AlmizanAlmizan logo
Jum'a 23 ga Ramadan, 1441 JBugu na 1445 ISSN 1595-4474

Rahotanni

Halin Da Mahaifana Suke Ciki A Yanzu

Daga Sayyid Muhammad Zakzaky


soji

Yau dai zan yi magana a kan dokar da ba rubutacciya ba, amma kuma ake aiwatar da ita wajen cutar da mahaifana; a tsammanina shirun da na yi zai taimaka wajen rage irin ukubar da mahaifana suke fuskanta.

Tun mahaifana na tsare a wajen DSS, kafin a mayar da su gidan kurkukun jihar Kaduna; mahaifina na fama da hawan jini sosai. Wata rana jininsa ya hau, wata rana ya sauka. Kullum dai haka yake fama da jiki, banda sauran nau’ikan rashin lafiya da yake fama da su.

Mahaifiyata kuwa, bayan dukkan matsaloli na rashin lafiya da take fama da shi, a yanzu haka jini ne yake zuba ta bakinta da hanci; saboda dama tana fama da wani ciwo mai suna Sinus, wanda ko kadan ba a taba yi mata magani ba a cikin shekaru biyar din da suka wuce.

A karshen watan Disamba an ba wasu Likitoci damar ganin su. Wadannan Likitocin sun bukaci a yi wasu gwaje-gwaje. Daga cikin gwaje-gwajen akwai wadanda dole sai an fita da su zuwa asibiti, amma shugabannin gidan yarin suka hana; a cewarsu sai kotu ta amince da hakan.

A ranar 24 ga watan Fabrairu, 2020, kotu ta ba su umurnin da su bari a yi musu duk abin da ya dace na magani. A ranar 26 ga Fabrairun 2020 Likitocin sun sake bukatar a yi wadannan gwaje-gwajen, kamar yadda suka bukata a baya; inda muka yi iya kokarinmu don ganin hakan ya faru.

Bayan makonni na shirye-shirye, da alkawura don ganin Likita da ma asibiti; da ma wasu shirye-shirye da muka yi da Shugaban gidan yari na jihar Kaduna, hakarmu ta kasa cimma ruwa, saboda shugabannin gidan yarin sun sake kawo mana cikas kamar yadda suka yi a baya.

Daya daga cikin Likitocin mahaifana, wanda shi ne zai yi gwaje-gwajen; da ma kuma shi kadai ne aka bari ya dinga duba mahaifana, ya shaida mana cewa, shugabannin gidan yarin sun bukaci da shi da sauran likitocin su rubuta bukata a rubuce, wacce a cewarsu za a kai Abuja, domin neman amincewa daga sama.

Don haka a cewarsu, dole ne mu zauna da babban Likitan gidan yarin jihar Kaduna, da kuma Likitan da yake wakiltar jihar Kaduna; a duk sad da suke da lokacin mu zauna da su din. Daga nan sai mu sake bin matakan da muka dauka a tsawon makonni uku, don sake sanya lokacin da za a gudanar da gwaje-gwajen a lokacin da ya yi musu.

Sannan sun shaidawa Likitan cewa, ba a yarda a gudanar da wadannan shirye-shiryen tare da wani Lauya ba. Mu’azu Dan Musa, wanda shi ne Shugaban gidan yarin jihar Kaduna, ya bayyana cewa muddin aka yi kokarin sanya Lauya a dukkan shirye-shiryen; to kamar an yi aikin banza ne, don kuwa a cewarsa in aka yi hakan, komai ya rushe ke nan. Wato ma’ana ba za su sake bari Likitoci su duba mahaifana ba.

Daga Muhammad Ibraheem Zakzaky

13/03/2020.