AlmizanAlmizan logo
Jum'a 17 ga Rabi'ussani, 1440 JBugu na 1380 ISSN 1595-4474

Rahotanni

An yi taron tunawa da shekara 1 na shahadar Shaikh Kasimu Umar

Daga Sulaiman musa Bodinga, Bala Bashar, Husaini Baba, Bilal Nasir Umar da Shehu Malami Illela


soji

Ranar Asabar din da ta gabata ne dubban ’yan'uwa musulmi almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky na sassa daban-daban na kasar nan, suka halarci gagarumin taron (zikira) cika shekara daya da shahadar Shaikh Kasimu Umar Sakkwato, wanda aka yi a filin kasuwar baje koli da ke unguwar Dambuwa a birnin Sakkwato.

Taron zikirar ya samu halarta manyan Malaman Harkar Musulunci da suka hada da Shaikh Abdullahi Ahmad Zango, Shaikh Abdulhamid Bello, Shaikh Saleh Lazare, Shaikh Abbare Gombe, Shaikh Muhammad Sani Zuru da sauran su.

An dai soma gudanar da bukin ne misalin karfe 9:30 na safe, inda bayan addu'a da karatun Kur'ani, sai aka gabatar da Harisawa, inda suka gabatar da kayataccen faretin girmamawa ga Shahid Kasim Umar.

Daga bisani kuma aka gabatar da Shaikh Sidi Munir Sakkwato, inda bayan jawabin maraba, ya shiga bayanai a kan rayuwar Shahid Kasim da zamantakewar da suka yi da shi ta tsawon shekaru.

Malamin ya ce, azzalumai sun kashe Shaikh Kasimu ne da tunanin ganin sun dakile fafutukar da ake ta kira ga gwamnati da ta saki Shaikh Zakzaky.

Da yake bayanin halin da ’yan'uwa suke ciki bayan shahadarsa da kuma gibin da aka samu na rashin sa, ’yan'uwa a wurin sun rinka fashewa da kuka har ya janyo Shaikh Sidi kuka ya rinjaye shi, ya kasa ci gaba da bayani.

Tun farko sai da Shaikh Sidi ya mika sakon jaje da ta'aziyya ga Jagoran Harkar Musulunci Shaikh zakzaky kan shahadar Shaikh Kasim Umar da ’yan'uwansa na jini da kuma ’yan'uwa baki daya.

A wurin, an gabatar da wasu ’yan'uwa wadanda suka yi dawainiya bayan an harbi Shahid. Dan'uwa Malami Alkanci na daga cikin wadanda suka maganta a wurin, inda ya ce, duk da harbin da aka yi wa Shahid babu wata damuwa a tare da shi. Ya ce ya yi mammaki har a kan gadon jinya Shahid yana kyauta. Ka zo duba lafiyarsa, amma kuma ya yi ma kyauta.

Haka ma a yayin bukin, an gabatar da dan'uwa Injiniya Abdullahi Musa Gwagwalada ya yi bayani a kan irin rawar da Shaikh Kasimu ya taka wajen tsayuwar ‘program’ din ‘Abuja struggle’.

Injiniya Abdullahi Musa ya ce, “ni na shedi Shahid Kasim Umar gwarzo ne mabiyin Shaikh Zakzaky na hakika. Ina iya tuna wani zancensa da yake cewa da ni, wallahi wannan ‘program’ na ‘Abuja struggle’ ba zai tsayu ba har sai ’yan'uwa sun ba da rayukansu.

Haka ma Injiniya Abdullahi ya yi amfani da damar ya bayyana wasu makirce-makirce da jahiliyya take shirin yi a kan Harka Islamiyya. Ya ce, lallai ’yan'uwa su farka, “ba za mu rungume hannuwa ba, Jagoranmu yana cikin wani hali. Za mu ci gaba da abin da muke na fafutukar nema wa Jagora ’yanci.

A nasa jawabin, Farfesa Dahiru Yahya ya ce, “na zo ne nan domin in sake mika sakon jaje da ta'aziyya gare ku kan wannan babban rashin na Shahid Kasim Umar Sakkwato. Ya ce, abin da ya faru ga ’yan'uwa a Tattakin Arba'in a Abuja, duniya ta yi tir da lamarin, musamman Uwar Shaidanu Amurka da sauran kasashen duniya.”

Har ila yau gabatar da babban dan Shahid Kasimu, Muhammadu Kasimu Gwarzo ya yi magana kan kyakkyawar alaka da kuma kulawar da Shahid yake masu. Ya ce, Shahid ba ya mu'amala da su a matsayin ’ya'yansa kawai, yana mu'amala da su a matsayin abokanensa na gwagwarmaya.

Sannan ya ce, kashe Mahaifinsu da azzalumai suka yi, sun yi a banza, don tamkar sun kara masu kaimi ne wajen neman shahada.

Shi ma Yayan Shahid Kasim, Alh. Bature Umar ya yi magana kan dangantakar su da Shahid. Ya ce, duk a gidan su, Shahid ya fi kowa kyakkyawar dabi'a. Kuma ni ta hannunsa ne na fahimci wannan Harka Islamiyya. Gab da zai yi shahada ya yi min wasiyya cewa, in rike al'amarin Harka Islamiyya, kuma kada in ji wata damuwa kan abin da ya same shi.

Ya ce, ko ba harbe shi ba, tunda lokacinsa ya yi, zai tafi. “Ya yi mana fatan mu samu rabon shahada a gaba.”

Shaikh Abdulhamid Bello da Shaikh Saleh Lazare, dukkan su sun gabatar da jawabai a wurin kan rayuwar Shahid Kasimu Umar Sakkwato. Sun bayyana shi a matsayin mutum Salihi mai karimci, wanda kuma yake da yakini a kan al'amarin Shaikh Zakzaky.

Har ila yau Shehunnan sun bayyana shahadarsa a yanzu da cewa babban gibi ne a Harka Islamiyya, don haka sun hori ’yan'uwa, musamman na Sakkwato da su tsayu kan abin da ya bar su a kai. Haka nan sun yi fatan Allah ya karbi shahadarsa.

Bayan an kammala taron, sai aka shiga sahu, inda aka taka daga muhallin taron zuwa makwancin Shahid, a yayin da ake tafiya, bayan faretin girmammawa da ake yi, an kuma daga hotunan Shahid Kasim, abin da ya kara janyo hankali jama'a, tare da yin Allah wadai a kan jami'an tsaro. Haka ma an raba takarda (Release) mai bayani kan kisan da jahiliyya ta yi wa Shahid din bisa zalunci.

Bayan an isa makwancin Shahid Kasimu, Shaikh Sidi Manir ya yi jawabin rufewa. Daga nan kuma aka ba da damar shiga a yi ziyara.