AlmizanAlmizan logo
Jum'a 17 ga Rabi'ussani, 1440 Bugu na 1380 ISSN 1595-4474

Labaran Harka Islamiyyah

LITTAFIN KISAN KIYASHIN ZARIYA


Maulid Sayyada Fatima

Sunan littafi: Kisan kiyashin Zariya.

Yawan shafuka: 474

Shekarar bugu: 2018

Kamfani: Mizani Publictions

Daya daga cikin hakkin da ke kan ’yan’uwa a kan waki’ar Zariya ta ranekun 18 ga watan Disamba na 2015 shi ne adana tarihi da taskace shi da kuma bayyana shi. Domin shi tarihi idan ba a yi maza aka tattara shi ba, aka rubuta tare da adana shi mantawa ake yi, ko kuma ya gurbata. Ko mai shi ya canza ra’ayi ya ki fadar sa.

Wani abin jinjina da kwarewa wanda ’yan Al-mizan suka yi shi ne, aika-aikan Zariya na faruwa, duk fitowar Al-mizan, sai an samu wani Ganau an yi hira da shi ya fadi abin da ya gani da idonsa ko ya ji da kunnensa, kamar in wani tashin bom ne ko harbin bindiga.

Labarin da zafi-zafinsa, wanda ya ga lamarin zai kawo shi dalla-dalla kuma daki-daki. A lokacin ba wata mantuwar wani abu da ta shigo masa na daga abin da yafaru. Al-mizan ta zama kamar wani hoto na bidiyo na kallon abin da ya gudana a Zariya.

Dan tsakanin lokacin. Al-mizan ta zama wata amarya, kowa ya kagara wani sati ya zo ya karanta da wa aka yi hira, me kuma ya gani? Ta kuma rika tafasa zukatan ’yan’uwa da kara tausaya wa ’yan’uwan da ta’addancin ya rutsa da su.

Wadannan hirarrakin sun kore duk wata jita-jita da algaitar Shaidan da makiya suka so su yi amfani da shi don kara rikita ’yan’uwa. ’Yan’uwa da yawa sun yi kokarin rika adana fitowar AL-MIZAN din don tarihi da tuna abin da ya faru.

Jaridar AL-MIZAN ta saba tattara bayanai don taskace tarihi, wanda a baya sun yi wasu littattafai wadanda suka shafi. Haka sun buga littafai da yawa na jawaban Sayyid Zakzaky (H) da tarihin Malam (H) da abin da ya faru a waki’ar Abacha.

Duk a littafan nan, wannan littafin na Kisan Kiyashin Zariya yana daga cikin littafi mafi amfani a Harkar Musulunci. Littafi ne da ya ba da bayanin wani ta’addanci wanda ba a taba irin sa ba a tarihin Najeriya, kuma daga wadanda suka gani, ba ’yan wane ya ji ga wane ba.

Littafi ne wanda ya kumshi wasu bayanai na abin da ya faru daga wadanda suka tsira bisa kudurar Allah, ba domin wadanda suka nufe su ba sun so su rayu. Za ka ji labarin da za ka yi tsammanin mummunan mafarki ne; amma da gaske ne ya faru.

Littafin ba ka iya ci gaba da karanta shi, ba tare da kana tsayawa ba kana mai da numfashi. Wani kuma sai ya koka, wani na zuci, wani na hawaye, wani ko har rurawa, kamar yadda ya rika faruwa ga wasu da suna bin hirarrakin da aka rika bugawa a Al-mizan.

Littafin wani kundi ne na tarihi, wanda aka tattara a kan kisan kiyashi, rashin imani da ta’addancin Zariya. Dama ce ga wanda ya rasa wasu daga cikin jaridun Al-mizan, yanzu ga shi an tattara masa duka hirar, sai kawai ya kai zuciya nesa, ya dake, ya bi su daki-daki, yana karantawa.

Littafi ne da ya kamata duk dan’uwa ya mallaki akalla hudu, ya ajiye daya a gida don kafa hujja, ukun kuma ya duba wasu masu tasiri da muhimmanci wadanda za su karanta ya ba su domin su karaanta su ji abin da ya faru daga wadanda suka tsira.

Yana da kyau a shiga da littafin a bitar karatuttukanmu. A kuma yada shi a cikin al’umma domin yanke masu uzuri, su karanta da kansu.

Littafin ya kumshi babi da ke maganar ana cikin halin ba a san me ake ciki ba a lokacin waki’ar. Gidan rediyon BBC ya tattauna da Malam Zakzaky (H). Me Malam ya fada wa BBC? Soja na ruwan wuta a Husainiyya da Gyallesu, wani mutumin kasar Iran ya bugo wa Malam (H) waya. Me ya shaida masa? Duk wannan cikakkiyar hirar, suna a cikin babin farko na littafin. Sai ka samu za ka ji ya aka yi?

Shaikh Kasimu Umar Sakkwato, wanda yanzu yake jinyar harbin da aka yi masa a kan muzaharar a saki Malam (H), kowa ya ga hotonsa a safiyar da aka yi waki’ar tare da ’ya’yan Malam (H). Ya aka yi ya tsira? Kusan duk wanda aka dauki hotonsu tare da shi sun yi shahada, shi ya aka yi ya tsallake? An yi hira da shi wanda ke cikin littafin.

Daya daga cikin ’ya’yan Malam Zakzaky (H) da suka rage a duniya ita ce Sayyada Suhaila; gabanta duk abin da ya faru, ya faru. Me ta gani, me ta ji wadanne ne kalaman Malam (H) na kusan karshe kafin soja su auka wa gidan bayan sun kammala ganin bayan kowa?

Daga cikin ’yan’uwa mata wadanda Allah ya jarabta da wannan gagarumar jarabawa ita ce Hajiya Jummai Karofi, an kashe ’ya’yanta, kuma har yanzu tana jinyar harbin da aka yi mata. Ta ga abin da ta gani, kuma ta tsira, ba ta rasa ranta ba a wani tsari da haka Allah ya so, kuma shi ya san hikimar da ke cikin hakan. A cikin littafin akwai cikakkiyar tattaunawa da ita.

A littafin an buga hirar da aka yi da ’yan uwa mata da maza har guda ashirin da biyar wadanda abin ya rutsa da su, kuma kusan dukkaninsu ba wanda bai rasa wani na kusa da shi ba. A wannan babin za ka ji labarai masu daga hankali da ta da hankali da motsa zuciya. Gargadina, wasu labaran kar ka karanta su da dare, don za su hana ka barci.

A cikin littafin akwai fassarar Rahoton binciken Amnesty International, da fassarar bayanin da Sakataren gwamnatin Kaduna ya yi a gaban hukumar bincike ta JCI, wanda ya yi bayanin yadda suka binne ’yan’uwa 347 a wani katon kabari da suka gina cikin dare.

Marigayi Malam Haruna Shelleng ya yi wani tsokaci a kan waki’ar kafin ya rasu. An kawo rubutun da ya yi, wanda a rubutun akwai ilmi da basira a ciki. Me ya rubuta?

Bayan waki’ar, Shaikh Yakub Yahaya ya yi taron manema labarai yana fada wa duniya halin da ’yan’uwa suke a ciki da abin da aka yi a Zariya. An dauko daya daga cikin hirar saboda muhimmancinta an sanya. A littafin me ya ce? Wadanne shawarwari ya ba ’yan’uwa a lokacin wadanne kuma ya bai wa gwamnati? Ka samu littafin ka ji zancen hikima daga bakin wadanda suka sallamar da rayuwarsu.

Na san wannan zai zama kamar bugun farko ne, a wani bugun wasu sabbin abubuwan za su kara fitowa, sabbin bayanai, sabbin hirarraki, sabbin abin boye da ya fito fili.

An buga littafin ne domin samar wa Al-mizan Gidauniya wadda za ta samu abin da za ta biya bassussukan da ke kanta, ta kuma sauke nauyin da ya doru kanta, ta kuma ci gaba da ilmantar da musulmi, kamar yadda kirarinta yake, “jarida domin karuwar musulmi.”

Yana da kyau duk wani dan’uwa ya sayi littafin nan a saye na kaddamarwa, ba saye na guda daya domin karatu ba, domin manufar aikin alherin da za a yi da kudin shi ne ci gaba da kafuwa da dorewa da kuma fitowar jaridar AL-MIZAN tare da kara ingantarta. Da fata da kuma rokon ’yan’uwa za su yi gagarumin hobbasa. Allah ya taimaka.