka yi a kasar Burma ga musulmin Rohinga, da wanda ake ma musulmin Indiya da Kashmir da musulmin kasar Chaina da na kasar Palasdinu da rashin imanin da aka yi a Zariya ta jihar Kaduna a Najeriya ya ishi Allah ya yi fushi, ya mai da duniyar baki daya kowa cikin tsoro, firgici da tashin hankali.

Mece ce kwayar koronabiyirus? Har yanzu takamaiman daga inda aka samo ta ana ta magana da tattaunawa. Akwai ra’ayoyi kusan kala biyar, kuma kowane ra’ayi ana aikin bincike a kansa. Mafi rinjaye shi ne daga wata dabba ce da ake samu a tekun kasar Chaina.

Tashin hankali a kan cutar shi ne, babu maganin riga-kafin ta, ba ta kuma da magani in an kamu. An ce hatta wadanda ke warkewa, ba wai suna warkewa ba ne da maganin da ake ba su. A wani mataki ne ake dauka na a kara ma garkuwar jikin mutuum karfi, shi kuma sai ya yaki cutar. In an yi sa’a sai karfin garkuwar jikin mutum din ya fattake ta, ya kashe ta, ya ci karfinta.

Wannan ya sanya aka ce, cutar ta fi kashe tsaffi da kuma marasa lafiya wadanda garkuwarsu ta yi rauni, don haka da ta shiga sai ta nufi inda take kassara mutum ta kammala da rayuwarsa. Matakan kare kai daga cutar da saukin gaske,wanda likitoci da masana suna ta bayani a kai.

Wani Darasi a kan al’umma shi ne yadda Allah ya gwada karfin ikonsa a duniya a bayyane, ba labari ko jita-jita ba. Ya samar da wata haliitta ’yar karama kamar kwayar zarra, amma ta sanya duniya baki daya cikin halin natsuwa.

Masana suna a cikin dakunan bincike na kimiyya a kasashe daban-daban na duniya, amma sun kasa gano lagon kwayar da ke haddasa cutar. Wani daga cikin su ya sanya hotonsa a shafinsa na intanet, yana shelanta kwanakinsa na saba’in bai ga barci ba, suna ta aiki, amma har yanzu ba su da albishir ga duniya. Abiin da kawai suke cewa shi ne suna iya kokarinsu.

Masanan da suka je sararin samaniya, suka je kasan ruwa, suka shiga karkashin kasa wadanda suke cewa sun ci ci gaban duniya da yaki, yanzu wata kwaya ’yar karama ta mai da karatunsu sabon zubi. Wannan shi ne karfin ikon Allah.

<4>

Siddabarun Kwayar Cutar Koronabairus<4>

Wannan kwayar cuta mai suna Koronabairus, wadda bisa karfin ikon Allah, ya amince da samuwarta da ba ta zamani, kamar yadda wata aya a cikin Alkur’ani mai tsarki ta nuna Shi ne ya yi halittar, kuma ya nuna mata hanya, bisa ganin damar Allah bisa hikimarsa da darussan da yake son koya wa duniya da al’ummarta.

Wata muhawara da ake ta yi a kan ta shi ne musabbabinta da inda ta faro, domin ko menene Ubangiji zai aiwatar, sai bisa wani dalili da kuma wata hanya, wadda ya tsara ta taso daga nan.

Na karanta wani rubutu a jaridar Weekly Trust ta satin da ya gabata, 4 ga watan Afrilu 2020 a wani fili mai suna da Turanci ‘Another Dimension.’ Wata ’yar jarida ce da ta shafe sama da shekaru talatin tana aikin, take rubuta shi mai suna Hajiya A’isha Umar Yusuf.

Rubutun A’isha Umar Yusuf yana daga cikin rubutun da sama da shekaru ashirin ake kafa hujja da shi, saboda saninta da kare dokokin jarida da rubutu a kan duk abin da zai fito daga wajen ta. Kuma mace ce mai son addinin Musulunci da aikata shi. Kusan duk hidimar addini da ayyukan addini tana ciki. Tare da ita aka kafa jaridar Daily Trust. Ita ce ma ta sanya wa jaridar suna Weekly Trust a farkon fitowarta.

A rubutun nata, kamar yadda zan fassaro wani bangare a wannan mukalar tawa, ta ce wani bincike ya nuna gwamnatin Amurka ta lura cewa, kasar Chaina na shirin shiga gabanta a komai a duniya. Tattalin arzikin Chaina yana bunkasa, kasashe masu tasowa suna komawa gare ta. Abokan huldar Chaina a kasashe suna bunkasa, misali a Gabas ta tsakiya Iran tana shirin zama kasa mafi karfi a yankin. Kasar Amurka ta yi yunkurin kawo ma kasar Chaina tarnaki. Ta ta da rikici a yankin Hong Kong da wasu yankuna; duk abin bai yi tasiri ba.

Don haka masana kimiyyar kasar Amurka da ke karkashin jami’an tsaronta suka samar da wannan kwayar cuta ta ‘Covid-19’ a wani lokaci, suka yi amfani da hanyoyinsu zuwa watsa cutar a tsaunukan birnin Wuhan, wanda yake gari ne da ke da matattarar dakunan bincike na kimiyyar kasar Chaina, wanda in cutar ta taso daga can za a zargi kasar da sakaci, kuma cutar za ta yi ma kasar barna da yaduwa cikin dan lokaci kankane.

Kasar Chaina ta gane cewa, an kawo mata farmaki da kwayoyin cuta, amma abin farko da ya kamata ta fara yi shi ne kare al’ummarta da kanta. Don haka ta fara nazarin kwayar, ta kuma fara gwajin wasu magunguna, duk ta lura basa aiki.

Abu na biyu da ta yi shi ne, masana kimiyyarta da ke sashen tsaro suka canza ma kwayar cutar fasali, suka sake inganta ta, suka mai da wa kasar Amurka da kawayenta. Sannan suka dawo fara aiki gadan-gadan kan yadda zasu fuskanci matsalar a kasarsu da jama’arsu.

Cutar na fara shiga kasar Amurka da kawayenta, sai masana kimiyyar Amurka suka dauko maganin da suka tanada don ita, suka fara gwadawa. Nan suka gane cewa, ai ita wannan kwayar cutar da ta dawo masu, ba wadda suka aika ba ce, suka kuma tanadi maganin ta. Wannan an canza mata salo, kuma ba ta jin maganin da suka tanada don ita.

Wannan ya sanya Shugaban kasar Amurka ya rude, har ma a jawabinsa a gaban manema labarai ya rika kiran cutar da sunan kwayar cutar kasar Chaina. Ya fadi wannan har a shafinsa na Twitter, kuma aka yi masa caa, amma ya kafe a kan matsayarsa. A wani taron manema labarai har gardama ya yi da wata ’yar jarida a kan ya kira kwayar da sunan cutar kasar Chaina. Trumph ya ce ya fadi hakan, kuma zai ci gaba da fadin. Masana na ganin saboda Trumph ya san me aka sanar da shi, shi ya sa ya fadi waccar maganar.

Kasar Chaina ta gane an kai mata hari ne da kwayoyin cuta, kuma ta dau matakin mai da farmaki, sannan ta dawo kasar don kare kanta da jama’arta. A birnin Wuhan, wadda aka nufa kuma, wani Likita ya fara gano ta, har ya ankarar, amma aka ki kula da shi, sai da bakin alkalami ya bushe (kamar yadda na kawo a rubutun nan a satin da ya wuce), sai mahukumtar kasar suka kulle Jihar baki daya ta Hubei (inda Wuhan ne birni mafi girma a ciki) mai mutane sama da miliyan hamsin, sannan suka fara daukar sauran matakai a ciki da wajen Wuhan da kasar baki daya.

Daidai lokacin da duniya ke tsuwwa a kan cutar, ita kasar ta yi nisa da daukar mataki. Daga Wuhan zuwa birnin Shanghai kilomita 629 ne, amma ba wanda ya kamu a Shanghai. Daga Wuhan zuwa Bejing kilomiota 1052 ne, amma ba wanda ya kamu a Bejing. Daga Wuhan zuwa kasar Italiya kilomita 8900 ne. Sama da mutane dubu goma suka mutu a kasar Italiya, sama da dubu dari sun kamu. Daga Wuhan zuwa kasar Ingila birnin London kilomita 8880 ne, amma sama da mutane dubu hamsin sun kamu, har da Shugaban kasar da babban dan Sarauniya. Sama da mutane dubu goma suka mutu.

Daga Wuhan zuwa birnin Paris kilomita 8700 ne, amma da yawa sun kamu, da yawa sun mutu. Daga Wuhan zuwa kasar Spain mutum 169,496 sun kamu, da yawa sun mutu, da yawa suna jinya. Daga Wuhan zuwa kasar India kilomita 3575 ne, da yawa sun kamu, da yawa sun mutu. Daga Wuhan zuwa Jamhuriyar Musulunci ta Iran kilomita 6560 ne, mutum 73, 303 sun kamu, mutum 4,585 sun mutu, da yawa kuma suna jinya.

Duk manyan biranen kasar Chaina babu inda aka kamu, yayin da manyan biranen duniya ake ta zaman juyayi da tunanin ina mafita? Ya za a shiga, ya za a fita? Abin akwai alamar tambaya da nazari. Kwayar cutar da ta fara daga birnin Wuhan a kasar Chaina, ta kasa watsuwa zuwa birane makwabtanta irin su Bejing da Shanghai, amma ta gallabi manyan biranen da ke nesa da ita.

Manyan biranen duniya an kulle su, ba shiga, ba fita. Birni daya aka rufe a Chaina, shi ne Wuhan (inda cutar ta samo asali). Shi ma har an fara hada-hada ta wasu awanni kowace rana. Kasuwanni a kasashe an rufe, kasuwanni a kasar Chaina bude suke ga ’yan kasa banda Wuhan.

Manyan masu rike da mukamai na mulki da siyasa a duniya sun kamu, wasu na jinya, wasu sun mutu a wasu kasashe. Misali Firaministan Ingila ya kamu. Likitan Shugaban kasar Amurka ya kamu, Likitan Shugabar kasar Jamus ya kamu. Ga su nan a ratsin kasashe da jinsin mutane. Babu wani babba a kasar Chaina da ya kamu. Farko-farko kafin kasar ta farga, wasu likitocinta suka kamu, wasu suka mutu. Amma tunda ta ankara, ta dau mataki, labarin ya chanza.

Kasuwannin hada-hada na hannun jari sun fadi, na kasar Chaina ne kawai yake tsaye da kafafunsa. Duk manyan kasuwanni da masana’antu sun rufe, na Chaina ne kawai ke ta shirin ko-ta-kwana don in duniya ta koma daidai su ci gaba da ba duniya kayan bukata. Yanzu birnin Shanghai ko Bejing ya fi zaman lafiya da kwanciyar hankali fiye da London, Paris ko New York. Duk duniya ana cikin firgici, su kuma sun natsu, saboda sun san me suka fuskanta, me suka yi?

Mene ne sirrin kasar Chaina? Me ya kawo kuma Yammacin Turai da Amurka suka kidime, kuma suka jawo hanklin duniya su shiga taitayinsu? Amsar ita ce sun san abin da ake ciki! Ana wani yaki ne na sinadarin kwayoyin cuta. An kai farmaki, an mai da martani, babu kuma magani ko rigakafi. Ana zargin kasar Chaina ta gano wani sirrin da ba ta son fada wa duniya na yadda ta dakile cutar a kasarta.

Yanzu duniya baki daya ta karkata ga kasar Chaina don neman mafita daga halin da kasashe ke ciki. Misali Shugaban kasar Amurka da kansa ya canza matsaya daga cewa cutar kasar Chaina ce zuwa wata musiba da yake neman taimakon kasar Chaina.

Rubutu na gaba kan halin da tattalin arzikin duniya zai shiga ne saboda wannan cutar. Kuma zai iya shafar kowa a ko’ina yake a duniya, ko da a kauyen kayau ne kuwa.

SHAN GIYAR BERA

Wani ya rubuto mani, bayan rubutuna na satin da ya wuce ya fito, yana tambaya ta mene ne ma’anar wata Karin Magana mai suna shangiyar bera? Bayan na tura masa amsar, sai na ga ya dace in kawo ta nan don amfanin makaranta. A kai, a kai, in ta kama irin wannan zaurancen magana mai sako, zan rika kawo labarin ta, tunda na lura masana da manazarta Hausa kan bibiyi shafin, sai su rika gyara mana da kuma hasakaka mana.

Shan giyar bera, cewa aka yi wani bera ne abin duniya ya ishe shi. Ga yunwa, ga babu ta yi masa yawa. Ya ji duniyar ma duk ta ishe shi. Sai ya fito yawo, sai ya ga wata giya an ajiye. Sai ya kwankwada, ya yi tatul. Ya fara tangadin maye da sumbatu na bugaggu. Yana tafiya yana tangadi, sai ya iske wata mage ta ci ta koshi tana irin barcin nan na sarauta, wanda takan tankwara kafa, ta dora kanta a kafafun gaba.

Sai beran nan, a cikin maye, ga damuwa, ya zo ya ja mata gashin baki, ya ce, tashi don kazar-kazar ki. Ta tashi cikin mamaki, ta ga bera a gabanta, ya rike kugu yana ta surfa mata ashar. Da ma ya ga ba ta ce kala ba, ya dunguri hancinta da bugun gabanta, ya ce, da ke nake! Duk abin da kike takama da shi, ki yi ga ni nan! Magen nan ta kalli beran nan, zuciyarta na saka mata me za ta yi masa? Sai ta yanke shawarar a yanzu ta rabu da shi, yana cikin maye da damuwa, kuma ita yanzu ma ba ta jin yunwa ko ta taune shi, ba wani gardin da zai mata a baki, balle maganin yunwa.

Beran nan yana tambele da zagen-zagen sa ya koma rami. Suna kallon kallo da mage. Magen ta ci gaba da fakon sa. Sai da ta bari giyar ta sake shi, abubuwa sun canza, duniya na shirin zamar masa sabuwa, zai fara tafiyar kankamba, sai ta wafce shi.