AlmizanAlmizan logo
Jum'a 17 ga Rabi'ussani, 1440 Bugu na 1380 ISSN 1595-4474

HANTSI

Kokarina na gano dukiyar masu rike da mukaman siyasa na jihar Katsina

DANJUMA KATSINA


 Dahiru Bauchi

A ‘Media chat’ na farko da Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya yi da manema labarai, wadda tayi farin jini sosai kuma an kalle ta, daya daga cikin ’yan jaridar ya yi wa Shugaban kasa tambaya a kan bayanin abin da ya mallaka, kamar yadda yake a ‘form’ din ‘Code of conduct bureau’. Shugaban kasa ya ba shi amsar cewa, “Dokar kasa ta amince duk mai bukata yana iya zuwa wajen ‘Code of conduct bureau’ ofis, domin a nuna masa”. Ba wai nasa ba kawai, nama duk wani dan kasa, wanda ke rike da mukami, wanda doka ta ce ya cika wannan ‘form’ din.

Wannan dalili ya sanya a Katsina na fara wani bincike a kan ko duk masu rike da mukaman siyasa sun cika wannan form din? Na rubuta takarda, wadda na rabar da ita duk kowane ofis. Wannan ya sanya da yawa, wadanda ba su cika ba sun cika. Wannan ya sa na samu cikakken goyon bayan cika wannan form a jihar Katsina.

Daga nan a ranar 9 ga Maris, 2016, na rubuta wata wasika zuwa ga ofis din ‘Code of conduct bureau’ da ke Katsina. A wasikata na kawo waccan magana ta Shugaban kasa, na kuma kawo wani bangare na ‘federal information act’. Na roki ina neman a ba ni dama in duba wasu daga cikin ‘form’ na manyan masu rike da mukaman siyasa na jihar Katsina.

Ofis din ‘Code of conduct’ sun ba ni amsa ranar 19 ga Afrilu, 2016, wanda suke cewa, duk ‘forms’na manyan masu rike da mukaman siyasa yana Abuja, babban ofis nasu. Wanda suke da shi, ba su da ikon ba kowa shi, sai da iznin babban ofis nasu a Abuja. Don haka suna shawarta ta in nufi Abuja.

A ranar 22 ga Agusta, 2016, na rubuta wata wasika ga babban ofis din ‘Code of conduct bureau’ dake Abuja, inda na kawo masu bukatata. Na roki cewa, a ba ni wannan dama na ganin ‘forms’ na manyan masu rike da mukaman siyasan Katsina da suka cika. A wasikata na kawo hujjar zancen Shugaban kasa da dokar ‘freedom of information act’. Na kawo wasikun da na rubuta wa masu rike da mukamin siyasa na Katsina da kuma wasika da amsar da na samu daga ofis dinsu na Katsina.

Zuwan farko da kaina na kai wasikar Abuja, na yi amfani da wata dama ta wata hidima da ta kai ni garin. Dana ji ba amsa, na koma na biyu domin jin me ake ciki? Na san yadda Najeriya take, wani lokaci sai da kamun kafa, wannan ya sa na yi wa ‘Judge’ na kotun ‘Code of conduct’ magana .’Justice’ Danladi Umar a kan ya sanya baki a ba ni dama in ga wadannan ‘form’ na manyan ’yan siyasar jiharmu masu rike da mukamai.

Na je ‘Code of conduct bureau’. Shugabanta Nista Sam Saba ya amshe ni da hannu biyu-biyu, cikin sakin fuska da mutumci. Ba wani boye-boye, na fada masa manufata da dalilin da ya sa nake wannan bincike. Mista Sam Saba ya jinjina mani ya kuma gode wa yadda na bi duk matakan da na bi a baya.Na fada masa cewa, matakina na gaba shi ne zuwa kotu don ta tilastawa a ba ni, in har ban gamsu da bayanin da zai mani ba, wanda har ya yi dariya.

Mista Sam Saba ya nuna mani bakin cikin cewa ba zan samu abin da na zo nema ba. Ya ce, wannan bukatar tawa ‘the answer is NO’. Ya fada mani cewa, sun rubuta takarda ga ‘Antoni-janar na kasa a kan ya ba su mafita a kan yadda ake yawan neman ganin ‘form’ na masu rike da mukaman siyasa a gwamnati daga ’yan jarida da lauyoyi. Mista Sam ya ce, amsar da ya samu daga wajen sa ita ce, kada su ba da. Saboda badawar ta saba wa wasu sassa na kundin tsarin mulkin kasa. Kuma tsarin mulki ya ce, duk dokar da ta ci karo da shi, to ita dokar ta fadi kasa,tsarin mulki na sama. Mun tattauna inda ya yi mani bayanin tsaka mai wuyar da suke ciki da shari’u a kotu da suke ta fuskanta.

Na kuma samu amsar wasikata daga ofis din a ranar 5/12/2016, wanda a cikinta ake gode mani, amma aka ce, ba zan samu abin da nake nema ba. Takardar ta ce dokar su bayar da wadannan bayanai ta ce,suna iya bayarwa karkashin sharadi da tsarin da Majalisar kasa ta shata. Wanda har yanzu Majalisar kasa ba ta kawo sharuddan ba.

Bincikena ya tabbatar mani cewa, masu rike da mukaman siyasa na da kariya ta doka a kan ‘forms’ dinsu da suka cika na ‘Code of conduct.’ Ba yadda dan jarida zai iya zuwa neman bayani kuma ya samu. Amsar kawai ita ce, Majalisar kasa ta fitar da sharadin da duk wanda ya cika su za a iya ba shi, ko kuma duk wanda yake da tabbacin kansa, in ya cika ya bai wa manema labarai kwafi. Ko kuma ya rubuta a rubuce, ya bai wa Hukumar cewa “duk wanda ya zo kuna iya ba shi ‘form’ dina ya gani.”

Shin shugaban kasa da ya ce, ana iya zuwa, ya yi ne bisa jahilcin hakan? Tunda yanzu ga gaskiyar yadda lamarin yake, me ya kamata a yi? Don duk mai bukata yana iya gani, kamar yadda ake ikirarin dokar ta tanada.

TSOKACI: Wannan rubutun ya fito da Turanci a wasu jaridun kasar nan. Kuma wasu Lauyoyi har sun fara tsokaci a kan binciken nawa.

Amsar wasikar farko da na samu daga ofishin ‘Code of conduct’ Katsina, sai kuma amsar wasikar da na samu daga ofishin ‘Code of conduct’ Abuja.

Wasikar da na rubuta Abuja.


Sanarwa

Sanarwa
Nan filin duk wani sanarwa ne daga duk bangarorin Harka Islamiyyah

  GAYYATA ZUWA MAKON IMAM KHOMEINI
  Imam KhomeiniDandamalin Dalibai da Malamai na Harka Islamiyyah (Academic Forum) na sanar da dukkan ’yan uwa cewa za a yi Makon Imam Khomeini na bana, wanda za a fara daga ranar:
  Juma'a 30 ga Mayu 2014 zuwa Laraba 3 ga Yuni 2014

  Masu Jawabi: Akwai Malamai da masana daban-daban da za su gabatar da lakca, ciki har da Jagoranmu, Sayyid Ibrahim Zakzaky (H)

  Wannan gayyatar na kowa da kowa ne. Allah ya ba da ikon halarta
  Za mu buga jaddawalin nan gaba kadan in sha Allah.


  Labarai cikin hotuna

  Hotunan YAUMUL MAB'AS na bana

  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asMalam Zakzaky yana jawabi
  • Yaumul Mab'asMalam Zakzaky yana jawabi
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron