AlmizanAlmizan logo
Jum'a 23 ga Ramadan, 1441 Bugu na 1445 ISSN 1595-4474

Labaran Harka Islamiyyah

Yadda na yi wa su Malam Turi da Mal. Mustafa Nasidi ganin karshe

In Malam Muhammad Mansur Suleja


Maulid Sayyada Fatima

Malam Muhammad Mansur Suleja, yana daya daga cikin ’yan’uwan da waki’ar Zariya ta rutsa da su a Gyallesu. Ya ga abubuwa da yawa a wannan waki’a. A karshe sojoji suka kama shi. Ya yi mako guda a hannunsu. A karshe aka kai su kurkukun Kaduna. Har daga baya Allah ya yi fitowarsu. Wakilinmu na Suleja Magaji A. Idris ya sami zantawa da shi. Akwai abubuwa da yawa da ba ku ji ba dangane da wannan waki’a, wadanda Mal. Muhammad Mansur ya warware zare da abawa. Sai dai kun karanta za ku ji yadda abin yake. A sha karatu lafiya.

ALMIZAN:- Ka sami zuwa Zariya a waki’ar 12-14/12/2019. Daga ina ka je Zariyan?

MUHAMMAD MANSUR:- Daga nan Suleja.

ALMIZAN:- Kai da wa kuka bar Suleja?.

MUHAMMAD MANSUR:- Ni da Musa Muhammad Sani.

ALMIZAN:- Ta yaya kuka samu kuka shiga Zariya?

MUHAMMAD MANSUR:- Da yake lokacin da muka sami labarin waki’ar, mun sami labari ne da yamma, bayan an fara a Husainiyya. Mun ma kira Muhammad Sani Fasa-kwalta, da Shahid Junaidu. Dukkan su sun tabbatar mana da ana waki’a a Zariya, kuma waki’a mai muni. To, da ni da shi Musan, sai muka kama hanya kawai. A Kawo, Kaduna magariba ta yi mana. A cikin motar da muke ne na ji wani fasinja da ya hau intanet yake cewa me yake faruwa ne a Zariya? Ga ’yan Shi’a nan sun tare wa Shugaban sojoji hanya. Har ma sojojin sun kashe musu mutane.

ALMIZAN:- Lokacin da kuka isa Zariya, Gyallesu kuka nufa, ko Husainiyya?

MUHAMMAD MANSUR:- Da yake Direban da ya dauke mu dan Zariya ne, mun so ya sauke mu a Kwangila ne, mu shigo ta Husainiyya. Sai aka ce ai babu hanya ta Husainiyya. Sai ya dawo da mu ta Dan Magaji. Ya sauke mu a Kofar Doka. Daga nan ne muka sami mashin muka wuce Gyallesu.

ALMIZAN:- Ta yaya kuka iya shiga Gyallesu? Musamman ganin cewa sojoji sun mamaye Gyallesu?

MUHAMMAD MANSUR:- A daidai wancan lokacin kusan tare da sojojin muka iso Gyallesu. Domin mashin dinmu na gaba, su kuma kwambar motocin sojojin na biye da mu a baya.

ALMIZAN:- Da kuka shiga Gyallesu, kafin a fara waki’a, kun sami shiga gidan Malam (H)?

MUHAMMAD MANSUR:- Da yake mun shiga Gyallesu ana cikin jin cewa komai na iya faruwa ne. Hakan ya sanya kowa na yin abin da ke gabansa ne. Babu mai kula harkar wani. Sai muka je sabon gidan Harisawa, muka ajiye kayayyakinmu. Muka yi Salloli. Sai muka fara tunanin cin abinci. To, abincin da ba mu ci ba ke nan har zuwa ranar Talatar da aka kai mu Depot din sojoji, sannan muka samu cin abinci.

ALMIZAN:- Ko za ka iya yi wa masu karatunmu bayanin yadda aka fara waki’ar, da yadda ta rutsa da kai. Da kuma yadda a karshe har ka sami kanka?

MUHAMMAD MANSUR:- Na’am. Lokacin, kafin a fara Waki’a, muna tare da Shahid Sirajo Sabon Wuse da Shahid Junaidu, kafin a harbe su. Ni da Shahid Sirajo Sabon Wuse muka shiga sabon gida muka yi Salloli. Sai na ce masa ni yunwa nake ji. Sai ya ce mani in tashi in je in ci abinci kafin shi ya kammala Sallar Isha’i. To, wannan maganar tamu ita ce magana ta karshe a tsakanin mu. Daga nan ban sake ganin sa ba, sai dai gawarsa. Sai na je wajen wani mai shayi. Na ce ya dafa mani indomi. Ina zaune ina jira, sai na ga mutane sun fita da gudu. Shi kansa mai shayin, yana cikin daga shayi, sai na ga ya saki kofunan, ya fita a guje. To, ashe harbi aka yi. Ni kuma ban ji harbin na farko ba. Ai ina ankara sai na ji harbi ko ta ina. Sojoji ne ke harbin mutane. Ni ma sai na fita a guje. ’Yan’uwa, wasu suka je Kofar Banedeen, wasu suka je kofar FCE, inda ake saida kayan miya. Ina cikin wadanda suka je kofar FCE, saboda kada sojojin su yi mana zobe. Sai muka kama wajen. A lokacin sai suka kasa karasowa wajen. Sun ta yin yunkurin kutsowa, amma Allah bai ba su ikon shigowa ba. A haka dai muka kwana a wajen.

To, da yake ni ina da wani abu. In dai zan je Zariya in kwana biyu, to sai na yi zazzabI, saboda sanyin da ake yi a Zariya. To, tun lokacin da muka isa garin, zazzabi ya rufe ni. Kuma har gari ya waye zazzabin bai sake ni ba.

Muna zaune haka, sai K/Mashi ya zo yana wakar nan tasa ta ‘Adrikna-adrikna ya Mahdi.’ A nan barci ya kwashe ni, saboda zazzabin da ya rufe ni. Ina cikin barci, sai na rinka jin harbi. Harsasai suka rinka wucewa ta kusa da ni. To, ashe inda nake babu kowa a wajen. Har sojojin sun zo sun wuce inda nake, amma Allah bai nuna musu ni ba. Ina tashi sai na danna a guje. Suka biyo ni suna harbi na, amma Allah bai sa sun same ni ba, har na sha kwanan sabon gidan Harisawa. To a nan dai muka hana su sakat. Aka dinga harbin su da duwatsu, har suka juya da baya. Haka muka tsaya a wajen ‘Tiransifoma’ wancan kafin Tiransifomar gidan Abbah, jikin wani gidan sama. A daidai wajen muka kafe su a nan. Su ka yi, suka yi su keta wannan shingen, amma suka kasa. Ko daga baya su ma sun fada cewa babu wajen da ya ba su wahala kamar wannan shingen.

A lokacin zazzabin nan ya sake dawo mani. Rashin lafiya ya rufe ne. Sai ya zamana idan na yi jifa, ba ta isa ga sojojin. Sai ta rinka fadawa kan ’yan uwa. Sai na koma wajen ’yan ISMA domin in sami maganin da zan sha. Ko da na je, sai na ga ba ta ni ake yi ba. Ana ta kokarin ceto rayukan wadanda aka harba ne. A nan ne na ga Yaya Junaidu Suleja. Har yake tambaya ta dalilin dawowa ta. Na ce masa rashin lafiya ne ya dame ni. Ya ce in je in sami waje in dan kwanta kafin wani lokaci. Na je na sami wani daki na kwanta. Ina kwance haka sai na ji muryar ko Dakta Nasiru Tsafe ne? ya shigo gidan, yana cewa, “zama fa bai gan mu ba. Mutanen nan suna so ne su kawo ga Malam (H).” To, duk da rashin lafiyar da ke damu na, a haka na yunkura na tashi na fita. Muka fito muka tunkari muyagun nan. A lokacin suna ta kokarin su keta shingen nan na kafin Tiransifoma na kusa da gidan Malam.

Ana haka, sai muka ga wani soja a saman rufin gidajen jama’a, yana ta harbin ’yan’uwa. Yana yi wa ’yan’uwa dauki dai-dai. Sai muka rufe shi da jifa. A haka dai ya sauka ya gudu. Muka ci gaba. Mutanen nan sun yi, sun yi, amma sun kasa keta wannan shingen. To, sai suka yi wata dabarar yaki. Suka jeru, mutane hurhudu kashi uku. Hudu a gaba, hudu a tsakiya, hudu a baya. Sai suka tunkaro mu. Hudu na gaba za su yi ta bude mana wuta, har sai harsasansu sun kare. Sai su koma baya, su ci gaba da dura harsasan bindigoginsu. A daidai wannan lokacin kuma hudun tsakiya za su ci gaba da bude mana wuta. In su ma harsasansu sun kare, za su koma baya. Sai hudun karshe su ci gaba da bude mana wuta.

To lokacin da suke wannan harbin, Shahid Turi yana bayanmu, ya fito daga gidan Malam Zakzaky (H). Lokacin yake cewa “Ba zai yiwu muna raye a ce harsashi na bugun gidan Malam ba, kuma Malam yana cikin gidan.” Ya fito har ’yan’uwa suna ta ba shi hakuri. Sai yake cewa in dai muna so ya bari, to mu mu fita mu tunkare su. Sai ’yan’uwa suka ce, to su za su fita. Sai Malam Turi ya ce, to bari ya zauna a nan. Sai ya zauna a dandamalin nan na karamin kofar gidan Malam (H). To, a lokacin ne sojojin nan wadanda suka jeru hurhudu suka kawo wajen. A haka ne suka harbi wani dan Sabon Wuse. A haka ne kuma suka harbi Muhammad Sani Fasa kwalta Suleja. A nan ne suka harbi Shaikh Turi. A nan ne kuma suka harbi Dakta Mustafa.

Yadda aka harbi Shaikh Turi kuwa shi ne, lokacin da wuta ta yi wuta, sai ’yan’uwa suka shawo kwana a guje. Sai Shaikh Turi ya tashi ya nufi wajen. Sai kawai ya sha gaban sojojin. Yana shan gabansu, sai suka harbe shi karo na farko, ya fadi kasa. Sai ya yunkura domin ya sake tashi tsaye, sai ya zame. Sai suka sake harbin sa. To, a lokacin ne bai sake tashi ba. A nan Allah ya yi wa’adinsa.