AlmizanAlmizan logo
Jum'a 23 ga Ramadan, 1441 Bugu na 1445 ISSN 1595-4474

Labaran Harka Islamiyyah

Labarin bikin ALMIZAN@30 a Birnin Bauchi

Daga Adamun Adamawa


Maulid Sayyada Fatima

Jaridar ALMIZAN ta Harkar Musulunci, ta shigo fagen samuwa, ta ga hasken rana a karo na farko ne a ranar 30 ga watan Rajab na shekarar 1411 hijira, wato shekaru 30 cif da suka gabata. Sai da ta shafe shekaru 10 cif sannan ta yi bikin haihuwarta a karo na farko a hotel din Jimharisson da ke birnin Zariya, inda nan ne garin da aka haife ta. Bayan wannan biki na “ALMIZAN 10 Years Annibersery”, ba a sake yi mata biki ba sai da ta cika shekaru 15 da samuwa, inda a karo na biyu aka yi taron a FIC Zariya a wancan lokacin. A dukkanin tarukan nan guda biyu, Jagoran Harkar Musulunci Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ne ke rufe su da jawabai masu albarka.

A bana da muke cikin shekarar 1445 hijira, shekaru 30 ke nan cif da samuwar wannan baiwar Allah ALMIZAN mai dimbin karamomi, wacce ke rayuwa da ruhin karfe! Kuma shi ne karo na uku na taruwa domin yin bikin murnar samuwarta. Wannan yana nufin an shekara 15 ke nan ba a yi bikin tuna ranar samuwarta ba, a sabili da haka taron ya zamo na musamman, cike da kumaji na musamman!

A rayuwa, ba a kodayaushe mutum ke samun abin da yake so ba, domin tun a shekarar 2015 aka so a yi bikin cikar jaridar ta ALMIZAN shekaru 25 da samuwa, abin da a turance ake kira ‘Silber Jubilee’, har ma an tattauna batun, to amma sai aka yi ta nazarin yadda za a samar da kudaden gudanar da taron, za a yi ne, ba za a yi ba ne, har mai aukuwa ta zo ta auku, aka tafka kazamar waki’ar Zariya, wacce ta canzawa komai akala.

Bayan an shafe shekaru biyu ana gigice, a shekarar 2017 sai aka sake ta da batun ya kamata a yi kara’in wancan biki na ‘ALMIZAN SILbER JUBILEE ANNIbERSARY”, nan da nan aka samar da kwamitin shirya bikin karkashin Oga Danjuma Katsina, ni ne Sakataren kwamitin a wancan lokacin, an fara shirya yadda za a yi taron, sai aka samu bambancin ra’ayi kan wasu abubuwa da yadda za a yi su, ba a gama warwarewa ba sai batun jinyar Jagora Shaikh Zakzaky (H) ta motsa, nan aka watsar da komai aka tunkari abin da shi ne ‘Ahammu’!

Batun bikin tunawa da ranar samuwar ALMIZAN bai sake motsawa ba sai a farkon shekarar 2020. A wannan karon ba ma wanda ya kawo shawarar gara a yi bikin balle a tattauna ko a kafa masa Kwamiti, saboda na farko dai Danliti Mugu ya jefa al’ummar kasar cikin bala’in yunwa da fatara, kowa ta yadda zai rayu yake tunani, ba ta bukukuwan mustahabbi ba. Na biyu waki’o’i sun yi wa ma’abota Harkar Musulunci dirar farin dango ta ko’ina, don haka babu amincin da za a iya sakankancewa da shi a tara zakakuran mutane muhimmai a wuri guda don gudanar da wani taro. Na uku ita kanta jaridar ALMIZAN din marainiya ce da ke rayuwa a hannun Allah, ba ta da karfin da za ta iya daukar nauyin duk wani taro da zai bukaci kudi komai karancinsu. Ke nan, bisa dukkanin ma’aunai taron bikin cikar ALMIZAN shekaru 30 zai yi wahalar yiwuwa a wannan halin!

Amma da yake babban taken jaridar ALMIZAN shi ne ‘IKON ALLAH’, shi kuma ikon Allah bai da ‘No Go Area’, sai ya zama duk abin da ya damfaru da jaridar shi ma yakan zama ‘IKON ALLAH’ ne! Kwatsam sai aka soma jin rade-radin cewa dandalin ‘A Takaice Kai Tsaye’ za su gudanar da taron cikar ALMIZAN shekaru 30. Daga baya sai maganar ta zama akasi. Ashe ba a ji da kyau ba ne, to amma tunda an riga an furta cewa za a yi, to ba makawa a dauki harama. Bature ya ce ‘Determination Leads To Success” wato ‘kuduri Jagoran Nasara.’ Daya daga cikin Limaman shiriya na Ahlul-Bait (AS) yana cewa; Himma Rabin aiki ce!’ Sannan Alkur’ani yana cewa; idan ka yi azama, to ka dogara ga Allah’. Duk wadannan zantuka suna karfafa mutum ne ga himma da kwazo wajen tunkarar abu, komai girmansa, da cire tsoro ko fargabar rashin yiwuwarsa.

An tunkari batun shirya bikin cikar ALMIZAN shekaru 30 ne da abubuwa biyu kacal, kuduri da kwazo, sai kuma dogaro ga Allah da neman taimakonsa. Da bashi aka soma shirya duk abin da ya shafi bikin, aka rika tsara hanyoyin da taron zai yiwu daki-daki, hawa-hawa, komai ana masa ‘Plan A to Z’ ne, za mu yi kaza; in kazan bai yiwu ba sai mu yi kaza, in shi ma bai yiwu ba, to sai mu je kaza! Kwamitin mutum biyar na wannan taro, sun bata hankalin darare, tare da aiki da ‘Maximum Capacity’ na kwakwalwarsu don ganin taron ya yiwu, kuma ya yi nasara.

Alhamdulillah, a karshe dai an cimma nasarar duk abin da aka tsara har ma da kari, taro ya yi taro, duk wani mai alaka da ALMIZAN ya halarta, ciki kuwa har da babban Editanta da azzalumai ke farauta, tun ran farko da shi aka fara, kuma har ranar karshe da shi aka kare. A jihohin Arewa kuwa, ba inda ba a samu wakilcin mutanenta ba, makalolin da kwararru suka gabatar a taron, sun warkar da cututtuka masu yawa, sun ilmantar kuma sun kara haska hanyoyin ci gaba. Mahalarta sun ga juna, sun karfafi zumunci, sun kara dimfaruwa da son junansu.

Yin taron ALMIZAN a wani gari ba Zariya ba a karo na farko, da kuma zabar yin sa a birnin Bauchi ya dace sosai, don ko ba komai, Bauchi ne mahaifar Manajan-Daraktan kamfanin jaridar, wato marigayi Alhaji Hameed Danlami, ke nan kawo taron Bauchi, wani nau’i ne na karrama shi da karin nuna godiya da yabawa bisa hidimar da ya yi wa jaridar.

A karshe, dole in jinjinawa wasu boyayyun bayin Allah da suka tsaya suka yi hidima kwarai a lokacin gudanar da wannan taro, wanda tsayuwarsu a kan ayyuka daban-daban ne ya kawata nasarar wannan taro, sune; Umar Babagoro Dukku, Bilyamin Hamza Dass, Umar Bandirawo, Oga Saleh Bauchi, da Bala Ningi. Wallahi har tausayin su nake ji, a lokacin da kowa ke hutawa, a lokacin da kowa ke bacci, su kuma a lokacin suke ta ayyuka, wanke-wanke, share-share, gyare-gyaren masauki da zauren taro, zirga-zigar abubuwan bukatu da dai sauransu. A bangaren mata da suka tsayu da abinci kuwa, dole mu jinjina wa Hajiya Ameena Habeeb, Malama Rukayya Ridwan, Zunairat Jibreen, Khadeeja Jibreen da Suwaiba Ahmad Hassan. Tabbas tsayuwar daka ta wadannan bayin Allah a fagen ayyuka ba dare ba rana, ita ce ginshikin nasarar wannan taro.

Gare mu ‘yan kwamitin shirya wannan taro, bikin cikar Almizan shekaru 30 a Bauchi ya yi cikakkiyar nasara, komai nasa ya tafi daidai, wani bangaren ma fiye da zatonmu, mafiya girman nasarori a taron sune; Yiwuwar taron a daidai lokacin da aka tsara shi ba tare da dagawa ko sau daya ba, yiwuwar dukkanin abin da aka tsara yin sa, halartar dukkanin muhimman mutanen da ake son gani a taron, halartar dukkanin bangarori da sassan da aka gayyata daga jihohi daban-daban, kammala taron a cikin nasara ba tare da wata matsala da za ta dagula taron ba, komawar dukkanin mahalarta taron gidajensu lafiya ba tare da ko da hatsari ba balle salwantar rayuka, karkare taron ba tare da samun basuka a kan Kwamitin shirya taron ba, da dai sauran nasarorin da ba za su fadu ba.

Ba na bukatar in ce wane da wane ne suka halarci taron, hotunan bikin sun fi zama shaida ga kowa, amma duk wani ‘Who is Who’ a ALMIZAN na da da na yanzu ya halarta, kuma mafi yawan manyan Malaman Harka Islamiyya sun halarta, sannan fitattun wakilan ALMIZAN da dillalanta duk sun halarta.

Harisawan Bauchi sun ce ba su taba ganin taro mai tsafta irin wannan ba, suka ce mahalarta taron kamar zabo su aka yi. Kowa ya san abin da yake yi, kuma kowa na yin abin da ya dace. Ba wanda ake cewa yi kaza ko ka bar kaza, kowa ya san abin da ya dace ya yi. “Wallahi ban taba ganin taron masu hankali da sanin ya kamata irin wannan na ’yan ALMIZAN ba! Da duk taro zai rika zama haka, da Harisawa sun huta da aiki!” in ji Kwamandan Harisawa na Bauchi, Oga Saleh.

Ta bangaren Basalafe Baban Takko kuwa, da aka saki dimbin hotunan taron bayan an kammala shi, nuna mamakinsa ya yi matuka na gudanar da irin wannan hamshakin taro da ya hada manyan mutane, amma ba tare da sanin hatta ’yan garin da ake taron ba. Ya wallafa a shafinsa na Facebook cikin mamaki cewa; “In har ’yan Shi’a za su iya gudanar da babban taro irin wannan, wanda ya hada manyan mutane haka, amma ba tare da kowa ya sani ba, to akwai matsala!”

Ni ne Dillalin Almizan na farko a Suleja

- Malam Shehu Adamu

Malam Shehu Adamu, wanda wasu da yawa a Suleja suka fi sanin sa da Shehu Almizan (da yake shi ne farkon wanda ya fara sai da Almizan a garin Suleja), ko kuma Shehu Kwamanda (da yake ya taba rike Kwamandan Harisawan garin Suleja) tsohon dillalin Almizan ne na farko a garin Suleja. A ci gaba da bukukuwanmu na cikar Almizan shekaru talatin, Wakilinmu na Suleja Magaji A. Idris ya sami zantawa da shi, inda suka tabo janibobi daban-daban, wanda sai mai karatu ya karanta ne zai ji abubuwan da suka tattauna. A sha karatu lafiya.

ALMIZAN: A tarihin Almizan a Suleja, za mu iya cewa kai ne dillalinta na farko. Ko haka ne?

MAL. SHEHU ADAMU: Eh, haka ne. A ’yan shekarun baya, da yake ni dan Zariya ne, nakan je Zariya ranar Alhamis, sai in yi Juma’a a can. To, sai na lura da cewa yanayin nan Suleja babu sakon kiran Shaikh Zakzaky (H). Sai na yi magana da wadanda suke kusa da Alh. Hamidu Dallami. Na ce ina so in zama mai kawo Al-mizan a wannan yankin. To, kuma sai aka yi sa’a ya amince. Muka zo gidansa a nan fadama. Ba na mantawa, aka kirga mani Al-mizan bugu daban-daban har kwafi dari biyar. Wato kowace fitowa guda dari. Na zo nan yankin suleja da ita. A wancan lokacin ina kai ta gidaje da ofisoshi, da wurin taron daurin aure, da taron suna.

ALMIZAN: Za ka iya tuna ko wace shekara ce?

MAL. SHEHU ADAMU: To ni a tunanina, ina tsammanin zai kai shekaru ashirin da bakwai. To, sai kuma na ji ga shi har ana bukin cikar ta shekaru talatin.

ALMIZAN: A wancan lokacin da ka kawo Al-mizan, za ka iya tuna ko bugu na nawa, da na nawa ne?

MAL. SHEHU ADAMU: Ba zan iya tunawa ba. Sai dai in fadi babban labarin wasu bugun da zan iya tunawa. Akwai bugun da aka yi mata kanu “Siyasa ko sakarci?”. Sai kuma wacce aka yi wa kanu da “Gwamnatin tarayya ita ta haddasa fitinar Kano”. Zan iya tuna wadannan bugu guda biyu.

ALMIZAN: Fitinan Kano, wacce fitinar Kano din?

MAL. SHEHU ADAMU: Na lokacin da aka yi jabun jihadi. Wanda aka haura katangar gidan yarin Kano, aka yanko kan Orka. Wanda a cikin masu kisan har da Sarkin Kano Sanusi mai murabus. Domin a lokacin shi ma almajirin Malam ne, a lokacin ne ya yi tawaye.

ALMIZAN: A wancan lokacin ana sai da Al-mizan nawa?

MAL. SHEHU ADAMU: A wancan lokacin ana sai da ta Naira biyu ne. Kuma a wancan lokacin ban tsaya a Suleja kadai ba. Ina kai ta Keffin Yamusa. Ina kai ta Gwagwalada. Ina kai ta Abaji. Har Kwaton-karfe na kai ta.

ALMIZAN: A wancan lokacin, mene ne ya ja hankalinka har ka fara kasuwancin Al-mizan?

MAL. SHEHU ADAMU: Sha’awar yada wannan sako na Mujaddadin wannan karnin ne ya ja hankalina. Domin kawai in ba da tawa gudummawar na dan abin da zan iya yi, na yada wannan sako a rubuce.

ALMIZAN: Tsakanin Amirai masu tashi su yi Pre-Khuduba a Masallatai, da kuma Al-mizan, wane ya riga wani zuwa wannan yankin?

MAL. SHEHU ADAMU: Lallai Al-mizan ta riga Amirai kawo sakon wannan kira zuwa wannan yankin. Domin a wancan lokacin ina zaune ne a unguwar Magaji, kuma a lokacin babu wani mai tashi ya yi tunatarwa da sunan Amir a nan Suleja. Har daga baya na samu ana aiko mani da ita ta hannun drebobi. Ma’ana ba sai na je Zariya na karbo ba. A lokacin ana kawo mani ita zuwa wajen Shehu mai gyaran rediyo na unguwar Zariyawa, ko kuma shagon Babanka marigayi, Allah ya ji kansa, baba Alh. Idi Zariya. Sai in je in karbo in rarraba ta, in kuma sai da wanda zan sai da a nan Suleja. Ta hanyar bin mutane shago-shago, Masallatai, wajen taron daurin aure, ko taron radin suna.

ALMIZAN: A wancan lokacin, akwai barazana na sai da Al-mizan daga jami’an tsaron Gwamnati, ko kuma ana sai da ita lafiya lau?

MAL. SHEHU ADAMU: Lallai akwai barazana. Sai dai ganin wanda yake sai da ita kamar ya cika musu idanu, sai ya zamana babu yadda suka iya. Ba kamar yanzu ba da za ka gan ta a hannun yara kanana suna sai da ita lafiya kalau.

ALMIZAN: Za ka iya tuna wata barazana da ka taba fuskanta a wancan lokacin, wanda ba za ka taba mantawa da ita ba?

MAL. SHEHU ADAMU: A wancan lokacin, mun taba samun barazana a lokacin da muka kai ta Abuja. Lokacin da aka yi bukin bude Masallacin kasa. A lokacin, jami’an tsaron SSS sun hana kasa komai a harabar Masallacin. Suna korar kowane dan kasuwa. Amma mu a wancan lokacin mun zo da yawa. Muka kasa Al-mizan ko’ina. Sai dai ka ga SSS ya zo wajenmu yana zare idanu kawai. Amma ba ya iya yi mana komai.

ALMIZAN: Ya za ka kwatanta mana halayya, da karimci na marigayi Alh. Hamidu Danlami?

MAL. SHEHU ADAMU: To, abin da zan iya cewa a nan shi ne, lallai marigayi Alh. Hamidu Danlami mutum ne mai saukin kai. Mai saukin lamari. Kuma mai hakuri, da juriya. A wancan lokaci bai san ni ba. Kawai na ce masa ne ina so ya ba ni jaridar don in zo in yada wannan sako a nan Suleja. Ba tare da ya bukaci sai na kawo mai tsaya mani ba, ya dauki kwafin jaridu masu yawa ya ba ni. Wannan iyakar saukin kai ke nan, da sallama wa kiran Shaikh Zakzaky (H).

ALMIZAN: Da yake ka ce a wancan lokacin da ka fara sai da Al-mizan ba a fara Pre-Khuduba ba. Su wa, da wa suke sayen ta a nan Suleja?

MAL. SHEHU ADAMU: To, zan iya tuna wasu. Akwai Alh. Abu, wanda gidansa yana kofar fada. Kuma yana da ofis a Ma’aikatar lafiya. A nan asibitin kofar Sarkin zango. Sai kuma marigayi Sarkin Zuba, lokacin kafin ya yi ritaya ya zama Sarki. Lokacin yana da gida a unguwar Town Hall.

ALMIZAN:- To daga baya sun fahimci Harka a dalilin karanta Al-mizan, ko kuwa mene ne kake jin shi ne dalilinsu na sayen ta a wancan lokacin?

MAL. SHEHU ADAMU: Ba su fahimci Harka, misali a ce sun zo an yi da su ba. Amma suna sane da abin da duk ake ciki. Sa’annan kuma ba mu taba jin furuci na suka daga bakunansu ba.

ALMIZAN: Ya za ka kwatanta yanayin sai da Al-mizan a zamanin waki’ar Abaca?

MAL. SHEHU ADAMU: A wancan lokaci mun yi bankwana da Al-mizan. Sai na jingina wa Da’ira a wancan lokacin. Na bar sai da Al-mizan a lokacin tana naira biyar. Na bar ta ne bayan bukin bude babban Masallacin kasa na Abuja.

ALMIZAN: Bayan ka bar sayar da Al-mizan, ka damka ta a hannun Da’ira. A wancan lokacin waye ya ci gaba da sai da ita?

MAL. SHEHU ADAMU: A wancan lokacin Da’ira ta damka sai da Al-mizan ne a hannun Shahid Muhammad Sani Sufi.

ALMIZAN: Da yake ka karanta Al-mizan a baya. Yanzu ma kana karanta ta. Meye bambancin ta a da, da yanzu?.

MAL. SHEHU ADAMU: To, a wancan lokacin namu, farin bugu ake yi. To, ga shi yanzu Alhamdu Lillahi ta koma kala. Lallai an ci gaba. Kuma muna yi mata fatan alkhairi.

ALMIZAN: Muna so ka yi wa jaridar Al-mizan addu’a.

MAL. SHEHU ADAMU: A’uzu Billahi minas shaidanir Rajeem. Bismillahir Rahmanir Raheem. Ina wa wannan jarida mai albarka, wacce ta wayar da kan al’umma fatan alkhairi. Allah ya inganta ta. Allah ya ba ta karfin gwiwa. Allah ya inganta wannan kamfani.

ALMIZAN: Mun gode.

MAL. SHEHU ADAMU: Ni ma na gode muku.

Hoto: Malam Shehu Adamu, wanda ya fara sai da Almizan a Suleja, jihar Neja