AlmizanAlmizan logo
Jum'a 23 ga Ramadan, 1441 Bugu na 1445 ISSN 1595-4474

Labaran Harka Islamiyyah

KORONABAIRUS: Yadda Tattalin Arzikin duniya Ya durkushe

Daga Danjuma Katsina


Imam Aliyu
A karon farko a tarihin kasar Iran, tun bayan juyin Musulunci, ta fito tana neman kawayenta na gaskiya su taimaka mata. Ministan harkokin kasashen waje yana magana a wani bidiyo da ya fitar mai ban tausayi, ya kuma yi hira da wasu manyan kafofin watsa labarai, inda yake cewa, kasar za ta amshi taimako daga wajen kawayenta na gaskiya a kan halin da ta shiga na tattalin arziki sakamakon cutar annobar koronabairus. An ruwaito, kasar a karon farko tana neman bashi daga wajen hukumonin tattalin arziki na duniya. Suna fadin cewa, in har suka samu, za su saka shi ne a cikin tattalin arzikin, wanda yake ta kasa sakamakon halin da kasar ta shiga na takunkumi, sai kuma ga annoba ta ‘covid-19’ ta shafe su sosai. Girgizar tattalin arzikin Iran zai shafi harkoki da yawa na duniya kai tsaye, zai kuma shafi wasu kungiyoyin jihadi da yakin kwatar ’yanci. Misali kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon da kungiyoyin yakin kwatar ’yanci na kasar Falasdinu, da ayyukan wasu kungoyoyi a Turai da suke kare martaba da muradun Musulmin duniya. Kusan duk ayyukan kasar da wasu ayyukan yada ilmi da makarantu a duniya sai an sake masu lale, dole a koma kasafin me ake da shi, me ke shigowa, ya kuma za a sarrafa shi? Wannan sai abin da lissafi ya gwada, amma tabbas za a ga canji a komai. Kasar da ta fi girgiza a sha’anin tattalin arziki daga wannan cuta ita ce, kasar Amurka, wadda ake ganin wannan shi ne zai zama sanadin karewarta, da durkushewarta. Lokacin da cutar na cin kasar Iran, har tana bayyana wa duniya cewa, tana cikin hali na yanayi, kasar Amurka izgili ta rika yi mata. Yanzu kasar Amurka na da wadanda suka kamu da cutar sun fi miliyan daya. Sannan wadanda suka mutu sun fi dubu sittin. Sama da mutane miliyan talatin suka rasa aikin yi. Kasar ta zuba sama da Dala Tiriliyan biyu don tallafawa tattalin arzikin kasar a yaki da cutar, sun shige ana maganar karawa. Man kasar ya yi karyewar da ruwan sha ya fi shi tsada a karon farko a tarihin kasuwar man fetur ta duniya. Wannan hali da kasar Amurka ta shiga sai ya taba duk tattalin arzikin duniya, saboda tattalin arzikin duniya ya ginu a kan kudin Amurka na Dala. Kuma duk manyan cibiyoyin kudi na duniya suna da alaka da manyan kasuwannin hannun jarin kasar Amurka. Wannan tabuwa na tattalin arzikkinta zai shafi shiga harkar wasu kasashe da take yi, wanda sukan yi wa kasa dodo da za su ba ta tallafi. Zai kuma shafi yadda take daukar nauyin wasu kungiyoyin kasa da kasa da kuma yadda suke sarrafa su da tallafin kudin da take badawa. Kamar yadda ta ce, ta janye tallafinta da take bai wa kungiyar lafiya ta duniya. Hatta taimakon da take badawa na rikewa da tabbatuwar wasu kasashe, duk sai ya girgiza. Misali, haramtacciyar kasar Isra’ila. A karon farko kasar Chaina, wadda ke fitar da mafi yawan kaya da na’urorin da duniya ke amfani da su, kasar ba shiga ba fita tsawon watanni. Duk manyan masana’antunsu sun kulle. Wasu kayan da aka sarrafa sun fara zama tsaffi, wasu kuma sun fara lalacewa, kamar yaddda gidan talabijin na kasar ya bayyana. Ya ce, an shiga kulle kasashe ne sakamakon cutar koronabairus, kwatsam babu shiri. Kasar ta yi hasarar dubban biliyoyin Dala don haka dole kasar sai ta yi lalen maganar tattalin arziki don fuskantar gaba. Kasashe da yawa sun dogara da kasar Chaina su rayu. Yanzu komai nasu zai canza daga abin da suke samu. Haka duniya ta dogara da kira da sarrafawar kasar ta Chaina. In ta canza lalenta, sai komai na shiga da fita ya canza farashi da yanayi. Sai mun koma daidai za a gane ina aka dosa. Wata kasa da ta jijjiga da wannan hali da aka shiga, ita ce kasar Saudiyya. Da farko dai dama tattalin arzikin na tangal-tangal sakamakon yadda suke daukar dawainiyar yake-yake a kasashen Yamen, Iraki, Siriya, da kasar Bahrain, da miyagun kudin da take kashewa ga wasu kungiyoyi don tallata akidarta da kuma wai rage tasirin Shi’a a dunya. Tattalin arzikin ya yi masassarar da ta kai ga har a tskaiyar shekarar da ta wuce 2019, hukumomin kasar suka tattara duk attajiransu suka tsare, sai da suka sanya hannu a wata kyautar dole. Kowane attajiri sai da ya ba da sadakar dole ta wani bangaren dukiyarsa. Aka ce wai ana zargin su da cin hanci da rashawa da kuma yi wa kasar zagon kasa a tattalin arziki. Harin da wasu mayaka daga kasar Yamen suka kai wa matatar man kasar na ARAMCO ya kara karya tattalin arzikin kasar. Kasar ta dogara da kasuwar mai da kuma shigar masu ibada, sai hannun jarin da suke da shi a kasashen Yamma. Kasuwar mai ta rushe, hannun jari ya wargaje. Yanzu an tsai da zuwa aikin Umara saboda cutar. Ba a san me zai faru a kan aikin Hajji ba. Kudin shigar kasar ya yi tsananin girgiza. Wanda shi ma zai shafi duniya, musamman kasar ke saka farashin duk wata hidimar shiga a yi ibada a cikin ta. Ba wanda ya san me za su zo da shi. Kasar Najeriya ta fi buguwa a kan wannan yanayi. Kasar ba ta da wani takamaimen tsari na tattalin arziki. Kudin mai da suka dogara da shi, ya fadi kasa warwas. Kayansu na noma ba a fitar da shi don samun kudin shiga. Ba a amfani da damar yawon bude ido. Babban inda aka dogara da shi a kudin shiga daga mai, sai harajin ma’aikata, sai kuma na ’yan kwangila. Wannan ya sanya kullum kasar sai shiga bashi da cin bashi da neman bashi take don ta yi ayyukan raya kasa da ci gaba. Kusan duk manyan ayyukan da ake yi, akwai inda aka ciwo bashi daga kasar waje. Misali, aikin jirgin kasa bashi ne daga kasar Chaina. Aikin hanyoyi bashi ne daga bankin Musulunci. A haka ake tafiya. Duk manyan kamfanoni suna rayuwa ne, tsaitsaye saboda halin fargabar cutar da ake a ciki. Masana tattalin arziki sun tabbatar da cewa za a dade duniya ba ta dawo daidai ba. Da lokacin annobar da bayan karewarta, tattalin arzikin zai rika rawa kuma za a dau lokaci ana tattala shi kafin ya tashi. Farashin komai za ya tashi, za a yi karancin wasu abubuwan. Yadda duniya ta shirya wa fuskantar yanayin da za a shiga, kowa ma ya kamata ya fara karatun ta-natsu na halin da za a fada nan gaba. Watau shi ne masassarar tattalin arziki, wanda kowa sai ya ji a jikinsa. Koronabairus da Koronayunwa, duk kisa suke Daga Sayyid Nuru Daruth-thakalaini Ku daina dankwafar da Mutane da cutar Kuronabairus don su zauna a gida ba tare da tallafa musu ba. Shi ma zaman a hakan wata cutar Kuronabairus ce. Ka sani Allah yana sane da gudummawar da ka bayar na ci gaba da zama a zalunci. Kada ka yi tunanin kai kana da albashi, gwamnati za ta ba ka, yi tunanin sauran jama'ar da suka fi masu albashin yawa da kullum sai sun je sun nema za a ci a gidajensu. Manzon Allah (S) yana cewa: "Azzulmu yabkaa bissukut." Idan ka san ba za ka fadakar da mutane su dawo kan hanyar Allah ba, su tuba su kama Allah, su ki yarda da wannan zaluncin na azzalumai, to ka yi shiru kawai ya fiye maka, don Rakib yana rubuta duk kalamanka don haka ka kiyaye. Sai dai duk da haka, wannan shari'a ba za ta yarda da cewa soyayya ce ta sa a Najeriya ka zauna ba, wallahi kiyayya ce da zalunci kawai. Hatta kananan kasashe suna tallafa wa dukkanin mutane don su samu su zauna a gidan, amma Najeriya ta kasa tallafawa ko da talakan da ba shi da wutar lantarki, babu ruwan wanka da wanki balle na sha. Babu abincin da zai ci na ranar ma balle na gobe, tare da Najeriya tana da tarin dukiyar da za a yi hakan ba tare da wahala ba. Amma kullum tunanin azzaluman Najeriya yaya za a sace kudin kasa ne kawai. Shi ne tunaninsu, ba wai taimakon ’yan kasa ba sam ko sauke nauyi! A yi karya a ce a ciyarwa wai an kashe miliyan 500, tare da kawai ana bayar da shinkafa ne kwano daya ko rabi da taliya leda daya. Wani garin ma Indomi ce kawai kwaya daya tal. Kasar Iraki ta fi Najeriya rashin Arziki, amma a hakan da suka killace mutane a gida, mutum daya ma dalibi ana ba shi kwai kiret biyar, kaza guda biyu, man abinci mai lita daya wajen takwas, da sauran abubuwa. Ku daina dukan taiki ku daki jaki, na tabbata a yau shugabanni su rarraba wa ’yan Najeriya ko da dubu 20 ne, ba sai an matsa kada kowa ya fito ba, ba mai fitowar. Ana maganin sababi ne, shi kuma da kansa sai ya warkar da cutar! Amman da zaman da fitowar duk sunanta koronabairus da Koronayunwa, kowanne kisa yake. Gwanda ka mutu a cikin izza na neman abin da za ka ciyar da iyalinka da kanka, a kan ka zauna yunwa ta kashe ka! Ku fadakar da Hukuma ta tallafa wa talakawa, sai su zauna; ba a ce su zauna babu tallafi ba; wannan zalunci ne. Manzo (S) yana cewa: "Addaalu alalkhairi ka fa'ilihi, waddaalu alashsharri ka faa'ilihi". Ka shiryar a kan taimakon mazlumai (Wadanda ake zalunta) ba taimaka wa azzalumai ba, sai ka mutu da izza. Idan kana da raunin imani, ka yi shiru ya fiye maka. Kar a yaudare ka wai Najeriya ba ta da kudi, karya ce! Abu daya ma zai wadata ’yan Najeriya, ba wai kawai ya ba su abinci ba. Na san ka san tsohuwar Ministan fetur a lokacin Jonathan, da Buhari ya hau ta dawo da wasu sashe na kudin da ta sata. Kimanin daruruwan Daloli ne. ’Yan jarida sun ce wadannan kudi mai tarin yawa ne. A lokacin idan aka ce akwai Najeriyawa mutum miliyan 190, yaro da babba, mace da naimiji, to idan za a raba musu wannan kudin da ta dawo da su kowane dan Najeriya zai sami kudi masu yawan gaske. Ko yanzu ka duba a ‘Net’ za ka gani. Ina kudin suke? Me aka yi wa ’yan kasa da su? Irin su suna da yawa wadanda wasu suka sata aka dawo da su har daga waje duk suna ina? Ku ji tsoron Allah, ku farkar da mutane irin zaluncin da ake musu!!! Duk da zaman ’yan Amerika a gidajensu, hakan ya hana su kamuwa da cutar ne? A kwanan baya sun kai kusan mutum dubu 30 ne suka mace, kuma wajen miliyan suka kamu, don haka ba zaman ne kawai ba! Abin da ya sa muka haramta almajirci -Gwamnatin Buhari Gwamnatin Tarayya ta yi karin haske a kan dalilin da ya sa gwamnontocin jihohi Arewa suka haramta almajirci, tare da kwasar su suna mai da su jihohinsu na asali, abin da ke jawo damuwa da cece-kuce a tsakanin jama’a. Sakataren gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha ne ya yi karin hasken a lokacin da yake jawabi ga manema labarai a kan halin da ake game da cutar Kornabairus ranar Juma’ar makon jiya a Abuja. Ya ce; “Babu wani abin damuwa don yara kanana sun tashi suna neman ilmin abin da zuciyarsu ta yi imani da shi, amma dai akwai bukatar a samar masu sana’o’in hannu da kayan aiki, a ba su ilmi a cikin jihohinsu, ta yadda za a ci moriyarsu a cikin al’umma nan gaba.” Boss Mostapha ya kara da cewa; “Idan ba haka ba kuwa, to muna kyankyashe wa kanmu wasu dakarun da za a wayi gari nan gaba za su addabe mu, kuma su addabi kasar nan har mu rasa yadda za mu yi da su.” An kiyasta cewa akwai yara sama da milyan 10 a Arewa da suke almajirci, yayin da gwamnatin Jihar Kaduna ta bayyana cewa ta samu 50 daga cikin almajirai 155 da aka dawo mata da su daga Kano suna dauke da cutar Kornabairus. Gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje, ta bayyana cewa ta kwashi almajirai 1098, wadanda ta mai da jihohinsu. A shafinsa na Twitter, Sanata Shehu Sani ya soki lamirin mai da almajiran nan jihohinsu ba tare da yi musu wani tanadi na musamman ba da cewa, “In kuka kame kazantaccen almajiri mai bara daga kayatattun biranenku, kuka ‘kora’ shi zuwa kauyensa, nesa da ’yan yawon shakatawarku, bakinku, wuraren holewarku da ganinku, to tamkar kuna boye ’yan kamfenku ne, maimakon wanke su.” Ya kuma kara da cewa, “Almajiran da kuka zabi ku ‘kora’ zuwa kauyuka, kuka ki ku ilmantar, tare da karbar su, to za su dawo gare ku a matsayin mahara da ’yan ta da zaune tsaye.” Dakile yawan mutuwa a Arewa Likitoci sun ba da shawarwari Daga Wakilinmu tare da www.bbchausa.com Wani bincike da wasu Likitoci suka gudanar kan mace-macen da ake yi a Kano ya nuna cewa suna da dangantaka da cutar Korona. Masu binciken, wadanda wasu Likitoci ne mata uku ’yan asalin Jihar Kano sun ce sun dau aniyar binciken ne sakamakon rahotannin karuwar mace-macen da ake samu a birnin Kano a lokacin da ake fama da cutar Korona. Daya daga cikin masu bincikin, Dakta Maryam Nasir Aliyu, Likita ce a Kano, kuma tana koyarwa a Jami’ar Yusuf Maitama Sule a Kanon. Sauran kuma Dakta Zainab Mahmoud, Dakta Khadija Rufa’i suna karatu ne da kuma aiki a Amurka. Sun tattara bayanan binciken ne a cikin kwanaki biyu, inda suka tattauna da dangin mutum 183 da suka mutu a cikin kwaryar birinin Kano daga ranar 18 zuwa 25 ga watan Afrilun 2020. Tun da farko dai sun shelanta daukar matakin a kafofin sada zumunta, inda suka nemi dangin wadanda suka mutu su tuntube su domin ba da bayanai. Dakta Maryam ta shaida wa BBC cewa, sun yi amfani ne da hanyar tattara bayanai ta yin hira da dangin mamatan, kamar yadda Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta zayyana. Sakamakon binciken ya gano cewa kaso 96 cikin 100 na wadanda suka mutu din tsofaffi ne da suka haura shekara 60, sannan da damansu suna fama da cutuka kamar ciwon zuciya da hawan jini. Binciken ya gano cewa, kaso 88 cikin 100 na wadanda suka mutu sun yi fama da zazzabi mai zafi. Kaso 76 kuma sun yi fama da tari, yayin da kaso 80 kuma suka samu matsalar numfashi, har ta kai an sa wa wasu na’urar taimakawa wajen numfashi. Sannan kaso 39 sun yi fama da matsalolin ciki da suka hada da amai da gudawa da kuma cushewar ciki. Haka kuma binciken ya gano cewa mutanen da suka mutu sun yi jinya ne ta tsawon kwanaki biyu zuwa kwana 14. Dakta Maryam ta ce; “Mafi yawan wadanda suka mutu din sun yi gajeriyar jinya ne, da ta zo da nau’in zazzabi, wasunsu kuma da alamomi na mura.” “Gaskiya dai a ganinmu din akwai wadanda alamu ya nuna cewa akwai Koronabairus,” a cewar Data Maryam. Sai dai ta ce ba za a yanke hukunci cewa cutar Korona ba ce tun da ba a yi gwaji ba. Ta kara da cewa daya daga cikin wadanda suka tattauna da su ya bayyana cewa Mahaifinsa “ya fara da zazzabi, sannan kuma sai ya fara mura, sai ya fara tari ba kakkautawa. Daga nan kuma sai numfashinsa ya fara sarkewa, har suka je asibiti aka saka masa iskar ‘oxygine’. Sannan daga baya aka sa masa na’urar taimaka wa wajen numfashi.” KULEN DA SUKA FUSKANTA Masu binciken sun ce babbar manufarsu ta gudanar da binciken ita ce gano musabbabin abin da ke yin ajalin mutane a Kano fiye da yadda aka saba gani. Sai dai sun ce binciken nasu ya fuskanci kule da suka hada da cewa sun gudanar da binciken ne ta kiran wayar mutanen da ba a san su ba gabanin lokacin binciken. Haka kuma wasu mutanen da aka kira sun ki ba da bayanai kan mamatansu, yayin da wasu kuma ba sa ba da sahihan bayanai ba. Sannan kuma a cewar su sun samu wasu bayanan da ba za su iya amfani da su ba, saboda wadanda suka ba da bayanan ba su da alaka ta kusa da wadanda suka mutu din. Don haka bayanansu ba za su zama sahihai ba. SHAWARWARI Masu binciken sun ba da shawarwari shida, mafi yawancinsu ga hukumomi. 1. Gudanar bincike a kan kari kan mace-macen, ta hanyar tattara bayanai daga dangin mamatan, da masu kula da makabartu da kuma asibitoci. 2. Kara yadda ake gudanar da gwajin cutar Korona a Kano, da samar da wuraren gwaji na tafi-da-gidanka kasancewar an kai matakin yaduwar cutar a cikin al’umma. 3. Samar da kayan kariya ga ma’aikatan lafiya, musamman wadanda suke fara ganin marasa lafiya. 4. A lura cewa an yi watsi da wasu cutukan da jama’a ke fama da su, sannan a duba yiwuwar tura duk wanda ba ya fama da wasu cutukan da ba Korona ba zuwa asibitoci masu zaman kansu da kuma kananan asibitoci. 5. A fitar da tsauraran ka’idoji wajen binne jama’a. 6. Bude muhimman wurare da kasuwannin sayar da abinci da magunguna.