AlmizanAlmizan logo
Jum'a 17 ga Rabi'ussani, 1440 Bugu na 1380 ISSN 1595-4474

Labaran Harka Islamiyyah

>‘Jami’an tsaro sun yi ta yunkurin harbe mu a Abuja’

Daga Aliyu Saleh


Maulid Sayyada Fatima

Abdulmalik Musa Gangarawa Malumfashi, na daya daga cikin wadanda jami’an tsaro suka kama a yayin Tattakin Yaumul Arba’in na Imam Husaini na bana da aka yi a Abuja. A yayin zantawar da Wakilinmu Zahraddeen Sani ya yi da shi, ya bayyana yadda jami’an tsaro suka yi ta dukan sa a ka da katako, auna su da bindiga, zaman su a kurkuku da kuma dalilin da ya sanya ya fahimci kiran Sayyid Zakzaky. Ga dai yadda hirar tamu ta kasance kamar haka:

ALMIZAN: Ka bayyana wa masu karatu sunanka.

ABDULMALIK MUSA: Sunana Abdulmalik Musa, Gangarawa Malumfashi.

ALMIZAN: Shekaru fa?

ABDULMALIK MUSA: Shekaruna 20 da haihuwa a duniya.

ALMIZAN: Malam Abdulmalik kana daya daga cikin wadanda waki’ar Tattakin Yaumul Arba’in ta bana a Abuja ta rutsa da kai, wane bayani za ka yi wa masu karatu?

ABDULMALIK MUSA: Kasantuwar ganin mun makara zuwa halartar Tattakin ta bangaren da ya kamata mu tashi, saboda haka sai muka tsaya muka bi ayarin da suka tashi daga Maraba.

Mun tafi lafiya ana ta gudanar da Tattaki lafiya, ga ma’aikata jami’an tsaro suna ta kara-kaina a bakin hanya, ana ta wucewa, ba ruwan kowa da su, kwatsam sai ga wadansu jami’an tsaro sun zo wucewa a bisa “bike”. Suna wucewa sai ga wadansu ’yan sanda da Sojoji wadanda suna wucewa gabanmu kawai sai suka fara bude mana wuta da harsashi mai rai.

Sun yi ta harbin ’yan’uwa babu kakkautawa, su kuma ’yan’uwa suna ta kokarin dauke duk wanda aka harba ana dora shi a bisa mashin ana barin wurin da shi. Kai da abin ya ta’azzara ma dai har masu mashinan suka daina daukar ’yan’uwa.

ALMIZAN: Da yake kana daga cikin wadanda jami’an tsaro suka kama, ta yaya suka kama ka, kuma me ya wakana bayan nan?

ABDULMALIK MUSA: To, a lokacin da suna ta harbe-harbe, bayan su Malam Abbari sun shiga mota sun tafi bayan an yi addu’a an tashi. To, mu ma sai muka bar wurin muka tafi da nufin mu koma masaukinmu.

Ina cikin tafiya, sai na hangi wani yaro Buraza yana gudu, sai na bi shi na kamo shi don kada ya auka inda jami’an tsaron suke. Da na kamo shi, sai na tambaye shi a ina yake? Sai ya ce mani a Maraba yake, sai na ce masa, to ya yi hakuri ya kwantar da hankalinsa zan tafi da shi Marabar. Muna cikin tafiya sai kuma ga wadansu Sistoci, sai suka ce mani don Allah in tafi da su in fid da su daga wannan wurin. Muna ci gaba da tafiyarmu kawai, sai muka gamu da wadansu ’yan iskan gari dauke da adduna da itace suna neman ’yan’uwa su buge su.

Ganin haka sai muka tsai da mai Keke NAPEP, muka ce ya kai mu Maraba. Har ya dauke mu ya fara tafiya, sai ya ce mu sauka ya fasa, ba zai kai mu ba. Don haka sai muka ci gaba da tafiya a kasa, muka shiga wani lungu, sai muka hadu da wani Bayarabe, sai ya ce mana mu zo ya kai mu gidan wadansu Hausawa ’yan’uwanmu, sai mu boye a can. To, da na ji ya fadi haka, sai na ce wa sauran su jira a nan in gano lafiya da amincin wurin. Muna tafiya, sai na ga wurin da ya nuna mani kusa da wani bariki ne na Mopol, don haka sai na dawo baya na tasa wadannan ’yan’uwa muka ci gaba da tafiyarmu.

Bayan mun ci gaba da tafiya, sai muka samu wani mai mota ya dauke mu. Muna cikin tafiya, kawai sai muka hangi Sojoji suna bude wuta a gabanmu, don haka sai Direban ya ji tsoro ya yi kwana da motar. Muna cikin tafiyar kuma sai muka ci karo da ‘Gate’ na Sojoji, muka wuce ‘gate’ na 1, na 2, na 3, na 4, na 5, to ana 6 sai aka tsai da mu Sojojin suka ce mani ni ma dan Shaikh Zakzaky ne? Sai na ce masu shi ne. Nan take suka jawo ni suka ci gaba da duka na suna yi mani maganganu na izgilanci.

Sun yi ta duka na da katako a ka kamar za su fasa mani kai. Daga karshe suka tattara mu suka watsa a mota suka kai mu ‘Police Station’. Sun yi ta mugun gudu da mu a mota suna hawan kabarin Mai Tatsine da nufin su wurgo mu kasa, musamman ni da nake daga karshen motar, wanda ganin haka, sai wani dan’uwa ya rike min kafafu don kada su wurgo ni in fado kasa. Haka suka yi ta gudu na wauta har muka isa ‘Police Station’.

Da isar mu ’yan sanda suka zo suka zagaye mu, suka yi kukin da bindiga za su harbe mu. Ganin ba mu tsorata ba, sai suka shiga da mu cikin ‘Station’. A cikin ‘Station’ din ma sun yi ta nuna mu da bindiga kamar za su harbe mu. Daga bisani aka sanya mu a bayan kanta aka dauki ‘statement.’

A haka muka kwana. Mun roki su bar mu mu yi Sallah, amma suka hana mu. Haka nan kuma sun yi ta tambayar mu cewa; nawa ake ba mu muna zuwa garin Abuja, domin yin taro da kuma gudanar da Muzahara? Mun bayyana masu cewa ba kudi ake biyan mu ba, mu muke daukar dawainiyar kanmu. A inda suka ce karya muke yi, ai an ce Amurka, Saudiyya da kuma Iran ne suke turo mana da kudade.

Sun yi ta gaya mana maganganu na izgilanci, kuma sun ce mana tunda mun hana su zaman lafiya, to mu ma ba za su bar mu mu zauna lafiya ba. A inda muka ce masu, ai mu aka zalunta, kuma ’yancinmu muke nema, kuma lallai ba za mu daina shigowa Abuja ba har sai an sakar mana Jagora, Shaikh Zakzaky.

Bayan mun kwana a ‘Police Station’, sai aka kwashe mu aka kai mu ‘State CID’. Da aka isa da mu ‘State CID’ din, sai wasu ’yan’uwa suka bukaci a ba su ruwan sha saboda tsananin kishin ruwan da ke damun mu. Nan take wani Mopol ya taso kamar zai cinye mu, yana cewa; “Ba za a ba ku ruwan ba, sai dai kishin ruwan ya kashe ku”. Haka ya yi ta fada mana miyagun bakaken maganganu. Don haka sai na ce wa ’yan’uwan su yi hakuri su daina tambayar su ruwan shan, domin kuwa wanda ya ki ba ka ruwa ka yi Alwala, yaushe zai ba ka ruwa ka sha? Akwai wani dan sanda da ya tausaya mana ya ce mu bayar da kudi ya sawo mana ruwan. Da na ba shi Naira 200. Yana sawo ruwan sauran ’yan sandan suka kwace ruwan suka hana a ba mu ruwan.

Bayan wani dan lokaci a ranar, sai aka wuce da mu ofishin SARS. A nan jami’an tsaro na SARS sun ba mu ruwan sha mai sanyi, har da ma lemu suka ba Sistoci. A daidai lokacin da ake daukar ‘statement’ dinmu a ofishin SARS din, sai ga Mopol sun kara kawo wadansu ’yan’uwan.

Suna sauke su daga cikin mota, kawai sai suka ci gaba da dukan su da kotar bindiga kamar za su kashe su. Ganin haka sai tausayinsu ya kama mu. Nan take muka ci gaba da yin kabbara da sauti mai karfi. Jin haka sai Shugaban SARS ya fito ya hana Mopol dukan wadannan ’yan’uwan.

ALMIZAN: To, a nan ofishin SARS din ku kadai ne aka kawo aka tsare, ko kuwa?

ABDULMALIK MUSA: A’a ba mu kadai ba ne, domin kuwa nan ne ya zama kamar matattara, don kuwa duk ’yan’uwan da aka kamo daga karshe nan ake kawo su a ajiye. Lallai mun kai kimanin 400 a wurin nan.

ALMIZAN: To, su jami’an tsaro na SARS sun azabtar da ku, ko kuwa?

ABDULMALIK MUSA: Lallai jami’an tsaro na SARS ba su azabtar da mu ba, kuma har Sallah sun rinka bari muna yi.

ALMIZAN: Tsawon wane lokaci kuka dauka kuna tsare a hannun SARS?

ABDULMALIK MUSA: Kwananmu uku a wurin SARS, sannan aka kai mu kotu.

ALMIZAN: To, da aka kai ku kotun, wane laifi aka tuhume ku da aikatawa?

ABDULMALIK MUSA: An tuhume mu ne da laifin wai mun tare I.G na ’yan sanda za mu kwace masa makamai, kuma muna yin taro ba da izini ba. Ko da dai daga baya sun daina wannan zargi, sai suka dawo suna cewa sun kama mu da duwatsu, sanduna, adduna da kuma kwayoyi. Bayan dage shari’ar ne, sai aka kai mu kurkuku aka tsare mu.

ALMIZAN: To, ya zaman kurkukun ya kasance?

ABDULMALIK MUSA: Kwananmu uku a gidan kurkukun aka bayar da belin mu. Mun isa gidan kurkukun ne muna ta kabbara a cikin motocin da aka kai mu cikin su, kuma jami’an tsaron sun yi ta kokarin su hana mu yin kabbarar da muke yi, amma muka ki dainawa. Lallai mun yi tablig da kuma kyakkyawar mu’amala da mutanen da muka iske ana tsare da su a gidan Yarin. Sun rinka girmama mu, tare kuma da nuna bukatarsu ta mu rinka tunatar da su a kan sha’anin addini, kamar yadda sauran almajiran Shaikh Zakzaky suke yi masu a duk lokacin da aka kawo su gidan Yarin.

ALMIZAN: Yanzu dai kun fito bisa beli ne, shari’a na ci gaba da gudana ke nan?

ABDULMALIK MUSA: Eh, an sako mu ne bisa beli, shari’a na ci gaba da gudana, ’yan sanda na gabatar da shaidu.

ALMIZAN: Kafin wannan, waki’a ta taba rutsawa da kai?

ABDULMALIK MUSA: Waki’a ta taba rutsawa da ni a Kaduna, amma dai jami’an tsaro ba su taba kama ni ba.

ALMIZAN: Da yake azzalumai suna yin haka ne domin su tsorata a daina abin da ake yi, to ya ka tsorata kuwa?

ABDULMALIK MUSA: Ina!! Ai ba batun razana, ko tsorata. Ai ni kwarin gwiwa aka kara mani. Gwagwarmaya ba fashi. Yanzu na fara. Hatta su jami’an tsaron mun bayyana masu cewa, mun kosa su sake mu domin mu ci gaba da fitowa muna taka kwalta ta garin na Abuja, muna jaddada kiran a sako mana Abbanmu, Shaikh Zakzaky.

ALMIZAN: Akwai bayanin da ya bayyana cewa, ka fahimci Mazhabar Ahlul Baiti ne sakamakon karya da kazafin da ake yi wa ’yan Shi’a, mene ne gaskiyar wannan lamari?

ABDULMALIK MUSA: Tabbas wannan zance gaskiya ne. Na fahimci wannan kira na Shaikh Zakzaky ne sakamakon zalunci da karairayin da ake yi wa ’yan Shi’a na cewa suna zagin Sahabbai. Wai suna da Alkur’ani na daban. Wai suna auren Mutu’a da dai sauransu. Don haka sai na ce bari in kusance su domin in tantance gaskiyar lamari. Da na kusance su kuma sai na ga akasin kazafin da ake yi masu. Hakika ban gane dadin dandanon Addinin Musulunci da kuma izzarsa ba, sai da na zama dan Shi’a almajirin Shaikh Zakzaky.

ALMIZAN: Wane kira ko sako kake da shi, musamman ga ’yan’uwanka matasa?

ABDULMALIK MUSA: Kirana ga ’yan’uwana matasa shi ne mu gaskata alkawarin da muka yi wa Jagora cewa rayuwarmu fansa ce a gare shi. Mu bar gidajenmu, mu koma Abuja mu tare har sai an sako mana Jagoranmu, Shaikh Zakzaky.

ALMIZAN: Mun gode.

ABDULMALIK MUSA: Ni ma na gode, Allah ya ba mu sabati.