AlmizanAlmizan logo
Jum'a 17 ga Rabi'ussani, 1440 Bugu na 1380 ISSN 1595-4474

Labaran Harka Islamiyyah

An yi min duka saboda na yi ‘Free Zakzaky’ a ofishin ’yan sanda a Abuja -Adamu Yaro Damaturu

Daga Saifullahi M. Kabir


Imam Aliyu

HANNUN WAHABIYAWA A KISAN-KIYASHIN ZARIYA

Waki’ar Zariya ta auku ne da nufin kawar da Shaikh Ibraheem Zakzaky da Da’awarsa baki-daya. Don haka ma tun kafin aukuwarta da kuma abubuwan da suka biyo baya, sun nuna balo-balo cewa akwai cikakkiyar gudummawar wadanda ake kira Wahabiyawa, wato akwai hannun tushen Wahabiyanci, gidan Sarautar Saudi-Arebiya a cikin duk abin da ya faru.

A nan, zan so mu dogara ga wasu abubuwa guda biyar da suka auku kafin, da kuma bayan kisan-kiyashin na Zariya, kamar haka:

1- Rahoton WISAL TV a kan yaduwar Shi’a a Nijeriya.

2- Kashedin Shekau ga Shaikh Zakzaky, da kuma kai mana hari da sunan Boko Haram.

3- Waki’ar Zariya da yabawar Sarkin Saudiyyah.

4- Rahoton AL’ARABIYYA a yayin zuwan Buhari Katar.

5- Rahoton DW na bayanin MBS a kan dakile tasirin Iran a Afirka.

6- Gudummawar Malaman Wahabiyawa/Izala a kan waki’ar.

RAHOTON TASHAR WISAL TV

Watanni kamar uku kafin aukuwar waki’ar Zariya, a cikin watan Satumbar 2015, wani gidan TV mai suna Wisal, mallakin kasar Saudi-Arebiya, sun yi wani ‘documentary’ inda a cikin sa suka nuna hadarin da ke fuskantar Nijeriya na yaduwar Shi’anci da tasirin Iran a tsakanin matasa, ta hannun Shaikh Ibraheem Zakzaky. Inda a karshe suka nuna takaici ga yadda aka kyale hakan na faruwa a kasar da tafi ko’ina girma da tattalin arziki a nahiyar Afirka.

Rahoton ya bayyana cewa: “A duk duniya, a yanzu babu wata kasa mafi hadari kamar Nijeriya, saboda yadda wata sabuwar fahimta ke yaduwa har ta mamaye Jihohi hudu, wadda a cikin su akwai masu wannan akidar kimanin mutane miliyan 25.”

Suka ce: “Wannan cutar da ta bulla a Nijeriya ita ce Shi’a, wacce take yaduwa a tsakanin matasa, wadanda suke makarantun boko suna karantar ilimin likitanci, Kanikanci da wasu fannonin na ilimin boko, wanda kuma ana daukar nauyinsu su je su kware a fannoni daban-daban. Wannan ya sa da yawan matasan ba su san ilimin addini ba. Don haka cutar Shi’anci ke yaduwa da gaggawa a tsakanin matasan Nijeriya.”

Suka ci gaba da cewa: “Wani matashi mai suna Ibraheem Yaqoub Zakzaky ne ya buya a bayan wasu abubuwa, kamar kokarin ’yanto Masallacin Kudus daga hannun Yahudawa da goyon bayan raunanan al’ummar da ake zalunta, yana yaudarar mutanen Nijeriya zuwa ga shiga wannan akidar ta Shi’anci.”

Suka ce: “Malamin, wanda aka san shi a matsayin dan tawaye, ana gayyatar sa ya je Iran don a kara masa ilimi a kan akidar Shi’a. Tsayuwarsa wajen yi wa Shi’anci aiki ya sa shi da mabiyansa sun kai ga suna shirya wasu Muzaharori kamar na Kudus da Ashura. Ya samu nasarar yada wannan cutar ne ta hanyar yin abin da ake kira TAKIYYA, wanda hakan ne ya sa jahilai suke bin sa. Da’awarsa ta fara shahara ne a shekarun tamaninoni (1980s), ta kuma ci gaba da yaduwa a 1990s. Abin da ya fi bata rai shi ne yadda Malamai suka kyale, suka yi shiru a yayin da wannan akidar mai hadari take ci gaba da yaduwa.”

Rahoton na Wisal ya ce: “Zakzaky din, ya yi fice a harkokin diflomasiyya, ta kai ga yana tura dalibai zuwa Jami’ar Tehran a Iran su yi karatu su kware a fannoni, har ma sun fara dawowa Nijeriya suna yada Shi’anci a tsakanin mutane.”

Suka ce: “Suna da wata Jarida da ake kira ALMIZAN, wacce ake buga ta da Hausa, wacce take yaduwa a cikin mutane sosai. Tana taimakawa wajen kara yaduwar Shi’anci. Kuma suna da Website na Hausa da Turanci, wanda suke yada manufofinsu. Kuma suna sayen lokaci a gidajen rediyo da talabijin da jaridu, don su yada manufofinsu ga al’umma. Wannan ne ya ba su damar samun alaka da kyakkyawar fahimta da masu bin Darikun Sufaye, suke haduwa don su fuskanci Ahlus Sunnah.”

Bayan kare rahoton, sai suka saka hira da wani mutum mai suna Dakta Muhammad al-Mubarak, inda yake sharhi a kan abin da aka fada. A ciki yake cewa: “A shekarar 1979, shekarar da Khumaini ya yi juyin-juya-hali, babu Shi’a ko daya a Afrika. Sam ba su san Shi’a ba kwata-kwata. Afirka nahiyar Musulmi ne. Eh, akwai wasu kasashe da mafiya yawan mutanen cikin su Musulmi ne, akwai kuma wasu da kadan ne Musulmi din, amma Shi’a, sam ba a san Shi’a ba a nahiyar baki daya. Haka nan abin yake a da yawa daga kasashen Musulmi, kamar Indinosia.”

Al-Mubarak ya ce: “Amma bayan juyin Khumaini a 1979, sai aka fara aikin yada akidar Shi’anci zuwa kasashe daban-daban. Za mu iya gani yanzu, abin mamaki, Shi’a ta mamaye mafi girman kasashen Afirka a yawan mutane da tattalin arziki. Yanzu muna jin hauhawar farashin mabiya Shi’a a Nijeriya.”

Wannan rahoton, wanda muke da ‘video clip’ dinsa, in mutum ya nazarce shi, zai ga cewa Saudiyya tana jin takaicin yaduwar da’awar Shaikh Ibraheem Zakzaky na Harkar Musulunci da yake yi a tsakanin matasan Nijeriya, wanda kuma suna wa Da’awar kallon Shi’anci ne, saboda ganin cewa Jagoran Harkar da mafiya yawan mabiyansa suna bin tafarkin Ahlul Baiti (AS) ne.

Don haka sun nuna a cikin rahoton cewa, akwai bukatar taka wa yaduwar Shi’ancin birki ta kowane hali, a yayin da suke kokarin nuna cewa Harkar Musulunci din, ko abin da suke kira Shi’anci, na daga cikin tasirin juyin-juya-halin Musulunci ta Iran, wacce Amurka, Isra’ila da ita Saudi-Arebiya din suke tsananin gaba da shi.

KASHEDIN SHEKAU DA KAWO HARIN BOM A KAN ’YAN’UWA

Ba a jima da yin wannan rahoton na Saudiyya a kan takaicinsu na yaduwar Shi’anci a Nijeriya ba, kamar wata guda bayan hakan, a karshen watan Oktoban 2015, sai ga Shugaban wata kungiyar Wahabiyawa da suke kai hare-haren ta’addanci a Arewacin Nijeriya da aka saka wa suna Boko Haram, mai suna Abubakar Shekau yana kashedi ga Shaikh Zakzaky da almajiransa a kan su gaggauta tuba daga Shi’anci.

A cikin garejeren bidiyon na Shekau, ya furta cewa: “’Yan Kaduna! Kai Zakzaky! ’Yan Shi’a, masu TAKIYYA! Ku tuba!”

Ku lura da wasu abubuwa a cikin wannan garejeriyar maganar ta Shekau, ta yadda yake kiran sunan Shaikh Zakzaky gatsai yana cewa ya tuba, alhali a baya Shekau bai taba kama sunan wani Malamin addini a kasar nan ya yi masa kashedi ba.

Kuma ku lura da yadda ya ambaci kalmar TAKIYYA, wannan kalmar da rahoton Wisal TV ya jaddada, cewa wai Shaikh Zakzaky yana yaudarar matasa ne ta hanyar yin TAKIYYA. Bai zama abin la’akari ba, a yayin da kalmomin Shekau suka dace da na Saudiyya?

To, bayan wannan kashedin kuma da wata guda, har ila yau, a karshen watan Nuwambar 2015, sai aka kawo wa ’yan’uwa Musulmi almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky harin bom a yayin da suke kan hanyarsu na Tattakin juyayin Arba’in din Imam Husaini (AS), daga Kano sun nufo Zariya.

Harin bom din da ya ci rayukan almajiran Shaikh Zakzaky kusan mutum 25, an yi nasarar dakile tashin na mutum daya, a yayin da na guda daya ne ya tashi ya kashe wannan adadin. Kwatam sai aka ji a kafafen yada labarai, wai Kungiyar Boko Haram ta dauki alhakin kawo wannan harin.

Sai ya zama kamar wannan ne ma’anar kashedin Shekau ga Shaikh Zakzaky da ’yan Shi’a, a yayin da yake cewa su tuba. Da ba su tuba ba, suka ci gaba da Shi’anci, ga shi ya kawo masu harin kunar bakin wake ma.

Sai dai Jagoran Harkar Musulunci a Nijeriya, Shaikh Ibraheem Zakzaky, a yayin da yake jawabi a wajen rufe taron Arba’in, kwana uku bayan aukuwar harin, ya bayyana cewa ba kowa ke da alhakin kawo harin ba face jami’an tsaron Nijeriya, wadanda dama suke da alhakin duk abubuwan da ke faruwa a kasar nan da sunan rashin tsaro.

Bayan Shaikh Zakzaky ya dora alhakin harin a kan jami’an tsaron, bisa dalilan da ya bayyana a cikin jawabinsa na ranar Arba’in din, wanda aka gudanar a ranar Alhamis, 3 ga watan Disambar 2015, ba a samu wata murya daga bangaren gwamnati ko jami’an tsaro da ta musanta zargin da Shaikh Zakzaky ya yi a wannan lokacin ba. Sai kawai martanin da sojoji suka bayar kwanaki tara bayan wannan jawabin, wanda shi ne ‘Kisan-Kiyashin Zariya’.

WAKI’AR ZARIYA DA YABAWAR SARKIN SAUDIYYA

Mun riga mun yi bayani a kan waki’ar Zariya tun a babin farko na wannan rubutun, kuma mun kawo yadda wata kafar yada labarai ta ‘Pars News Agency’ ta ruwaito a ranar 16/12/2015, kwanaki biyu bayan gama waki’ar ta Zariya, cewa Sarkin Saudiyya, Salman Bin Abdul’azeez ya kira Shugaban kasar Nijeriya, Buhari ya taya shi murna a kan aikin da ya yi na murkushe Harkar Musulunci da sunan wai fada da ta’addanci.

Sarki Salman, ya bayyana kisan-kiyashin Zariya a matsayin yaki da ta’addanci da murkushe ’yan ta’adda. Wanda a rahoton Wisal TV da ya gabata za mu iya gane suna nufin tasirin Iran a Afirka da yaduwar Shi’anci ne suke nufi da Ta’addancin, kamar yadda kuma za mu gani a gaba.

RAHOTON AL’ARABIYYA TV A YAYIN ZUWAN BUHARI KATAR

Kwatsam sai ga tashar talabijin ta AL-ARABIYYA ta yi wani rahoto a kan ziyarar da Shugaban kasar Nijeriya Muhammadu Buhari ya kai Katar, wanda suka dora ‘video’ din rahoton a shafin gidan talabijin din a ranar Talata 1/03/16. Suka yi masa take da “Sabon gargadi daga Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari, game da masu yada busharar Shi’anci a Afrika.”

Suka ce: “Buhari ya hangi wani hatsari da ke tunkarowa na yaduwar wata akida mai hatsari, wacce manufarta ita ce, tayar da fitina, raba kan al’umma da kawo hatsaniya.”

Rahoton ya ci gaba da cewa: “Nijeriya wacce take Cibiyar Afrika; ta fi kowace kasa a Nahiyar ta Afirka yawan mutane, wacce ake kiyasta Musulmin cikin ta sun kai miliyan 85. Daga cikin su akwai kasa da miliyan 10 ’yan Shi'a, sauran kuma Musulmi ne mabiya Sunnah.”

Su ci gaba da cewa: “Shi’a ta yadu daga baya (a Nijeriya) ta hannun Ibraheem El-Zakzaky, wanda Iran ta nasabta shi a matsayin Wakilin Hizbullah a Nijeriya. Jami’an tsaro sun kama shi ne a watan Disambar shekarar da ta gabata; bayan sun tuhume shi da yunkurin kashe Shugaban Hafsan Sojojin Nigeria, a lokacin da yake kan hanyarsa ta wucewa Zariya; wacce ake ganin ta a matsayin wuri mafi muhimmanci ga mabiya Shi'a da suke zaune a Arewacin Nijeriya, kuma nan ne mazaunin Shugabanta da ke samun goyon bayan Iran.”

A nan sai suka sanya bidiyon Buhari yana cewa: “Arangamar (ta Zariya) faru ne a lokacin da ya yi kokarin dakatar da tawagar Hafsan-Hafsoshin sojojin Nijeriya. Daga baya Shi’a ta yi karfi. Kuma muna da masaniyar cewa tana samun karfafa da abin da ya yi kama da haka daga Iran”.

Sannan suka ci gaba da sharhi da cewa: “Shugabannin siyasa da sojojin Nijeriya ra’ayinsu ya zo daya a kan cewa Shi’a a Nijeriya - wacce take da goyon bayan Iran – ra’ayinsu daya da kungiyar Boko Haram, wacce ta yi wa Da’esh bai’a.”

Suka ce: “Dalilai da dama ne suka sabbaba yaduwar Shi’a a Nijeriya. Daga cikin su akwai talauci, jahilci, ba da tallafin karatu, (da Shi'a suke badawa) da kuma yaudarar mutane ta hanyar taken ’yanto Masallacin Al-Aksa. Wadannan dalilan ne ke sa mutane tudadar shiga wannan Mazhabar da Iran ke karfafawa.”

Mai karatu, ka lura da yadda bayanan mutanen nan ke zuwa a tare; yaduwar Shi’anci, tasirin Iran, goyon bayan Iran, da batun TAKIYYA, ko taimakon raunana. Wadannan sune duk abin da suke kokarin su nuna cewa Harkar Musulunci na samu don habakar ta. Kuma shi ne abin da suke kokarin a dakile.

Kuma har ila yau, kalaman Buhari ya nuna maka kai tsaye mai suka yi a Zariya, sun auka wa Shaikh Zakzaky ne da almajiransa, don su dakile yaduwar tasirin Iran a Afirka, musamman a Nijeriya. Amma ba wani abu wai tare hanya ne ya sabbaba kashe mutum 1,000, da kama Shaikh Zakzaky a daure tsawon shekaru da rauni a jikinsa ba, kamar yadda za mu ji daga bakin Yariman Saudiyya a gaba.

RAHOTON DW NA BAYANIN BIN SALMAN KAN DAKILE TASIRIN IRAN A AFIRKA

Sai aka zo, a ranar 24 ga watan Afrilun 2018, sashen Hausa na gidan rediyon DW da ke Jamus ya fitar da rahoton murya, inda Yariman Saudiyya, Muhammad Bin Salman ya furta a sarari cewa su ke da alhakin harin da aka kai wa Shaikh Zakzaky a kokarinsu na dakile karfi da tasirin Iran a Afirka!

Rahoton na DW, ya bayyana cewa: “A wata hira da jaridar TIMES ta Amurka ta yi da Yarima mai jiran gado na Saudiyya, Muhammad Bin Salman ya ce kasarsa ta kai gouro-ta-kai-mari a Afirka don ganin ta rage tasirin Iran a nahiyar, yadda ya zuwa yanzu ta yi nasarar karya karfin kasar ta Iran a Afirka da kimanin kaso 95 cikin 100.”

A shafinsu na sakar sama, DW, sun rubuta a karkashin wani hoto da suka saka, cewa: “Muhammad Bin Salman ya ce kasarsa (Saudi-Arebiya) ce ta dakushe karfin Ibraheem al-Zakzaky a Nijeriya”

Sannan rahoton nasu ya ci gaba da cewa: “Dakta Zayeed Al-Amri, mamba a Cibiyar tsara dabarun mulki da tunkarar matsaloli na kasar ta Saudiyya, ya yi karin bayani kan manufar Yariman, inda yake cewa ‘abin da Yarima ke nufi a nan shi ne tun bayan da ya ayyana shirinsa na tunkarar makiya, Saudiya ta yi nasarar karya tanadin Iran a Yemen da Somaliya da Djibouti da Sudan, kamar yadda ta lalata yunkurinta na kafa makamanciyar kungiyar Hizbollah a Nijeriya da hana Ibraheem Zakzaky yin juyin mulki a kasar.”

Kafar ta DW, ta kuma ruwaito Dakta Amani al-Taweel ta Cibiyar bincike na Al-Ahram a Masar, inda take cewa: “A gaskiya Saudiyya ba abin da ya fi damunta tamkar yada akidar Wahabiyyanci a Afirka fiye da kulla huldar kasuwanci da alakar diflomasiyya ta ban gishiri, in ba ka manda.”

A wannan rahoton, Muhammad Bin Salman da sauran masu sharhi sun bayyana karara dalilin kisan kiyashin Zariya, cewa kwangila ce ta gidan Sarautar Saudiyya zuwa ga Shugaban Nijeriya da jami’an tsaronta a kan su dakile mata Shaikh Zakzaky da abin da suke kira Shi’anci, a kokarinsu na dakile tasirin Iran a Afirka da kuma karfafar yaduwar akidarsu ta Wahabiyyanci.

GUDUMMAWAR MALAMAN WAHABIYAWA A KAN WAKI’AR

Ya gabata tun a kashi na biyu na wannan jerin rubutun, na kawo yadda Malaman Wahabiyyawa suka rika zame-zame da gwamnati da kuma yin wasu kalamai na nuna farin cikinsu kafin da kuma musamman ma bayan abin da ya faru na kashe wadanda suke kira ’yan Shi’a fiye da 1,000 a Zariya.

Mun kawo yadda a ranar Asabar, 19/12/2015 wasu daga cikin Gwamnonin Arewa, karkashin Kashim Shettima, suka gabatar da zama a Kaduna, inda suka tattauna yadda za su bullowa taka wa Harkar Musulunci burki a Jihohinsu.

Da kuma zaman Kungiyar Limamai da Malamai na Jihar Kaduna a ranar 28/12/2015 da suka gana da Nasiru El-Rufa’i, inda suka bayyana goyon bayansu a kan fadan da yake da ’yan Shi’a a Jihar tasa. Suka kuma bayyana masa cewa hakan da yake yi wani aiki ne da addinin Musulunci ke maraba da shi.

Mun kuwa kawo yadda a 14 ga Junairun 2016, shi ma GOC I Division, Manjo-Janar Adeniyi Oyebade, ya gana da wasu Malaman Wahabiyawa da Limamansu, ya yi masu bayani a kan shirin jami’an tsaro a kan Shi’a da kuma gudummawar da ake bukata daga Malaman, har ya ba su kyautar Naira dubu 500 su raba.

Mun kawo kuma inda a ranar 21/12/2015, Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi; daya daga cikin masu ra’ayin Wahabiyanci ya yi jawabi, inda yake yaba wa sojoji a kan abin da suka yi, da sunan hakan taimakon Sunnah ne da magance masu zagin Sahabbai.

Kungiyar Izala, musamman ta bakin shugabanninta, Shaikh Sani Yahaya Jingre, Shaikh Abdullahi Bala Lau da Shaikh Kabiru Gombe sun yi ta wa’azozi suna masu murna da abin da aka yi a Zariya.

Wani abu da ban kawo ba a baya shi ne bayanin daya daga cikin Malaman Izala, Shaikh Gero Argungun ya yi a fadar Sarkin Yawuri, Dakta Muhammad Zayyanu Abdullahi, kwanaki kadan bayan kisan kiyashin na Zariya, inda bayan ya gama yin karairayi ga Shi’a da Shi’anci a karshe ya shiga bayyana alakar su da Shugaban kasa, Muhammadu Buhari wajen kokarin magance Shi’anci a Nijeriya.

A cikin ‘audio’ din jawabin nasa, Shaikh Gero ya bayyana cewa: “Iran komai suna iya yi, shi ya sa da suka gayyaci Shugaban kasar Nijeriya, Muhammadu Buhari, muka yi ‘meeting’ tare da shi, muka fada masa ya yi hattara da wadannan mutane. Muka fada masa ka ji, ka ji ka ji (dangane da Shi’a). Ya ce to zai lura. Muka ce to in kuma ka je Iran kar ka sa bakaken kaya, don yana cikin hanyar yaudararsu, za su yi maka hoto su yada wa duniya cewa ai kai mamba ne daga cikin su.”

Gero ya ce: “Duk alkawuran da ya yi mana, da ya je Iran ya cika su, kun gan shi a ‘setilayit’ cikin fararen kaya.” Ya ci gaba da cewa: “Da (Buhari) ya dawo ya kira wasu daga cikin mu da muka yi ‘meeting’ da shi (kan ya tafi), ni ban samu zuwa ba. Ya ce duk abin da kuka fada mana kun rage, ni na je Iran na gani da idona, Wallahi babu Musulunci.”

Mai karatu, ba za mu tambayi kanmu cewa mene ne damuwar Shugaban kasar Nijeriya, kasar da ba ruwanta da Allah da addini, ba ruwanta da me kake bautawa a ka’idarta, da akidar Shi’anci ko Mazhabar Ahlul Baiti (AS)?

Kuma hatta taron da Buhari ya je Iran taro ne na wasu kasashe guda 8 masu arzikin man fetur a duniya ne. Ko da yake ya gana da Shugaban addini na kasar Iran, Sayyid Khamene’i, amma sam ganawarsu ba ta da alaka da Musulunci ko Shi’anci, face ya ba shi shawarwari ne a kan muhimmancin dogaro-da-kai da nisantar kasashe masu yin mulkin-mallaka.

KARKAREWA

Daga abin da ya bayyana ga mai karatu, zai fahimci cewa tabbas waki’ar Zariya da aka dira a kan Shaikh Zakzaky da almajiransa, wani yunkuri ne na kokarin kawar da Harkar Musulunci da abin da suka kira Shi’anci, ko tasirin Iran a Afirka. Ya fi karfin wani wasan kwaikwayo na cewa, wai an tare hanya ne kawai sai hakan ya auku, kuma har yau bai kawo karshe ba!

Don haka ne ma duk abin da suka yi na kokarin ganin bayan Harkar ta Musulunci abu ya ci tura, har yanzu ba su hakura ba. Suna ci gaba da tsare daruruwan almajiran Shaikh Zakzaky, da shi kansa Shaikh din da maidakinsa, duk da cewa babbar Kotun Tarayya a Abuja ta ba da umurnin a sake shi.

Amma sun take dokar, yanzu ma sun komar da shi Kaduna ne sun gurfanar da shi a gaban wata kotu suna masa haramtacciyar shari’a, wacce insha Allah a rubutu na gaba za mu tashi da bayanin yadda aka dawo da Shaikh Zakzaky Kaduna daga Abuja, zuwa yadda ake gudanar da haramtacciyar shari’arsa a wata babbar kotu da ke garin Kaduna din.